Showing 33001 words to 36000 words out of 189325 words

Chapter 12 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

243

yi ba don ta yarda ba, ta sani Humaira akwai juriya da nuna jarumta, sai dai kuma itama ai ?ar adam ce, tana da zuciya ta kuma san meke ma ta zafi. KafaWarta ta dafa.

"Na sani su Anna ba su ..."

"Raihana mu bar zancen, ya wuce wallahi. Ai komai mai ?arewa ne. Lokaci ne." Cewar Humaira da sauri tana katse Raihana don a duniya yanzun idan da abin da ta tsana bai wuce a ambaci sunan Anna ba. Ta tsani mutum da ba ya ganin kowa da gashi. Tsohuwar sam ba ta ri?e girmanta.

"Kinga kuwa mutuminki koda wasa bai ?ara gangancin kirana ba?"

Maganar Raihana ya katse tunaninta. Cikin rashin fahimta ta ce.

"Wa fa?" Ta yi tambayar don har ga Allah ta mance, sai kuma bayan ta yi ta tuno da Musaddam din. Ta Wan Waga gira.

"Au, Wan iska za ki cemin."

Suka Wan yi dariya. A haka su Tasleem suka shigo Wakin suka iske su.? Zuwa yanzu Raihana ba ?aramin haushi take ba su ba don haka daga kallo daya ba su kara bi ta kansu ba. Tasleem ta nufi sif din kayanta ta buWe? ta sa hannu a ?ugu tana kallo.

"Oh God! Ni wane kaya ma zan saka? Wallahi gaba daya na diririce."

Futuha da ta faWa saman gadonta ta yi dariya.

"Atoh, sai ki ?ure a daka ko ba komai dai wannan ne first meeting Winku."

Raihana na jin haka ta mike da sauri ta karasa ga Futuha.

"Wai Hamza D ne zai zo?"

Harararta suka yi a tare, Tasleem ta ja tsaki.

"Ina ruwanki? Ai ke yanzu munafuka kika zama. Ba a sirri da ke."

Humaira ta yi tsam ta mike ta fice a dakin ba ta ko kalle su ba. Cin fuska ne ta san za a yi mata.

***
Rayuwar ta ci gaba da gudana, Humaira tun tana ganin ire-iren bautar da Jannat ke sanya su na ?are ne abin dai ya ci tura. Daidai da wankin pant da rigar mama su take ba, Mami ke tsawatarwa a wasu lokutan shiyasa kawai su ke hakuri. Idan kuwa ta kai Humaira abin ya ishe ta rantsuwa take yi da ?ari cewar ita ba za ta wanke ba, sai Ummita ke tausarta ta karSa ta wanke gudun samun matsala.

A wannan gaSar kuma ba irin takurawar da Fadeel ba ya yiwa Humaira, iyakar ?ularwa ya yi mata, ta yi bakaken maganganun amma ko gezau, kusan kullum sai ya aiko mata da sa?onninsa da ke yiwa Raihana dadi. Ita ke karSa ta yi ta karantawa har a wasu lokutan ta yi yunkurin ba shi amsa, Humaira ta nuna ba ta so.

Jannat ba ta bar gidan ba sai da ta yi wata Waya cif. A sannan tuni Mubarak ya tattara ya koma, shima daf yake da kammala Masters. Yayinda? Yassar da?Dawud suka soma jarrabawar ?arshe na kammala degree dinsu a jami'a. Su Ummita ma tuni an koma karatu, Humaira kam ta yi nisa a fannin girke-girke don yanzu girki WaiWaiku ne ba ta iya ba, kama daga cimar fulawa har dai sarrafa shinkafa da sauran kayayyakin abinci. Girkin gidan zuwa lokacin ya koma kan ta rankatakaf don kowa burinsa ta girka ya ci. Ita kam ko a jikinta, za ta yi girkin ba son jiki amma fa ba ta yarda da wulakancin su Yassar da Tasleem masu cewa su na son cin wani abu daban.?

Yassar su na dab da kammala jarrabawarsu ne suka tada hankalin Mami lallai sai ta tambayar musu Abba kuWin da za su haWa party da abokan karatunsu sai dai duk inda? suka Sullo Mamin ta ?i asalima cewa ta yi su tuntuSi Abban da kansu.

Yassar ya mike tsaye yana huci.

"Shikenan, idan Abban ya zo zamu yi mishi maganar. Mu dai gaskiya wannan karon ya sakar mana mu fita kunyar abokai. Wannan rayuwa har ina."

"Ni ban san irin Abba ba wallahi, Mami ke ma ba kya mishi magana, tun farko ai Anna ta fadi, ke kika ba da damar ba ya hidimta mana sosai. Nifa Allah kuwa har kunyar nace Babana mai kudi ne nake, saboda ba a gani a jikina."

Dawud ya fadi yana daga tsaye dafe da kujera. Mami ta yi mishi da?uwa.

"KarSi nan Dawud, shi uban naku sa'anku ne da ku ka tsaya ku na wannan Sarin zancen a kansa? Kuna maganar kamar yau idan kun je gabanshi za ku iya maimaitawa? Kunsan Allah ku kiyaye ni, gaba daya zan tattaraku na kai kararku wajensa tun da dai shi kuna shakkarsa."

Suka ?ara tunzura, Humaira na gefe tana gogewa Mami mayafi bayan ta kammala goge nata kayan dalilin wutar nepa da aka kawo, biki ne Mamin za su je har da ita na Wiyar mijin Anti Laila malamar girkinta. Katin gayyatar har ita aka ba da ta kuma tabbata saboda mutuncin da suke yi da Shema'un ne, sannan Anti Lailar ma ba ta da matsala ko kaWan.? Gaba Waya hirarsu babu wanda ba ya shiga kunnuwanta, tana mamakin irin wannan rashin tarbiyya na su Yassar da ba sa tauna zance kafin su furzar kan kowa ma. Haka suka yi ta mita a karshe dai kiran sallar la'asar ya sanya su tattarawa su bar falon.

"Allah ya shiryamin ku."

Humaira jin furucin da Mami tayi kafin ta wuce dakinta yasa ta amsa da amin, zuciyarta sai ta cika da tausayin Mamin. Matar dai na iyakar kokarinta a kansu. Ba zato ta ji an watso mata kaya saman kafafunta da ke mi?e a harWe. Ta Waga kai ta dubi mai wannan aiki. Futuha ce tsaye daga ita sai vest da leggings. Gashinta a barbaje a gadon bayanta take duban Humairar fuska a yamutse.

"?an dannemin kayan nan kafin su dauke wuta." Kallonta ba ta kara yi ba ta hadiye zafin da ta ji na wannan kalar rashin mutuncin na Futuha. Itama daga haka ta juya zuwa daki, ?wafa ta yi ta kuma rantse ba za ta yi ba. Hakan yasa tana kammala na Mamin, ta hada da nata kayan da ta goge ta mi?e bayan ta Wauke dutsen gugar a wajen gudun kar su Waleed su taSa.
?? Dakin Mamin ta soma shiga, sallah ta iske ta tana yi don haka ta ajiye mata a saman gadon kusa da wani haWaWWen leshinta peach colour da ya sha adon duwatsu, ya hau sosai da mayafin. Humaira har sai da ta murmusa don tuni ta hango Mamin a ciki, karshen kyau ko ba a faWa ba ta sani kalar da kuma kayan za su karSe ta. Abar ka da farar mace.

Koda ta shiga Wakinsu Tasleem na tsaye tana fente fuskarta da hoda. Ita kuwa Raihana tuni ta shirya tsaf cikin wata maroon atamfa mai haske an yi adon yellow colour jikinta sai dai bai yi dau ba. Tana tsaye ta karkace sai hotuna ta ke yi a gaban window. Futuha da alama tana bandaki. Suka dubi juna da Raihana, da wani irin zumudi ta karkace hadi da Wan Waga gira.

"Ya? Na yi kyau?"

Humaira ta yi mata murmushinnan nata mai fiddo da zahirin kyawunta.

"Kin fito tsab. Masha Allah."

Raihana ta yi dariya, ita kuwa Tasleem dogon tsaki ta ja. Ba wanda ya ce mata ci kanki a cikinsu. Kasancewar ta yi wanka kafin zaman guga kuma ba ta da sallah hakan yasa ta kawai ta shiga sauya kaya. Itama atamfar ce amma nata dark brown ce mai haWe da milk colour. Tana cikin shafa hoda Futuha ta fito daga wanka tana baza ?amshin sabon showergel da suka ci arzikinsa a zuwan Antinsu Jannat gidan. Kallon Humaira ta yi kafin ta kalli gadonta ta gani wai ko ta ajiye mata kayan amma wayam. Don haka a fusace ta dube ta.

"Ina kayan da na ba ki guga?"

Humaira ta kalle ta da irin kallon wulakancin da suka saba yi mata itama.

"Ai gugan Mami kika iske ina yi ko?"

"Shekara kika yi kina gogewa Mamin mayafi? Don tsabar is..."

Ba ta kai ga ?arashewa ba Wif aka Wauke wutar, aikuwa Raihana ta tuntsire da dariya itama Humaira sai da murmusa a ranta tana fadin Allah ya ?ara.

Nan fa Futuha ta hau zuba fada wai Humaira na sane iskanci ne ta fara sabo, tunda har ba a isa a sanya ta aiki ta yi ba. Ta tattara ta ba banza ajiyarta duk da cewa ranta wani irin tafarfasa ya ke yi na irin zagin da Futuha ke yi mata. Korar yunwa dai ya ?i fita a bakinsu, ta kasa jurewa ta juyo, kamar ta maida martani da cewa su dinma asalin uwar Maminsu Nijar din ne, daga can suka fito can kauyen Agadas sai dai ta haWiye tuna albarkacin Mami. Ummita ta shigo dakin, ita tuni dama ta shirya cikin atamfarta mai kyau ruwan sararin samaniya. Fitar da ta yi aiken Mamin ne zuwa siyan kati.

"Mami ta ce ku yi sauri."

Wannan ne ya katse zancen, kayan da Futuha ba ta sanya ba kenan sai kuwa wani ta sauya. Ba wata kwalliyar hayaniya Humairar ta yi ba amma iyakar kyau ta fito tsaf. Ba su suka yi haramar tafiya ba sai biyar da kusan rabi.

Koda suka fito baki daya, Ladidi kawai aka bari tana musu a dawo lafiya sai kuwa su Muhsin dake can Sangaren Anna, Ummita ta dube ta da murmushi.

"Kin yi kyau sosai."

Ta ri?e haSa.

"Idan babu wadannan buzayen a kusa ko?"

Suka yi dariya. Anan farfajiyar gidan suka sha hotuna a wayar Raihana dake faman jan su, su Tasleem na gefe su na kallonsu ita da Futuha, ko me suke tattaunawa?

Mami na fitowa suka shiga mota, kai tsaye ?awataccen hall Win Marhaba suka nufa inda anan ne taron bikin.

"Ba ku mance katinanku ba dai ko? Ba na so a je wurin taro mutum ya yi tsaye kamar wanda ya zo gayyar soWi."

Tasleem ta haWiye dariyar muguntar da ya so kwace mata har sai da Futuha ta Wan zungureta akan ta nutsu. Katin Humaira tun fitarta kiran Mami, ta Wauke shi ta raba gida biyu ta wurga shi bayan gadonta.

Ummita da Raihana suka amsawa Mamin bayan sun duba sun ga katinansu, ita kuwa Humaira ko jakar ba ta buWe ba tunda dai ta riga ta sani duk wani abun bu?atarta ta jefa a ciki.

"Humaira, Tasleem da Futuha fa?"

Suka amsa da eh su ma yana nan.

Su na isa bakin ?ofar kowaccensu ta fito, motoci ne na alfarma fake a wurin. Yanmata har ma da manyan mata ?an gayu kawai kake gani a wurin, kasancewar Angon Shema'u Wa ne ga kwamishinan ?an sanda hakan yasa motar ?an sandan har biyu a wurin su na lura da shige da fice.

Mami ce ta soma gaba suna gaisawa da wata ?ar uwar aminiyarta ta mi?a kati ta shige. Hakan ba karamin dadi ya yiwa Tasleem da Futuha ba sanin muguntar da suka shiryawa Humaira. Suka shige abinsu zuciyarsu fari kal bayan sun mi?a katinansu, Raihana ma tuni ta yi gaba. Ummita kuwa ganin yanda Humaira ta rikice da bincike jaka ya sa ta tsayawa gami da ja baya ta ba wasu hanya.

"Lafiya? Ya kika tsaya?"

Humaira ta ja guntun tsaki.

"Wallahi ban ga katina ba. Kinga ba ya cikin jakar."

Ta dafe kirji.

"Ba dai a gida kika bar shi ba?"

Ta girgiza kai cike da takaici, ta kasa cewa uffan ma. Ganin su na tsaye kawai ya sanya ta duban Ummita.

"Shiga ciki kawai, ni sai na koma gida."

Girgiza kai Ummita ta yi.

"Aa wallahi, sai dai ni na koma. Keda Shema'u da kanta ta dam?a maki kati?"

Nan fa suka yi ta ja in ja a ?arshe dai Humaira ta ce.

"Toh naji, shiga ciki sai ki sanarwa Mami mu ji me za ta ce. Allah kuwa ba inda zan je ina nan zan jiraki."

Ummita duk sai ta ji ba dadi, sosai Humaira a daren jiya ta ci burin bikin ba don komai ba sai cewa da ta yi tana so ta ga ya ake gudanar da biki a ?asarnan. Ba ta taSa halarta ba. Ganin ta tsaya yasa Humaira dafa kafaWarta.

"Rantsuwa fa nayi, kinsan ina nan din babu inda zan je."

Jin haka yasa ta gyada kai ta juya ta shige ciki ita kuwa ta ja baya ta koma can gefen titi jikin wata ba?ar mota me tinted ta tsaya.
FADEEL
Fitowarsu kenan daga Bristol Palace dake kam titin farmcenter, Ibb ke jan motar yayinda shi kuwa ya kwantar da kai jikin kujera idanunsa lumshe. Babu abin da ya kai su face gaishe da abokin baban Ibb da ya zo daga Kaduna zai tashi zuwa Egypt sakamakon rashin lafiya.

"Hall dinnan ba ya rabo da biki."

Jin haka ya sa a hankali Fadeel ya buWe idanunsa. Cikin iko da hukuncin Ubangiji, dubannasa ya sauka kan Humaira dake tsaye ta harWe hannuwa a kirji fuskar nan a Waure kamar koyaushe.

"Wait please."

Yanda ya yi maganar da sauri ya sa Ibb shima soma tafiya a hankali gami da neman wurin parking. Sai da ya daidaita motar a gefe kafin ya dube shi da alamar tambaya.

"Lafiya?"

Fadeel ya soma kokarin cire seat belt.

"Ita ce. Ba na so na ?ara rasa damar da za ta kubcemin."

Ganin yana kokarin bude ?ofar yasa Ibb saurin dafe hannunsa. Fadeel ya dube shi.

"What? Kana nufin kar na je?"

Girgiza kai Ibb ya yi.

"No, ba haka nake nufi ba. Sai dai ina so ka ba ni damar muje tare, idan kuma da hali kar ka ce komai. Ma'ana kada ka yi mata zancen soyayya da ma sauransu. Ni zan san ta yadda zan Sullo mata, ok?"

Fadeel ya sauke ajiyar zuciya yana hangenta ta jikin side mirrow. Ba tare da ya dauke idanunsa ba ya amsa.

"Ok."

Daga haka Ibb ya kashe motar, suka fito kusan lokaci guda. Gaba Wayansu ?ananun kaya ne jikinsu. Fadeel ba?ar tshirt ne a jikinsa mai ?aramin hannu sai blue jeans.? A tsintsiyar hannunsa kuwa, agogo ne Waure na fata ba?i, sumar kansa ba?a wuluk sai she?i take yi. Ya fiddo gilashinsa ba?i a aljihu ya rufe ?wayoyin idanunsa, a yanda ya karanci Humaira a farkon haWuwarsu hatta da kallo ta tsana. Ba ya jin kuma abu ne da zai iya jure bari ne, wato kallonta, musamman ma da ya kasance sun fi watanni biyu ba su sake haWuwa ba.

A Sangaren Ibb kuwa, blue tshirt ya sa da ba?in wandon jeans. Kallo Waya idan ka yi musu sai ka kara. Fadeel fari ne tas kuma dogo, har ya so ya fi Ibb tsawo. Shi kuwa yana da Wan duhun fuska balle idan ya jera da Fadeel, kai tsaye za a kirashi ba?i.

Tana nan tsaye ba ta motsa ba har suka ?arasa wajenta. Wani irin bugu kirjin Fadeel ke yi, kallonta yake tun daga sama har ?asa, ba ya jin ta haura shekaru sha takwas, idan ma ta cika hakan kenan, amma ?irarta ko a yanzun abin a kalla ne ina kuma ga nan gaba? Ya ja numfashi daidai sadda suka ci burki a gabanta. Sallama Ibb ya yi gareta, ta bar duban wayar da take yi a kokarinta na kiran Mami ta ce mata ita kam gida za ta koma. Zaratan samarin suka sanya wani irin kwarjini ya mamayeta da har ta kasa tantance su Win ko su wane ne, ta mance ma a inda ta san su. Da?yar ta amsa sakamakon nauyi da harshenta ya yi, daga haka kuma ta? dauke kai ta raba jikinta da motar da nufin barin wajen.

? ? "Kamar ba ki gane ni ba ko?"

Cike da ?osawar ta tafi ta dube shi. Kallo na ?urilla don ta fahimci ko dagaske yake ta san shi Win, duk da cewa ba wannan ne karon farko da samari suke mata irin rainin hankalin nan ba idan sun ga ba ta kula su ba, amma hakanan a ranta ta ji wannan dai ya yi kama da kamilallan mutum, ba ta jin zai yi mata ?arya. Bayan gama kallonsa ta maida kwayar idanunta kan Fadeel, ba ta ci nasarar ganin halittar kwayoyin idanunsa ba, shi kuwa wani yarr ya ji tun daga tafin ?afarsa har tsakar kansa. Dakyar ya iya jarumtar juya fuskarsa gefe kafin ita Win ta kai ga Wauke nata kwayar idanun a kansa. Ta tsuke baki ta ce.

"Ban gane ku ba."

Ibb ya yi mata bayani a ta?aice, nan da nan kuma ta Wan sakar mishi fuska. Ko babu komai ta ji dadin mutunta da ya yi a wancan ranar wanda tun daga shi, Musaddam bai ?ara gigin shiga hurumin Raihana ba. Ba ta da masaniyar ko Fadeel mai yawan kiranta shi ne tsaye a nan ko kuwa dai wani abokin na Ibb ne daban kusa da ita hakan yasa ta gaishe su a jam'u. Suka amsa, Fadeel kam lebbansa ne suka motsa amma tuni ya yi nisa a kallonta, bai san lokacin da ya ?ara mayar da hankalinsa kacokam kan kyakkyawar fuskarta ba.

'Wallahi ina sonta.' Ya yi furucin a can ?asan ransa kafin ya sa ha?ori ya cije lebbansa ya sauke numfashi nannauya.

A cikin Wakin taron kuwa, Tasleem da Futuha suka hana Ummita zuwa ga Mami, karshe suka ce ta zauna su za su je su shigo da Humairar wurin taron. Suka fito suka kara amsar katinsu suna dariyar mugunta, kawai burinsu su ga fuskar Humaira a karshe su ce Mami ta ce ta wuce gida ba za ta sanya ta ro?on kati a nan ba. Haka suka fito su na ta rarraba idanu, Futuha idanunta ya kai kan Ibb dake tsaye yana zuba wannan murmushin nasa mai tsada, a gefensa kuwa wani haWaWWen matashi ne da ya zarce shi a haWuwar. Ta dan murza idanu tana kara dubawa, tabbas Ibb ne.

"Ke, zo ki raka ni. Wayyo zuciyata, me Ibb ke yi a wajen bikin nan? Ko abokin Ango ne?"

Tasleem ta juyo, tuni Futuha ta soma tafiya ganin haka kawai ta mara mata biya.

Shi kuwa Ibb babu abin da ya sanya shi murmushi illa gani da ya yi Humaira ta Wan saki jiki da shi tana sanar mishi cewa ai kam daga ranar Musaddam bai ?ara shiga rayuwar ?ar uwarta ba.

"Alhamdulillah. Hakan na da kyau. Sai ki ci gaba da yi mata nasiha. Allah ya ?ara nesanta ta da ire-irensu."

Murmushi Humaira ta yi lokacin da ta ke amsawa da amin. Kallon Fadeel ba ta ?ara ba balle ta fahimci hankalinsa kacokam a kanta yake. Har za ta tafi sai kuma ta kara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login