Showing 45001 words to 48000 words out of 189325 words

Chapter 16 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

252

da faWan da ta saba. Sai kawai ta zame wayar daga kunnenta ta katse kiran. Daidai lokacin da aka ba su hannu, juyawar da za ta yi suka yi ido hudu da shi, kallonta ya ke bilhakki har sai da na bayansa suka cikamasa kunne da hon, ta yi saurin kauda kanta. Kallon ya dawo mata da sabuwar tsanarsa, ta ji ranta ya Saci, ta kuma rasa dalili. Ba ta kara juyawa ba har suka yi mishi nisa, ba ta kuma san inda shi ya yi ba. ?arar shigowar sa?o wayarta ya sanya ta buWewa.

_"Kin min kyau. Ina ro?on Allah ya nunamin ranar da Fadeel zai mulki zuciyarki gaba Waya. Ya zame maki haske maganin kowane duhu. Ameen."_

Ta yi saurin maimaitawa sau Waya ta jefa cikin jakarta. Ana zuwa kasuwar rimi ta sauka bayan ta fidda facemask dinta a jaka ta rufe hanci da baki. Haka ta dinga kutsawa ta kammala siyayyar Mami, ba ita ta bar kasuwarnan ba sai yamma lis duk ta jiga ta. Washegari ma haka ta kara tashi ta fita zuwa haWo kayan kwalam na yin Snacks iri-iri. Hatta da kayayyakin haWin salad sai da ta siyo. Wannan karon dai Abba ya saki bakin aljihu domin shi dai idan har watan azumi ne yakan yi bakin kokarinsa wajen wadata gidansa, hakanan da sallah. Ya kuma ce lallai lallai su Tasleem da Futuha su dinga shiga kicin su koyi girki wajen Humaira. Rana Waya idan suka yi fashi, za su yi karo da fushinsa.

***
Murja ce durkushe gaban Alhaji, ya kalleta dakyau jin ta kasa magana. Da murmushi dauke a saman fuskarsa ya ce.
"Kin yi shiru Murjanatu, kiyi magana."

Ta ga dai shirunta zai sa ta cuci kanta don haka ta muskuta ta soma cewa.
"Dama Yaya Fadeel nake so a auramin."
Jin haka kan Alhaji ya Waure, ya yi sakato yana kallonta.
"Shi Fadeel din ya sani?"
Ta girgiza kai tana kara sunne wa kamar mai jin kunya.
Alhaji ya yi shiru sai kuma ya ce.
"Shikenan, ni dai ba na yiwa yarana dole balle kuma namiji. Zamu yi maganar da Fadeel duk amsar da ya bayar za ki ji daga Antinki."
Ji ta yi kamar Alhajin ya harba mata mashi a ?ahon zuciya, da irin wannan amsar ai gwara kawai ya ce mata aa kansa tsaye. Abu ne da ya sani kamar yanda ta sani, zai wahala Fadeel ya amince da shi, ta yi zaton yanda Alhajin ke yabawa da nutsuwarta zai ce ya amince ya zaSawa Fadeel din ita matsayin matarsa. Haka ta mike ta fice gwuiwa a sake. Bayan fitarta Alhaji ya yi shiru, ta ina zai soma Sata ran Wannasa wanda a baya ya sha ba?ar wuya a dalilinsa da mahaifiyar Fu'ad? Ya musguna mishi, bai duba maraicinsa ba na rashin uwa ya yi watsi da shi. Karshe don kansa da ya gaji bayan ya yi hankali ya fice ya koma dangin mahaifiyarsa a can ?asar Kamaru. Sai kuma bayan da ya kwashe dogon shekaru har kusan biyar ya dawo yanzun kuma ya hargitsa shi komai ya ?ara hargitse mai? Yaransa biyar kacal a duniya, Fadeel ne babba sai Fu'ad sai kuwa ?anwar Fadeel uwa Waya uba Waya Hannatu dake aure a can Adamawa, sai yaran Anti Amarya biyu, Khadija da Abdulmaleek. Shi hakanan Allah ya yi shi ba mai yawan haihuwa ba, matansa babu me yin tsarin iyali.
? A ?arshe dai ya yanke zai mishi maganar auren don shi kansa yana damuwa kwarai akan zaman yaran haka(wato Ibb da Fadeel) ba tare da iyali ba. Har ga ?aninsu Fu'ad ya yi auren ya bar su.

***
? Fadeel ya nutsu a gaban mahaifinsa, bai katse shi ba har ya kai aya. Sai a lokacin ya yi magana.

? "Na ji bayananka Alhaji, ina neman addu'arka musamman a wannan wata mai alfarma da za mu shiga akan neman zaSin Allah. Sai dai kuma ba na kaunar Murja, ba na sonta matsayin matar aure. Don Allah abar zancenta."

Jinjina kai Alhaji ya yi, ya Wan murmusa kaWan.

"Shikenan, Allah ya sa hakan ya fi alheri. In sha Allahu zan tayaku kai da Wan uwanka. Ya kamata ku maida hankali."

Fadeel ya amsa a ladabce. Daga nan suka rufe wannan babin suka cigaba da tattaunawa akan abubuwan alheri na sadaka da neman lada da Alhaji ke yi duk shekara idan watan azumi ya kama. Kamar yin kunu da abincin sadaka, kyautar butoci, ruwa, dabino da ma sauransu a masallatai., daukar nauyin tafsir, sai kuwa idan sallah ta matso ya yiwa ?an uwansa marasa ?arfi da marayu da dama sutura. Da wannan suka rufe babin Murja da ma batun aure. Anti Amarya dake laSe a bayan labulen Wakin Alhaji, ta ji ciwon cewa da Fadeel ya yi ba ya son ?anwarta. Ta yi ?wafa, ai idan ya san wata bai san wata ba.

***
A daren ranar Lahadi gaba Waya garin aka dau murnar ganin watan Ramadan. Lokacin Sahur gaba Waya gidan suka tashi aka yi idan ka cire Tasleem wacce ba ta da sallah.
? Lokacin shan ruwa na kawo kai, Humaira da Ummita har Raihana ana kicin ana faman kai da kawowa, Tasleem ba ta shiga ba don langaSewa ta yi wai mararta na ciwo. Ita kuwa Futuha tana tsaye kawai tana yatsine-yatsine da gwatsale wani abun idan Humaira ta yi wai ba haka ake yi ba. Ita dai ba ta tanka mata ba albarkacin watan da suke ciki na ibada. Sai da suka kammala komai sannan suka jera a tsakar falon bayan shimfiWa ?atuwar ledar cin abinci. Na Abba kuwa can Sangarensa suka kai aka shirya komai. Itama Anna, Raihana ta kai mata komai ta bar ta tare da su Muhsin don a duniya Anna ba ta fiye son zuwa falon Mamin ba sai da kwakkwarar dalili.

? Sai a sannan Tasleem ta shiga kicin din ta Wibi abinci ta dawo falon tana ci ta a yatsine fuska wai gishiri ya yi yawa. Ba ta ko jin nauyin yan uwanta maza dake zaune a falon su na taSa hira. Haka aka sha ruwa aka yi zaman cin abinci bayan kowa ya yi sallah. Mazan suka dinga santin girkin amma da zarar sun yi ido da Humaira su watsa mata harara idan ka cire ?asim wanda tun wata rana da ya shiga Wakin Mami zai Wau kuWi ta gan shi kuma ta rufamasa asiri ba ta faWawa kowa ba, tun a ranar ya soma ganin ta da ?ima a idanunsa. Ya ke kuma jin kunyarta. Yassar kuwa faWi yake ai ba basirarta ba ce, koyamata aka yi. Futuha? ta ja tsaki.
? "Wai kai kana wani zance, ina abin yake? Ni ba abin da ya kara Satan rai wai sai da Abba ya ce wani mu shiga kicin mu koyi girki wajenta. Don Allah ku ji wani abu."

Dariya suka yi idan ka cire ?asim dake faman cin sandwich da ya ji kaza da su cheese yana santi.

"So ya ke ki je ki yiwa Alhaji Yakubu kar a ji kunya mana."

Jin an ambaci Alhaji Yakubu nan da nan ta Waure fuska. A duniya yanzu babu wanda ta tsana irinsa, mutum dai kamar maye. Abu daya da ta sani shi ne, daga maganar zuwa kamawar watan da suke ciki na azumi ya yi mata Sarin kuWi sama da dubu Wari, wannan kaWai shi ne ya burgeta musamman ganin cewa Tasleem ba? ta samu hakan ba. Rabu dai da Hamza akwai kulawa a baki amma babu ko asi da ya taSa kawomata. Wannan abu na yiwa Tasleem ciwo kuma yana fasawa Futuha kai, tana son ta ga ba ta son mutum yana bibiyarta kamar jela.

"Kar ka sa na tashi, har wani tsami na ji abincin ya soma yimin a baki."

Yassar da Dawud suka kwashe da dariya. Tasleem ta yamutse fuska ta ce.

"Gulma, a bakya so kike kwace ?an chanjinsa. Fuska biyu."

Futuha ta dire fork din hannunta da ta ke cin haWin salad da shi, tun ba ta kai ga haWiyar wanda ta ke tauna ba ta soma balbaleta da masifa.

"An kwata Win, ina ce albarkacin kaza dai ?adangare ke shan ruwan kasko? Ko kin manta abin da Mami ta ce akan amfanin kudin?"

Tasleem ta hadiye zancenta, ta tuna Mamin cewa ta yi Futuhar ta saki jiki da Alhajin ta dinga nuna masa kulawar koda iyaka baki ne, muddin dai zai bayar da kuWin ba za a ji kunya a auren ba tunda ba su da tabbacin samun yanda ake so daga wajen Abba. Wato na siyayyar kayan Waki da sauransu. Maganar Futuha ta katse ta.

"Kuma ko banza gwara Yakubu tun daga nan an san zai iya ri?e mata biyu, wani kuwa da ko Wayar ma ya kasa nunawa zai iya sai afkin waya da ?al?alar? turanci kamar tsatson sarauniyar Ingila." Suka kwashe da dariya. Ran Tasleem ta kai kololuwa a Saci, su Humaira na zaune su dai su na shan ruwa abin su daga gefe suna kallon ikon Allah. Raihana ce ta tofa.

"Kai Adda Futuha, ramuwar gayya fa akwai zafi kar ki kai Adda Tasleem bango."

Aikuwa tana cewa haka kamar ta kara zuga Tasleem sai kuwa ta yi caraf ta ba ta amsa.

"Kyale ta Raihana, ai mugun abu ya ?are a gindinta tunda ko ba komai nidai auren soyayya zan yi, Hamza gani ya yi yana so a mutunce. Wata kuwa sai bayan an jefe ta da kalmar karuwanci, ?ar rawar Tiktok sannan ta yi na'am da Alhaji mai zubin moWa."

Lallai, baki idan ya san me zai faWi bai san me za a mayar masa ba. Aikuwa Futuha ta yi kukan kura har ta na cilli da bowl din salad dake saman cinyarta zuwa ?asa, ta yi kan Tasleem da kokawa. Itama Tasleem kasancewar a wuya ta ke kawai sai ta biye mata suka hau jibgar juna. Dakyar Yassar ya shiga tsakaninsu gudun kar Abba ya ji.

Tasleem na? huci ta ce.

"Ni kuWi bai dameni ba tunda zan auri wanda yake sona nake sonsa. Arzikin dai ai na Allah ne, kuma ko makaho ya shafa ya san Hamza ba talaka ba ne. Alhamdulillah ba a taSa yimin wannan mugun ?azafin na karuwanci? ba."

"Shegiya! Ni kike kira karuwa, ai gwara ni sharri ne, ke kuwa sau nawa kina yiwa Mami sata? Ko ranar da aka yi na Humaira, ina ce ke ce kika kawo shawarar a yi mata wannan sharrin don ki wanke kanki. Ke ce kika Wauki kuWaWen, ganin Yassar ya kama ki sai aka shiryawa Humaira tuggu don kar Mami ta zarge mu."

Humaira da ke shirin kai kofin kunu bakinta ta yi saurin ajiyewa, ashe ma Sarayin biyu ne? Ba ma wannan kadai ba sai ganin yau dai Allah ya karSi addu'arta gaskiya ta yi halinta. Tasleem gaba Waya ta yi wuri-wuri da idanu, ko kaWan ba ta zaci Futuhar za ta yi mata wannan tonon sililin ba. Yassar ya dakamusu tsawa amma kasancewar girma ya faWi ko a jikinsu, sai dai tsawar farko daga Abba ya sanya gaba daya suka yi tsit. Ashe yana tsaye a bakin ?ofar falon tun sadda suka soma kokawa, Mami na biye da shi a baya. Gaba Waya hankalinta a tashe, wato dai ya allura ta tono garma? Ba wannan ba ma, babu uwar da za ta so ganin yaranta kansu a rabe. Gaba daya falon ya yi tsit su Tasleem sai rarraba idanu ake.

Ya shigo tsakiyar falon ya wanke su ganin ba su duba girman watan da ake ciki ba na ibada su na yi mishi faWa a falo. Daga nan ya nemi sanin abin da ya faru da Humaira a baya, nan fa Raihana kamar wacce ake tsikara ta ba shi labari. Humaira kanta a ?asa tana hawayen farin ciki, wato da Allah ya tashi wanke ta sai ya sa Abba da kansa ya ji zancen ba iyaka Mami ba. A ranar su Yassar da Futuha sun ga tashin hankalin Abba, ya kuma ci alwashin saSawa duk wanda ya ?ara jarraba musgunawa Humaira. Hatta da Mami mai kokari akan Humaira a ranar har da ita ya haWa ya ce ai laifinta ne da ba ta tsawatar musu shiyasa suka samu sake. Haka Abba ya yi faWan da ba su zata ba har Humairar daga nan ya fice daga falon. Mami ta bi yaran da kallo sai kawai ta juya ta bi bayan mijinta. Humaira ta mike ta kalle su fuskarta dauke da murmushi ta juya zuwa Waki.? Ranar jin ta take ranta babu ko Wigon bakin ciki sai dai ba ta ji dadin dorawa Mami laifin su Yassar da Abba ya yi ba. Amma ta yi mamakin Abban, a baya tana tunanin ko sonta ne ya daina, ko ya manta ma da ita a lissafin ?an gidan sai kuma abin da ya yi yau Win ta fahimci tana nan daram a zuciyarsa kawai dai ba shi da lokacin kansa balle na hira saboda yanayin kasuwa.? BanWaki ta shige ta Wora alwala ta dawo ta zura hijabinta ta shiga lazimi. Ta na nan zaune ta yi shiru, wani lokaci can take tunowa ita da Dada musamman a wata irin na azumi yanda suke zama bayan shan ruwa a yi hira kafin lokacin sallar isha'i.
? ?arar wayarta ya katse mata tunani, ta sa hannu ta Wauka. Fadeel, shi ne? sunan da ya bayyana saman screen din, haka Raihana ta adana mata lambar ba da son rai ba. Albarkacin watan da suke ciki ya ci ta Waga da sallama. Ya amsa daga can ransa fari sol.
?? "Ina fatan kin sha ruwa lafiya?"

"Lafiya kalau." Ta amsa a ta?aice. Shiru ya Wan biyo baya, ya rasa me zai ce yana gudun ya yi furucin da zai sa ta katse wayar gaba Waya. Ya kasa hakuri balle ya danne don haka ya ce.

"Sai yaushe Humaira? Sai yaushe za ki samarwa wannan Wan marayan gurbi a zuciyarki? Ba zan gaji da ro?o ba, ki ba ni dama Humaira. Wai kin san so kuwa?"

Nan da nan ta ji ya har ta soma harzu?a a sanadin kalmar so da ya ambata, cike da gatse ta ce.

"Sai nan da shekara."

"Kin yi al?awari nan da shekarar za ki amince ki yarjemin da batun aure?"

Ta dauki maganar a zancen banza, ta sani babu wahalallen da zai yi dakon shekara ya auri budurwar da ba ta ko son zancen auren balle auren. Don haka babu dogon tunani ta amsa.

"Eh, na yi muddin za ka rabu da kirana ka bar takuramin."

Shiru na wasu lokutan sai kuma ya sauke nannauyan ajiyar zuciya.

"Za ki same ni da bin umarninki, amma kiyi hakuri koda sa?o na dinga aikomaki ta waya. Ke kuma ki daure ko da sallama ki amsamin domin na san kina sane da ni."

"Naji."
Ta amsa gabanta na faWuwa ba tare da ta san dalili ba, ta ji zufa ta keto mata. Tsanarsa ta ke ji yayinda a wani gefe can a ?asan ranta ta ke jin wani abu da ba ta tantance ba.

"Na bar ki lafiya, ki yi hakuri na adana dukkan wayoyinmu, abin nufi nayi recording tun daga farkon wayarmu har na yau. Hakan kan Webemin kewa wasu lokutan idan son jin muryarki ya ci ?arfin kwakwalwata. Ki dage da addu'a a wannan wata mai alfarma. Ina ro?on Allah ya yi maki zaSin abokin rayuwa nagari, koda ba Fadeel ba."

Yana kaiwa nan bai jira cewarta ba ya katse kiran. Ta yi ?uri tana duban wayar, hakan na nufin wayar ?arshe ce tsakaninsu sai nan da shekara? Ta taSe baki, ta sani cewa ta ba shi aiki mai wahala. Kuma ba zai ma iya shekara yana wahala a kanta ba. Watakila ma kafin sannan ya yi aurensa. Ta watsar da tunani ta yi jifa da wayar ta mike jin an soma kiraye-kirayen sallar isha'i.

***
Anna ce ke yiwa Mami faWa kamar ta ari baki.

"Kin bari miji ya rainaki ya raina uwarki, dama tun akan batun auren Futuha na san cewa Isuhu ya sauya daga yanda na san shi. Wato yanzun ya ci moriyar ganga ya yar da koren, ke yanzu ban da ke sakara ce wawiya, kina tunanin har wani karfin iko kike da shi a wajensa? Mutumin da ya dubi tsabar idon mahaifiyarki ya ce ba zai janye kudurinsa na aurar da Futuha ba? Toh wallahi Maryama ki shiga taitayinki tun kafin dare ya yi maki, mazan nan dai babu amana bar ganin wai girma ya soma kama shi, don ya dankaro maki kishiya ?ar zamani ba komai ba ne. Tun wuri ki ?watarwa yaranki ?anci a wajen mahaifinsu, ki murje idanunki dakyau ki daina bari yana wula?anta min jikokina akan wasu bare can. Ban da ma mutum mai shegen mantuwa, Isuhu ko kare ne ya fito daga gidan su Fatima zai kalla da daraja? Matar da ta nunawa duniya cewa ta tsane shi har kwanciya ciwo take akan sai ya sauwa?e mata ta koma garinsu? Mts, Allah ya wadaran naka ya lalace."

Har Anna ta kai aya ita dai Mami ba ta ce komai ba banda huci da take furzarwa, daga ita sai zuciyarta ta bar wa sanin abin da take tunani. Dakyar ta taushi zuciyar ta soma magana bayan sakin ajiyar zuciya mai nauyi.

"Anna ki yi hakuri, babu amfanin mayar da hannun agogo baya tunda mai afkuwa ya riga da ya afku. Na ba ki wu?a da nama akan ?watarwa jikokinki ?anci, ki yi abin da kika ga ya dace. Sai dai ki sani, ni Maryam ba da yawuna ba saboda daidai gwargwado yarannan su na kyautatamin, ba ni na haife su ba amma su na bi na sau da ?afa fiye da ma yaran da na haifa a cikina. Kiyi hakuri idan maganata ta maki zafi."

Anna ta wurga mata harara.

"Au haka kika ce ko? Toh shikenan, ni zan san abin yi a kai kamar yanda kika ce. Koda kuwa zan rasa kwabo a asusuna, zan kwatarwa jikokina ?ancinsu, sai ya zama Isuhu ba ya ganin kowame Wa a gabansa idan ba su ba. Mu zuba ni da ku."

Mami ganin yanda ta Wauki zafi kawai sai ta mi?e itama ranta a jagule ta bar mata Wakin. Da ace Anna ta san damuwar da ke cin ranta da ba ta soma ?ara mata fetur a kan wutar da ta riga ta soma babbaka a zuciya da kwakwalwarta ba. Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login