Showing 147001 words to 150000 words out of 189325 words

Chapter 50 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

218

a kansu amma tamkar dai maganganunta ba su samu wani matsuguni ba. Shi Yassar idan dai bushasha da arziki ne, babu irin wacce ba ya yi a dukiyar Abba. Ya zama Wan karya da kashewa mata kudi. Dawud ma yakan yafici rabonsa amma ya fi Yassar tsoro wannan ya sanya na sa bai fito fili ba. Toh idan dama don kudin ne suke jin haushi da ganin kamar an fi kyautatawa Humaira, ai dai yanzun su ma suna yagar na su. Wannan ya sanya ko a jikinsu.

***
Humaira da sallama a bakinta ta tura kai dakin Mami, ta iske ta tsaye ri?e da wayarta tana dannawa amma ganinta sai ta yi saurin juyowa tamkar wata marar gaskiya can kuma ta basar ta hanyar saita kanta ta ajiye wayar ta nufi gaban madubi don goge jiki.

"Mami ina wuni."

Ciki-ciki ta amsa.

"Lafiya."

Shiru ya Wan biyo baya, ita ba ta ce uffan ba hakanan Mami dake shafa mai a jiki. Wayar Mamin ce ta yi ?ara Humaira ta mike da zummar Wauka ta mi?a mata, amma kafin ta kai ga wayar ta ji Mami ta dakamata tsawa.

"Kar ki kuskura!"

Tana fadin haka ta taso da wani mugun sauri ta kai hannu ta dauki wayar, WZY ne ya kira. Humaira dai tana tsaye kamar an shuka icce tana kallon Mamin har lokacin kirjinta duka yake don ba kaWan tsawar da Mamin ta yi ta tsorata ta ba. Mami ta Wan saci kallonta sannan ta katse kiran, a karshe ma ta danna Airplane mode yadda ba zai kara kira har ya same ta ba.

"Ina ruwanki da wayata? Bana son iskancin wofi, kin wani shigo kin min tsaye a ka, toh kin gaishe ni ba ina ce shikenan ba sai ki juya ki tafi?!"

Ta numfasa.

"Kiyi hakuri Mami, Raihana na zo karSarwa maganin ciwon kai ya matsa mata kuma daga nan na..."

"Kiyi me?! Raihana ni ba?uwarta ce da ba za ta iya zuwa ta karSa da kanta ba? Har akwai wani shamaki tsakaninmu ina uwarta mahaifiya?!"

Kalaman sun daki Humaira da har ba ta iya Soye mamakinta ba ta dubi Mami dakyau amma sai ta ji miyan bakinta ya kafe ta kasa cewa uffan. Tsakin da ta ji Mami ta yi ne ya maido ta cikin tunaninta.

"Kiyi hakuri nayi zaton da kai da kaya duk mallakar wuya ne, ban Wauka akwai bambanci tsakani ba. Amma zan kiyaye tunda an ankarar."

Tana kaiwa nan ba ta jira me Mamin za ta ce ba ta yi gaba da sauri ta fice ta bar kofofin hancin Mamin da sha?ar ?amshin da ta bari. Bayan fitarta Mami ta Wan dafe goshi, meyasa? Meyasa ta ke kasa sarrafa kanta a kwanakin nan, gaba daya ta kasa hakurin Soye abin da ke ranta. Amma ta sani adalilin wannan daukakar da ta zo ga Humairar ce alhalin nata yaran na watangalili a gidan mazajensu sun kasa samun jin dadi da walwalar da ta so musu.

"Ya zama dole na kula kada taSarSarewar abubuwa su fi wanda nake fuskanta a yanzu."

Ta yi furucin a fili, ta kalli wayarta ta ?i fitar da ita daga plane mode ba don komai ba sai gudun abin da Wizzy zai fesar mata. Ta san ba za ta ji mai kyau da kuma dadi ba don haka ta yi watsi da lamarinsa.

***
Futuha ce kwance a falonta tana danne-danne a waya kamar yanda ta saba, sai ta wuni gida a ?azance idan har ba yarinyar da ke mata aiki ce ta zo ba. Ba ta kauda ko tsinke, girki ma hakanan take hakuri da yanda yarinyar ke jagwalgwalawa ta kawomata.

Kira ne ya shigo wayarta, sunan ?awarta Aina'u da ta gani ya sanya ta Wagawa.

"Marar mutunci, sai yau kika tuna da ni?" Cewar Futuha cikin walwala.

Tsaki Aina'u ta ja.

"Ba dole ba, ke yanzu don wulakanci da daukata da kika yi ?ar iska kika kasa sanar da ni abin bakin cikin da ya sameki, koda dai na ji muryarki ma babu wata alama na Sacin rai."

Sai tunanin Futuha ya ba ta ko batun Anti Jannat take yi, kasancewar Aina'un ta san Jannat sadda suke gida.?

"Toh banda abinki wannan ai ba abin yayatawa ba ne, don ma dai kudaden da aka bu?ata babu wani yawa, just 10millions fa."

Wani uban ashariya Aina'u ta saki ta wayar kafin ta ce.

"Kada dai ki cemin ba ki da labarin auren da Yakubu mijinki zai yi da ?ar Snow?"

Ai sai ga Futuha a tsaye kirr saman ?afafunta. Kirjinta wani dukan tara-tara ya shiga yi.

"Wannan zancen banza ne kike yi, Yakubu fa yana Dubai. Wace ?ar Snow din kike maganar zai aura?"

Wata dariya Aina'u ta saki.

"Lallai Futuha wayonki ya tashi a banza. Toh ita ?ar Snow din kika san ina take? Wallahi tana tare da shi a can ma suka hade lefen nan da kika ga hotunansu, ina maki magana ba cikin satin nan ya ce maki zai dawo ba? Toh tare za su taho da ita kuma yana zuwa aure za'a daura. Gidan da ya fidda ki a ciki, nan zai ajiye ta har an ?ara yi mata wani mahaukacin gyara ya yi kyau."

Ihu mai karfi Futuha ta saki har sai da ta razana Aina'u.

"?arya kike yi! Ba dai mijina ba! Ke uban wa ya fadamaki duka wannan?! Aina kar ki kashe ni, kirjina zafi yake ina ganin dishi-dishi."

Aina'u ta hau rantsuwa da Allah akan dagaske take yi, kuma ta ce tunda har ba ta aminta ba za ta hankaWo mata hotuna ta sha kallo. Ko sakanni biyar ba su yi ba da ajiye wayar Aina'u ta aikomata hotunan da ?ar Snow ke Worawa tana rufe fuskar Angonta. Gaba daya Yakubunta ne a hoton. Ta kuwa buga wayar jikin talabijin dinta gami da fasa uban ?ara. A haukace ta shiga daki ta dauki mayafi sai gida.

***
Raihana bayan da ta lura hankalin kowa ya tafi akan Humaira da Hajjo ke yiwa gyaran jiki kasancewar yaran Baba Amina sun zo itama tana dakin, sai ta mike ta nufi bangaren Abba. Mami ta fita unguwa, cikin sa'a ta iskeshi zaune shi Waya ya kammala shan fura. Ganinta ya sanya shi Wan zubamata idanu da amsa sallamarta.

Ta ?araso ta zauna a gefe.

"Rahane (sunan da ya ke kiranta a wasu lokutan), ba ki da lafiya ne kwana biyun nan?"

Ta sunkuyar da kai gami da bude baki cikin sanyin jiki ta amsa.

"A'a Abba, lafiyata kalau."

"Kin kasa cire maganar can a ranki ko? Meyasa ba kya jin nasiha? Nace maki ki bar komai a hannuna tun da na riga da na ankara toh da yardar Allah hakan ba zai ?ara kasancewa ba. Ai wataran za a kuma kwatawa, kinga sai ya kasance muna da shaidu ba kamar yanzu ba."

Raihana da tuni hawaye sun ji?a fuskarta ta gyaWa kai da Wan jan majina.

"Toh Abba, dama na dauki lambar wanda Mami ta kira a ranar ne shi ne nace bari na kawomaka nasan zai taimaka wajen bincike."

"Ya aka yi ta bari kika taSa wayarta? Na sha gwada yin hakan amma ban samu nasara ba."

Ya fadi cike da jin dadin wannan nasara, ko ba komai za'a bincika a kamo shi yaron da aka sanya ya aikata laifin. Ta ba shi labarin yanda aka yi ta dauka sannan ya fiddo wayarsa ta sanya masa lambar.

"Kiyi hakuri Raihana, na sani daga ni har ke mun kasa yarda da abin da yake a zahiri saboda inda ake zatonsa ba anan aka iske shi ba. Abin ya zo da daure kai da al'ajabi, ina fatan wannan ba zai hana ki cigaba da yin biyayya gareta ba, kema kuma ina fatan da zarar kin kammala jarrabawa ki yiwa shi yaron can magana ya fito a yi magana."

Gyada kai kawai Raihana ta yi, ita yanzu komai ma na duniyar ji take ya sire mata, har kullum fargabarta bai wuce da idanun da za ta dubi Humaira idan wannan Wanyen aikin na Maminta ya fito ba.

Daga haka suka rabu da Abban. Shi ko Abba kai tsaye ya tura lambar zuwa ga D.P.O sannan ya kirashi suka yi magana. D.P.O ya tabbatar masa da yardar Allah za su bincika har su cafke mai wayar. Da haka suka yi sallama.

***
Babandi kenan, ba?in kuma gabjejan ?ato mai tumbi zaune saman kujera ya ci uban rawanin da ko zafi bai yi masa. Mami na daga gefensa a zaune, falon tsaf sai iskar fanka ta ko'ina domin gidan Malam Babandi solar ce ke aiki. Tsohon Malami ne kuma babba da ya ci ya hantse da haram. Ya dubi Mami dakyau.

"Gaskiya Hajiya Maryam akwai matsaloli sosai. Na farko kin yi saken da yaranki suka san komai dangane da abin da kika shuka, wannan idan ba ki manta ba yana daga cikin sharuWWan da na taSa gindaya maki a baya, wato kar ki kuskura a yanda kika faro mu'amalarki da kowa, ki bada ?ofar da wani ko wata zai ji. Idan ban manta ba kwanaki can kin faWamin kin sanar da ita babbar yarinyarki, koda muka bincika muka ga ba zai haifar da matsala ba amma duk da hakan ai na kwaSe ki. Yanzu dai ita wannan yarinya taki ta biyu, Yasmeen take ko?"

"Tasleem." Mami ta gyara masa da muryar da ta fito daga can ?asan ma?oshinta, a duniya ba ta son rashin nasara a kan komai ma ba wai iyalinta ba.

Babandi ya cigaba da zancensa.

"Yauwa Tasleem, yarinya ce mai taurin kai da kafiya a yanda na gani, zai wahala ta iya bar wa cikinta komai."

"Nidai don Allah Babandi a yi dukkan abin da ya dace idan har kwalliya za ta biya kudin sabulu, sannan batun auren ita Humaira da yaron can, kiyi hakuri, ban hango wani katanga da zai yi sanadin rushewarsa ba. Sai dai abu Waya, ki zaSi ta Sangaren da kike son a musgunawa rayuwarta mu gani ko zai yiwu. Abu na gaba kuma wato mijinki Isuhu, ba zan ce maki ga abin da na gani ba, amma wacece Maijidda? A zuri'arsu akwai wata mai suna hakan ne?"

Gaba daya abubuwan da yake faWi tana jinsa ba don tana fahimtar komai ba, ba ta tashi dawowa hayyacinta ba a gigice sai da ya ambaci Maijidda. Ta ji dam! Wata iriyar faWuwar gaba. Idanu waje take dubansa.

"Me..me kake son ka ce?"

Babandi ya girgiza kai.

"Tambayarki nayi ko akwai Maijidda? Ai ban ce ba tukunna."

"Babu, ba mu da wata Maijidda hakanan shi kansa Alhajin."

Babandi ya yi wani irin murmushi gami da girgiza kai.

"Toh ai shikenan."

Ta dube shi cikin fitar hayyaci.

"Me zai faru da shi Isuhun da Maijiddar?"

Ya Wan zubamata idanu sai kuma ya numfasa.

"Duhu na hanga, ban gane komai ba. Na dai ga wata an kuma cemin Maijidda ce. Ban san manufar hakan ba."

Gumi ne ya shiga kwaranyo mata. Maijidda dai? Toh don uwar Maijiddan me za ta yi a rayuwar mijinta? Kada dai waccan tsohuwar kilakin da duk mijin da ta aura mutuwa yake yi ita ce Maijidda da Babandin ke nufi? Toh ma da take tunanin aure ne zai faru tsakanin shi Isuhun da Maijidda?

"Ina!! Wallahi na rantse maka idan ni Maryama ina raye Babandi ba ka isa ba! Ashe dama kai macucin banza ne?! Wato aure ka hanga tsakanin ba?ar annobar can da mijina shi ne za ka yimin na ?an bariki?! Lallai kai cikakken marar hankali ne da tunani! Ni Maryam kake tunanin ina raye san bari Isuhu ya auri wata bayan ni?!"

Babandi ya ji zafin maganganunta.

"Hajiya Maryam kar ki sake ki zage ni. Ni nace maki na hangi aure ko zama tsakani? Har yau duk da irin shekarun da muka kwashe da ke ki iya kallon cikin idanuna ki kira ni da marar hankali kuma macuci?!"

Idanun Mami sun rufe ruf akan ba?in kishin da ya tasar mata, ji ta yi kamar Abban take gani zaune a gabanta. Babu abin da take haskowa sai tabbatuwar aure tsakanin Maijiddan da Abba. Jikinta kuwa har rawa yake yi don haka a harzu?e kuma cikin kururuwa ta daka masa tsawa.

"An kiraka Win! Nace ka yi uwar da za ka yi Isuhu! Ni ce ma banzar da na zauna sauraron tatsuniyoyinka marasa kan gado. Yo mutumin da yake da mata har huWu hakan bai isheka ba kana neman almajiranka maza kai zan tsaya ka magancemin matsalolina alhalin kodayaushe lalacewa yake! Ni nan na ishi kaina! Zan yiwa kaina komai! Daga yau idan ka kara ganin ?afata a inda ka ke kirani da wani sunan ba Maryam ba!"

Tana kaiwa nan ta yi gaba tana ji yana fadin sai ta yi muguwar nadamar zageshin da ta yi amma ba ta ko juyo ba balle ta ji nadamar kalaman da ta yi mishi.

***
Kamar tare suka isa cikin gida da Futuha wacce ke faman kwara ihu tana kiran wayyo. Mami duk da yanayin tashin hankalin da take ciki sai da ta ji cikin ya yi mugun Wurar ruwa, idan akwai wani abu da ta tsana a rayuwarta bai wuce ta ji ko ta ga wata masifar ta afkawa yaranta ba. Yaran da ta ci kwakwa wajen ganin rayuwarsu ta inganta. Ta Soye ainahinta ga duniya domin ta samu kyakkyawar shaidar yaudarar mutanen da take tare da su duk don ingancin da ta ke son rayuwar yaranta su yi.

"Ke! Meye haka? Wannan wane irin hauka kike yi kina neman tara mana jama'a?"

Futuha cikin kuka take sanar da Mami labarin auren ?ar Snow da Yakubu. Ta ?ara da faWin.

"Ni wallahi Mami ba zan zauna da ita ba, na fasa aurensa dama ai bakin cikin abin da ta aikata min na Sata sunana a soshal midiya ne ya sanya na aureshi. Toh wallahi na gama aurensa!"

Jiri sosai ta ji yana nema ya kayar da ita, daidai lokacin kuma aka buWewa Fadeel katon ?yauren gidan ya shigo ya yi parking, ganin Mami ya sanya shi fitowa sai baza ?amshi yake har wata ?ar ?iba ya ?ara saboda kwanciyar hankali da murnar samun farin cikinsa. Ya ci ado cikin shaddarsa coffee da hula kalarta.

Mami kallonsa take yi, kallon kai ne silar rugujewar rayuwar Wiyata Tasleem, kai ne kuma silar da aka kama ?ar uwata Jannat. Shi kuwa a kunyace da kuma ban girma ya Wan russuna ya gaisheta. Madadin ta amsa sai ta buWe baki da zummar gasa masa ba?a?en magana amma ta fasa hango Yassar da ta yi ta baya yana mata alama da hannu, alamar ro?on ta yi hakuri ta bar wa cikinta. Yana jin duk yanda suka yi da Futuha, ta harari Fadeel kawai ta ja hannun Futuha da ta Wan danne kukan ganin Fadeel din zuwa ciki. Bai yi mamakin hakan da ya gani tattare da Mamin ba don ya lura tun a kotu take sha?e da shi saboda kama Jannat, amma a zatonsa tunda har dai kauna ta don Allah ta ke yiwa su Humaira ai ya ci ace ta ji dadin tonuwar asirin wanda ya Sata musu suna. Sai Yassar ne ya ja shi zuwa masaukin ba?i.

***
Suna shiga falon suka yi karo da Humaira ta yi kyau shar da ita cikin lemon green din leshi ta yafa ba?in mayafi. Ba ta yi kwalliyar a zo a gani ba amma fa fatarta ta gogu tas. Ganinsu ya sanya ta gaida Mami gami da yi mata barka da zuwa bayan ta Wan kula da yanayin tashin hankalin dake saman fuskokinsu har ita Futuhar.

Mami ba ta amsa mata ba sai ta yi gaba, itama Humaira ganin hakan sai ta soma tafiya domin ta fita.

"Ke!"

Ta tsaya gami da juyowa ga kallon Mamin.

"Ki yimin farfesun nama yanzu ina jin yunwa."

Humaira ta Wan yi turus, ta mance rabon da Mamin ta sanya ta koda tafasa ruwan zafi ne. Sai yanzun da Fadeel ya zo sannan za ta kirkiro aiki?

"Ko ba za ki yi ba?"

Tambayar Mamin ya katse tunaninta, jiki a sanyaye ta ce.

"Zan yi."

"Toh wuce ki je."

Daga nan Humaira ta kama hanya ta nufi kicin. Wannan ya faranta zuciyar Tasleem dake zaune har da kyakyacewa da dariya.

***
A can kuwa Fadeel da ke zaman jira shiru, yana kokarin kiran wayar Humaira sai ga Abba ya shigo. Bayan sun gaisa ya ce


"Ba ta fito ba ne?"

Fadeel yana Wan sosa ?eya amma bai ce komai ba.
"Shikenan." Abin da Abban ya furta kenan ya nufi ciki.
*DUKAN RUWA*
_Ba zai hana gwarje amo ba._


Da Raihana ya soma kiciSus ta fito daga kicin inda ta tarar Humaira ta kama aiki ranta duk a Sace don ta yi duk iyaka yinta ta bar mata aikin ta tafi amma ta ce sam tunda Mamin ta sanya ta za ta iya yi ta je ta ba wa Fadeel hakuri ya tafi kawai. Ganin Abban itama sai ta ji sanyi ba ta ko gaida shi ba ta tafi kai tsaye kan abin da ke cin ranta.
"Abba ga Humaira ta bar Yaya Fadeel ya.."

"Ya isa, kiramin ita."

Abban ya katse ta, ya yi daidai da fitowar Mami daga dakinta. Ganinsa sai ta haWe girar sama da ta ?as, kallo daya ya yi mata ya kauda kai shima ta sa fuskar a Waure sakamakon fitar da ta yi ba da izninsa ba a yau, wani abu da ya zame masa ba?on abu wanda ba ya jin ta taSa yi masa hakan. Humaira ta shigo falon tare da Raihana, hawaye kwance saman fuskarta kafin ma ta kai ga cewa wani abu Abba ya tari numfashinta.

"Shirya ki je kin bar mutum zaune yana ta jiranki."

Jiki a sanyaye ta dauki mayafinta dake saman kujera, Mami itama zuciya a sama ta ce.

"Ni kuma ban miki iznin fita ba! Aiki na sanya ta ai, don me shi ba zai iya jiran ta kammala ba tunda ganinta a yau din ya zame masa tamkar rubutu a saman dutse?"

Humaira sai ta yi turus, Mami dai ba za ta daina shayar da ita mamaki ba. ?iyayyarta a fili na wannan auren ta ke nunawa ba ta ko iya Soyewa.

"Duk ikonki akan ta bai kai ya ni ba, daga ita din har ke din karkashina ku ke, babu dalilin da zai sa na zuba idanu a mayar da ni sakarai a gidana. Don haka Humaira kar ki yarda na ?ara ba ki umarni na biyu, ki wuce yanzu."

Ambatonta da Humaira da Abban ya yi wanda bai taSa kwata hakan ba ya sa ta fahimci abin ba mai sauki bane don haka sum sum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login