Showing 12001 words to 15000 words out of 189325 words

Chapter 5 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

255

fito a bakinsu hakanan za su watsa musu ba tare da taunawa ba, toh wace riba ake samu a hakan? Ita tunda ta zo ma ban da Ummita da Raihana sai Muhsin masu ?okarin zuwa islamiyya, ba ta ga wani cikin su Tasleem na zuwa ba. Bar su dai da yawon gidan ?awaye a Soye Abban bai sani ba. Itama dai Raihanan ba zama take sosai ba amma takan tsaya har a biya karatu da ita,? wasu lokutan sai dai ta ji tana amsa wayar zasu haWu da wani saurayin idan ta fita makaranta.
? ? A yanzu kuwa daga maganganun Mamin ta fahimci watakila Yassar kuWi ya nema ko wani abin da bai samu ba ya faWi abu game da Abban shi ne take goranta mishi.

"Muje Humaira, ya zo."

Ta amsa da toh ta bi bayan Mamin cike da jin tausayinta, kowace uwa na son ta ga nata na bin ta sau da ?afa, amma Mami ba ta samu wannan biyayyar ba na yara. Daga manyan har ?ananan, koda dai ta ji Ummita na cewa shi dai babban Wan nasu ya bambanta da sauran, kuma su na masifar shakkarsa, akwai abubuwa da dama wanda idan yana nan ba sa aikatawa. Ta ce daidai da hantarar da suke yi mata idan har yana nan ba sa yi.

Har dai suka soma tafiya a titi tunane-tunane take yi, hankalinta jiya bai kwanta ba sai da ta tsinkayi Tasleem na hira da Raihana su na tsokanar Futuha akan marin da ta sha har su na faWin gobe ma ta ?ara. Daga baya dai ko don tana Wakin ne sai suka juye harshe zuwa turanci, ta lura ba su fiye yin buzanci ba su kam, a yadda Ummita ta ce ma, ba komai suka iya faWi a yaren ba, sun dai fi ganewa idan an musu magana ba su iya mayarwa yadda ya kamata ba. Wannan sai babban yayansu. Shi dai yana ji sosai.

Daidai wani babban gida motar ta tsaya, suka fito suka nufi ciki. Kyau da tsaruwar gidan har ya so ya kere na su. Da murmushi Mami ta dubi Humaira lokacin da suka shiga farfajiyar gidan.

"Gidan aminiyata kenan Hajiya Lubna, ita ce za ta kai ki wajen koyon girki. ?anwarta ke yi."

Humaira ta gyaWa kai ranta ya yi fari sol, ta san dai Mamin ta ce ta shirya zasu je unguwa amma ba ta kawo a rai fitar ta shafe ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ta ba. Daidai za su shiga babban falon suka yi karo da Wan Hajiya Lubna shi kuma zai fito, matashin saurayi mai jini a jika, ya sha ?ananun kaya abinsa ya yi tsaf. A fuska ba za ka kira shi da kyakkyawa ba sai dai hutu da jin dadi ya sa fatarsa murmurewa. Gaisawa ya ke da Mamin amma hankalinsa kacokam na ga Humaira wacce daga kallo Waya da ta yi mishi ta kauda kanta don ita kam a duniya ta tsani kallo. Mami na lura da yanayin kallon da yake jifan Humairar da shi, ita kanta bai mata ba don haka don ta katse shirun ta ce.
?
"Hajiyar dai na ciki ko? Don na san ta yanzu sai ta iya ficewa ta bar ni zaman jira."

Dariya ya Wan yi yana shafo ?eyarsa.

"Tana ciki Hajjaju. Ku shiga kafin na shigo."

Ta amsa mishi ta yi gaba Humaira ta bi bayanta da sauri har tana tuntuSe saboda kallon da yake bin ta da shi. Mami ta kalleta kawai ta kauda kai ba ta ce uffan ba. A falon gidan suka iske ?an mata da yara ana kallo ana hira, wuta tarr a gidan madadin gidansu wanda idan har ba wutar Nepa aka ci sa'a suka kawo da rana ba, zai yi wahala ka ga hasken fitila a gidan sai Magriba zuwa ?arfe sha biyun dare.

Gaba Wayansu suka gaida Mami, ta amsa. Ta dubi Humaira.

"Ki zauna ki jira ni bari na ?arasa wajenta." Ta amsa da toh ta nemi wuri ta zauna. Ta lura gidan dai ?an boko ne, ba su ko damu da ita ba sai mai aikin gidan da ta mi?e ta kawo mata ruwa da lemu ganin da ta yi tare suke da aminiyar uwar Wakinta. Godiya ta yi mata amma ba ta sha ba, hankalinta kacokam na garesu, wani shiri suke kallo na india, sun maida hankalinsu kacokam. Itama sai nata hankalin ya tafi can. Ta shafe mintuna goma a nan tana jiran Mami, can sai ga wani Wan yaro ya sauko daga benen da Mamin ta hau.

"Ki je ana kiranki a sama."

"Toh" Kawai ta ce ta mi?e ta nufi hanyar da yaron ya fito, kafin ta ?arasa ta tsinkayi wata muryar babbar mace na faWin.

"Ke dai ki bi a hankali, kar ki yi garaje kamar yadda ki ka so yi a wancan lokacin."

Sallamarta yasa suka kalli hanyar da sauri, ba ta lura da yanayinsu ba ta karasa ta durkusa gefe ta gaida matar wacce kamanninta sak da wannan matashin da suka gani Wazun. Matar ta amsa mata fuska a sake.

"Ah Maryam, ki ce Wiyar tamu kyakkyawa ce masha Allah. Humaira ko?"

Humaira ta gyaWa kai tana sunkuyar da kai murmushi a saman leSbanta.

"Masha Allah, Allah ya yi albarka kin ji? Allah ya gafartawa Hajiya Fatima, idan kika biyo halinta kin more. Mace mai hakuri da kawaici. Allah ya gafarta mata."

Ta ji wani sanyi a ranta, a duniya tana jin daWin a yabi Mahaifiyarta. Ta amsa da amin ita da Mami.

Mamin ta dube ta.

"Toh Humaira, gobe idan Allah ya kaimu koda ba ni ba, sai ku zo da Ummita a kaiki gidan koyon girkin. Na faWamaki ta gida ce, ?anwar Hajiya Lubna ce. Sai ki mayar da hankali ga abin da ya kai ki. Nasan kina da fahimta da saurin Waukar abu, don Allah kar ki ba mu kunya kin ji ko?"

Ta amsa da toh Mami. Kafin Mami ta Wora daga inda ta tsaya wannan saurayin na Wazu ya hayo. Suka maida duba gareshi. Wani irin ajiysr zuciya ya sauke yana duban Humaira sannan ya maida kallonsa ga Mami.

"Ai na Wauka har kun tafi."

Mamin ta Wan yi murmushi kaWan ta girgiza kai.

"Ina nan Kabeer, amma yanzun za mu tafi. Abban yara ya kusa komawa gida."

Ya karasa ya zauna. Hajiya Lubna nan da nan fuskarta ta sauya ganin kallon da yake jifan Humaira da shi. Mami ta dubi Humaira ta bata umarnin ta koma ?asa ta yi jiranta za ta sauko su tafi. Daga fitarta shi ma ya mi?e caraf ya bi bayanta. Hajiya Lubna za ta yi magana, Mami da sauri ta hana ta ta hanyar Wan dafe kafaWarta. Dole ta fasa. Amma ta kudurce a ranta lallai za ta yiwa abin tufka don ita kam Wiyar ubangidan mijinta take so ya aura, ta kuma lura da yadda yake bin Humaira kamar jela to akwai wata a ?asa. ?wafa kawai ta yi ta watsar suka Wora hirarsu daga inda suka tsaya.

A can kuwa Humaira duk ya takura mata, ita ba ta saba da wannan rayuwar ba. Kawai wani garjejan saurayi ya zauna yana jan ta da hira ba hadin uwa da uba, ita kam abin ya girmi kanta. Ta kula bai ko damu da jama'ar falon ba waWanda su din ma kallonsu kawai suke jifa-jifa su na mayar da hankalinsu ga tv.? Tambayoyi yake mata iri-iri, amma ba ?ar Mami ce ke ba? Yaushe ki ka zo? Karatu? kike? Da dai sauransu ita dai eh ko aa kawai take ce mishi duk ta takura. Haka Mami da Hajiya Lubna suka sauko, ganinsu ya sa ya mi?e yana shafar ?eya.

"Wai Kabeer ina aiken da na maka ne? Idan ba za ka je ba, ka fadamin na aiki Bala direba."

Hajiya Lubna ta faWi rai bace tana watsa mishi harara, sarai ya gane manufarta, amma shi kam yana ji a ransa ko karatu Humaira take yi zai iya dakon jira ta kammala ya aure ta. Ya lura auren jari Hajiyartasa take so ya yi.

"Sorry Hajjaju, bari na tafi. Mami ku gaida gida, sai na tako har falonki na ?ara gaida ki."

Mamin ta yi dariya.

"Ai babu laifi Kabeer, ko da wacce ka zo ka shiryawa amsar da za ka samu."

Ganin ta Wago shi ya fice yana ?ar dariya gami da faWin.

"Na shirya Maminmu, amma dai ba zan ja baya ba."

Mamin ta ?ara darawa. Humaira ta mi?e suka kara yin sallama da Hajiya Lubna, har farfajiyar gidan ta rako su. Humaira dai har ta Wan kwashe mintuna a mota ba su gama tsayuwarsu a bakin ?ofar falon su na tattaunawa ba, ba ta san me suke cewa ba dakyar dai Mamin ta taho ta shiga motar suka tafi.
***
Humaira ce zaune a falo da safe, yaran gidan duka sun fice makaranta kasancewar sun soma jarrabawar zango na uku (Raihana da Ummita kenan), a yadda Ummita ta ce mata, daga jarrabawar to aji na gaba za su je.
Kallon tashar Arewa24 take inda ake hasko wani wasan kwaikwayo na marigayi Ibro. Ta shagala gaba daya tana tuntsira dariya ta ji Wif, wuta ta Wauke. Guntun tsaki ta ja, ita kam ba ta san matsalar wuta a nijar ba domin koyaushe akwai. Ba ruwanka da tayar da janareto. Ganin haka kawai sai ta mi?e da zummar komawa Waki.

"Humaira."

Muryar Ladidi ta katse ta, ta juyo ta amsa. Tire ne a hannun Ladidin ta karaso gareta. Fuskarta duk ta yi narai-narai alamun ro?o.

"Ki taimakamin don Allah ki mi?a sashen Anna, kinga suyar agadar Mami nake kada ya ?one. Kuma Annar za ta sha magungunanta ne lokaci na tafiya."

Kirjinta ya Wan buga dam, ta kasa magana. Toh akan me za ta cewa Ladidin ba ta taSa shiga sashin Anna ba? A ganinta hakan su ta shafa. Ganin yadda Ladidin ke magiya yasa ta karSa, godiya ta yi mata ta koma kicin. Ita kuwa Wan hanyar da take ganin su Muhsin na yawan zirga-zirga zuwa wajen Annar ta zubawa ido sannan ta sauke ajiyar zuciya ta nufi wajen. Anna Win ai mutum ce ba aljana ba balle ta illata ta, za ta je ta ga me zai faru idan ta yi karo da ita. Koro ta za ta yi daga Wakin ko kuwa dai duka za ta yi mata. Da haka ta tunkari hanyar.

A hankali ta tura ?ofar Wakin da sallama, jin shiru yasa ta maimaita. Wata murya ta amsa, ta tabbatar ba shakka muryar ta Anna ce. Shiga ta yi ta karasa ta ajiye saman ?aramin tebur dake wurin. Anna dake zaune gefen gado ta soma magana tana laluben gilashinta.

"Ladidi sai yanzu ake kawomin abin karin? Yau me ya tsaida ki haka? Ina gilashina na jefa?"

Humaira ta hadiyi miyau, kenan dai Anna ba ta san ma wace tsugune a gabanta ba. Ta daure ta ce.

"Ina kwana. Ya karfin jiki?"

Jin? ba?uwar murya ya sa Anna saurin sanya medicated glass Winta wanda da shi ne ta ke gani sosai ba dishi-dishi ba. Yarinya budurwa ce dur?ushe a gabanta, fara sol. Kanta duk da cewar akwai hula, sumarta ba ta Suya ba don hatta da goshi da bayan ?eyarta sumar ce kwance. Ta ?uramata idanu tana ?okarin tuno inda ta san fuskar. Sai dai a Wan lokacin ba ta ankare ba don ita shaf tuni ta mance da wata wai Humaira a gidan tunda ba su taSa karo ba. Ba ta damu da shiga sashin Wiyarta ba, ya fi rayuwa anan dai Sangarenta.
Daidai lokacin Mami ta shigo Wakin kamar wacce aka jefo, ta samu labari daga Ladidi cewar Humaira ta tura kai wa Annar kari. Shigowarta ya sa Anna mayar da dubanta gareta.

"Ina kika samu yarinya ha..."

Sauran kalaman Anna suka ma?ale a fatar bakinta, shakka babu ta tuno komai. Ta tuna ashe akwai wani ran bayan jikokinta a gidan da aka ce tsatson Fatima ce. Ta tuna Humaira kamar yadda ta ji sunanta a bakin su Yassar masu yawon kawo ?orafi a kan fifikon da Mami ke yi mata sama da su. Nan da nan ta haWe girar sama da ta ?asa. Daidai lokacin Humaira ta ?ara gaidata wannan karon muryarta har Wan rawa yake. Ta nuna Humairar da yatsa idanunta akan Mami.

"Me wannan abar ta zo yi wurina? Me na faWamaki? Ban ce maki ba na son ganin baragurbi? a wurina ba? Ke don uwaki wa ya ba ki iznin zuwa wurina, ko ni na haifi uwarki?!"

Maganar sosai ta daki Humaira, nan da nan idanunta suka cicciko da kwalla, uwarta kuma? Uwar dake kwance a kushewarta? Mene dalilin sanyo ta ciki? Ba ta jira umarnin Mami ba ta mi?e a zuciye ta kama hanyar fita daga Wakin, Mami ta ri?e hannunta wannan ya dakatar da ita sai dai ba ta ko juyo ba. Daidai nan kuma hawayen suka sauka saman kuncinta. Da harshen buzanci Mamin ta yiwa Anna magana, Annar kuwa cikin harshen da Humairar za ta ji ta amsa a fusace cikin Waga murya.

"Au! Don na zage ta kike kirana marar adalci? Ni Maryama kike kallon idona ki ce ba na adalci? Toh anyi rashin adalcin. Idan maye ta manta ai uwar Wa ba ta mance ba. Ke da kika ga za ki iya haWiye duk ba?in cikin da kika ris?i kanki a baya, ki yi. Nikam ba da ni ba, kuma ke duk radda kika kuskure ki ka ?ara gangancin takowa Wakin nan sai na sa jikokina sun nakastamin ke. Sauran yunwa kawai."

Humaira tuni ta janye hannunta a na Mami ta bar Wakin da sauri.
Kai tsaye Wakinsu ta nufa ta zube saman kafet ta shiga kuka kamar ranta zai fita. Ita fa duk abin da matar ta ce bai dame ta ba kamar sanya uwarta da ta yi a ciki. To me Mamarta ta yiwa Mamin da har Anna ke batun ba za ta mance ba? Wane irin zama suka yi a baya? Ita Mami da ma ?an uwan Abba, sun yiwa Mahaifiyarta kyakkyawar shaida, amma me Anna ke nufi da kalamanta? Ko kuwa dai ita ke taya Wiyarta kishin kamar yadda Ummita ta taSa faWi?

Ba ta ji shigowar Mami Wakin ba sai ji ta yi an kama hannunta an Waga ta. Ta mi?e tsaye, Mami ta yi mata murmushi.

"Ki yi hakuri Humaira, kin san iyaye ne sai mun yi hakuri da su mu samu a rabu lafiya. Ki taya ni yi mata biyayya,? kar ki kara zuwa Wakinta har sai don kanta ta nemi hakan wataran wanda in sha Allahu nake fatansa nan kusa. Kar ki sa komai a ranki, ki kuma shirya anjima da kaina zan kai ki gidan koyon girki. Ki cire komai a ranki ki mayar da hankali, ni kuma anan gida idan kin dawo zan dinga iyakar ?okarina wurin ganin an samar maki dukkan kayan girkin da ki ka koyo a can ki yi a nan mu ci mu WanWana, kin ga daga haka hannunki zai mi?a. Wataran sai a wayi gari kina odar biki da suna har ma da wuraren party ko? Kin zama Hajiya."

Zancen Mamin ya sanya ta murmushin da har wushiryarta ta bayyana. Mamin ma murmushin ta ?ara yi. Daga haka ta fice a Wakin. Humaira tuni ta share batun Anna ta tattara ta watsar.

***
Sun je gidan Anti Laila ?anwar Hajiya Lubna tare da Mami, ta ba da form bayan sun biya komai, Mami da kanta ta cikewa Humairar. Anan aka ajiye ranar litinin matsayin ranar da za ta fara zuwa koyon girkin. Daga nan suka yo gida ranta fari sol.

Kai tsaye Waki ta nufa hannunta ri?e da na Waleed wanda zuwa yanzu daga shi har Muhsin sun sake da ita,? fuskarta a sake, zuciyarta wasai. Ummita ce kaWai zaune tana karatun jarrabawa, ganin haka Humaira ta dubi Waleed.

"Tafi wajen Muhsin ku yi wasa ka ga Adda Ummita karatu take yi. Anjima sai ka zo ka koyamin turanci ko?"

"Okay! Bye."

Itama ta amsa da bye din tana dariyarsa, ya dage a lallai zai koyamata turanci, haka za ta biye mishi tana Wan tsintar wasu abubuwan da ya iya. Ummita ta kalle ta tana murmushi.

"Yau dai fara'arki ta musamman ce. Kada dai ki cemin har kin soma shiga aji?"

Dariya Humairar ta yi daidai sadda take zama a gefenta.

"Aa fa, amma an gama komai an biya, litinin zan soma zuwa."

"Kai naji dadi wallahi. Allah ya nuna mana."

Ta amsa da amin, ta mike ta hau cire kaya da zummar shiga wanka. Ta dai kula kamar Ummitan ranta a jagule ya ke, ba ta ce mata komai ba har ta shiga wanka ta fito. Anan kuma ta ga ta amsa waya ta yi jifa da wayar saman gado tana Wan goge fuska. Jiki a sanyaye ta ?arasa gareta ta zauna.

"Ummita, lafiya? Meyafaru?"

Ummita tana kallon littafin amma ta kasa karatun sai kawai ta girgiza kai tana shirin cewa ba komai amma tuni hawayenta ya zuba saman littafin. Humaira ta janye littafin.

"Don Allah meke faruwa? Anyi wani abu ne bayan fitar mu?"

Nan ma girgiza kan ta yi. Ganin haka sai kawai Humaira ta mike ta nufi sif dinta, har ta sanya kaya jiki a sanyaye Ummitan ba ta da niyyar cewa wani abu. Ganin haka sai ta ?arasa wajenta karo na biyu.

"Na tambayeki mene ne kin kasa cewa komai, kuma kina kuka." Jin ta yi shiru ne yasa Humaira fadin.

"Toh bari na kira Mami mai yiwuwa ita za ki faWamata."

Har ta mi?e da sauri Ummita ta ri?e hannunta. Suna haWa idanu ta girgiza mata kai, itama Humaira tuni idanunta sun cicciko don a duniya ta tsani kukan mutum. Kuka ma irin na waWanda? ta ke yiwa ?auna domin Allah. Duk abin da ya shafi irin mutanen nan tana jin abin a ranta tamkar ita ya shafa.

"Kar ki je, zauna na faWamaki." Ta koma ta zauna tana mai zuba mata ido bayan ta share kwallarta.

"Yayar Mamana ce ta kira ni daga Bichi, kwanakin nan duk sun takura akan lallai sai na fiddo miji na yi aure wai karatun ya isa hakanan. Su sam hankalinsu bai kwanta da zamana a gidannan ba. Ita Babbar yayar Mamana, Anti Maijidda cewa take yi wai har mafarke-mafarke take yi a kaina don haka za su yiwa Abba magana a dakatar da karatun nan, ida n ma aure ne dai a yimin. Ni kuwa na dage akan ba zan yi aure yanzu ba, na ce musu ko zance

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login