Showing 171001 words to 174000 words out of 189325 words

Chapter 58 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

254

kaWan, kinsan ai ban ce masa da ke zan zo ba, ban ma nunamasa muna tare ba ballanta ace don saboda ke zai min ?arya. Ki dai bari zamu je din, zan kuma tuntuSi Hajiya Zainab batun zuwa Kamaru da zamu yi, ya kamata muje a kwanannan"

Da wannan suka rarrashi juna Mami ta wuce gidanta.


***
Cikin satin aka sanya ranar auren Raihana da Ummita lokaci guda, a sannan Ummita ta dawo Kano wurin Baba Amina inda ta bar Ahmad a can gidan Anti Maijidda don yaron sosai ya yi wayo ya saba da su. Tafiyar Ummitan sai ya kasance ko a jikinsa.

Suka yiwa gidan Humaira tsinke, sun mata bazata domin ko kadan ba ta da labarin zuwansu. Zo ka ga murna da farin ciki har da su hawaye a wajensu. An kwana biyu ba a ga juna ba don Raihana ma sau daya ta taSa le?a mata ta kafa hujja da jarrabawa. Sun sha hirar duniya tamkar kada su rabu, babu inda ba su taSa ba. Har zancen auren Abba da Anti Maijidda da ita Humaira ba ta da labari sai a lokacin, kwatanta irin farin cikin da ta yi da ji ba zai misaltu ba.

Sai bayan sati da saka ranar su Raihana sannan Abba ya je wajen Anti Maijidda kuma Alhamdulillah sun kara fahimtar juna. Kasancewar abu na manya nan aka tsaida sati guda kacal domin daurin aure. Haka Abba ya dawo gida zuciyarsa tamkar bai san wata abu mai suna bakin ciki ba saboda kyakkyawar tarba da shimfidar fuskar da ya samu daga Anti Maijidda da iyayenta.

***
Mami duk abin da ake ciki ba ta da labari, na sanya ranar Raihana kawai Abba ya fadi mata shima sai bayan dawowarsa daga Bichin da ba ta san ya je ba.

Wani malolon abu ya tsaya a ma?oshinta.

"Yanzu Isuhu har a sanya ranar Wiyata ka kasa faWamin? Ai ba Amina ce ta haifamin ita ba! Toh na rantse maka sai Raihana ta dawo gidannan tunda dai ni ce uwarta babu banzar da ta haifamin ita!"

Ta fadi cike da bori tana jijjiga hancinnan duka ya buWe tsabar masifa. Abba ba ya tunanin wani hargaginta zai Sata masa rai, shi fa har ya soma jinsa a angon ma tun kan a Waura aurennan. Wani murmushi ma ya saki.

"Ba Amina ce ta haifi Raihana ba ke ce, amma kuma ni Isuhu tunda har Raihana ta nuna ta fi ra'ayin zama a gidan yar uwata ba ki isa ki juya ni ki sa na maido ta nan ba. Idan kin ga Raihana da Ummita a gidannan toh ki sani aurensu ne ya gabato."

Ta wurga masa harara kamar idanunta za su tsinko su fado.

"Kai ka san wannan Isuhu. Ni dai nasan ni na raini cikin Raihana na kuma haife aba ta, babu wanda ya isa ya yimin iko da ita. Mu zuba mu gani!"

Tana kai wa nan ta yi gaba. Yassar da tun soma zancen nasu yake durkushe gaban Abba sakamakon kiransa da ya yi su tattauna batun kasuwa ya ji babu dadi ko kadan, wai yaushe Mami ta sauya ne? Ko dai dama haka take? A yanzu rayuwa ta ladabtar da shi, ko kuma ace soyayyar da yake yiwa wata budurwa da lokaci guda ta nuna ba ta kaunarsa, abu ne da bai taSa faruwa gareshi ba. Sanadin yarinyar ya nutsu ya kuma rame don tunani. Ya kara shiga cikin hayyacinsa, ya bar dukkan wata fankama da karya da yake yi don koda ya soma nunamata facakar kudi nunamasa ta yi ba su ne a gabanta ba.

"Kai ina magana ka yi shiru? Ina tunaninka ya tafi?"

Da wannan ya ba tunane-tunanensa da mamakin yanda maganganun Mami ba su yi wani tasiri sun Sata wa Abban rai a wannan karon ba.

***
RANA BA TA ?ARYA...
Yan uwa da kuma abokan arziki ne suka shaida daurin auren Hajiya Maijidda Bukhari da mijinta Alhaji Isuhu Mai Agogo a garin Bichi. A ranar kuma Abba ya juyo inda aka tsaida kwanaki uku na zuwan Anti Maijidda kamar yanda ta bu?ata.

Ranar da ta kama na kawo kayan Wakin Anti Maijidda wanda Abba da kansa bada aka yi, cikin iko na Ubangiji a ranar Mami ta fice zuwa gidan Babandi ita da Hajiya Lubna. Ita kuwa Tasleem ta kaWa yawonta gidan Futuha don a yanzu gaba daya komai na duniya ya yi mata ?unci.

Baba Amina ta iso, aka sanya komai a Sangaren Anna. Babban falo ne sai Wakuna biyu kowanne da bandaki a ciki sai kuwa kofar kicin da ke a gar?ame. Tun farkon ginin gidan dama Abba wuri biyu ya yi, Mami ba ta ko firgita ba don a sannan tana ganin ko giyar wake Abban ya sha ba zai kara gangancin yi mata kishiya ba. Karshe ma zuwan Anna sai wurin ya koma nata.

Koda aka kammala, Baba Amina ba ta bar gidan ba domin a ranar ne Anti Maijidda za ta shigo Wakinta. Har yamma tana kicin suna aikin tarbar ba?i ita da Ladidi da ta ji labarin auren da Abba ya yi a bakin Baba Amina. Sosai lamarin ya ba ta mamaki, tana kuma da tabbacin uwar Wakinta ba ta da masaniya. Ta sani dai akwai babbar matsala idan ta dawo gidan.

Toh hatta su Yassar da suka dawo daga kasuwa tare da Abba, sai a lokacin Abban ke sanar da su. Ba su ce komai ba sai fatan alheri. Sun dai kame bakinsu daga sanar da wani cikin yan uwansu bisa umarnin Abba akan shi da kansa zai faWawa Mamin. Abin dai bai musu dadi ba musamman jin wacce Abban ya auro, matar da ba sa ga maciji tsakaninta da uwarsu.

***
A gidan Babandi kuwa, Mami da Hajiya Lubna suna ta kai ruwa rana da shi inda ya ce shi sam daidai da fuskar Mami ba ya kaunar gani a yanzu. Ya kara da faWin.

"Idan har za ta mance ala?ar shekara da shekaru ta ci mutuncina, ki faWamin ta yadda ni kuma zan kasa Waukar fansa akan Wiyarta? Ke dai Hajiya Lubna ai kinsan irin ba?ar wahalar aikin da na ci akan kishiyarta mai rasuwa Fatima wanda a ?arshe muka ci galaba kuma aka aika da ita lahira. Amma duk wannan bai hana Hajiya Maryam runtse idanu ta zazzageni ba?"

Mami dai ta ma hakura da ban bakin ta yi shiru kawai, ranta zafi yake don ita haushi ma yake bata, toh mutum dai tunda an ba shi hakuri ai shikenan mene ne kuma na jan magana ta yi tsawo har yana tone-tone?

"Hakuri dai za ka yi Babandi tunda mai afkuwa ya riga da ya afku sai komai ya shige. Ita kanta Hajiya Maryam yanzu ta fahimci komai na rayuwarta ba zai tafi daidai ba sai da sanya hannunka (Wa'iyazubillah), yanzu dai a sulhunta ka yi mana maganin kokenmu."

Ya yi wata bahaguwar dariya.

"Shikenan, yanzu naji komai ya wuce. Ku fadi bu?atunku don sauri nake zan shiga kasuwa, gobe sammakon tafiya Kamaru zan yi a ta mota, akwai wani sirri da zan je karSowa wurin kakana."

Ganin haka Hajiya Lubna ta gyara zama ta karanto mishi nata damuwar, fin ?arfin da surukarta matar Wanta Kabir ke kokarin nunamata a kansa kai kace ita ta haifamata shi, ta?amarta kuma don ubanta ya fi Kabir din da ma uban Kabir din kudi, sai kuwa batun auren da mijinta ya yi ta kara da fadin.

"Ni wallahi ko irin aikin da aka yiwa Fatima ne shi nake bu?atar ka yi mata matu?ar za a dace."

"Ai inaa, Hajjaju ba za ki iya irin kissar da Hajiya Maryam ta yi ba. Hatta da ni ina yabawa wannan kokarin da ta yi na tsawon shekarun nan. Ke kuwa kina da saurin fushi da zuciya, ba za ki Soye abin da ke ranki ba irinta. Ki dai bar komai a hannuna. Ke kuma Hajiya faWi muji naki."

Mami ta dan muskuta ta soma magana.

"Babandi ka riga da ka san nawa. Na tsani na budi idanu na ga Humaira cikin gidan daula alhalin nawa yaran su na terere. So nake ko haukata ta ne ayi idan na ba za ta rabu da tsinannen can, to don Allah a yi abin da itama ba ta mori rayuwar ba. Sai abu na gaba, Alhaji fa kawai kallona yake yana kuma zaune da ni ne amma bai yarda da ni ba kwata kwata, yana zargina sosai. Ina bu?atar na mallakeshi ko ta wane hali, wallahi wannan karon na shirya Babandi, ko mene zan iya aikatawa muddin zan mallaki Abban yara. Sai kuma na ?arshe, ka taimakamin da wani aiki da zai yi sanadin cikin Tasleem, kar ta haifarmin abin da zai jawo na ji kun..."

"Aa, a'a Hajiya Maryam, kar ma ki fara! Koda wasa kar a yi gangancin taSa halittar dake cikin Tasleem, ina son abina. Ta haifa ta kawomin, na samu gagarumin albishir daga cewa wannan abin da za ta haifa shi zai ?ara daukaka darajata kuma zan yi mahaukacin arzi?i. Ki bar ta ta haifarmin, idan da rabo ma bayan ta haihu sai ki ga na aure ta mun rayu cikin daula. Sauran maganganun naki kuma ki barmin wuka da nama. Komai zai tafi daidai da zarar na dawo. Na fadamaku wani sirri zan karSo, wannan sirrin kuwa na kai shekaru takwas ina nemansa, sai yanzu na samu Kakana ya aminta zai bani, na rantse maku ba mazajenku ba, ku hatta da abokansu da ma danginsu sai kun dinga yi musu kwarjini kun ?ara zama abin so a wajensu."

Suka ji wani sanyi na ratsa zu?atansu, suka dubi juna da murmushi a saman fuskokinsu.

"Lallai kuwa idan har wannan aiki ya kammalu na maka alkawarin tafkeken gidan da ya fi wannan Babandi."

Hajiya Lubna ta furta da wani zumudi don har ta hasko tana juya Baban Kabir da ma mutan gidan. Ita kuwa Mami ta tuna da akwai sauran zance a bakinta don haka ta tari numfashin Babandi dake shirin magana.

"Toh amma ya zancen Maijidda da ka taSa yimin? Kar ka manta sanadinsa muka samu matsala, nidai ka taimaka idan wani abin ka hango tsakaninta da Alhaji ka sanar da ni a yiwa abin tufka tun yanzu."

Babandi ya girgiza kai.

"Aa Hajiya Maryam, ai ko wancan karon ban ce maki aure ba. Ke ce dai guguwar kishi ta kwashe ki kika aikata abin da kika yi. Na dai ce ki kula don kuwa na hangi akwai wani abu da shi mijinnaki zai iya samu sanadinta, kodai ta aura masa diyarta ko kuwa dai ta nemo masa matar aure. Nidai ban ga wani aure tsakaninsu ba."

Mami duk da ta ji tashin hankali na cewa wai Abba zai iya kara aure bayan ita kuma ta hannun Anti Maijidda hakan bai san ya ta firgita kamar a farko da tunaninta ya bata cewa ai Maijiddar za'a aura ba.

"Kar ka damu Babandi, don dai ta wata diyar Maijidda ko wata can abu ne mai sauki wanda na tabbata ba zai gagare mu ba. Dama ita Maijiddar ce ba na kaunarta har abada, na tsane ta fiye da irin tsanar da ta yimin kuma har da ganin ba ta da tsoro shiyasa amma ko wace ce zan cin ubanta matukar ta rabi inuwar mijina."

Suka dara gaba daya yayinda Babandi ke yiwa Mamin kirari na musamman. Sun Wan jima suna tattaunawa akan Tasleem inda Babandi ya ?ara tabbatar mata bai aminta da zubar da ciki ba, karshe ta yanke tura Tasleem din can Agadez wajen Anna ko ta ?i ko ta so kuwa. Babandi dai ko a jikinsa, shi dai yace cikin ne bai ga wanda ya isa ya zubar ba.

***
Tasleem ta yiwa Futuha kallon tsaf, gaba daya ta rame ta Wan yi duhu don dai ita din farar gaske ce ma da ba ta san yanda za ta ganta ba.

"Wai Futuha ke kukan dadi ma kike yi. Da aurenki da mutuncinki, kawai ke dai sauyin yanayi da Yakubu ya yi maki da kuma auren cin amanar da ya yi su kadai ne matsalolinki. Ni kuwa me zan ce? Na rabu da mijin dake sona tsakani da Allah saboda hangen dala, na zo nayi biyu babu karshe ma sai ga ni da cikin Boka Babandi a jikina. Wallahi Futuha ina ji kamar na kashe kaina ko na huta da wannan azababbiyar rayuwar da nake yi marar ?anci."

Futuha ta share nata hawayen, tabbas gaskiya Tasleem ta fadi, duk lalacewar nata rayuwar ai aure ya mata sutura. Ita ko ga babu aure ga kuma ciki wanda tun ma kafin ta kai ga cika iddarta ta same shi.

"Hum, na sani Tasleem, na san kin fi ni. Amma ba kya ganin irin yaudarar da Yakubu ya yimin? Yanzu fa zancen da nake maki har sabon bidiyo Yar Snow ta dora a shafinta na Tiktok wai ya shirya mata haWaWWen birthday party kuma har tana ba shi kyakkyawan albishir na cewar tana da juna biyu amma wallahi mutumin nan ko a fuska bai nuna Sacin rai ba sai ma rungumota da ya yi jamaa na musu tafi. Ni shegen ya hana ni daukar ciki ya yimin dadin baki, nayi zaton haihuwar ce ba ya so, kenan da ni ce ba ya kauna? Mutumin nan idan ya shigo gidannan tamkar akan ?aya yake, ga raba dare yana hira da ita ta whatsapp, hum."

Ta kasa cigaba da magana sai kawai ta hau sharar kwalla, Tasleem ta dan bai gidan da kallo.

"Toh ba dole ya dinga jinsa a kan ?aya ba, duk fa yanda na kai ga rashin tsafta wallahi kin fi ni kazanta Futuha. Ji don Allah wannan farantin gar ya bushe ban san tun yaushe kike ajiyarsa anan ba. Shikenan don ?ar aiki ta bar zuwa sai ki zauna ko ya ya ba za ki Wan gwada tattara gida ba? Zanin gadonki kuwa inaga ya fi wata a shimfide, ai ina ji tun kafin Anti Jannat ta wuce Agadez."

Tsaki Futuha ta dan ja.

"Naji zan gyara. Zan sa a bincikamin wata ?ar aikin."

"Kuma kina da kudin biyanta?"

Shi ne tambayar da ta watsa mata kawai. Sai ta kara yin gum, ina ta ga kudin? Dama ai da bazar Yakubu take rawa amma yanzu ya maida ta bola, hatta da na cefane sai ya ga dama yake ba ta abin kirki. Haka suka yi ta tufka da warwararsu, suka zage Raihana akan yanda ta guje su kafin kuma su hau jajantawa kansu na irin daular da Humaira ke ciki wanda a tunaninsu su suka fi cancantarsa ba ita ba. Wannan shi ya yi sanadin da Tasleem ba ta bar gidan ba sai magriba bayan Futuha ta dafamusu Indomie sun ci. Sai da ta yi dakyar ma ta lallaSa Tasleem din ta taimaka suka dan rage ?azantar gidan da sunan ranar girkin Futuhar ne Yakubun zai zo. Ba ta damu da yin girki da shi ba domin ba ci yake ba, watara ya zo da filas na abincin da ?ar Snow ta girka masa wasu lokutan kuma Takeaway.

***
Ta dawo gidanta cike da kwarin gwuiwa da kuma wata irin nutsuwar da ba ta taSa tsintar kanta ciki ba tun bayan cafke Wizzy. Hankalinta ya kai ga wata ba?uwar mota a ajiye, ta Wan bita da kallo sai kuma ta yi tunanin watakila cikin abokan Yassar ne wani ya kawo mishi ziyara don haka ta karasa shigewa ciki inda su Waleed da Muhsin suka tarbe ta da murnar oyoyo. Mami ta yi murmushi tana Wan rungumesu. Yau daban take jinta.

"Oyoyo ?a?an Mami, ku bar ni haka toh kar ku kayar da ni."

"Mami! Mami! An sanya gado mai kyau da kujera da kafet har da labule a dakin Anna."

Jin maganar Muhsin ta yi kamar saukar aradu a tsakar kanta. Ta ji faduwar gaba. Ta dube shi.

"Kai Muhsin, bana son karya wane irin gyara kuma?"

"Lah, Allah kuwa Mami dagaske ne. Baba Amina ma tana can da wasu mutane suna cin abinci."

Ai sai ta ji kirjinta ya buga da karfi, Amina dai? Tare da wa toh? Dakyar ta iya jan ?afarta ta nufi tsohon Sangaren Anna a baya, kunnuwanta na dauko mata muryar Waleed na ihun fadin "Amarya ce wai dakin Amarya ce inji Baba Amina."

Ba ta iya juyowa ba dai wani sabon himma da ta ji da wani ja da ta ji tamkar ana mata da lantarki ta daWa sauri har sai da ta sadu da sashin Anna. Wani ?amshi ya soma bugar hancinta na turaren wuta mai Wankaran sanyinda dadi, babu wacce tuna da ta ji ?amshin face Fatima sai ko Jamila uwa ga Ummita waWanda ba su rabo da turarukan wuta haka.

Ta bankaWa labulen ta shiga, idanunta kuwa suka soma shiga na Amarya Hajiya Maijidda Mrs Isuhu Maiagogo. Ta yi kyau iya kyau cikin wani leshi uban ubansu kalar kore. An mishi aiki wanda ya yi kyau ya fiddo ta, fuskarta kuwa kwalliya ce sosai da ta fiddo fuskarta kai kace wata ?ar budurwa ce mai ?ananan shekaru. Koda dai dama Maijidda idan ka ganta ka kuma ga yaranta ba za ka ce ita ta haife su ba don jikinta bai nuna ba sai dai abin da ba za'a rasa na girma ba wanda ya zama dole.

"Maijidda! Uban me kike yi a gidana?!"

Ta fadi cikin mugun kaduwa da fita hayyaci don ?afafunta har kakkarwa suke yi. Baba Amina da yan uwan Anti Maijidda hudu dake zaune suka mike tsaye ganin ikon Allah, dama sun shiryawa hakan sun san za ta kaya tunda dai Abban bai sanar da ita komai ba.

Wani murmushi Anti Maijidda ta yi.

"Idan kin nutsu kin kwantar da hankalinki, shi wanda ya ajiyeki ya kuma ajiyeni a yanzu, zai sanar dake."

"Kina nufin ki cemin Yusuf ne ya ajiyeki? Aurarki ya yi ko kuwa me?"

Mami ke wannan tambayar domin jinta ta yi tamkar an zare mata dukkan wani laka na jiki. So take Maijidda ta ce a'a, duk da iskar fankar dake kaWawa bai hana gumi lulluSe ta ba.

Wayar Mamin ce ta yi ?ara, ba ta ko damu ba ballantana ta daga, Abba ne domin Baba Amina ta mishi text cewar ga Mamin a sashin Maijidda. Har ya katse ba ta Waga ba, ita kuwa Maijidda dariya ta yi kawai ta wuce zuwa daki.

"Ke Maijidda! Amina ku fadamin meke faruwa?! Yusuf wannan karuwar ya aura ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login