Showing 9001 words to 12000 words out of 189325 words

Chapter 4 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

195

a fili ga Suhaima, kin kasa Soyewa har sun harbo jirginki, ke ba ki iya kwantar da kai ba? Ai irinsu da sannu za ki shige mata har ta yarda dake ki zama aminiyarta, kika san wane Don Win za ki samu ta hanyarta? Ko kin mance cewa ubanta fa ya fi naki arziki, koda dai namun akwai sai ma?o." FaWin Futuha tana ?arashewa da murya a ?asa gudun kar ta yi shuka a idon makarwa. Suka kwashe da dariya, shiru Tasleem ta Wan yi sai kuma ta ce, "Ke kuma fa haka ne wallahi, don ba ki ga wani arnen gaye da ya taba zuwa wajenta a makarantar ba, wallahi ?arshen dai haWuwa ya haWu, ba wai kyawun fuska ba aa, motarsa ma kanta abin a kalla ce."
"Ahaf, to kin gani. Ai kinga kakarki ta yanke sa?a muddin ki ka samu irinsa. Bare ma yanzu da Abba ya yi sanyi da batun auren, da ace ban da Mami ta shawo kansa ya bari ai da yanzun mun haihu. TaS ni nasan da yarana biyu."
Suka yi dariya, hankalinsu ya koma ga ni?i-ni?in kayan da Ummita ta shigo da su daga bangaren Abba.
"Ke." Cewar Futuha. Ummita yarinya mai sanyi da hakuri, ta juyo ta kalle ta. Da yatsa ta nuna ledojin kafin ta ce.
"Wannan fa? Daga ina zuwa ina?"
Duk da tambayar ta rainin hankali ne, amma ta amsa, "Aiken Mami ne, ta ce a kai wa Humaira."
Daga haka ta ci gaba da tafiya, dukkan su ukun ba wacce ta tanka sai faman furzar da hucin Sacin rai da ba?in ciki. Can sai Tasleem ta ja tsaki tana ture kwanon da ta ci Wanwake da ?afa.
"Mami! Mami!! Wallahi ban taba ganin uwa irin tamu ba wacce ba ta damu da lamarin yaranta ba. Kunsan Allah, ba don kamanni da kuma Ann dake ?ara ba mu tabbacin cewa ita din mahaifiyarmu ce dagasken ba da zai yi wuya na yarda."
Cikin taSe baki Futuha ta amshe zancen.
"Uhum, kema dai kya fada. Ai shiyasa nake so mu samu mazan kece raini da za'a kalla a ?ara kalla. Ko ba komai za mu huta da ba?in cikin Abba da Mami."
Tsaki Tasleem ta ja ranta na zafi, sai dai ta kasa magana karshe kawai ta mike ba ta ko kara kallon kwanon ba kuma babu niyyar Waukewa. Bayan wucewarta kallon Futuha ya koma kan Raihana wacce ta maida hankalinta ga waya tana? murmushi.
"Ke kuma ke da wa? Mu gani."
Raihana kamar wacce aka tsikara ta mike tana ja baya da dariya.
"Toh sa ido, ina ruwanki da wayata?"
Futuha ta taSe baki.
"Kya ji da gulmarki dai, kullum latse-latsen waya, wayarki ta munafukai babu wanda kika taSa bari ya ga meke ciki. Ni ban san irinki ba, ko hoto za ki nunawa mutum sai dai ya kalla haka tana dunkule hannunki kamar wacce za'a sacewa."
Raihana na dariya ta yi hanyar waje gami da fadin.
"Eh Win dai, wasu ma ba a san me suke shukawa ba. Gwara ni ko failed ban taSa samu ba sai ku masu C.O."
Futuha ta yi kwafa kawai tana huci, zafi biyu ya haWe mata.
***
Murna sosai Humaira ta yi da wannan kyautar ban girman. Ta Waga wata riga ja mai adon fulawa ruwan madara tana mannawa a jikinta. Ha?ora a buWe ta dubi Ummita, "Kinga kamar Mami ta auna, daidai da ni."
Ummita ta yi dariya.
"Eh mana, sai ki sa hijabi su na falon Abba kiyi musu godiya. Kinsan Allah, Mami tana ban mamaki. Wai fa har cikawa ta yi da kudinta ta ?arasa yi maki siyayya, nidai ban taSa ganin mace mai kirkinta ba."
Humaira ta jinjina kai tana murmushi cike da gamsuwa da zantukan Ummita. Tabbas itama a farko ta yiwa Mamin gurguwar fahimta, amma yanzu kam ta ga saSanin tunaninta. Sai kuma da sauri ta dubi Ummita.
"Wai anya ban yi wauta ba? Kin ga ban je na gaida Anna ba tun da na zo."
Ummita ta Wan yi shiru alamar damuwa, har dai Humaira ta ce, "Lafiya kika yi shiru?" Girgiza kai ta yi.
"Anna fa ba ta wani murna da zuwanki, ta cewa Mami koda wasa kar ta sake ta turo ki Sangarenta. Ki share kawai, ni nasan Mami za ta shawo kanta, kuma tunda kuna tare a gidan dole watarana ku haWu ai. Zance ne kawai irin na Anna. Kinga jeki ki yiwa su Abban godiya mu wuce, yamma na yi." Humaira ta gyada kai kawai ta numfasa, dama ba dole ne kowa ya ?aunaceka ba. Ba tare da damuwa ba ta zura hijabin ta fice a Wakin. Humaira ta ware idanu tana ?arewa garin Kano kallo a hanyarsu ta komawa gida bayan sun kai wa telan Mami dinkunan an kuma auna ta, sosai akwai bambanci da inda ta fito koda dai dama ita din a ?auye take. Sai dai kuma hatta da titunan garin burgeta suke yi. Ummita ta kalleta ganin yanda gaba Waya hankalinta ke a waje, murmushi ta yi.

"Humaira kenan, idan dai garin nan ne har sai kin gaji da shi ina tabbatar maki."

Jin haka sai ta yi dariya.

"Anya kuwa? Nidai sosai ya burgeni wallahi. Ji nake tamkar kada mu koma gida."

Dariya Ummita itama ta Wan yi.

"Shiyasa ai na ce a bi da mu ta wannan hanyar ba ta farko ba, kinga sai ki ?ara kalle garin sosai ko?"

Jinjina kai Humaira ta yi tana murmushi sannan ta jefo mata tambaya.

"Ni kuwa yar uwa su Abba su nawa ne a wajen Umma? Umman na raye?"

"Umman su Abba tun ina firamare, yaranta uku kawai Allah ya ba ta daga nan ba ta ?ara haihuwa ba sai ko yaran ?an uwa da ta ri?e ta aurar. Kinga Abba shi ne babba sannan Babana, sai autar Wakinsu Baba Amina, ita a can gadon kaya take zaune da mijinta. Kuma Kakanmu wanda ya haifi Abba shi ya riga ma Umma rasuwa, ita kadai ce matarsa har ya bar duniya. Kar ki damu kedai, tun da kika zo garin nan babu gidan da ba zamu je ki ga ?an uwanki ba in sha Allahu."

Murmushi ya suSucewa Humaira har ta Wan lumshe idanu ta buWe su, ranta ya yi fari sol, burinta ya cika. Yadda ta san kaf ?an uwan Mamarta, yau Allah ya nufa za ta san na Abbanta. Haka suka karasa su na tafe Ummita na mata nuni da wuraren ?ayatarwa a garin.

***
? ?
Dattijuwar mace ce hakimce saman kujera ta haWe girar sama da ta ?asa. Banda tsufanta da ya fito muraran, kallo Waya idan ka yi mata za ka ga tsantsar kamannin da ta yi da Mami har ta so ta fi Mami hasken fata. Ta gyara zama gilashinta gami da amsa sallamar da Mami ta yi mata ciki-ciki. Anna sam ba ta iya Soye abin da ke ranta wannan ya sanya a kallo daya Mami ta gane fushi take da ita. Da harshen buzanci ta ce.

"Anna yanzu zancen nan ba zai wuce ba? Ina ce na yi maki bayanin komai?"

Anna da sai a sannan ta dubeta ta ba ta amsa cikin yare don ba kasafai take yin hausa ba, kaWan-kaWan take ji.

"Ki ka ce bayani? Yanzu ke har kina tunanin zan gamsu da bayananki na wofi Maryam? Kina da masaniyar irin
wahalar da aka ci a baya? Wato ke dadi miji ko?"

Mami gaba Waya ta dube ta fuskarta duk a jagule.

"Haba Anna, idan ban godewa bawan Allahn nan ba? bai kamata na watsa mishi ?asa a ido ba. Mutumin da ya amince na zauna tare da ku, muke rayuwa. Duk da irin son abin hannunsa, hakan bai sanya shi watsi da lamarinki ba. Duk wata kulawar da mai shekarunki ya dace ta samu, babu Waya da ya taSa nuna gajiyawarsa wajen yi. Toh mene ne aibu a ciki don Wiyarsa guda Waya ta zauna a hannuna?"

"Shashashar banza da wofi, dama nasan ba alheri ne zai fito a bakinki ba. Wato dai gori za ki yimin ko? Dama nasan akwai ranar ?in dillanci ai, dadin abin da baza? ta kike rawa. Shikenan zan sa maki ido na ga inda wannan rashin hankalin naki zai kai ki. Kin fi kowa sanin wahalar da aka sha a baya ai."

Mami dai ba ta ce komai ba, ta so a bar maganar a sanyo wata amma sam ba ta samu fuska wurin Anna ba dole haka ta mi?e ta kama hanyar barin Wakin, daidai ?ofa ta Wan dakata kafin ta juyo ta sakarwa Anna wani murmushi da ita kanta Anna ya ba ta Wumbin mamaki da ba?in ciki, to wannan sabon raini ne ya gifta tsakaninta da Maryam din ko kuwa dai kishi ya taSa kwakwalwarta tun a shekarun baya? Haka Anna ta cigaba da sa?e-sa?enta da babu mai warware mata.

***
? A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, har a yau Humaira ke cika sati uku cif a garin Kano. Abubuwa da dama sun faru na alheri a rayuwarta da suka rinjayi sharrukan ciki. ?aya daga ciki har da ?arin suturu da ta samu, sai kuwa gadonta da sif din kayanta da Abba ya sa aka yi mata. A gefe guda Abba ya mallaka mata wata ?aramar waya ?irar Vivo sai dai tana yin whatsapp, kuWin wayar dai dakyar suka? fito daga aljihun Abban nan ma sai da Mami ta sha fama har ta nuna Sacin rai ?arara, a duniya kuwa babu abin da Abba ya tsana kamar ganin Mami ta sauya mishi, nan da nan take cin galaba a ka sa muddin bu?atarta bai shallake tunaninsa ba.
? Ummita ta yi mata rakiya wurin dangin Abbansu na kusa, sun yi murna kwarai da ganinta. Sun kuma karSe ta da hannu bibbiyu, babu abin da ya fi faranta ran Humaira irin shaidar kirki da suka yiwa mahaifiyarta. Ta kuma ji dadin hakan ba kaWan ba. Rashin abin yi ne ya sa kusan koyaushe idan ba ta komai tana kan wayar tana danne-dannenta ganin ta ri?e abubuwan da Ummita ta koyamata tunda dai harshen turanci ne, ta kuma sani koda faransancin aka mayar ba za ta tsinci abin kirki ba. Abba ya sanya mata lambar Kawunta, sun gaisa sau Waya ta waya don ita kam ko whatsapp ma cewa Ummita tayi kada ta buWe mata, ba ta ga wanda za ta yi hira da shi ba. Ta dai gwammace ta kunna rediyo ta yi ta saurare don hatta da wa?o?i iri-iri na soyayya da Ummitan ta sanya mata ba ta damu da su ba.

? A wannan yammacin kamar koyaushe tana zaune a Wakinsu gefen gado ta buWe labule iska mai daWi na dukanta, garin wuni aka yi cikin zafi yanzu kuwa sai ya Wan huce. Rabin hankalinta yana ga farfajiyar gidan inda take hango Yassar tsaye da abokinsa wanda ta ji ana kira da Affan su na hira, a gefe Waya Muhsin ne da ball yana wasansa tare da Waleed, daidai nan Futuha ta buWe gidan ta shigo, dawowarta kenan daga makaranta, Humaira na lura Affan na mata magana ko kallonsa ba ta yi ba, daga yanayin tafiyarta za ka fahimci ba a nutse take ba, har ta gifta hankalin Humaira na kanta, ta san dai babu lafiya, tana kuma fatan ba gurguwar shawarar da ta ji jiyan wata aminiyarta Aina'u da ta zo tana ba ta ba shi ta gwada a yau Win, gabanta ya faWi. Ba ta mance kalaman da suka fito daga bakin Aina'un bayan Futuha ta gama amayar mata da damuwarta akan mahaukacin soyayyar da take yiwa Ibb Gusau.
"Ke ki na ban mamaki wallahi Futuha, ki na da kyawun da babu namijin da zai kalleki bai ?ara ba. Da ace ni ce ke, wallahi babu abin da zai hana na kai wa Ibb Gusau kaina. Kina da sura irin wadda da zarar kin tallata mishi kanki zai ji nan duniya babu wata sai ke. Ke idan ma wannan bai yi ba, ki zo na raka ki wurin Malam Aci Bulus, na rantse maki ko me kike so za ki samu. Ke wallahi sai kin mallaki malamin nan kin juya shi kamar waina a tanda."
Gaban Humaira ya yi wata iriyar faduwa, ta ambaci Allah a ranta, ta yi nisa da sa?e-sa?en zuci ta ji an banko ?ofar Wakin an shigo, ta juyo da sauri, Futuha ce. Ba ta ko lura da ita ba ta kife a saman gadon Tasleem tana kuka har da sheshshe?a. Humaira ta yi shiru, kafin ta lalubo abin faWi duk kuwa da cewar ba shiga sabgar juna suke yi ba, Tasleem ta shigo Wakin da sauri a bayanta kuma Raihana. Za ta soma magana amma idanunta na sauka kan Humaira ta fasa, cikin haWe rai ta ce.
? "Malama ba mu waje za mu yi magana." Jin haka tsam, Humaira ta mi?e ta kama hanyar barin Wakin, bayan fitarta Raihana ta karasa ta rufe ?ofar har da sanya mu?ulli sannan ta dawo. Futuha suka Wago su na magiyar ta sanar da su abin da ya faru. Dakyar ta iya tsaida hawayenta ta shiga ba su labari.

"Ai na faWamaku yadda muka yi da Aina ko?"

Suka gyaWa kai duk sun ?agu su ji komai.

"Shi ne..shi ne.."

Sai kuma ta yi shiru ta rasa me ma za ta ce. Tasleem ta zaro ido.

"Shi ne me Futuha? Kada dai ki cemin kin gwada aiwatarwa?"

Futuha ta runtse idanu gami da shafa gefen fuskarta tana kuka sosai. Sai a sannan idanunsu ya kai ga gefen fuskar, ya yi ja ya yi ruWu-ruWu alamun dai mari ta sha. Koda alama ma ba guda Waya ba.? Ba ta bari sun nemi ba'asi ba ta cigaba da maganarta.

"Na iske shi zaune a ofishinsa shi kaWai yana aiki a system, koda na shiga bai Waga kai ya kalle ni ba, daga motsawar leSSansa na gane ya amsa sallamata. Duk da cewa gabana na faduwa hakan bai sa nayi ?asa a gwuiwa ba na karasa ga teburinsa. Na sauke mayafina yanda rabin kirjina ya bayyana, na shagwabe murya ina mai batun ban gane abin da ya koyar a aji ba. Koda naga bai kalle ni ba, sai na yi gangancin kai hannu saman nasa, shi ne ya gaggauramin tagwayen maruka a kuncina. Ya kum rantse idan na ?ara shiga ofishinsa sai ya Salla ni kuma daga kaina masu tunani irin nawa za su dawo hayyacinsu."

Tana kaiwa nan ta ci gaba da kukanta. Tasleem da Raihana kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya. Raihana ta ja tsaki.

'Kema dai Futuha wataran kina abu kamar Waleed marar wayo wallahi. Ke kin manta tun farko itama Aina'un sonsa take yi wai? Ko don ta Sata ki a wurinsa ku yi biyu babu kinga ai za ta ba ki gurguwar shawara. Ai mun faWamaki amma ke idanunki ya rufe."

Tasleem ta amshe.

"Yanzu shikenan koda ace wannan mutumin na ganinki da mutunci kin Sarar da shi, yadda za'a yi ki gyara ma nikam ban sani ba. Kada dai garin gyaran a ?ara jagula abubuwan shi nake tsoro. Ke!!! Wai don uwaki shi kaWai ne namiji a duniya ma? Aikin banza kawai! Ga samari ?an kasuwa da ?an bokon su na matowa a kanki a instagram amma kin tsaya biyewa wani so, so, ke fa kike ban shawarar na shigewa Suhaima don na samu na yi mata koda snatching ne, amma ke nan kin tsaya Sata lokaci akan wani kuturu gurgu."

Jin haka ran Futuha ya Saci, ta harari Tasleem kafin ta ja tsaki.

"Da ace kun san mene so da duk baku Sata bakunanku ba. Sannan Ibb Gusau lafiyayyan mutum ne kar ki kara aibata shi. Tunda kuma ba ku da shawarar da za ku ban, ni nasan me zan yi."

Tana kai wa nan ta mi?e ta yaye mayafin ta faWa banWaki ba tare da ta amsawa Raihana da ke jefomata tambaya akan abin da za ta aikata ba.

***
? Mami ce tsaye a farfajiyar gidan ta haWa cikin atamfa ruwan ?asa mai adon fari, ta sha mayafi ruwan ?asa hakanan takalminta. Ta dai yi kyau ?arshe, idan ka kalle ta ba za ka ce ita ta haifi yaran ba saboda daidai gwargwado ta iya Waukar wanka. A gefenta Yassar ne su na magana yana ?orafin shi dai mota yake so tasan yadda zata yi Abba ya siya mishi. Mami jinsa kawai ta ke yi tana yi kuma tana duban gate, da ta gaji ta ja guntun tsaki.

"Wai ina Yakubu ya je ne? Daga jeka ka sha mai shikenan har yanzu bai dawo ba?"

Yassar ya taSe baki yana zura hannu a aljihun wandonsa.

"Mami ina magana ba ki amsamin ba, koda dai nasan wannan halin na Abba zai wahala ma ya siyamin. Amma fisabilillah ina Wan jami'a ina kallon abokaina har ma da matan da na raina su a makaranta su na da motocin kansu ni kuwa ko keke Abba ya kasa siyamin saboda mamma?o."

Ran Mami a Sace ta dube shi.

"Yassar ka shiga taitayinka, mahaifin naka kake yiwa waWannan kalaman marasa daWi? Toh ya yi maku mamma?on, kai ai namiji ne, namiji kuma da nema aka san shi. Guminsa ne ya gina wannan gidan, ya kuma mallaka mishi motocinsa, kai ma ka yi zuciya ka mayar da hankali a karatunka watarana ba Abbanku ba, da kanka sai ka siyawa kanka motar, ba na son shirme. Ni kiramin Yakubu a waya ka ce ya yi sauri ya ?araso, ina Humairar take ne..."

Ba ta ?arasa zancen ba ta waiga, Humaira na tsaye a gefensu kasancewar su na magana ba su ko lura da ita ba. Itama ta yi shirinta tsaf cikin atamfarta koriya wacce tana Waya daga cikin Winkunan da aka yi mata. Ta yi kyau sosai, murmushi ta Wan yiwa Mamin.

"Mami na fito ai."

Yassar ya ja tsaki ya bar wajen don takaicin Mamin da kuma na ganin Humairar da yake jin haushi da kishin tattalinta da iyayen nasu suke yi sai ka ce su ba ?a?a ba ne, Mami na kwala mishi kira amma bai ko waigo ba sai amsawar da ya yi da ?arfi.

"Zan je na Wau wayar ne na kiramaki Yakubun."

Daga haka ya ci gaba da tafiyarsa, Mami ta girgiza kai fuskarta Wauke da matsanancin damuwa. Sai jikin Humaira ya yi sanyi, wannan kalar zamantakewar mutanen gidan na ba ta mamaki, ace ?a?a ba sa ganin iyayensu da gashi, kowace magana ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login