Showing 78001 words to 81000 words out of 189325 words

Chapter 27 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

239

ma ta kasa fita sakamakon kukan da ya ci ?arfinta.

"What nonsense! Takardu da za a ce kawai sun Sata? Kar ki rainamin hankali mana!"

Daga yanayin yanda yake zancen ma ka san a ruWe ya ke. Cikin nutsuwa ta labarta mishi duk yadda komai ya faru har da batun cigiyar da aka sanya a jiya a gidajen rediyo da ma hotunan Humairar duk da ta Wora a media. Ta ?ara da faWin.

"Ka taimake ni Yaya Fadeel a nemo su, wallahi ba zan iya rayuwa ba idan babu su. Jinin jikina ne."

Idanunsa suka kaWa, ya ji wani ma?o?on abu ya tokare masa a ?irji, ga kansa da ya yi mugun sarawa, bai iya cewa komai ba ya datse kiran. Zama ya yi dabas a ?asa har lokacin yana ri?e da kansa da yake ciwo tamkar zai fashe. Ashe dagaske mafarkinsa ne zai tabbata? Humaira na cikin tashin hankali?

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Ya furta a fili. Kafin wayewar gari tarr jikinsa ya Wauki tsananin zafi, amma hakanan ya daure ya Waga wayar Ibb wanda shima ya ci karo da hoton Humaira dake yawo a media. Hankalin Ibb tashe ya ce.

"Fadeel ka ji labarin abin da ya faru da Humaira?"

Shiru ya kasa ba shi amsa sai wasu irin zafafan hawaye da suka kwaranyo saman fuskarsa. Ya runtse idanu, fatansa bai wuce ace mafarki yake yi ba, inama duk abin da yake ji yanzun a mafarkin ne.

"Fadeel, are you ok?"

Ibb ya ?ara tambayar jin ya yi shiru. A sannan ne ya soma magana dakyar ha?oransa har su na bugun juna saboda wani mugun sanyin da yake ji.

"No Ibrahim, i am not, Humaira rayuwata ce. Ibrahim ka taimakamin, ina tunanin mutuwa zan yi."

Yana kai wa nan ya ajiye wayar shi bai kashe ba, shi kuma bai ?ara sauraron abin da Ibb din zai faWi ba , yana ta faman Hello hello amma shiru kake ji.

Yana nan kwance ya dai ji shigowar Alhaji dakin amma daga nan bai ?ara sanin inda kansa yake ba. Alhaji wanda ya samu waya daga Ibb a gigice ya tallafo shi ya hau kiran sunansa, Anti Amarya itama faWowa ciki ta yi sanye da hijabinta har ?asa.

"Ya kamata a tafi asibiti."

Jin abin da ya fito daga bakin Anti Amarya ya ankarar da shi abin da ya kamata ace shi ya ya yi wannan hankalin. Ya ba ta umarnin ta sa a fiddo mota yayinda shi kuwa ya taimaka da kama Fadeel suka fita.

Murja da ta ji hayaniyarsu daga farfajiyar gidan ta fito daga Wakinta tana murza idanu daga ita sai riga da wando na bacci ko sallah ba ta yi ba. Suka yi karo da Anti Amarya da ta shigo sauya sutura don ta bi bayan su Alhajin a wata motar.

"Anti meke faruwa?"

"Fadeel ne ba lafiya."

Nan da nan ta ji tashin hankali, sai kuma ko me ta tuna kawai ta danne damuwarta. Wani abu ya tokare kirjinta kawai sai ta ce Allah ya ba shi lafiya, daga haka ta juya ta koma Wakinta fuskarnan kamar an aikomata da sa?on mutuwa. Sai da ta dubi ?ofar shigowa Wakin ta tabbatar babu mai tahowa kafin ta Wauki waya ta danna kira sau uku ba a Waga ba, ?arshe kawai sai ta aika da sa?o kamar haka.

*_Lokacin aiwatar da aikin ya yi. An tafi da shi asibiti yana cikin halin rashin lafiya kuma bana raba Wayan biyu a sanadinta ne._*

Iyakar abin da ta rubuta kenan a sa?on ta tura zuwa lambar da ta yi saving da suna BLANK. Ta koma ta zauna gefen gado tana murmushin da ita kaWai ta san ma'anarsa kafin ta ?ara fiddo wayarta ta lalubo sa?on da aminiyarta Saddy ta aikomata na labarin Satan Humaira da kuma hotuna. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta Waga yatsunta biyu a kan hoton Humaira gami da girgiza kai ta ce

"Good bye Humaira, daga yanzu kin fita daga rayuwar Fadeel, fita na har abada."

***
Ruwan sanyi ?arara aka she?a musu a fuska wannan ne ya yi sanadiyyar da firgigit suka farka daga baccin wahalar da ya kwashe su. Idan ka kalle su, ba za ka ce su ne wadannan ?anmatan Abban ba masu iya ado da kwalliya uwa uba kuma tsafta. Sun rame sun yi ba?i a kwanaki huWu kaWai da suka yi a wajen, ga fatar jikinsu da ya yi ruWu-ruWu saboda cizon sauro da ma cinnaku. Ummita fama take yi da mugun zazzaSi, ita kuwa Humaira a kwanakin amai kawai take kwararawa ga gudawa, gaba Waya sun zama wasu ?azamai na ?arfi da yaji. Suka kai duba ga wanda ya yi musu wannan aika-aikar, wannan dai azzalumin ne mai suna BadBoy. Ya ?araso ya ja Ummita kasancewar babu kuzari a jikinta kawai ta tafi luu, ya dakatar da ita ta hanyar tura ta da hannu ta faWi tim a saman busassan aman da Humaira ta yi. Ya fisgo hannunta ta koma ta zauna kafin ya sa ba?in kyalle ya tamke mata idanu. Humaira da ta kasa koda Waga yatsa sakamakon galabaitar da ta yi na amai da gudawa ya koma kanta, ya toshe hanci jin ?arni da warin dake tashi a jikinta, mari ya kifa mata.

"Don ubanki ke wace iriyar ?azama ce da ba za ki shiga banWaki ba. An faWamaki nan gidan gyatuminki ne da za ki yi mana kashi a wuri? Za ku wa ki raina kanki."

Ya fisgota itama ya ?ullemata idanun. Daidai nan Wizzy ya Wan le?o da kai yana mai zu?ar sigari.

"Wai ya ne? Ka tattaro su mu bar nan."

Daga haka ya titsa ?eyarsu Wizzy na kundumawa Humaira ashar ganin yadda ta yi kace-kace sai tashin hamami take yi. Ya rantse ba za su shiga motarsu a haka da ita ba. Wannan ya sa anan suka Wauki ledar kayan Raihana dake hannunsu a falon gidan suka dam?amusu a hannu.

"Ku sauya kayan kar ku kuskura ku gwada wani motsi idan ba haka ba sai na ciremaku kai da wu?arnan." Daga gargadin da ya fito a bakin Wizzy, sai Badboy ya tura Humaira banWakin da ke falon wanda ya fi na Wakin da suke ciki kyau shi har da ruwa a ?aton bokiti. Idanunta ya kunce mata sannan ya fice ya tura ?ofar. Humaira dakyar ta Waga rigar da suka bata, doguwar rigar Raihana ce na atamfa sai Wankwali. Kuka ya kufcemata da wani irin kewarta. Ba ita ta iya saiya kayan ba sai da Badboy ya bugamata ?ofa da ?arfi ya na zaginta akan ta yi sauri, wannan dalilin ya sa cikin rawar jiki ta shiga rage kayan dake jikinta, ta Wan watsawa kanta ruwa a gaggauce har da Wora alwala sannan ta sa kayan ta fito. Itama Ummita hakan ta yi duk kuwa da cewa ga zazzaSi a jikinta, amma tana bu?atar tsaftar jikinta ko yaya ko don sallah. Itama dai kayan Raihanar ce riga da siket ?an kanti.

Wizzy ya kallesu su biyun yana mai haWiyar yawu ma?wat. Shakka babu sun kai a kira su ?anmatan da za a nuna, ban da ma ba?ar wahalar da suka ci ai ya sani sun haWu ne ?arshe musamman Humaira da ya kasa Wauke idanu a kanta. Sa?e-sa?en dake ransa, hakan ne a na Badboy wannan ta sanya shi duban Wizzy.

"Ga nama amma babu damar ci."

Wizzy ya busar da haya?i gami da yin wani shu'umin murmushi.

"Akwai ranar ?in dillanci. Yanzu dai mu yi ha?uri mu ci miliyoyin kuWaWen nan idan ya so ko mene ne sai a yi."

Badboy ya jinjina kai, ya ?ulle idanun su Humaira wadanda duk iyakar kalle-kallensu sun kasa gane inda suke. Wizzy ne ya soma fita ya Wan duba wuri sannan ya ba Babba dake gaban mota umarnin tayarwa daga haka ya sa Badboy fitowa da su Humaira suka tura su cikin motar mai ba?a?en gilasai suka bar wurin da gudun gaske.

***
Fadeel wanda likitoci suka du?ufa a kansa dakyar cikin taimakon Allah suka samu ya dawo hayyacinsa. Sai dai har lokacin zazzaSinsa bai sauka ba wannan ta sa suka yi mishi allurai suka Wora masa ruwan drip ganin gaba Waya jikinsa babu kwari saboda aman da ya yi mai yawa bayan farkawarsa.
Ganin ya kasa nutsuwa sai kokarin mi?ewa yake yi yana cewa zai je neman Humaira hankulan Alhaji da Ibb wanda tuni ya iso suka tashi, Likita dole ya yi mishi allurar da zai sanya shi bacci.
Bayan fitarsa Alhaji ya dubi Ibb.

"Wai meke faruwa ne? Me ya samu Humairar?"

Ibb ya sanar da Alhajin labarin Satan su Humaira. Shi kansa ya jinjina lamarin. Shi tun daga sadda Fadeel ya ce mishi zai yi jiran Humairar ya fahimci irin zurfin da ya yi a kaunarta.

"Toh ban da abin Fadeel, ai ba sanyawa zuciyarsa damuwa ya haifar mishi da ciwo ne mafita ba, mafitar ita ce a yi addu'a sannan a ?ara magana da hukuma don ganin an ?arfafa bincike."

Ibb ya jinjina kai.

"Hakane."

Suna nan zaune Daddy ya iso tare da Maman Ibb. Anan suke jin silar ciwon, shi ma dai irin hangen Alhajin ya yi. Daga nan ya ce Ibb ya yi mishi rakiya zuwa gidan su Humairar. Shi ma Alhajin ya bi su yayinda Mama da Anti Amarya wacce ta iso lokaci guda da Fu'ad suka zauna anan asibitin.

***
Abba bai yi mamakin ji daga ?asim cewa ya yi ba?i ba domin tun faruwar lamarin yake ta samun ba?i daga kan ?an uwa har abokan hulWa. ?azun ba jimawa ?an uwan Maman Ummita na Bichi suka iso su ma.
Falonnasa na saukar ba?i ya shiga. Daddy da Alhaji suka mi?e aka yi musabaha da Abba sannan duk aka zauna shima Ibb ya gaida shi. Daga nan kuma Daddy ya gabatar da kansu matsayin iyayen Fadeel yaron wajensu dake neman auren Humaira. Abba ya ji zancen banbarakwai, Alhaji kuma sanin da ya yi cewa Fadeel bai bi maganarsa ba na gabatar da kai ga Abban yasa shi fahimtar komai. Nan ya yiwa Abban bayani cewa ai yaron nasu bai kai ga zuwa wurinsa ba. Abba ya Wan saki fuska, watakila dai shiyasa Humairar aka ce ba ta kula kowa, kenan tana da wanda ta ke so. Nan kuma aka shiga jajanta batun Satan su Humairar, Abba ya ?ara ba su labari daidai sadda Raihana ta zo kawo ruwa kamar yadda ?asim ya shaida mata sa?on Abban. Ta shigo da zumSulelan hijabi idanunta duk a kumbure, gaishe su ta yi. Abba ya bita da kallon tausayawa, sai a kwanakin nan ne ta soma magana amma tun bayan faruwar lamarin ta zama ?ar kallo. Suka amsa gaisuwarta, jin Ibb ya kira sunanta gami da jajanta mata ne ya sanya Abba kuma yarda dagaske dai akwai sanayya tsakanin Humaira da wanda suka kira da Fadeel.

"Ina Yaya Fadeel?" Ta furta tana duban Ibb don tun wayarsu take ta neman layinsa yana ?ara ba a Wagawa. Ya sanar mata da yana asibiti, tausayinsa ya kamata, ta yi fatan Allah ya ba shi lafiya suka amsa da amin daga haka ta mike ta koma ciki.

Daddy a take ya yi kiran Commisioner na ?an sanda wanda ya kasance abokinsa ya shaida mishi batun Satan su Humaira, nan ya ce ya san da maganar. Ya ?ara ro?onsa akan a tsaurara bincike ko Allah zai sa a dace. Daga haka suka yi sallama, suka yiwa Abba bankwana da zummar za su dawo, shima Abban ya tabbatar musu zuwa anjima zai shiga duba Fadeel.

***
Raihana ta ci karo da Mami a falo, Mami ta ce.

"Su waye ba?in?"

?an murmushin dole Raihana ta yi.

"Iyayen Yaya Fadeel ne wanda ke son auren Humaira suka zo jajantawa Abba. Shima yana asibiti ba lafiya."

Daga haka ta yi gaba ta bar Mamin a tsaye shiru. Sai kuma can ta ankara ta kai duba ga mutanen dake falon, ?an uwan mahaifiyar Ummita ne da suka iso daga Bichi sai kuwa yan uwan Abba zaune ana ta jajantawa waWanda wasunsu a cikin magana suke watsawa Mami habaici da ba?ar magana. A ganinsu wannan ba tsautsayi bane, akwai lauje cikin naWi. Juyawa ta yi ta shige Wakinta da sauri ta rufe da mu?ulli.

***
A wannan daren sai ga waya daga kidnappers din Humaira kai tsaye Abba suka kira. Ya Waga ba tare da sanin ko su waye ba, lokacin su na tare da makwaftansa da wasu cikin yan uwansa maza ana zaune.

"Da Alhaji Yusuf muke magana?"

Abba ya amsa da sauri.

"Eh, ni ne."

"SharaWi na farko, idan a cikin mutane ka ke ka tashi ka bar wajen. Ko da alama kar ka nuna wani abu da zai sa a fahimci wani abu a saman fuskarka. Ka tashi maza ka koma Waki muddin kana son yaranka su tsira da rai da lafiyarsu."

Jin haka Abba ya mi?e gabansa na dukan tara-tara, wannan kiran yake addu'ar ji don ya shirya salwantar da duk abin da ya mallaka matu?ar su Humaira za su dawo gida cikin aminci. Hanyar Waki ya nufa ba tare da ya da kowa komai ba suka bishi da idanu kawai. Muryarsa har tana rawa ya ce.

"N..a.na..matsa. Ni kadai ne a Waki."

Wata shu'umar dariya aka saki da ?arfi sannan aka ce.

"Dakyau! Ka buWe kunnenka ka saurare mu dakyau! Kana da nan da awanni arba'in da takwas ka kawo kuWin fansar yaranka miliyan biyar muddin kana son su ?ara sha?ar numfashi a duniya. Idan kuwa ka yi gangancin furtawa ?an sanda wannan zancen toh shakka babu sunan msu matattu. Kar ka manta muna sane da komai dake gudana a nan. Idan kunne ya ji toh jiki ya tsira."

Abba da tuni hawaye sun wanke mishi fuska yana shirin magana ya ji sun daka tsawa.

"Don ubanku nace ku yi magana da Babanku! Ku tabbatar masa kuna hannunmu!"

Sai kuma ji ya yi muryar Ummita ta zabga uban ihu, sai Humaira mai kiran sunan Abba da iyakar muryarta. Da alama dai wani ba?ar muguntar aka yi musu.

Abba ya mi?e tsaye yana fadin.

"Ummita! Humaira! Ku yi hakuri don Allah kar ku cutarmin da ?a?a, in sha Allah zan ?o?arta cika umarninku."

Jin haka sai aka she?e da wata iriyar dariya daga Waya Sangaren sannan aka ce.

"Idan ka yi hakan ka taimaki kanka da kuma su. Ka kiyaye sharuWWanmu ko kuma ka yi dana sanin abin da zai biyo baya!"

Abba kuka yake sosai ya amsa da toh, aka datse layin kiran. Har lokacin bai bar rawar jiki da kuka ba, muryoyin yaransa na mishi amsa kuwwa a cikin kunne, ya rasa me zai yi, mene ne mafita? Ga shi nan dai an hana shi yin furucin ga ?an sanda dole haka za su yi shiru da iyalinsa su tattauna a haWa kudaden a biya kudin fansa.
***
A can kuwa, Wizzy yana kammala magana da Abba ya fidda layin a wayarsa ya kakkarya ya zubar, lokaci guda kuma ya mayar da layinsa. Suka dubi juna suka kwashe da muguwar dariya. Humaira da Ummita aka titsa ?eyarsu zuwa cikin Wakin. Babu laifi wajen da suka sauya ya fi wancan kyau, komai tsaf sai ?ura kuma ga dukkan alamu sabon gida ne da ba a kammala aikinsa ba. BanWakin akwai ruwa har da butar alwala. Wajen dai ya fiye musu Wayan amma kuma hankulansu ba a kwance suke ba. Ai babu wani gata da za a yi musu alhalin su na hannun azzalumai abin ya yi musu daWi su samu kwanciyar hankali. Daga Ummita har Humaira tun sadda aka gar?ame su a Wakin ba sa aikin komai sai kuka hakan na da nasaba da jin muryar Abba da suka yi wanda gaba Waya sun fitar da ran ?ara ji ko ganin wani cikin fuskokin da suka sani.

Wizzy kuwa bayan dawowar Badboy daga rufe ?ofar ya dube su ya ce.

"Aski fa idan ya zo gaban goshi ya fi zafi, wannan lokaci ne da zamu ?ara zage damtse kuma mu yi takatsantsan don cik umarninta, a ?arshe mu ma mu kwashi rabonmu, ta sallame mu."

Babba wanda ke faman hura hanci yana fitar da huci ya soma magana a kausashe.

"Wai ni fa bana son rainin hankalin da take yi mana! Matar nan tun da ta bamu aiki ba ta yarda ayi waya da uta sai rubutun sa?o. Ita ba ta san hatsarin da ke tattare da hakan ba? Idan fa ta yi sakaci har wani ya yi ya gani to fa akwai matsala. Sannan ta ?i ta bayyana kanta sai Wan aiken da ta ke turowa, ita kenan ko kama mu za a yi ta tsira kenan? Ba mu san wace ce ba, kuma ba mu san komai a kai ba, namu kawai aiwatarwa idan an cafke mu ta ci bulus kenan?!"

Wizzy ya Waure fuska bai ce komai ba, ganin haka Badboy ya cafe.

"Kai Babba ka iya kalamanka, ka sani koda wasa idan har ba mu ne muka so ba, toh fa ba za mu taSa kamuwa ba. Mun fi ta iya shege ai kai ka sani. Ni fa duk ba wannan ne damuwata ba, yarannan su na hargitsa lissafina amma kai Oga ka ?i bani damar gwangwajewa. Kenan haka muna ji muna kallo za mu bar su shikenan sun sha?"

Sai a sannan Wizzy ya kalle shi.

"Ba wannan aka umarcemu? da yi ba, asalima don horo ne ya sanya muka kai su tsohon gidan gonar can don kawai su shiha taitayinsu amma tun farko ba ya daga cikin bajat dinmu. Kai ne ka fiye garaje, ai na ce maka akwai lokacin da hakan za ta kasance, mu bari mana har mu samu tabbacin kuWaWen nan za su faWo hannunmu tukunna mana, sai mu yi duk abin da muka ga zamu iya. Mu dai tabbatar ba mu kashe su ba don ba shi aka sanya mu ba."

Suka yi shiru babu wanda ya tanka masa musamman Badboy da ke jin ha?urinsa na dab da ?arewa akan ?anmatan musamman Humaira da surarta ke fisgarta.

***
? Hankalin Anti Maijidda (babbar yayar mahaifiyar Ummita ta Bichi) a tashe ta shigo babban falon na Mami da jama'a ke zaune ana jajanta wannan lamari na su Humaira. Ba ta ?asar gaba daya ta je Umarah sai a jiya ta diro Kanon, ko gida ba ta je ba kai tsaye ta ce a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login