Showing 84001 words to 87000 words out of 189325 words

Chapter 29 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

235

na ba ka kenan Abban yara, sai kuma naji dadi da ka kasance mai yarda da ?addara. Siyar da gidan zai fiye mana alheri matu?ar dai za su bar yaranmu su dawo garemu."

Abba ya jinjina kai.

"Hakane Maryam, dama na riga da na yi magana da lauyana, na kuma bada damar an sa gidannan a kasuwa, ina ta tunanin ta yadda zan sanar maki kada ki ji abin daga sama shi..."

"Haba Abban yara, wace irin magana kake yi ne? Mene ne ciki don ka sadaukar da abin da yake mallakinka don fansar yarana? Idan da ace yau nima na mallaki wata dukiya kana tunanin ba zan iya sadaukar da ita domin ceto ransu ba? Don Allah kada ka sa naji kamar kana bambanta Humaira da Ummita da yan uwansu."

Tun faruwar al'amarin na su Humaira, Abba bai yi koda murmushi ba sai a yanzun, ya kamo hannun Mami ya ri?e gam cikin nashi.

"Ina kaunarki Maryam, Allah ya yi maki albarka. Nagode da kika fahimce ni."

Itama murmushinta ta faWaWa gami da shafar gefen fuskarsa.

"Nima ina kaunarka. Yanzu ajiye godiyarnan, ka daure ka sa abu a cikinka sai a je a san ya za'a yi. Ina fatan dai ba ka faWawa? D.P.O yadda ku ka yi ba ko?"

Abba har ya buWe baki zai magana sai ya tuna yadda suka yi da D.P.O da safe. Sun tattauna ya sanar da shi komai bai rufe ba akan batun kuWaWen fansa da aka nema.

*_Koda wasa YallaSai kar ka nunawa kowa ka faWamin yadda ake ciki. Komai kusancinka da mutum, ka Soye wannan tattaunawarmu saboda mutane su na da ban tsoro, koda ace ka faWawa wanda ka yarda da shi yadda muka yi, to fa zai iya sanar da wani ma?iyin. Kaf duniya tun da dai daga ni sai Alhaji Bashir (Daddy) muka san da hakan, to ya tsaya iyakar nan, koda ace sun ?ara kiranka a waya kar ka bari wani cikin iyalinka ko ma waje ya sani.? Mu kuma zamu yi iyakar yin mu, mu yi kokari mu cafke su duk sadda ka tashi kai musu kuWin._*

"Ya naji ka yi shiru?"

Mami ta nemi sani tana mai ?uramasa idanu. Ya numfasa.

"Babu komai Maryam. Ina tsoron na furta masa su ji labari tunda sun gargaWe ni. Bana fatan a samu matsalar da yarannan za su rasa rayukansu."

Ta jinjina kai.

"Ina ji a jikina za su dawo gida cikin aminci."

Daga haka ta jawo kayan abinci ta shiga zubamasa tana mai lallaSa shi don ya ci. Dakyar ya tsakuri kaWan ya mi?e ya yi shiri ya fita don ganin ya kammala kafin ya kai.

Cikin rashin nasara, aka rasa mai siyan gidan Abba, a karshe dai tayin da ya ?i karSa a farko na iyayen Fadeel hakanan ya karSi cikon miliyan huWu ya haWa aka tashi kuWin fansa, babu abin da ya rage sai jiran waya daga kidnappers don a ji lokaci da kuma wurin da za a mi?a kuWin. Mami ba ta san ya aka yi da batun gida ba, Abba dai ya ce mata an samu an haWa kudade. Daga nan bai ?ara ko harafin A ba.

***
Humaira da Ummita na rakuSe a lungu guda na Wakin sun yi shiru don zuwa lokacin kukan ma ya ?i fita, aka banko ?ofar Wakin aka shigo. Su ukun dai da suka zame musu tamkar ba?a?en kumurci su ne suka shigo. Suka ?ura musu idanu tamkar za su lashe su, Wizzy kamar koyaushe sigari ne a hannunsa, ya fesar da haya?in ya dubi Babba da Badboy cikin murmushi ya ce.
? "Ni zan fara, ku kuma sai ku biyo baya."

Ba su ji dadin wannan hukuncin ba amma babu yadda suka iya, hakanan suka lashi lebbansu suka ja gefe. Shi kuwa kai tsaye ya ?arasa ya finciko Ummita wacce ta ?an?ame jiki guri guda ga jikinta dake masifar rawa.

"Ina za ku kai ta? Ku yiwa girman Allah ku yi hakuri."

Humaira ke zancen cikin ruWu da tashin hankali. Suka kwashe da dariya.

"Haba Baby, kema ai zan zo kanki. Duk inda zan kai ?ar uwarki kema za ki je. KuWin fansarku aka kawo, za a tafi da ku gida."

Humaira sam zancen bai shige ta ba balle Ummita da ba ta san lokacin da ta shiga kuka sosai ba, su na jan ta tana tirjewa, Humaira na zabga uban ihu suka dauke ta da mari suka fidda kyalle suka rufemata baki da idanu. Wizzy haka ya ja Ummita har sai da ya dangana ta da wani Wakin.

Humaira da suka fita suka rufe kamar ta yi hauka haka ta dinga bugun ?ofar tana gurnani tamkar wacce ake? zarewa rai. Babban fatanta bai wuce su ceto Ummita da ko ihunta ba a ji ba sakamakon rufemata baki da aka yi da kyalle.

Ummita na ji tana gani Wizzy ya keta alfarmarta. Tsananin azaba ya sanya ta sumewa ba tare da sanin inda kanta yake ba. Shi kuwa ya fito yana sharSar gumi, ya dubi su Badboy cikin annashuwa ya ce.

"Ku bari shegiyar ta farfaWo sai ku ?ara farr mata, suman dadi ta yi."

Suka kwashe da muguwar dariya. Yana kai wa nan ya shige wurin Humaira.

Tana ji an bude ?ofar ta yi saurin karasawa gami da sha?e wuyan rigar Wizzy tana um um saboda bakinta da ke ?ulle ta ma kasa magana. Ya yi dariya gami da tura ?ofar da ?afarsa ta baya ya dam?e hannunta.

"Haba my love? Kokawarnan da kike wani sanyamin ?arfi ai sai ki jigatar da kanki tun ma ba a je ko'ina ba."

Daga nan ya soma kiciniyar raba ta da kayanta yana taSa wasu Sangare na jikinta, nan da nan ta ji kanta ya soma wani irin sarawa, wani irin ba?in ciki da ba ta za ta iya kimantawa ba ya tsaya mata cak a ?ahon zuci. A sadda Wizzy ya yi nasarar keta rigar dake jikinta, a lokacin ne gaba Waya tsikokin jikinta suka mimmi?e. Idanunta suka ?ara turuwa suka yi ja, ba ta san lokacin da ta sha?o wuyansa ba har ya shiga kakarin mutuwa. Duk iya ?arfin da ya sa da zummar ?watar kansa ya kasa, ga shi ba damar ihu saboda koda ya yi abokan aikinnasa za su yi zaton na lafiya ne. Haka suka ?arasa har jikin ?ofar da ba ta rufe gaba Waya ba.

Anan ne Badboy da ke zaune saitin ?ofar ya hangi hannun Wizzy na lilo, da wani irin gudu-gudu ya tunkari ?ofar, shima Babba ya mara mishi baya. Da?yar suka tura ?ofar ta buWe. Abin da suka gani ya yi mugun rikita su, Humaira dai ta zame musu tamkar wata ?a??arfar damisa, da?yar da suWin goshi suka ?wace Wizzy a hannunta, Babba ya fice da shi daga dakin yayinda Badboy ya tunkareta da niyyar kifamata mari sai dai yanayin da ya ga ta taso ta yi kansa ne ya sa shi ficewa babu shiri. Nan ta kife zaune tana rirri?e kanta dake azabar sarawa tana huci ga uban gumi kuma ga baki a ?ulle. Kukan nan da ta saba yi ta shiga rerawa mai mugun tsuma zuciya, ta fi rabin awa a haka har ba ta san an shigo da Ummita an watsa ta a kusa da ita ba.
? Abin da Humaira ta aikata ne ya sanya Wizzy dakatar da su daga ketawa Ummita haddi, ya ce su kyale su kafin su kashe su labari ya sauya tunda gobe za su cafki kuWadensu. Da wannan suka rufe su gam suka bar gidan su Babba da Badboy na Wacin ran ganin samu da kuma rashi lokaci guda. Ganin haka Wizzy ya yi musu al?awarin zai ba su sabuwar yarinyarsa da ya yi a wurin mashayarsu kowannensu ya more da ita, sun Wan ji dadin hakan tunda ko ba komai ita bariki ke yayi a lokacin. Kowa kuma mararinta yake.

Ummita da har lokacin ba ta da kuzari, kusan ma yanzun suman zaune ta yi. Ga uban azaba da ta ke ji a ?asanta, gaba Waya hawayenta ya kafe ta ma kasa koda kukan, tun shigo da ita abu Waya ne a bakinta take furtawa sanadiyyar ?yallen da aka ciremata, Innalillahi kawai take ambato daga farko har ?arshe, wannan daren babu wanda ya runtsa sai Humaira da bayan gama koke-koken wani bacci marar dalili ya Wauketa kamar yadda ta saba.

***
A firgice Raihana ta farka daga mummunan mafarkin da ta yi wai an soka wu?a a wuyan Ummita, Humaira kuma tana kwance cikin jini. Wani ?ara ta saki mai firgitarwa ta zabura ta mi?e daga gadon Mami ta nufi hanyar fita daga Wakin. A hanyar ?ofa ta ci karo da Mami kasncewae asuba ta kawo kai, Abba ya fita masallaci. Cikin tsananin ruWani Mami ta ri?e ta.

"Meyafaru Raihana?"

Ta ru?un?ume Mamin sai kawai ta fashe da kuka mai tsanani. Mami ba ta ce mata komai ba ta shiga shafar kanta. Don kanta Raihanar ta sassauta kukan sannan ta Wago kai ta ce.

"Mami nayi mafarki marar daWi akan su Humaira. Har yanzu ba su kira Abba a waya ba? Mami a kai kuWaWennan a dawomin da ?an uwana yanzu kafin lokaci ya ?ure. Kar su kashemin su."

Mami ta ri?e hannuwanta.

"Kar ki damu da mafarkin da ba lallai ya kasance gaskiya ba. Ki yi addu'a da fatan alheri. Ina mai tabbatar maki babu abin da zai faru da su, lafiya kalau za su dawo gidannan ki gan su."

Raihana ta Wauki maganganun Mami kawai don ta kwantar mata da hankali ta faWi, amma ina da ta ke da tabbacin ganin ?an uwannata cikin kwanciyar hankali? Haka dai ta dinga lallaSa ta ?arshe ta samu nutsuwa ta fice ta Wora alwala ta tayar da sallah amma har sannan kirjinta na dukan tara tara. Wannan dalilin ne ya sanya ta tsaya ta yi addu'a sosai har ta jawo Al?ur'ani ta karanta ta ro?arwa yan uwanta tsari daga sharrin dukkan masu sharri.

***
?arfe shida na safe daidai sai ga kiran Wizzy ya shigo wayar Abba.? Abba ya Waga jiki na rawa. Nan yake tambayar ko kuWaden sun samu, ya amsa da eh. Daga nan ya yi mishi kwatancen inda za su haWu, ya ?ara da faWin.

"Ina ?ara gargaWinka, kar ka sake ka yi kuskuren zuwa da jami'an tsaro idan ba haka ba a gabanka zan yanka wuyan ?a?anka."

Abba ya hau girgiza kai tamkar Wizzy na gabansa.

"Aa aa, ni kadai zan zo. Ba zan saSa al?awarinku ba."

Daga nan kit aka kashe wayar, ya Waga kai ya dubi lokaci, yanzun shida da mintuna, an kuma ce mishi bakwai daidai ya isa wannan dalilin ne ya sanya shi mi?ewa ba shiri ya janyo jakar kuWaWen. Tunanin ya kira D.P.O ya sanar masa yake amma kuma yana jin tsoron kar su cutar da su Humaira sai dai ya Wan yi shahada ya dannawa D.P.O kira, suna cikin magana Mami ta iso, Abba bai ko lura da ita ba don hankalinsa ya yi gaba. D.P.O ya ce za su fito su ma cikin kayan gida da kuma motar da ba ta aiki ba, ya kwantarwa da Abban hankali ya nunamasa kar ya damu su Humaira za su kuSuta a hannun ko ma su waye.

Mami ta dubi Abban a rikice bayan ya gama wayarsa.

"Abban yara sun kiraka ne naji kana sanar da D.P.O?"

Bai kalle ta ba ya ja akwatin jiki na tsuma ya ce.

"Eh Maryama mun yi waya da su. Bari naje kar lokacin ya ?ure mintuna kawai suka ba ni."

Mami ta sha gabansa.

"Meyasa za ka yi ganganci da rayuwar yarana? Mene dalilin sanar da D.P.O? Ba ka tsoron su cutarmin da su?"

Sai ta fashe da kuka jikinta babu inda ba ya rawa.

Abba bai da lokacin rarrashinta sai kawai ya ce.

"Kiyi hakuri, babu abin da zai faru da su lafiya kalau zan maidomaki su in sha Allahu. Ku sanya ni addu'a har na dawo dai."

Yana kaiwa nan ya fice ri?e da mu?ullin motar Jannat da Mamin ta aro masa tun jiya an kuma zuba mai dama jiran su kira kawai ake. Tasleem dake laSe ta yi baya da sauri zuwa dakin Anna jikinta har tsuma yake.


Abba yana hanya ma sai ga kiran Fadeel, Abban ya kwantar masa da hankali ya ce sun yi waya yanzun yana hanyar fita amsar su. Ya tambayi Abban inda suka ce, kamar ba zai faWi ba sai dai ya faWamasa. Fadeel ya ce zai biyo bayansa. Dakyar Abban ya hana shi gudun samun matsala.

***
? Bakwai da mintuna uku Abba ya iso dab da kogin da suka yi masa umarni. Yana tsayuwa ya ji wayarsa na ringing. Jiki na rawa ya fiddo ya Waga.

"Mun ganka, ka fito da jakar ka ajiye gefen wannan kogin, mu kuma za mu turomaka yaranka. Ba ruwanka da kalle-kalle, ka saukar da kanka ?asa har ka ajiye ka bar wurin."

"Toh."

Yana faWin haka a gaggauce ya ja jakar ya fita.? Bisa bin umarnin nasu kansa yana ?asa amma fa ta ?an maza kawai yake sai dai zuciyarsa na ta harbawa da ?arfi. Sunayen Allah ya shiga ambato da fatan samun matsaya.

Wizzy kuwa da suke can gefe ?asan wata ?atuwar bishiya, su na ganin fitar Abban ya sanya Badboy da Babba cicciSar su Humaira da suka ba su kwayoyi suke ba a cikin hayyacinsu ba suka nufi motar Abban da nufin sanya su ciki. Kiran da Wizzy ya samj ne game da batun zuwan ?an sanda wurin ya sanya shi fitowa gami da dakawa su Badboy tsawa.

"Ku dawo da su mu bar nan! Shegen ya kira ?an sanda!"

Jin haka sai kuwa aka soma harbi, dayake Allah ba azzalumin bayinSa ba, sai kawai suka yashe su a wurin sakamakon harbin da aka yiwa Badboy a kafaWa ya saki ?ara,? da gudu suka koma cikin motar kiii suka tayar suka soma yunkurin barin wajen.

Abba da sai kawai maganganu ya ji da ?arar harbi bai san sadda ya juya ba a ruWe hantar cikinsa na kaWawa don ya gama sadda?arwa su Ummita aka harba. Sai dai ganinsu a yashe a tsakar filin ya sa shi sakin jakar kuWin ya nufe su da gudun da a shekarunsa bai san ma zai iya ba. Su Wizzy tuni sun bar nan su na cizon yatsar wannan babbar asarar da suka yi. Yayinda D.P.O da mutanensa suka ?araso cikin jin zafin kubcewar da suka yi musu.

"YallaSai ba kuka ya kamata ka yi, kamata ya yi mu mi?a su asibiti."
Jin haka sai Abban ya ji kamar an masa tuni, ya Waga Humaira, macen ?ar sandar da ta biyo su ta Waga Ummita suka sanya su a mota sai asibiti. Jakar kuWaWen kuma yana cikin motar ?an sandan suka mara musu baya. Fadeel da ya kasa ha?uri ya biyo bayan Abban, kafin ya kai ga ?arasawa ya hango Abba a mota kawai sai ya yi reverse ya bi bayansu jikinsa babu inda ba ya kaWawa. Yana son ya kira Abban don jin ko an same su amma yana tsoron jin akasin haka daga gareshi wannan ne ya hana shi kiran gaba Waya.
***
Murja ta jima tsaye jikin tagar falo tana hangen fitar Fadeel a gigice. Ranta idan ya yi dubu toh ya Saci. Hankalinta kuwa idan akwai abin da ya fi gaban tashi toh ta ya yi wannan dalilin ne ya sanya ta komawa cikin daki da sauri-sauri ta Wauko gyalenta sai ko waya da jaka ta fice daga gidan a birkice har Anti Amarya wacce ta fito daga nata Wakin tana tambayar ko lafiya kuma ina za ta je amma babu amsa.

***
Kasancewar tare suka isa asibitin da ?an sanda wannan ya sa a gaggauce aka karSi Humaira da Ummita zuwa emergency. Abba ya kasa zaune balle tsaye, ban da hawaye babu abin da ke fita daga idanunsa, ga jiri na kwasarsa yana ta ambaton sunan Allah kamar zai ciri baki. Daidai lokacin Fadeel ya shigo a birkice ya ?arasa ga Abba.

"Abba sun fito? Su na ina? Me ya same su?"

Dukkan waWannan tambayoyin ba a hayyaci yake yin su ba. Abban ma da ba a wani nutse yake ba sai ya kasa tanka mishi kawai sai ajiyar zuciya da kallo ga lebban na motsi amman ko harafi guda ya kasa fitarwa sai D.P.O ne ya karSi zancen ya yiwa Fadeel bayani.

"Ka kwantar da hankalinka, in sha Allahu babu abin da zai faru garesu. Likitan ya tabbatar mana ga dukkan alamu kwayoyi aka Wura musu amman in sha Allah za su yi iyakar ?o?ari a kansu."

Fadeel ya dafe kansa ya yi juyin, ya yi safar ya dawo ya kai marwar amma wannan kalmar ta ya kwantar da hankalinsa ya kasa samun matsaguni a zuciyarsa. Kwayoyi? Ya ma rasa inda zai jefa zancen a kwakwalwarsa ballanta ya samu ya yi aiki da shawarar D.P.O Salahuddeen.?

***
A can gida kuwa, Tasleem tun sadda ta kai labarin tafiyar Abba fanso su Humaira, Jannat ta dauki waya hankali tashe ta kira Bokanta. Kaca-kaca suka yi sosai tana zaginsa akan ita fa ba su yi haka ba. Wannan ya sa? Boka tun a wayar ya ci alwashin sai ta girbi wannan tozarcin da ta yi masa. Kasancewar idanunta sun rufe ruf sai kawai ta ja mugun tsaki ta katse kiran.

Awa bai fi Waya tsakani ba, sai ga wayar Abba zuwa ga Mami, a gaggauce ya sanar da ita kuSutar su Ummita ya kara shaida mata cewar su na asibiti. Hankali a mugun tashe suka fice tare da ?asim da Raihana wacce lokaci guda wani mugun zazzaSi ya rufe ta musamman jin cewar su na asibiti. Suka yi kiciSus da Kawun Humaira da matarsa Hajjo wadanda isowarsu kenan garin. Ba su tsaya yi musu dogon bayani ba, Kawu ya bi su yayinda ya ce Hajjo ta tsaya ta jira dawowarsu a gida.

***
? BAYAN AWANNI...

Mummunan labarin da ya iske su Abba na keta alfarmar da aka yi ga Ummita ya sanya shi sumewa bai ko iya jin ?arshen ba balle ya san ko har Humairar ma an taSa. Nan aka kwashe shi shima don ba shi taimakon gaggawa. Raihana kuka kamar ranta zai fita yayinda Mami ke taya ta. Kawu da Fadeel kuwa tashin hankalin da suke ciki ba zai misaltu ba. A gabansu aka fiddo su bayan an yiwa Ummita Winki na mugun raunin da aka ji mata aka sauya musu Wakunan zuwa na hutu, daki mai gado biyu. Fadeel ya ?urawa Humaira idanu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login