Showing 63001 words to 66000 words out of 189325 words

Chapter 22 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

201

Ba? ta kara bi ta kan Humaira ba, itama ganin haka sai kawai ta ja zani ta faWa banWakin. Ranta ya Saci ganin yanda aka yi kaca-kaca da shi, ba ta iya wanka ba sai da ta wankeshi tas har Raihana na kwankwasa kofar tana mitar ta san wankin bandaki take tayi biris da ita.

A gaggauce ta sanya doguwar riga da mayafinsa ta tayar da sallah, Ummita na zuwa suka Wunguma suka fice bayan kowacce ta dauki dukkan abin bukata. Babu nisa sosai da unguwarsu, Yahaya Gusau sula je gidan wata yayar ?awar Raihana ta makaranta, ana kammalawa suka shirya a gaggauce matar ta yi musu Wauri. Tsayawa kwatanta irin kyawun da suka yi ma Sata baki ne. Idan ka kalli Raihana ka yaba, idanunka na sauka kan Ummita za ka ce ta fi su kyau duk kuwa da cewar ta fi su duhun fata, amma idan kallonka ya sauka ga Humaira sai ka yi saranda. Sun fito fes cikin ankonsu na atamfa na kamu. Raihana ce ta biya kudin kwalliyar ta account dinta, ta dai ce musu Mami ce ta ba su don haka ba su matsa da tambayar ba. Ta Soyemusu daga aljihun Fadeel ya fito, shi ne kuma ya matsa mata akan sai ta karSa yana son Humaira ta yi kyau. Hotuna sosai Raihana ta dauke su, ta tura mishi na Humaira kaWai.

A? gidan suka bar kayansu suka fice. Kai tsaye Manal Event Center suka nufa. Wurin ya tsaru iyaka, kowa ka gani da irin nasa haWuwar. Babu laifi kamu ya yi kyau sosai, Humaira tun da ta nemi guri ta ?ame ba ta ko motsa ba ballantana ta yi rawa. Ummita dai ta Wan fita amsa wayar Sahabinta, ta kuma dawo Anti Jannat ta haWa ta da ?an biyu akan ta zauna da su kar su fita, hakanan ta zauna tare da Humaira da wasu cikin yan uwan Abba, su din ma ba duka suka zo ba.

? A gajiye suka koma gida, kowa ya nemi wuri ya kwanta bayan idar da sallah. Su Futuha gaba daya sun bar kwana a dakin, daki daban suka koma tare da kawayensu wanda babu komai ciki, daga shimfiWaWWen kafet sai katifu sai kuwa fanka dake wulwulawa.
?
***
? Tafe yake zuwa sashin Anti Amarya. Kusan kwanaki sama da biyar kenan rabonsu da juna, ba don komai ya dauke kafa daga shiga cikin gidan ba sai Murja da take neman matsawa rayuwarsa da kallo da kuma hirar dole. Tuni ya taka mata burki da zuwa sashinsa tun bayan da Alhaji ya sanar da shi sa?onta.
? Yau Win ma, Alhaji ne ya ritsa shi akan Anti Amaryar tana tambayarshi wai ko ba ya gari. Nan fa Alhajin ya yi mishi faWa sosai ya ba shi hakuri. Don ya wanke kansa ne kuma zai je a yau din. Da sallamarsa a baki ya tsaya har aka amsa sannan ya shiga. Wacce ba ya kaunar ganin ya ci karo da ita kuwa a kwance tana chatting, daga ita sai vest da dogon wando. Ya kauda kai ya juya zai koma, sai ya tsinci muryar Anti Amarya.

"Ah, Fadeel ya za ka juya? Shigo mana. Ke kuma je ki suturta jikinki." Ta karashe maganar ?asa-?asa tana duban Murja. Ta kuwa mike da saurinta ta yi Waki, yau ji take kamar an mata albishir da gidan aljanna, ba ta san haka ta yi kewar Fadeel din ba sai da ta gan shi a gabanta yanzu babu zato. Don haka da sauri-sauri ta zumbulo hijabi ta dawo falon. Lokacin ya maida hankali suna gaisawa da Anti Amarya.

"Ai ni Fadeel na rasa laifin da na aikata gareka. Na ma yi zaton ko ka yi tafiya ne ashe kana gidan amma ka Suya."

Ya yi murmushi yana Wan shafar ?eya.

"Ko Waya Anti, babu abin da kika yi. Abubuwa ne suke Wan ri?e ni, nakan fita da wuri sannan lokacin da zan shigo dare ya yi shiyasa. Amma tuba nake, ganinan yau na shigo."

Ta yi ?ar dariya.

"Toh shikenan ya wuce. Dama Alhaji ne na ga kana kawowa Meatpie da Samosa mai shegen dadi, har nake tambayarsa inda kake odarsa. Gaskiya ya yimin sosai, ina so ne a yimin na birthday Win autanku (Abdulmaleek) nan da two weeks, ko zan iya samun lambar waya?"

Fadeel ya yi murmushi, ya na so a duniya ya ji an yaba da girkin Humairarsa. Kafin ya ce komai sai ga Murja ta tsoma baki.

"Eh wallahi Anti, nima naji dadi. Babu tauri kuma komai ya ji a ciki sosai. Please ki yi order a wurin."

Ya yi shiru kaWan, ya sani ba shi da matsala koda ace ya ba su lambar Humaira tunda dai oda ne zasu yi. Ba ya tunanin kuma Murja ta san wacece, ba ma ita ba, shi kansa Alhajin bai san daga inda Fadeel ya yi odar ba don haka hankali kwance ya ce.

"Toh Anti, zan turomaki ta message sai dai zuwa yanzun suna cikin biki ne ba za a samu ba. Kafin dai zuwa kwanakin da za a yi taron sun kammala."

Anti Amarya ta jinjina kai. Murja dai Wif ta yi da ta fahimci ko ma wace ce dai mace ce yar uwarta. Abin damuwar tana da aure? Sunanta Humaira? Shi ne ba ta da masaniya. Ita a duniya yanzu mai suna Humaira take son gani wacce Fadeel ya mato a kanta. Dama kawai take jira ta buWe wayarsa ta bincika wanda hakan da kamar wuya.

***
?A can gidan Alhaji Isuhu kuwa, yau aka wayi gari da daurin auren yarannasa wanda ya tara dubban jama'a daga wurare daban daban. Babu ma kamar jama'ar Alhaji Yakubu kasancewarsa mutum na mutane.
Cikin gidan ko tun bayan da suka samu labarin an Waura auren, nan ya rincaSe da guWa da murna. Su Futuha amaren zamani idanun nan ko Wigon hawaye babu sai ma murmushi da suke dokawa. Sun sha kwalliya da farin leshi sun yi kyau har sun gaji. Su Ummita kuwa shadda ce ruwan madara da aka yiwa kwalliyar stones suka sanya wanda Mami ta yi musu. Duk inda suka wul?a sai an kalle su an kuma. ?an uwan Mami gulmar masu gulmarta suna yi, a cewarsu ta ri?i bare kamar ?an cikinta, wataran za a wayi gari sun mata butulci. Yayinda a gefe dangin Abba ke yabon Mami da irin yanda ta Wauka ki Humaira da Ummita, sun sani ba ta da laifi ko kaWan a rashin zuwansu gidan sai ko na Mahaifiyarta Anna. Shi ma Abban da bai ba su fuskar su shigo jikinsa ba ya sanya suke ja baya. Sam Abba ba mai sakin aljihu ba ne, hakan ya sa yake ganin kamar duk wani da zai raSe shi a yan uwan toh fa bu?ata ce ya zo da ita koda ba hakan ba.

An sha hotuna sosai, da yamma Amare suka kara shiri cikin atamfarsu mai Wan karen tsada. Aka sha yini, sannan bayan Magriba aka hau shirin Dinnerparty.
Nan ma ya yi kyau sosai, Angwaye da Amare sun sha ado, Amaren sun yi shigar golden lace su kuwa angwayen golden shadda. ?awayensu ?an ?arya kowacce ji take da kanta. Su ma Humaira leshi Mami ta yi musu coffee colour mai ratsin golden. Sun yi kyau kwarai.
Washegari aka tattara da yammaci aka mi?a Amaren Wakunansu. Gidan Futuha a rijiyar zaki yake. Dan?areran gida ne na Alhaji Yakubu mai Sangare uku, nashi sai uwargidansa sannan na Futuha a gefe. Yan uwanta sun yaba sosai da gidan, ga kaya na alfarma da Abba ya yi musu bisa jajircewar Mamin akan ya daure ya fita kunya. Koda suka nufi sashin Uwargida suka iske shi a gar?ame, sun bubbuga ya fi a kirga amma shiru, dole haka suka juya da ita zuwa nata Sangaren suna mita. Wasu na fadin tana nan sun ga sadda aka buWe labule ana le?en zuwansu daga wani window a sama.

Daga nan suka wuce Kuntau inda anan ne gidan Tasleem yake, babu laifi shi ma ya haWu. Flat house ne amma an kashe mishi kudi daidai misali. Ita kadai ce a gidanta sai dai gidan iyayen Hamza na kallon gidan, sai da aka shigar da ita wajensu suka karSe ta da hannu bibbiyu aka yi ?ar nasiha da addu'a kafin a kai ta gidanta.

***
A sati guda kacal, gidan gaba daya an watse sai mutan gidan. Mubarak ma wanda bai fi watanni biyu suka rage ya kammala karatu ba ya tattara ya koma a yayinda a gefe daya Yassar da Dawud ke shirin tafiya bautar ?asa. Gidan ya zama gwanin dadi ga Humaira, babu wani da ke matsa mata yanzu balle kallon banza. Raihana da Ummita sun je gidajen amare ita kuwa ko le?e ta ?i yi. Ta dai yi musu cincin bisa umarnin Mami, an kai wa kowaccensu gidanta saboda tarbar ba?i.
Raihana da Ummita suka maida hankali a karatu don sun soma shirin jarrabawar fita aji SS2 zuwa SS3. Ita kuwa Humaira a sannan ta kammala darussanta na makarantar Anti Laila, hakan yasa koyaushe tana gida idan har ba wani aikin ta samu ba. Sai ya kasance ita ke girkin gidan, a cewar Mami, hakan zai Webe mata kewa. Ta kuma yarda da hakan dari bisa dari, ita kanta ba ta son zaman shirun don yana jefa ta tunani kala-kala.
Ranar ta kama laraba tana tsaye tana shanyar undies dinta a gefe kuma tana sauraron wa?ar Ala mai suna Shahara. Jin wa?ar ya tsaya ne yasa ta fahimci kira ne ya shigo. Ta Wan goge hannunta da sauri ta dauka ganin ba?uwar lamba a ranta tana fatan ya kasance oda ne ta samu don dazu suke magana da Mami take nuna rashin jin dadin yanda kwanaki biyu shiru ba'a samu ba. Da sallamarta ta Waga. Aka amsa daga can, muryar mace ce. Suka gaisa a mutunce. Nan take shaida mata ta samu lamba ne daga Waya daga cikin kwastamominta, tana son a yi mata snacks na birthday din yaronta da za ta yi. Nan fa Humaira ta ji dadi sosai, ba ta kawo kowa a kwanyarta ba sai Hajiya Rukayya, ita ce mai kokarin haWa ta da mutane. Suka yi magana ta lissafa mata kalolin snacks din da take yi, ita kuma ta zaSi kala uku. Nan ta fadi adadi. Suka yi sallama da zummar za ta turo rabin kuWin, rabi kuma idan an kai za ta cika. Ta bukaci Humaira ta turamata acc no ta text.
Da wannan farin cikin ta karashe shanyar da ta fara, ta dauki bokitin ta shige gidan ta kofar kicin ta baya. A falo ta hadu da Mami. Ta sanar da ita batun odar da suka samu, Mami ta ji dadi kwarai.

***
Ita kuwa Anti Amarya tana ajiye wayar ta dubi Fadeel da murmushi saman fuskarta ta ce.

"Yauwa mun yi magana. Zan tura mata kudin yanzu idan ta aiko."

Ya Wan murmusa.

"Ok Anti. Bari na wuce ofis, sai na dawo."

"Toh Allah ya ba da sa'a."

Har ya soma tafiya ta kira sunansa, ya juyo.

"Amma meyasa ka ce kar na ambaci sunanka?"

Ya yi murmushi cikin son nemo abin faWi can ya ce.

"Saboda ba za ta gane ni ba, ba ni ke yin odar ba. Sister Rukayya ce ke yi mana. Idan kika ce Haj Rukayya za ta san ta."

Cikin gamsuwa Anti Amarya ta amsa. Daga nan shi kuma ya fice. Murja dake jin su tana daga dinning table a zaune, ta bishi da kallo. Yana fita ta yi saurin karbar wayar Anti Amarya, tana tambayarta me za ta yi, babu amsa. Sai da ta kwafe lambar Humaira fes sannan ta adana a wayarta.

"Me za ki yi da lambar?"

Ta dan sha mur.

"Ina tunanin ita ce budurwan nan tasa da yake mutuwar so."

Dariya Anti Amarya ta yi.

"Kin samu matsala Murja, me zai yi da ita toh? Nikam jikina bai ba ni hakan ba. Daga jin muryar wannan Win ma kin girme ta. Ba na ji a gaskiya zai kula yarinya, yaron ba ya son raini tun farko idan kin lura."

Murja ta dan ji hankalinta ya kwanta, amma hakan ba zai hana ta bincikawa ba tunda dai ta kasa Waukar wayar Fadeel, idan ma ta Wauka to ya sanya password ba ka iya shiga.

Tsayuwar mota suka ji a farfajiyar gidan. Murja ta le?a, ganin Fu'ad tare da Matarsa Kausar wacce a yanzun take dauke da karamin ciki, ta ja guntun tsaki.

"Waye ne ya zo?"

Yamutsa fuska ta yi.

"Wannan dogon ne mana mai hankali a gwuiwa tare da matarsa. Ni na rasa wannan jaraba, mace da ciki sai shegen yawo."

Ta kara jan tsaki. Anti Amarya ta bude baki ganin wannan karfin hali na Murja, mutum da gidan ubansa sai a hana shi kawo matarsa? Za ta yi magana ta fasa ganin Kausar din ta shigo. Ta tarbe ta da fara'a suka gaisa ta karaso. Shi ma Fu'ad ya biyo bayanta hannunsa rike da jakarta na kaya. Bayan sun gaisa ne yake cewa Antin tafiya zai yi na kwanaki uku zuwa Abuja zasu yi meeting da shugaban kamfanin da ya ke aiki shi ne ya kawo ta gidan ta zauna dayake ?an gidan su Kausar din sun yi tafiya Saudia. Anti Amarya ta karbe ta hannu bibbiyu, ta sa Murja kai mata jaka daki. Murja na kumburi haka ta ja akwatin kayan zuwa Wakin da babu kowa ciki wanda a baya ya kasance na Hannatu ?anwar Fadeel.
Kausar wayayyiya ce sosai kuma gogaggiyar ?ar boko da ba ta daukar raini koda na sakan, tun farkon zuwanta gidan ta ga take-taken rashin kunyar Murja wannan ne dalilin da yasa ba sa ga maciji. Ba ta shiga harkarta ko kadan. Murja kuwa ta tsani a duniya ta ga wanda ya fi ta iya kwalliya da komai ma a wuri, balle kuma kuWi da uban Kausar ya ninka baban su Murja. Gaba da baya dai yarinyar ?ar gata ce kuma gatan da ta samu bai yi sanadin taSarSarewar tarbiyyarta ba. Tana da girmama mutane amma ba ta daukar raini. Hatta da wayarta sabuwar version ne na Iphone, hakan ya sa Murja ko kallonta ba ta yi idan tana dannawa tsabar bakin ciki. Wannan ne kuma ya kara mata son ganin ta mallaki miji irin Fadeel, ta san komai take so za ta same shi cikin sauki.
Koda Fu'ad ya bar gidan, Anti Amarya da Kausar sun taSa hira kadan kafin ta mike ta nufi Wakin da aka tanadar mata don sosai bacci ne a idanunts. Ciki ya sanya ta zama kamar wata kaasa. Murja ta bi bayanta da harara. Anti Amarya kuwa ta kalleta dakyau ta ce.

"Ke banza ce, ba ki da wayo ko na sakan, yanzu a gaban Fu'ad kike share matarsa? Ke da kike neman gurbi a zuciyar yayansa, to ta ina zai tayaki ya?in? Ki cigaba da nunawa duniya ba ki da kunya, wallahi ina maki kashedi, ba a samun kan mutane sai an haWa da kissa. Ai koda ace kina mata ?in mutuwa bai kyautu ki nuna ba. DaWina da ke sam babu wayo sai aukin Sata rawarki da tsalle."

Murja gaba daya sai jikinta ya yi sanyi.

"Kuma fa hakane Anti. Ni wallahi abin ne ya soma yimin yawa. Wanda nake so bai san da zamana ba, na rasa ta ina zan soma Anti."

Wani murmushi Antin ta yi.

"Au, kin dawo hanya kenan? Da ba malamai kika Waura Wamarar bi ba? Ke da ace na bi hanyar malaman za ki ganni a gidannan har i yanzu? Toh uwar Fu'ad abinda ya kashe ta kenan, ta nuna ?iyayya da makircinta a fili karshenta kuma yanzu ga gidannan ya gagareta zama. Malama duk wata Wabi'a mummuna watsi da shi za ki yi. Ki sauya salon shigarki zuwa na matan arziki. Wani matsewa ki fiddo sura ba shi ke burge Fadeel ba, idan kin lura yana son ya ga mace mai tarbiyya. Sai kin sauya sosai, ki kuma daina rawar ?afa a kansa, a hankali nan gaba ko malamin ne sai a bi a shawo kansa. Amma kafin wannan matakin ke za ki sauya takunki."

Murja ta dinga gyada kai tamkar ?adangaruwa, sosai darasin na Anti Amarya ya shige ta, sai dai ta ina za ta fara? Sun jima Anti Amaryar na ?ara wayar mata da kai tana Wauka, a karshe dai ta saki ranta sosai ta kuma gane Antin nata ba ta wasa ba ce.
***
Da taimakon Allah ta kammala aikin odar da aka bata. Kamar yanda ta saba, wannan karon ma waya ta yi akan a zo a karSa. Aka ba ta lokacin zuwa karfe sha biyun rana. Bayan sun yi sallama ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin wani irin nishaWi. Hamdala ta yi kamar koyaushe kafin ta fiddo manyan ledojin mai tambarin Deelsha's Delicacies ta sanya.

***
? Murja ta kammala shiri tsaf sai rawar jiki take yi ta je ta ga Humaira me snacks. Kausar na zaune a falo tana taya Khadija da Hanifa (?iyar Saddika yaya ga Anti Amarya) hura? balan-balan su na tarawa. Murjar ta fito. Kallo ba ta ishe ta ba, ta gefen ido Murja ta watsamata harara. Daidai lokacin da Anti Amarya ta shigo bayan ta dawo daga farfajiyar gidan inda mai decoration ke ?awatawa don anan za a gudanar da birthday din Abdulmaleek na cika shekaru uku a duniya.

? "Ni na shirya zan wuce."

"Toh tsaya na baki cikon kuWinta. Don Allah ki yi sauri kina karSa ki wuce ki karSo Cake din."

Ta amsa da toh. Anti Amarya na shiga ciki sai ga Fadeel ya shigo falon ri?e da Abdul yana mishi wasa. Nan da nan Murja ta ji ranta ya yi wani irin sanyi. Ta kuramasa idanu tamkar ta lashe shi musamman ganin yanda shigar jan t-shirt da ba?in jeans ya haskaka shi abinka da fari. Ta sauke ajiyar zuciya tana ji inama kawai ta tsinci kanta a faffaWan ?irjinsa. Sai da ta ji suna gaisawa da Kausar sannan ta dawo hayyacinta. Ajiyar zuciya ta sauke, ta ?arasa ta zauna ita mai shirin fita. Murya cike da yanga ta ce.

"Yaya Fadeel barka da rana."

Kallo Waya ya yi mata ya kauda kai, shi a yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login