Showing 69001 words to 72000 words out of 189325 words

Chapter 24 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

244

zato ba. Da haka suka karasa gidan Tasleem.

***
A yau Murja ta yi niyyar zuwa sashin Fadeel don ta rantse ko ta yaya sai ya saurareta ya ba ta damar amayar da abin da ke ranta ido da ido. Kwanakinnan ko bacci kwakkwara ba ta iya yi tsabar so da tunaninsa da ke neman zautar da ita, wannan ya sa ta zuri takalmanta kawai ganin an yi Magrib tana kuma da tabbacin yana nan ta nufi sashinsa.

Yana zaune ya kafe manyan frames guda biyu da aka yi mishi na hoton Humaira da idanu yana kallo. Ta yi kyau matuka, daya tana tsaye ne a farfajiyar Manal Event Centre ranar bikin su Futuha, dayan kuwa wanda ta dauka da sallah ne?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ba ta san ma an yi hoton ba ta rike kafaWar Ummita tana dariya mai bayyana wushiryarta. Ta yi kyau ainun, masifar son da yake yiwa hotunan ne ya sanya aka wanko da zummar zai adana duk radda suka yi aure ya kafe su a Wakin baccinsa. Uzurin bandaki ya kama shi, ya mike ya shige ?uryar dakin don kama ruwa. Daidai lokacin Murja ta hau kwankwasa ?ofar dakin, tana ji kamar ta tura kanta ciki ko ba izninsa. A yau ta kai ma?ura a so da kauna da begen ganinsa.
Ganin Fadeel ba shi da niyyar buWewa sai kawai ta murWa ta tura kanta falon. Babu kowa, ta Waga ?afa da niyyar bin bayansa zuwa Wakin, sai wata zuciyar ta kwaSe ta. Ba ta son Sata rawarta da tsalle, har ta juya za ta bar falon idanunta ya sauka saman hotunan dake ajiye. Jikinta har rawa yake yi ta karasa ta Wauka. Ji ta yi kirjinta ya yi wani irin bugu da karfi, numfashinta kuwa dakyar ta iya jawo shi ta furzar. Ita ce! Humaira mai Deelsha's Delicacies, ita ce dai masoyiyar da Fadeel ke so. Kafin ka ce me idanuwan Murja sun soma zubar da hawaye. Ma?o?on ba?in ciki da tsantsar kishi suka tokare kirji da ma?oshinta. Ta tuna ko Wazun sai da suka gaisa ta waya da ita, ashe ba ta sani ba da rival dinta take mu'amala? Ji ta yi kwakwalwarta na rayamata kawai ta tarwatsa hoton a ?asa idan ya so komai ta fanjama fanjam! Aikuwa ta Waga a zuciye da wannan niyyar amma ba zato ta ji tsawar Fadeel a kanta. Ya ?araso ya fisge hoton a hannunta, murya a Wage ya ce.

"Me ya kawoki Wakina?! Uban waye ya baki iznin kutsowa ba tare da sanina ba?"

Kamar ta ce mishi Ubanka ne amma ta danne, kishi dai bala'i ne. Ta kasa samun nutsuwa, ta kai hannu ta dafe kai har lokacin kuka take, ko kaWan tsawar Fadeel bai razanar da ita ba. Wannan kaWan ne akan yadda take jin raWaWin azabar kishin Humaira a zuciyarta. Dakyar ta iya tattaro kuzarin da ya yi mata saura ta soma magana.

"Dama akan wannan yarinyar ka ke wula?anta soyayyata? Yaya Fadeel ina sonka ka sani amma ka ke nuna kamar ba ka san da zamana ba. Meyasa? Da me ta fi ni? Me za ta nunamin? Wallahi Yaya Fadeel muddin ka aureni zan maka fiye da abin da kake tunanin samu daga wannan yarinyar."

Ransa ya Saci ainun.

"Ke a naki tunanin koda ace auren zan yi don kyau ko suea? kin kai na aureki?! Toh ke ba komai ba don ba ki da suffar da zan gani har naji kwaWayin aurenki. Daga yau ina maki gargaWi ki fita harkata, na rantse maki duk sadda na ?ara ganin ?afafunki a nan sai na SaSSallaki. Get out!!"

Ta razana sosai, ga ba?a?en maganganun da ya fesamata ga kuma tsawa, ta kalleshi tana jin ranta na suya sannan ta kara kai duba ga hoton Humaira kafin ta juya a guje ta fice daga Wakin. Fadeel ya yi tsaki ya zaune yana jin zuciyarsa na zugi. Da ace yana da ikon fitar da yarinyar daga gidannan da tuni ya aiwatar.

***
? Tasleem ta buWe ?ofar kyauren, suka shigo. Humaira? ta bi ta da kallo, ba laifi itama ta yi kyau ta kara haske. Ta rungume Futuha suna murnar ganin juna, ba ta ko kalli Humaira ba suka shiga ciki zuwa Waki suka bar Humaira a falo zaman jira.

? "Shegiya, haka gidanki ya yi kyau?"
Cewar Futuha, Tasleem ta ji zancen kamar zagi hakan ya sa ta ja tsaki.

"Ba dai ba?a kike faWamin ba ko? Bayan naki gidan an ce ya kere nawa nesa ba kusa ba."

Ta yi dariya.

"Abar wannan zancen, ya ne? Kin ji labarin tafiyarmu ko? Kai Tasleem burina zai cika zan shiga jirgi nayi selfie, na kuma ga wurare da dama irin yadda su ?ar Snow suke gani su na hoto suna mana yanga."

Baki buWe Tasleem ke kallonta cike da Wumbin mamaki.

"Futuha, anya kina cikin hayyacinki kuwa? ?ar Snow dai da ta yi maki ba?in ?azafi ita kike farin cikin za ki zarta? Wallahi ina rabaki da shiga harkar ?an Tiktok, lallai idan kika sa kanki cikinsu sai kin yi kukan da na sani fiye da na baya."

Futuha tun da Tasleem ta soma magana take faman doka murmushi, ta ba wa ranta cewa kawai ba?in ciki ne ke cin Tasleem saboda a duniya ta fi ta burin hawa jirgi da fita ?asar waje sai kuma ya kasance ita ce ta samu wannan damar, ta ba kanta lallai Tasleem dai da biyu take wannan sabuwar nasihar.

"?ar uwa kenan, ki bar wanda ya samu duniya ya ci abinsa da tsinke, ai komai da kike gani lokaci ne. Wasu ma damar da suka jima su na burinta kenan amma ba su samu ba. Mu kuwa tun da Allah ya kashe ya ba mu kinga kenan sai mu dama kununmu yadda muka ga dama."

Tasleem ta yi dariyar ya?e.

"Ai shikenan, Allah dai ya kaiku lafiya. Nidai please and please ki yo min tsarabar dogayen riguna."

Futuha ta yi farr da idanu tana dariyar itama.

"Kar ki samu damuwa ?ar uwa, ai ke tawa ce."

A falon kuwa, Humaira na nan zaune tana karewa gidan kallo aka yi sallama aka shigo. Ta Waga kai, wata budurwa ce da ba ta wuce sa'arta ba ta shigo kai tsaye ta nemi wuri ta zauna suka gaisa fuska a sake.

"Anti Tasleem na nan?"

Humaira ta amsa da eh.

"Ok, bari na jira fitowarta a nan. Kema ?anwarta ce ko??? Na tuna fuskarku da biki, ku uku cikin shiga iri Waya aka ce sisters dinta ne."

Humaira ta Wan yi murmushi.

"Eh, ?anwarta ce."

"Ok, amma ba Uwa Waya ba? Naga su kamar buzaye ne."

Humaira dai ta Wan yi jim, ta rasa wannan maganganun da ake mata na babu gaira babu dalili. Sai a nan kuma ba ta amsa ba. Budurwar ganin haka ta sauya darasin.

"Allah ba ?aramin so Yaya ke yiwa Anti Tasleem ba. Akwai wata cousin sister din mu da ke masifar sonsa amma ko kaWan ya ce shi ba ya yinta, kuma fa ..."

Sauran zancen ya ma?ale a fatar bakinta sakamakon fitowar Yayannata daga Waki. Humaira ta gaida shi, ya gane fuskarta sarai don takan fito kawo masa abin motsa baki lokacin da yake zuwa zance wajen Tasleem. Ya amsa gaisuwar fuska a sake, daidai lokacin kuma su Tasleem suka shigo falon. Nan aka hau sabuwar gaisuwa da Futuha anan take sanar da shi batun tafiyarsu Dubai da mijinta. Ya yi mata murna kwarai. Daga bisani suka yi sallama har bakin mota suka raka su, sai bayan sun tafi ne suka koma ciki. Har lokacin Hamza bai sakarwa Tasleem ba sakamakon haushinta da yake ji na irin kalaman da ta yaSa masa. Ita kuwa budurwar ?anwar tasa mai suna Fauziyya ba wani jimawa ta yi ba, daman shigowar don ta ganewa ?ar uwarta Ramlat irin zaman da ke gudana a gidan Hamza wanda har gobe yana nan daram a ranta. Akwai kuma da yawa cikin yan uwansa masu taya ta kishin Tasleem. Ciki kuwa har da Fauziyya.

***
Daki guda na saukar ba?i Futuha ta ba Humaira, nan ta zauna. Madaidaicin gado ne a Wakin sai kafet a shimfide da bandaki a ciki. Ya yi ?ar ?ura kaWan ba ta damu a haka ta kakkaSe bayan ta idar da sallah ta yi kwanciyarta tana danna waya. Tana nan kusan awanni biyu wuraren ?arfe tara na dare ta ji shigowar mota. Ba jimawa kuma wayarta ta Wau ?ara, Futuha ce. Ta Waga da sallama, ba ta ko amsa ba ta ba ta umarnin ta zo falo ta gaida Maigidan. Kashe kiran ta yi ta mike tana jan guntun tsaki. Mace ko sanin darajar sallama ba ta yi ba, an yi amma madadin ta amsa sai ta yi share. Hijabi ta sanya ta fito, su na nan falon dake saman, yana zaune ita kuwa tana saman cinyarsa tana zuba ruwan shagwaSa. Sallamar da ta yi har aka amsa bai sa sun sauya a yanayin da suke ba, Humaira sai ta sunkuyar da kanta domin ba ?aramin kunya suka ba ta ba. Wannan wace iriyar fitsara ce? Koda dai dama ta riga da ta san wace ce Futuha, matar dake tsayuwa gaban waya ta ti?i rawa ta Wora a midiya, ai kuwa ba za ta ji kunyar idanun kowa ba idan tana tare da mijinta. Haka Humaira ta ayyana a ranta.

"Kika wani tsaya daga ?ofa, Malama ki ?araso ki gaida shi."

Muryar kamar ba ta Futuha ba don gaba Waya ta wani ?an?antar da ita irin yadda ta saba idan tana waya da samari a baya. Humaira ta karasa shigowa ba tare da ta kallesu ba ta gaida Alhaji Yakubu, ya amsa murya a sake. Daga haka ta mi?e za ta yi ciki, Futuha ta dakatar da ita ta hanyar nuna mata wata leda akan ta Wauka ta ci. Ta dauka ba musu ta fice daki. Ita dai mamaki kawai take yi na irin wannan wayewar zamanin.
Tana shiga ta buWe, shawarma ce a naWe a paper sai ko gashin kaza rabi, ta cinye tas don dama yunwar take ji ta wanke hannu da baki ta dawo ta nemi makwanci.

***
Kwanakinta a gidan Futuha babu abin da take yi sai Wirkar aiki, akwai ?ar dattijuwar dake zuwan yini tana tafiya. Takan kama ayyukan gyaran ?asa, ita kuwa Humaira ta gyara saman tas, duk wata dauWa da Futuha ta bari tun zuwanta babu gyara kaca-kaca sai da ta dawo yana kyalli. Ga girkuna masu dadi da ta ke yi musu safe da yamma, Futuhar da ba ta Wan sakarwa Humaira fuska, tsabar jin daWin yadda ta ke mata bauta sai ga shi ta soma saki, babban ?udurinta kuma bai wuce idan sun dawo daga tafiyar da zasu yi ba ta yi dabarar da Humairar za ta dawo ?ar?ashinta gaba Waya.
Ana gobe su Futuha za su tafi ne, Humaira ta fito ta zagaye can bayan Wakunan inda anan ne aka yi wasu shuke-shuke masu ban sha'awa, a lokacin babu koda a Sangaren Futuhar, Baba Furera ta wuce gida, Futuha kuwa an tafi gyaran gashi da jan ?unshi. Hakan yasa kaWaici ya yi mata yawa, ga dai wuta nan daga safe har dare amma ta gaji da kallon balle kuma danna wayar. Wannan ne dalilin zagayawarta baya tana kallon shukokin masu burgewa da Waukar ido. Tana nan tsaye tana murmushi tana shafar su gami da shinshinar ?amshin da ke jikinsu, ta kai duba ga sararin samaniya yadda hadari ya yiwa garin ?awanya, a hankali ta lumshe idanu saboda jin daWin yanayin. Sai dai kuma lokaci guda kamar wacce aka mintsila ta bude idanuwanta tarr jin kukan jariri da ke tashi sosai. Ta kai duba ga inda sautin ke fita har ?irjinta na bugu da sauri-sauri. Sashin dai da aka ce na uwargida ne, daga nan ta dinga jin kukan na tashi. Cikin sauri da gudu-gudu ta bar bayan ta dawo bangaren Futuha, daidai nan suka yi kiciSus da mai ba shuka ruwa. Ta dube shi, ganin yadda take faman haki ya sanya shi tambayar ko lafiya. Da yatsa ta yi mishi nuni da hanyar Sangaren Uwargidan da ake kira Hajiya Saratu.

"Me aka yi a wurin?"

Ta haWiyi miyau.

"Da mutane a ciki ne?"

Sai tambayar ta ba shi mamaki.

"Hala ke ba?uwa ce? Ai Sangaren Hajiya ne, tana nan. Ko wata biyu ba ta yi da haihuwa ba."

Sai hankalin Humaira ya Wan kwanta amma kuma sai ta hau wani sabon mamaki da al'ajabin. Don haka ta kuma dubansa ta ce.

"Dama ta dawo daga tafiyar da ta yi ne?"

Ya yi ?ar dariya.

"Ko kusa, babu inda ta je tana nan. Ai da yake ba ta fiye fita ta wannan ?ofar ba, akwai ?ofa ta baya, ta fi fita ta can idan ta tashi zuwa unguwa. Kuma gaskiya dai ni zan iya cewa tun ma da ta haihu ba na tunanin na ji ance ta fita. Koda dai ba ganewa ake yi ba tunda Hajiya motar haya take shiga."

Ya ?arashe da wani irin jimami, har ya buWe baki zai ?ara magana sai kuma ya girgiza kai kawai ya fice. Humaira ta bishi da idanu tana mai cike da al'ajabi. Idan maganganunsa gaskiya ne? Toh me Alhaji Yakubu yake nufi da Soyewa? Ita dai ta ji Futuha ta ce Uwargidansa ba ta nan su na Dubai da yaranta. Toh idan hakane su ne a gidan, meyasa ko da wasa ba a ganin gilmawar yaranta tunda dai ai yaro ba zai yarda da rayuwar ?ulle ba?
Amsoshi ne da ba ta da amsar su kawai sai ta ja ?afafunta da suka yi wani irin sanyi ya bar wurin.
Humaira ta kama bakinta koda wasa ba ta sanar da Futuha komai ba, ba ta ga dalilin sanar da ita abin da bai kamata ta ji daga bakinta ba wannan ya sa ta bar abin a cikinta. Washegari da misalin ?arfe biyun rana sai ga su Raihana a gidan sun zo rakiya Airport, daga nan direba zai mayar da su gida gaba Waya.
? Jirgin dare ne wannan ya sa sai bayan magriba suka hau shirin tafiya, Humaira ta tattara kaf kayanta, dama ta gaji da gidan babban burinta shi ne kawai ta koma cikin ?an uwanta. Sakewar da Futuha ta yi da ita bai sa ta iya sakin jikinta ba don ba ta saba da shi ba, ta fi ganewa rayuwarsu ta baya yadda suke hantararta a abu ?alilan amma sam zuciyarta ba ta amince da wannan sauyin ba.

?arfe goma jirginsu ya tashi, su kuma aka kai su gida. Humaira ranar kamar an tsoma ta a aljanna, farin ciki biyu ya haWe mata, na farko bai wuce dawowarta gida ba daga zaman u?uba da bautar da ta ke yi a gidan Futuha, na biyu kuwa jin daddaWan labari daga bakin Raihana cewar iyayen Sahabi nan da kwanaki biyu za su zo tambayar auren Ummita. Ranar dai bacci Sarawo ne ya sace su don raba dare suka yi ana hira.

***
? Anna ta dubi Mami ranta a tsananin Sace ta ce.

"Ke kam da a asibiti na haihu zan iya rantsuwa sauyamin ke a ka yi wannan ba jinina ba ce. Ni dai kaf zuri'armu babu macen da za ta aikata wanan abi da kike aikatawa na rashin sanin ciwon kai da kuma rashin zuciya. Wannan rawar ?afa da murna da kike yi ko kuWin auren Raihana aka kawo sai haka."

Tana kai wa nan ta ja tsaki, Mami ta yi Wan murmushi. Kawo kuWin gaisuwar iyaye da sanya rana da aka yi na Ummita a yau ne ya sosa zuciyar Anna take wannan zantukan. Ita idan irin hakan ma abu na farin ciki ya afku ga Humaira ko Ummita har ba ta kaunar ya zo kunnen Anna saboda irin waWannan bakaken kalaman da ba ta ha?ura ta bar wa cikinta sainta furzar. Kamar ko yaushe a kwanakin nan, wannan karon ma Mamin shiru ta yi ba ta ce uffan ba. Itama Annar don kanta ta gaji ta bar zancen. Ta sanyo wani batun bayan ta kora ruwa a cikinta.

"Af, yar uwarki tana nan tafe ?arshen watan nan."

Cike da mamaki Mamin ta dubi Anna ta ce.

"Jannat kuma? Me zai kawo ta nan kusa alhalin yara ba hutu suka yi ba?"

"Toh kina ba?in ciki da zuwan nata ne?"

Jin haka da sauri Mami ta ce.

"Ko Waya, Allah ya huci zuciyarki. Allah ya kawo ta lafiya."

Anna ta amsa da amin, ganin tana neman Wora maganar Wazu sai kawai Mami ta mi?e tana mai ba ta uzurin zuwa wurin mijinta. Yamutse fuska kawai Anna ta yi ba tare da ta ce komai ba.

***
Alhaji ne zaune saman darduma a barandarsa yana latsa waya, isowar Fadeel ne ya sanya shi ajiye wayar ya mayar da hankali garesa. Bayan amsa gaisuwarsa ya gangara kan batun da yake son yi.

"Babban dalilin kiranka bai wuce kan maganar aure ba. Lokaci ya yi da za ka tsaida hankalinka wuri guda ka nemawa kanka abokiyar rayuwa. Kana gani dai ga Wan uwanka nan har an soma batun zuwa gaisuwa da ro?on iri. Toh an kai lokacin da zubamaka idanun da aka yi ya kamata ace ya zo ?arshe, ga baffanninka nan a ganinsu har da laifina a ?in matsa maka da zancen. Har cewa suka yi idan babu dama ka je can gida ka zaSa cikin ?annenka wacce ku ka daidaita sai a yi magana. Rashin ba su goyon baya akan haka ba yana nufin na amince da zaman naka hakanan ba Fadeel. Shekaruna gaba suke ?ara yi ba wai baya ba, lokacin ?ure mana yake ?ara yi. Alhamdulillah ka fara gini, koda ace bai yi nisa ba, ina da tabbacin nan da shekara dai ka haWa komai. Kai yanzu Wan uwanka ba abin koyi ne gareka ba? Ka gwammace kana ji kana gani ya yi aure ya bar ka nan zaune? Har zuwa yanzu babu wacce ka tsayar?"

Fadeel ya ?ara sunkuyar da kansa, ya sani dama tun da har zancen auren Ibb ya tashi, toh fa Daddy da Alhaji ba za su Waga masa ?afa ba. Yana kuma da tabbacin yadda Alhai ya yi mishi magana, to fa shi ma Daddy zai Wora da nasa bayan kwanaki.

"Ba ka ji ne?"

Ya Wago ya Wan ja numfashi, babu amfanin Soye-Soye, babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login