Showing 99001 words to 102000 words out of 189325 words

Chapter 34 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

216

ta yi mishi ba ya taSa sauya magana. Mutum ne mai magana daya wannan ya yi matukar Waga mata hankali har ta kasa siyasar data saba na danne abin a zuciyarta. Fuskarta ta nuna tsantsar Sacin rai na gaske, idanunta har wani kaWawa suka yi tsabar bala'i.

"Mubarak! Kar ka kuskura na kara jin makamancin wannan maganar daga bakinka. Wacce kake faWawa ka dinga tunawa ita ta haifar maku ni. Ka kiyayi harshenka!"

Mubarak ya yi shiru kawai yana jin zafin maganganun Anna har lokacin suna tarfafasa zuciyarsa. Anna kuwa ta hau zagin Mami tana fadin ta yi mata shiru ai da sa hannunta a rainin da yaran suka yi mata. Shi dai ya dubi Mamin ya isar da sakon Abba akan ta fito su wuce asibiti sannan ya kaWa kai ya bar musu dakin. Mami ta mike ba ta ko biyewa maganganun Anna ba ta bar dakin. Wannan kalma ta so da Mubarak ya furta yana yiwa Ummita ya tsayamata a ?ahon zuci, abu ne da har abada ba za ta bari ya afku ba muddin rai.

***
A kokarin zubar da cikin Ummita aka kusa jaza mata matsala, zubar jini sosai ta shiga yi dakyar aka samu ya tsaya. Sai dai cikin hukuncin Allah mai kaddarawa cikin yana nan daram bai fita ba. Haka aka shafe watanni hr biyu ana fama da abu daya amma cikin bai ko girgiza ba wannan dalili ya sanya Abba cewa a hakura kawai amma gudun masu shiga da fita na gidan Ummitan ta rage fitowa falon idan ya so duk abinda take so a kai mata daki.
Ga biki ya matso amma sun kara neman alfarma an Waga bisa hujjar kayan dakin da ba a kammala haWawa ba na Ummitan. Wannan abu mai yiwa iyayen Sahabi da shi kansa dadi ba, ga raWe-raWin da aka kawowa uwar Sahabi wai Ummita na da juna biyu, ko kadan ba ta ji ta amince da zancen ba, da hakan ne ai ta san iyayen Ummitan masu dattako ne ba za su Soye musu ba. Wannan yasa inda ta ji zancen anan wurin ta bar shi kuma a cewarta ai ciki ba ya Suya, idan har akwai to fa zai fito.

Mami ta yi nasarar samun wayar WIZZY. Wayarsu ta farko ya nuna bai ma san zancen da take yi ba don gaba daya hankalinsa ba a nutse yake ba gani yake kamar an hada baki ne don a kai musu cafka.

Sai da aka kwashi lokaci mai tsawo sannan ta kara nemansa a waya ganin dai cikin dake tattare da Ummita ya ?i fita uwa uba ga wani irin kulawa da Mubarak ke yiwa Ummita wacce har gobe ba ta da walwala. Wannan abu ya tashi hankalinta ya kuma jefa ta cikin rudani da tsoro. Ya tabbata kenan idan ciki bai fita a cikin Ummita ba za ta iya zama rabon Wanta nan gaba. Ta kuwa gwammace gwara ta sanar da Wizzy cewa Ummitan na dauke da cikinsa har na watanni hudu don su ga matakin da za a dauka a kai.

Cikin sa'a ya Waga wayar.

"Wai Malama ba mun gama aikin da kika sanya mu ba? Kiran da kike yimin na mene ne bayan kin jaza mana asarar ma?udai?"

"Kaga Wizzy, kar ka yimin rashin kunyar banza da wofi! Ni na jazamaku asara ko kuwa ku ne kuka jazamin? Da na ba ku aiki na ce ku ketawa yarinya haddi ne? Shegen halin akuyancinku ya sanya kun afkamata yanzu yarinya tana dauke da ciki har tsayin watanni hudu."

Wizzy ya kantamo wata ashariya ya saki.

"Ciki kuma?!! Don uwarta ita din akuya ce daga yi sau daya sai ciki!"

Mami itama ji tayi tamkar ta sakar masa ashar, da kusa da ita yake a yadda take ji za ta iya sha?ar wuyansa har lahira.

"Ko mece ce ni ba wannan ne ya sa nayi kiranka ba. Mafita nake so, idan kuma babu to lallai kuWina ya dawo. Sadik shi ne sunanka na gaskiya, kai din haifaffen Katsina ne. Ina da kaf tarihinka na kuma san inda zan sameka, wallahi muddin ka bani matsala sai na yi maganinka."

Shiru ya Wan biyo baya tamkar ba zai ce komai ba don ba karamin dauremasa baki ta yi ba, ita kuwa Mami ta san komai bisa shawarar Hajiya Lubna, tun ma basu kai ga ba da aiki ba sai da suka sanya aka nemi dukkan bayanan sirri na wadanda suka ba aikin sannan suka amince.


"Hajiya bai kai ga nan ba. Ni dai yanzu kudi mun ci ubansu. Kawai dai abin da ya kamata a bar ta ta haihu, ni kuma zan zo na dauke gudan jinina na kai garinmu."

"Me kake so ka ce?"

"Eh ina so nace maki ni Sadik Wizzy ina son abina. A bar min ciki ta haihu na karSi abina."

Mami ta yi shiru tana nazari. Idan har Ummita ta haihu ya karSi abin da ta haifa watarana asiri zai tonu, ita kuma ta rantse ta gwammace gwara abin da za ta haifa din ya mutu da dai wannn gurguwar shawarar ta Wizzy.

"Ya ne wai kika yi shiru Hajiya? Ba ki ji nace maki ina son abina ba? Toh ina son abina, duk wanda kuma ya yi yunkurin aika shi lahira nima zan sanya shi dogon bacci. Ina fatan kin fahimta? Idan na karSe abina ba sai ta je ko uwar ina za ta je ba mu raba gari?"

Zufa sosai ya rufe Mami, gaba daya kanta ta ?ulle ta kuma rasa mafita. Dole haka ta amsa da toh suka yi sallama.
***
*LITTAFIN NAN NA KU?I NE. SIYA AKAN NAIRA ? 400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645



Ganin lamuran bana ?are ba ne, ya sanya a dole suka rungumi ?addarar cikin Ummita. Babu yanda suka iya don a gaban idanunsu an yi dukkan wani kokari don a zubar amma hakan bai yiwu ba. Hankalin su Abba da ma kansu su Humaira ya Wan kwanta ganin yadda Ummitan ta samu nutsuwa don sosai take kokarin Soye nata damuwar saboda samarwa ?an uwannata nutsuwa musamman Mubarak wanda kullum kokarinsa ya kyautata mata. Shi ne siyo banza siyo wofi, kunna mata fina-finai a wayarsa da ma bidiyon sanya nishadi da dariya, tun ba ta dariyar har ta zo ta Wan soma murmushi. Ranar da abin ya ishi Mami sai da ta tunkari Abba a siyasance tana ba shi shawarar ya dace Mubarak ya dinga fita kasuwa kafin lokacin da zai tafi bautar ?asa. Abban ya nuna hakan daidai ne sai dai ya kara da fadin.
? "Amma na so ace ya hakura da kasuwarnan ya cigaba da daukewa yar uwarsa hankali ta hanyar hirar da yake taya ta. Naji dadi kwarai da na ga murmushin fuskarta jiya, na kuma sani hakan yana da ala?a da shi. A duniya yanzu bani da burin da ya wuce na ganin farin cikin yarinyarnan. Ina kuma cike da fargabar yanda yan uwan Mahaifiyarta za su karSi batun cikinta."

Wannan magana ta Abba ko a fuska ba ta yiwa Mami ba. Ta fakaici idanunsa ta watsa mishi harara sai kuma da ta ga ya kalleta ta gyara fuskar sosai kai ka ce gaba daya damuwar duniyarnan ita aka Worawa.

"Ni kaina hakan yana yimin dari bisa dari, sai dai kuma hakan fa ba mai Worewa ba ne tunda wataran din dole ne ya wuce bautar ?asa. A yi hakan dai yanzu, na maka alkawarin in sha Allahu zan tsaya tsayin daka wajen ganin ba ta faWa cikin ?uncin baya ba. Ga yar uwarta Humaira ma kullum tana nan tare da ita."

Sai da ta ambaci Humaira sannan Abba ya ce.

"Af, kinga zan manta, mun yi magana da iyayen Fadeel, mun kuma yanke nan da watanni shida zuwa sadda shi Fadeel din ya kammala gini za a tsaida zancen aurensu."

Wani irin jiri ya nemi kwasar Mami daga zaune, ta hadiyi miyau sannan cikin ya?e ta ce.

"Wannan abin farin ciki ne sosai Abban yara, amma kuma ba ka ganin kamar zai zama mun zalunci yarinyarnan? Har wannan lokacin fa Humaira ba ta kula shi, ba ta kaunarsa."

Abba ya dan dau???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?re fuska.

"Bar ja'irar yarinya marar wayo. Ai ba ita ta haife mu ba. Ni na gaji da wadannan mugayen dabi'unnata na korar samari da wulakantasu. An kawomin ?ararta ya fi a ?irga, a yan watannin nan da fitowarsu dalilin da yasa ban tayar da maganar manemanta ba saboda halin da yar uwarta ke ciki ne, amma ko sati ba a yi ba akwai wanda ya same ni bayan na fito daga masallaci cewa Wansa ya gani kuma yana so. Hakuri dai na bayar. Ni ba zan biye mata ba. Aure ne dai sai ta yi, idan ba ta son shi Fadeel din ta zo ta kawo wani."

Tsaki Mami ta ja a ?asan ranta, kamar ta sha?o wuyan Abba haka ta ji. Kamar yanda ta saba kuma sai ta shanye bacin ran, fuskarta a Wan daure ta ce.

"Aa fa Abban yara, nikam ba wanda zan yarda ya yiwa Wiyata dole. A dai bi abin a sannu. Yanzu dai ya muka kwana batun kai ta wurin mai magani."

Girgiza kai Abban ya yi, wato dai Mami ba ta taSa ganin laifin ?a?anta.

"Duk sadda ku ka shirya zuwa Mamin Humaira, ni mene nawa a ciki zan mata dole ta je ne?"

Ya fadi cikin gatse da kuma zolaya hakan sai ya ba Mamin dariyar da bai kai ciki ba, ta Wan dara Win tana mai farr da idanunta.

"Naji din, ko ma me za ka ce hakan ne kawai. Yau dai muna da ba?i, yaran Abba zasu kawo mishi ziyara. Zuwa gobe sai muje."

Abba murmushin shima ya yi, ya gane Tasleem da Futuha take nufi.

"Toh Allah ya kawo su lafiya."

Ta amsa da amin.

Humaira ce ta yi girkin gidan a ranar, ta dawo da aikinta tu?uru na shiga kicin ganin hakan yana Webemata dukkan damuwa sai dai kuma har gobe masu neman ta karSi odar su ta kasa, ko Mami ba ta sanarwa ana neman odar abinci ba saboda a ganinta ba ta da nutsuwar da za ta yi abin da ya dace.

Bayan ta kammala komai ta zuba a kuloli, ta bar Ladidi da gyaran kicin din ta koma nasu dakin. Kamar dama jira yake, sai ga waya ta shigo. Koda ta duba Fadeel ne, wani irin Sacin rai ta ji ya danne wani sashi da ke kokarin sanyayamata rai, ta kasa fahimtar yanayin da take ji akan Fadeel tamkar dai guda biyu ne. Farin ciki da bakin cikin da ya danne wannan farin cikin. Babu walwala ta amsa da sallama. Shima ya amsa sallamarta.

"Ina fatan ban takuraki ba? Fatan kuna lafiya?"

Ta tsuke baki, tsiwa take son ace ta yi amma sai ta ji tamkar wani Sangare na zuciyarta na kwaSarta. Ta kai duba ga Ummita da ke kwance idanunta a kan Humairar. Sai ta ji dagaske ta kasa tsiwar a gabanta don haka murya ciki-ciki ta amsa.

"Lafiya muke. Fatan kaima haka?"

Daga ma muryarsa za ka fahimci ya ji dadin yanda ta amsa ba kwanaki da take balbale shi da faWa da bakaken maganganu ba, shi kuwa bai ma san zafi biyu ne suka hade mata a baya ba, ga na halin da cikin jikin Ummita ya jefata, ga kuma na wani ciwon kai da bacin rai da muryarsa ke haifar mata marar dalili.

"Lafiya kalau nake. Ina neman Wan wata alfarma wajenki Boddo."

Sarai ta san me yake nufi da wannan sabon sunan da ya raWa mata, wato kyakkyawa. Sai ta zaSi ta basar ta hanyar fadin.

"Ina jinka."

"Zan iya shigowa mu gaisa?"

Ta Wan yi jim, ba komai take tunawa ba sai zuwansa na karshe a watannin baya da har Mami ta ji babu dadi. Yanzu idan ta ce ya zo kuma fa? Ta ji wani abu na tafasa zuciyarta, bakin cikk na saukar mata da ba ta san na mene ne ba. Wani bangare na jan ta da kokarin ta furta ya zo din, amma wani bangaren na kwaSarta da nuna ta tsane shi, ta tsani ganinsa to me zai zo ya yi mata?

"Toh."

Ta ji lebbanta kawai sun ba da wannan amsar. Shi kansa sai a ya ji wani shock don bai zaci wannan amsar zai ji ba. Ya yi makamancin tambayar ya fi a ?irga amma kullum amsar aa, karshe ma ta kashe wayar da hujjar ya dame ta.? Ya yarda addu'a tabbas na tasiri akan Humaira, don duk sadda ya dage iya dagewa a kan lamarinsu sai ya ga sauyi tattare da ita, ya kuma soma yarda da hasashen Hannatu kanwarsa da kafin ta koma Yola da ta ji irin yanda Humairar ke yi da komai ta ce ba yin kanta ba ne a nema mata magani.

"Nagode Boddo, sai na shigo."

Yana fadin haka ya katse kiran, itama Humaira ba ta ce komai ba ta sauke wayar daga kunnenta. Ta dubi Ummita da ke kallonta cikin murmushin da ba ta san dalili ba.

"Mene ne?"

Ta tambaya. Ummita ta girgiza kai.

"Ba komai, ina dai ganin wani abin mamaki ne a saman fuskarki. Idan ban yi karya ba kina mutuwar son Fadeel amma na rasa meke danne wannan son."

Humaira ta dan harareta da wasa.

"Ni ba sonsa nake ba. Mu bar zancen don Allah kafin raina ya Saci."

Murmushin dai Ummita ta ?ara yi, ba ta ce komai ba ta lumshe idanu tana ci gaba da jan carbin dake hannunta. Ita kadai ta san tunanin da take yi, Humaira ta dube ta. Tausayinta sosai ta ji, Sahabi har ya gaji da zuwa hira don ba fita take ba, hakanan ta daina daukar wayarsa. Kullum zancenta guda daya ne, ba za ta yaudari Sahabi ba, ta fi kaunar ya san ita din ta haramta aurensu koda kuwa bayan ta sauke nauyin cikin dake jikinta ne. Ba za ta aure shi ba sam. Ba ma za ta yi auren a duniya ba kamar yanda ta ke faWamusu a yanzu.

Shigowar Raihana Wakin ne? da sallama ya sa Ummita bude idanun, itama Humaira ta kauda dubanta daga gareta zuwa ga Raihanar. Wannan ne ya katse tunanin dukkansu.

"Mami ta ce ku fito ku gaisa su Tasleem sun zo."

"To." Shi ne amsar da Humaira ta bayar ba don tana kaunar ganinsu ba domin ta gama sanyawa a ranta su din ba masoyansu ba ne. Ba kuma zasu kaunace su ba har gaban abada. Sai da Raihana ta kara maimaitawa sannan Humaira ta mike, Ummita daman tuni ta yi gaba. Cikinta bai da girma bai fito ba.

Tasleem wacce daga makaranta ta shigo gidan sanye take cikin uniform dinta ga tirtsetsan cikinta dan watanni takwas sai faman taunar aya take yi suna hirar makarantar da Mami, watanni shida kawai ya rage ta kammala karatun gaba daya. Ba ta yi ko mintuna uku ba sai ga Hajiya Futuha ta shigo tana ta faman shan ?amshi. Tasleem ta harareta ta gefen idanu ta kauda kai tana Wan huci, fatar Futuha ta kara kyau kamar ka taSa jini ya fito, kamshin turarenta kuwa ya buWaWe falon gaba daya. ?asim na rike da jakarta yana take mata baya, babban burinsa shi dai ta ba shi na kashewa.

Yassar ya dube ta.

"Ka ga manya matar Alhaji naku daban da nasu. Irin wannan ?amshi haka? Gaskiya zan zo a sammin turaren."

Ta karaso ta zauna jikin Mami tana dariya.

"Har ka bani kunya Wan uwa. Idan dai turare ne, ko direba zan aiko ya kawomaka na siyo su kala-kala a Dubai."

Aka sa dariya Dawud na fadin.

"Inyeee! Ka ga Hajjaju mutan Dubai."

Mami dake murmushin jin alfahari ta ce.

"Ya ishe ku hakanan toh."

Tasleem dai ba ta tanka ba sai dariyar ya?e kamar bakinta zai rabe biyu amma ?asan ranta ji take tamkar ta kurma ihu.

Shigowar Ummita da su Humaira ya sanya hirar ta tsagaita, suka gaishe su, Futuha ta amsawa Humaira faram-faram don tsakani da Allah so take ta wuce da ita gidanta ko don girki. Tana da mai aiki amma ko kusa ba ta iya abincin da Alhaji Yakubu ke so ba kullum sai ya yi mita wannan dalilin ne ya sanya take son tafiya da Humaira gidan koda na kwanaki ne ta nunawa yar aikinta yanda take sarrafa tukunya.

"Humaira sannu, bayin Allah har kun dawo hayyacinku wallahi."

Fadin Futuha, sai kuma Raihana ta sanyo wani zancen gudun kar a tada abin da zai sosa musu inda ke ?ai?ayi. Yassar da sun riga sun samu labarin komai kuma har a zuci ba su yi farin cikin ?addarar cikin Ummita ba sai ya sanyo hirar abinci yana kiran a kawo a ci ya kwaso yunwa daga kasuwa. Tasleem kuwa ?uri ta yi da idanunta akan Ummita ba ta ko ?iftawa musamman ma da Ummitan ta mike tsaye ta sauya wurin zama. Da ta kammala tabbatar da zarginta sai ta ga ta nan a tsaye ta mi?e har ayar da take ci na zubewa a saman kafet.

"Kut! Me nake shirin gani Mami?"

Ta yi furucin har a sannan idanunta na kan Ummitan. Gaba daya suka dube ta, Ummita kuwa ganin idanun Tasleem a kanta ya sanya ta Wago me take son fadi, wato dai itama ta gane tana da ciki don haka sai ta mike da sauri-sauri ta shige daki saboda kukan da ya tahomata na tsantsar damuwa.

"Me aka yi kike mana ihu? Ita kuma wannan me aka yi mata ta mi?e?"

Futuha ta jero tambayoyinta lokaci guda.? Tasleem ta cafe zancen tana kara hura hancinta da ya buWe saboda ciki.

"Ciki na gani jikin yarinyar nan."

A razane Futuha ta buWe idanunta ta dubi Humaira da kuma Raihana sannan ta maido hankali ga Tasleem.

"Wa kenan?"

"Ummita mana. Mun shiga uku, shikenan yarinyarnan za ta Sata sunan gidanmu, image din gidanmu zai lalace a idanun duniya. Meyasa ba a zubar da cikin ba Mami?"

Humaira wani tururi zuciyarta ke yi na Sacin rai, wato ita Tasleem ba ta ko tausayawa halin da Ummitan ke ciki ba balle tayata jimami. Kamar ta tofa sa kuma albarkacin Mamin dake zaune a wurin ta ja baki ta kuma zuba idanu ga Mamin don ganin me za ta ce. Mami kuwa ta gefen idanu ta ga irin duban da Humaira ke mata don haka nan da nan ta daure fuska.

"Idan ita ba ta Sata mana suna ba, ke gashinan ai kina ihun da makwafta za su ji su fahimci halin da muke ciki! Wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login