Showing 123001 words to 126000 words out of 189325 words

Chapter 42 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

231

addu'ar Allah ya tashi kafaWunsa.

A Waki kuma ta iske wani tashin hankalin, wato Ummita ce cikin halin na?uda, duk da ba ta san ya ake haihuwa ba amma daga yanda ta ganta tana ta juyi da rike riken baya tana kirarin mutuwa ya sa hankalinta ya yi mugun tashi. Babu wani abu da ya zo mata a lokacin sai mafarkinta. Ta shiga kwala ihun kira amma ina! Gidan an watse an tafi ga Abba don haka a guje ta fito zuwa sashen Anna neman Wauki cikin rufewar idanu saboda tsabar tashin hankali.
Tana shiga ta iske Annan tare da Jannat su na ta hirarsu cikin yare. Ganin yanda ta faWomusu sai da ta tsorata su. Cikin tsawa Jannat ta ce.

"Baki da hankali ne za ki faWo mana Waki ba sallama babu komai?!"

Humaira ta durkusa a gabanta tana kuka.

"Don Allah ki taimaka mu kai Ummita asibiti, haihuwa zata yi kar ta mutu."

Maganar ta Wan shigi Jannat, ko babu komai Ummitar ta yi mata bautar da wani a yaran Mamin bai mata ba, ta kuma fi Humaira yin biyayya a gareta. Anna ta yatsine fuska.

"Ke har kin gane haihuwa ce za ta yi? A ina kika san wata na?uda? Watakila ma juyi ne."

Jannat ta dubi Anna cikin yare take ce mata ai Ummita cikinta ya haura takwas, daga nan ta bi bayan Humaira bayan ta yafa mayafi saman kanta da ko dankwali babu, Humaira dai da ta gaji da maganganunsu ne ta kuma fitowa don tunanin kiran wayar Mamk da ya faWo ranta.

"Ke! Ina za ki je? Muje ki taimaka mata ta fito, bari na sanya a nemo mana abin hawa."

Tana kai wa nan ta fita farfajiyar gidan, motarta su Mami sun wuce asibiti wurin Abba da ita. Dawud ta yi karo da shi wanda shigowarsa kenan gidan bai ma san wainar da ake toyawa ba don wayarsa na kashe babu chaji.

"Yauwa maza nemo abin hawa Dawud, Ummita ke na?uda yi sauri."

Ai jin haka a gaggauce ya juya, can kuwa Humaira na kukan halin ciwon da ta ga Ummita ciki ya zo ya kuma lafa mata kaWan a haka ta daure ta zuramata hijabi ta taimaka mata ta mi?e suka fito ko takalmi Ummita ta kasa sanyawa sai salati take yi da kiran ta tuba a yafemata, Humaira ta nema mata gafarar kowa da ta ke mu'amala da shi. Wannan ba ?aramin tada hankalin Humaira ya ?ara yi ba. Har sun shiga abin hawa Jannat ta maida ta tace ta dauko kayan da aka haWa na tarbar haihuwa, itama sai lokacin ta tuna. Mami ce ta haWa komai ta ajiye a Wakinta saboda ba a son Ummita ta gani balle har damuwarta ya ?ara ninkuwa. Da saurinta kuwa ta fita ta koma Wakin Mamin tana lalube saboda tsabar ruWewa? ba ta ma gan shi a gefen madubi ba a ajiye cikin karamin akwati, dole sai Jannat ce ta je ta dauko bayan ta balbale Humaira da masifar ruWewar banzar da ta yi, acewarta.

A cikin Wan sahun ma haka Ummita ta dinga salati da nanata kalmar a nema mata yafiya har Jannat ta gaji ta ja tsaki wai ta fiye raki da yawa. Dawud na gefe kusa da Wan sahun shi kansa sai dai Ummita ta ba shi tausayi ya ji dama haka haihuwar take? Tun su na tafe Jannat ta yi waya ta sanar da Mami nan da nan ta ce su taho da ita asibitin da Abba yake don shima ya warware kawai dai maganin bacci ne bai sake shi ba acewar likita yana bu?atar hutu.

***
Gadan-gadan aka karSi Ummita don har ta soma? zubar da ruwan na?uda, gaba daya ahalin gidan hankalinsu tashe idan ka jira Jannat dake ta chatting abinta. Tashin hankalin Mami bai wuce na fatan Allah yasa abin da za a haifa ya mutu ko don ta huta da bibiyar da Wizzy yake mata musamman yanzu da Ummita ta shiga watan haihuwar kusan koyaushe sai ya yi mata wani shegen gajeran sa?o a whatsapp cewar KAR KI MANTA. Wannan kalaman su kadai yake ce mata daga su ba ya ?ara koda harafi Waya. Ga Mubarak kuwa, babban burinsa Ummita ta rayu kar ya rasa ta. Gaba daya ya kasa sukuni sai safa da marwa yake yi, Raihana dai na gefe tana danna counter tana jan salati yayinda Humaira take zaune shiru.
? Kafin a kai ga fitowa a sanar musu ta haihu suka ji kukan jariri ya karaWe inda suke, nan da nan duk suka nufi ?ofar suka yi cirko-cirko. Jimawa kaWan Waya a cikin Nurses din dake ciki ta fito fuskarta a sake tana kallonsu ta ce.

"Alhamdulillah, ta sauka lafiya an samu Wa namiji."

"Nos ya Ummitan?" Tambayar da Mubarak ya cilla kenan.

"Tana cikin ?oshin lafiya sai dai da alama ?ar shagwaSa ce sai kuka take mana tun bayan da ta haifo santalelan saurayin."

Wani guntun tsaki Jannat ta ja, su kuwa babu wanda ya ce uffan kowa da kalar tunaninsa. Humaira dai ko ma mene ne, ko wane irin tabo ne da yaron ita ta godewa Allah da har Ummita ta sauka lafiya ta kuma rabu da cikin da ta tsana lafiya. Hakanan ma tunanin Raihana. Babban burinta na kasancewar lafiya yar uwarta ta sauka.

Ga Mami kuwa ba su iya sun fahimci halin da ta ke ciki ba sai dai ga dukkan alamu akwai wata damuwar da take ciki don gaba Waya fuskarta ta nuna. Sun fi kyautata zaton kuma saboda lamarin haihuwar Ummita ne. Wa zai yi murna da haihuwar Wan da aka same shi ta fyaWe? Babu shi kam, amma kaddara ce babu yanda suka iya.

"Ku je gida zan zauna a wurinta. Ke Humaira ki yo mata abu mai Wan ruwa da zafi wanda za ta ci ki kawo."

Ba ta so tafiya ba tare da ta ga fuskar Ummita da ba amma sai ta daure ta amsa da toh ganin kamar har a lokacin fushi sosai Mamin ke yi da ita ba ta huce ba.

Bayan tafiyarsu idan ka dauke Mubarak da Mami ta kora don dubo ko Abba ya farka, babu kowa a asibitin sai ita (Mamin). Tana zaune ta yi shiru cikin tunani, toh yanzu idan ta kasance za ta kai wa Wizzy jaririn nan wa za ta sanya wannan aiki? Kuma ma a ina za su haWu? Ta dai san ba za ta taSa iya raba Ummita da abin da ta haifa a asibitin nan ba saboda babban asibiti ne kuma mai tsaro sosai ga kyamarori (CCTV) ta ko'ina don haka sai ta zaSi neman shawarar abokiyar shawararta a ire-iren waWannan gaSoSin. Wato Hajiya Lubna. Mi?ewa ta yi ta fice can farfajiyar asibitin ta danna mata kira, ringing hudu ta Waga ana biyar. Ko sallamar da dama ba ta wani WaWa su da ?asa basu yi ba Mami ta tare ta da sauri.

"Lubna ina cikin tashin hankali, ga dai yarinya ta haihu an sami namiji amma kaina ya ?ulle. Yanda yarannan suka sanya idanu a kan jaririn nan ta ina kuma ta wace hanya zan soma dauke shi na kai wa wancan Wan shegiyar?"

"Kai Maryam, wannan ai abu ne mai sauki duk kin bi kin wani sanya ni fargaba. Kar ki yarda ki sanar da shi an haihu ki bari har sai an kwana biyu yanda idanu ba zai dawo kanki ba. Duk lokacin da kika samu wata wawakekiyar damar ba sai ki fiddo da shi ba ko da haWin bakin wani amintaccen ma'aikacinku ba? A Soye dai aka fitar da shi ni na tabbatar ba za a zargeki ba, toh ke wa ma kike tunanin zai zargeki bayan wannan halin iya wuyar da kika gwada musu a rayuwa tsawon zama?"

Sauke ajiyar zuciya Mamin ta yi na samun Wan sau?i daga damuwarta.

"Shikenan, zan yi iyakar kokari na ganin bai samu labarin ba zuwa lokacin da? zan aiwatar da shirina."

Daga haka suka yi sallama bayan Hajiya Lubna ta ?ara jaddada mata lallai ta yi kokarin aikata hakan ko ba komai ?imar gidan nasu zai dawo idan ya so sai su san me za su yi a gaba don cimma sauran manufofinsu wadanda babu Wigon alheri.

***
Dakyar Ummita ta iya tsaida kukanta, sun gyarata tas an kuma yi mata sauyin Waki amman ko Waga kai ta kalli abin da ta haifa? da ya kwaso kamanninta tamkar an tsaga kara an karya? ba ta yi ba. Ya yi kukan har ya ha?ura ya tura yatsa baki yana tsotsa a haka ya yi bacci.
? Itama gajiya ta sanya bacci mai nauyi Waukarta. Koda Mubarak ya shigo haka ya iske su, ita bacci jaririn ma haka. Fuskarta ta yi wani fayau kuma ta Wan sauka ba kamar Wan kumburin da ta yi a fuskar ba kafin ta haihu. Ya kai duba ga jaririn, kamannin da yaron ya yi da Ummitan sai ya ji ya shiga ransa sosai. Tausayinsa kuma ya mamaye shi, ire-irensa su na nan birjik a faWin duniya waWanda ?addarar samuwarsu ta hanyar da ba ta sunna ba ta faWamusu musamman ma a yanayi irin na Ummita ta hanyar fyaWe. Amma hakan ba ya wanke tabon da suka riga suka goga daga ubansu, sai a dauki tsangwamar duniya a Wora a kansu alhakin da ace son ransu ne su ma za su fi kwadayin a haifesu ta hanyar aure. Ya ?ara kai duba ga Ummita, ya tabbata ko ganin jaririn ba ta son yi saboda tsana, fatansa Allah yasa watarana zuciyar wannan Uwa ta russuna har hakan ya jawo mata kaunar Wanta. A hankali ya sa hannu ya Wauki yaron ya yi mishi addu'a har ma da yi mishi huWuba bisa umarnin Abba wanda ya samu lafiya bayan Mubarak din ya shaida masa abin da ke faruwa ya sanya shi yiwa yaron huWuba da suna Ahmad. Abba kuwa ya tsaya domin rama sallar da ta kubce masa.

Yana nan tsaye bayan ya shimfiWa jaririn haka Mami ta shigo, ganinsa a nan sai ta haWe girar sama da ta ?asa, ba ta son abin da zai sanya Mubarak Win raSar Ummita da ma abin da ya shafe ta gaba daya. So take kawai ya tattata ya bar garin zuwa Camp kafin ya Sallo mata wani abin da ba za ta iya Wauka ba.

"Kai kuma me kake yi anan?"

Ya dubi Ummita gudun kar Mami ta Saro wani batun har ta yi sanadin tashinta daga bacci sai bai ce uffan ba ya juya ya fita, Mami ta Wan dubi inda suke kwance sannan ta juya ta rufe ?ofar ta bi bayansa. Ya sanar da ita sa?on Abban da ma huWubar da aka yiwa yaron da suna Ahmad.

"Sai kuma a rasa wanda zai yi sai kai? Meyasa zai yimin haka? Ina ruwanka da sabgar yaron da ba a san asalinsa ba?"

Mamaki ya ?ume Mubarak.

"Mami, wai lafiya kwanaki biyun nan ranki duk a Sace? Haba Mami, don Allah ki bar faWin hakan kada ki faWa gaban Ummita abin babu dadi."

Kamar ta kifa masa mari haka ya ji, shi kuwa sosai ransa ya Saci. Ga damuwar da Futuha ta jefa Abbansu ciki ga kuma wannan haihuwa da ya tabbatar za a sha daga da Ummita akan duk abin da ya shafi Wan.

"Toh ubana, sai ka faWamin abin da ya kamata da wanda bai ma dace ba ka ga ai zan ji tunda kai ka haife ni. Mubarak tun muna mu biyu ina mai ?ara gargadinka akan ka fita hanyar yarinyar nan ka kuma gaggauta cire ta a zuciyarka don na rantse ni dai Maryam muddin ni na haifeka kai ma ba shegen bane ba za ka taSa aurenta ba."

Ya ji kansa ya yi wani irin sarawa, a duniya ko mis?ala bai taSa fuskantar zai samu matsala daga Mami ba akan Ummita, ya fi tunanin zantukan su Anna da Jannat ne ya sanya ta zama haka amma ba wani abu daban ba. Madadin ya yi magana sai kawai ya ba ta hakuri ya bar wajen don ba ya so su haWa wata diramar a asibiti.

Da ficewarsa sai ga wayarta ta dauki ?ara, dubawar da za ta yi ba kowa ba ne face Wizzy. Sai da ta yi taga-taga za ta fadi da sauri kuma ta dafa ?ofar Wakin. Ganin mutane a wajen sai ta yi tunanin shigewa dakin da Ummita take, ta ji Nos ta ce za ta jima tana bacci wannan ya sa kanta tsaye babu shakkar komai ta shiga amsa wayarta.

"Mene ne? Kiran na meye ka ke yimin? Ba nace maka kar ka kuskura ka kirani har sai ta haihu ba?"

Ya yi ?ar dariya.

"Hajjaju kenan, kina tunanin za ki yanke ala?a da ni da wuri alhalin kina tare da abu mafi soyuwa a rayuwata? Ina! Ai ba zai yiwu ba, koda ace yau gudan jinina ya fito a duniyarnan ki sani kin samu jikan da zai kiraki da kaka ko da kuwa daga bangon duniya ne. Ni kiran da nayi shi ne, ya ake ciki? Ina magana a whatsapp sai wani you no care kike nunamin, to idan ba so kike nayi eh yane ba wato na yi dirar mikiya a gidan ki gaggauta sanar da ni halin da ake ciki. Ta fesar da cikin ko kuwa ya na nan a dun?ule?"

Wani irin zufa ya karyowa Mami. Ta ji hatta da jikinta ya Wau rawa, ta juya inda Ummita ke kwance ganin ta Wan motsa ya sanya da sauri ta bude ?ofar ta fita ba ta ce masa uffan ba har sai da ta ?arasa ficewa zuwa farfajiyar asibitin.

A Sangare Ummita kuwa, tsaf ta ji muryar Mami tana yiwa abokin wayarta magana akan me zai kirata, sai dai ko alama ba ta tsinkayi abin da ya ce ba. Motsin da ta yi na farkawa tana????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
kokarin tashi ya sanya Mamin ficewa a dakin, ta buWe idanunta tarr ga wani jiri dake kwasarta daga kwance tsabar yunwa. Tunanin maganganun Mamin take son yi amma lokaci guda kukan da jaririn dake gefenta ya tsala ya sanya ta dan karkata kai ta kalleshi. Kallo na ?urillah, burinta ta hango kamannin Ubansa ko ta samu shaidar da za ta nuna domin a binciko inda yake a cafke shi, sai dai kuma ban da su din waye ya taSa ganinsa? Kukan yake yi tana jin wani iri a zuciyarta, yanayin da ba ta taSa hangensa akan yaron ba yana zuwar mata a sannu sannu. Ta kasa mi?ewa zaune balle ta samu damar kai masa tallafi a haka su Humaira suka shigo Wakin suka ris?eta. Ganinsu sai ya sanya ta komawa ta kwanta sai kawai ta soma kuka a hankali, da sauri Raihana ta ?arasa ta W an rungume ta tana kokarin maida ?wallar da ta cika mata idanu.

"Ya isa hakanan don Allah. Kiyi hakuri tunda Allah ya raba lafiya yar uwa."

Humaira kuwa sai ta ajiye kwandon kayayyakin da suka taho da su ta shiga haWa mata bisa umarnin Mami da suka yi karo da ita za ta fice da waya a kunne, ta dai katse kiran ta musu magana kusan ba a nutse ba sannan ta sa kai ta karasa ficewa zuwa farfajiyar, su kuwa suka yo ciki. Raihana ta saki Ummita ta karasa ga Bebin da ya Wan jinkirta da kukan ta Wauke shi ta zuba masa idanu. Can kuma ta kalli Ummita, kamar ta ce kun yi kama sai kuma ta ji tsoron kar ta ji haushinta. A haka aka kwankwasa kofar dakin da sallama suka amsa aka shigo,? Baba Amina ce ?anwar Abba sai ko Abban da kansa a bayansa kuma Mubarak. Abban da kansa ya yi kiranta ya sanar da ita zancen haihuwar wannan ya yi silar zuwanta. Ita ta taimakawa Ummita ta sha shayin ta ci abinci kadan, anan kuma Abban da ita suka hadu wajen yiwa Ummita nasiha da nunamata muhimmancin yarda da ?addara. Sosai kuma maganganunsu suka shige ta, sai anan ma take ji Mamin ta je gida ta dawo a bakin Abba. Bayan fitar su Abban da Mubarak ne kuma Baba Amina ta zage wajen taimaka mata ta yi wanka ta shirya tsaf, shima yaron ta wanke shi ta sanya mishi sabbin sutura, wankewar da ya sanya kamannin mahaifiyarsa ya ?ara bayyana muraran a fuskarsa hatta da Wan ba?in tabon da Ummita keda ahi a gefen kumatunta haka jariri Ahmad ma. Ta yi ta satar kallonsa cike da sha'awa ga wata iriyar ?auna da ta yiwa zuciyarta ?awanya. Ba zato ta ji Baba Amina ta mi?a mata shi har ya kusan faWuwa ba don Allah ya sa ta tarba da hannunta ba.

"Daure kiyi hakuri ki ba shi ya sha Ummi, in sha Allahu wataran zai zamo maki abin alfahari. Kar ki duba hanyar da kika same shi, kiyi hakuri ki yarda wannan wata jarrabawarki ce da ba ki isa kin kufce mata ba. Watarana sai labari da yardar Allah."

Kwalla suka cicciko mata, nan Baba Amina ta taimaka mata yaron kuwa ya cafka ya soma tsotso kamar zai tsige mata fata, haka yana sha tana jin wani irin ciwo a mara ga zafin fisgar da yake yi har hawaye ta soma tana jujjuya kai. Humaira da ta zuba musu idanu sai ?arar wayarta ta katse ta. Ganin sunan Fadeel na yawo saman screen ya sanya ta fita a dakin fuskar dauke da ?aramin murmushi. Da sallama ta Waga wayar, ya amsa mata a sake.

"Boddona wato idan Fadeel ayyuka suka hana shi kiranki, ba za ki dauki waya ki kirashi ba ko?"

?ar dariya ta yi kaWan da har ya tsinkayo sautinta, ita sau da dama yanayin shagwaSar da muryar da Fadeel kan yi mata na ba ta mamaki da kuma dariya, shi dai a lallai ta ji tausayinsa koyaushe.

"Oh, dariya ma na baki? Toh aikuwa yanzu zan bar dukkan abin da nake yi ki gan ni da yammacin nan."

Ta dan rausaya idanu kaWan tana murmushi.

"Ka yi hakuri toh, ni ba na ma gida, Ummita ta sauka lafiya muna asibiti."

"Allah Sarki, me aka samu?"

Da sanyin jikin tausayawa yaro Ahmad ta amsa.

"Namiji ne, an masa huWuba da Ahmad."

Ya yi addu'ar fatan alheri gareshi kafin kuma ya ?ara kwantar mata da hankali da nunamata su ne suke kusa da ita, su kasance masu jarumta su dinga ?arfafa mata gwuiwa. Kamar dai sun haWa baki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login