Showing 102001 words to 105000 words out of 189325 words

Chapter 35 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

205

wane irin rashin tunani kike aikata mana? Kina haukar tonawa yar uwarki asiri?"

Jin haka sai Tasleem ta koma ta zauna, ta ja guntun tsaki ba ta ce uffan ba. Ita wannan duk bai dameta ba kamar yanda kawayenta da dangin miji da ma abokan hulda da ake kunya za su samu labarin cikin Ummita ya zamar musu abin habaici da zagi. Futuha kuwa, babu abin da take hangowa sai irin yanda labarin zai karaWe social media alhalin ta gama karaWe ko'ina da nuna hotunan su Ummita tana shaidawa duniya su din kannenta ne. Yanzu idan zancen nan ya fita ai ta shiga uku.

Yassar ne ya basu labarin duk fadi tashin da aka yi don ganin an zubar amma abu ya faskara. Tasleem ta ja tsaki karo na biyu.

"Ba dai abi hanyar da ta dace ba. Ni wallahi da tun farko an faWamin da kaina zan zo na yi mata alluran da na tabbatar sai cikin ya zube. Amma yanzun ma ai ba ta Saci ba, me zai hana a markaWe shi?"

"Wai Sis Tasleem meyasa ba ki da imani ko ?an?ani? Kina magana babu ruwanki idan an yi ko Ummita ta mutu ta rayu."

Tasleem ta harzu?a da zancen Raihana.

"Da wannan abin kunyar ba gwara ace ma mutuwar ta yi ba! Ai gwara mu lulluSe ta cikin sutura a kai ta kabarinta da dai ta haifa mana shege."

"Sai dai ke ki mutu! Ai dama wanda bai sonka ba zai taSa sonka ba. Na kuma gama gas?atawa ke din azzaluma ce da ba kya kaunar naki. Ciki kuma ?addarar Ummita ce da bai wuce faWawa kan kowa ba koda kuwa matar auren ce. Nawa aka yi? Yanda ba kya kaunarmu har abada ba zamu taSa kaunarki ba, yanzun ma albarkacin masu albarkar kika ci da ban Waga yatsuna na watsa a saman fuskarki ba."

Humaira ce ke wannan zantukan cikin tsananin rufewar idanu jikinta har tsuma yake yi. Tasleem ta yi la?was, ina za ta mance sha?ar da ta yiwa Anti Jannat, me ya yi mata zafi da za ta yarda ta yi katoSarar da itama za a sha?e ta ga tsohon ciki. Falon gaba daya aka rasa mai tankawa Humaira, su Yassar wadanda sun soma hankali sun ragewa zu?atansu ?iyayyar Humairar ba wanda ya goyi bayan zantukan Tasleem din.
Mami kuwa kamar yanda ta saba danne bakin cikinta da soyayyar yarannata a lokuta barkatai don siye zu?atan yaran wannan karon ma haka ta yi.

"Koda wasa kar na ?ara jin makamanciyar wannan magana daga bakinki. Kina kiran mutuwa ga yar uwar da ke ganin girmanki. Ban san me yarannan suka tare maki ba. Kina dai kan gaSar haihuwa ki ji tsoron Allah."

Mami na kai wa nan ta mike tana Sata rai ta kama hannun Humaira suka yi daki wurin Ummita. Itama Raihana ta mara musu baya.

Tasleem ta ja tsaki.

"Ni ban ga amfanin abin da Mami take yi ba. Duk lalacewar naka, naka ne. Ta guji ranar da wadannan mutanen za su yi mata butulci."

"Uwar biyu kenan, sai kin zauna da su sosai za ki fahimci ba su da kowace matsala. Ni kaina a farko rashin ba Humaira dama ya sanya ni tsanarta amma yanzu da na dan zauna na saki jiki da su na fahimci kirkinta. Wallahi sosai na tausaya musu sadda suka yi nesa da mu, na kuma gane ina kaunarsu a jinina, ba zan iya fasalta yanda labarin cikin nan ya jefa ni ba. Duk da ban kai Yaya Mubarak shiga damuwa ba."

Fitowar wannan zancen daga bakin Dawud ya ba Futuha da Tasleem mamaki, dama akwai ranar da Dawud zai fadi mai kyau akan su Humaira? Yassar wanda shima bai jin ?insu ko kuma kaunarsu a zuciyarsa, dariya ya yi.

"Kai babban yaya ai ya faWa, rannan Anna ke fesamin wai son Ummitan yake yi. Tana ta masifa da tsinewa zancen ta ce ko bayan ranta ba da yawunta ba."

"Wallahi ba za ta saSu ba. Tab! Me Yaya Mubarak zai yi da sauran ?an ta'adda?"

Futuha ta yi furucin a zafafe. Tasleem kuwa ta ma kasa cewa komai ji take kamar abin da ke cikinta zai fito idan ta ?ara magana saboda tsabar takaici da ya yi mata lulluSi a ?irji.

"To sai me? Ni wallahi don ya riga ni furtawa ne amma na ?udurta ni zan aure ta matukar wancan Sahabi ya guje ta."

Cewar Dawud. Kiran sallar azahar ne ya tashi mazan, Tasleem ta dubi Futuha.

"Me kike tunani akan maganar cikin nan?"

Futuha ta yamutse fuska.

"To me zamu iya yi tunda an binne zancen ba a sanar da mu ba sai da ya fito?"

Tasleem ta yi ?wafa. Ta ciro wayarta ta kira Jannat ta fesamata abin da ke afkuwa. Jannat ta feshe da muguwar dariya.

"Dakyau! Ki ce abu ya yi dadi? Toh ai wannan maganar ba abin a Soye ba ne. Ke ban da abinki tunda har ya afku ai zai fito. Kawai mu juya zancen mu yaWa cewar dama karuwancinsu suka tafi, itama Humaira an keta mata haddi. Idan har duniya ta yarda ta amince kinga ai shikenan? Ban da Abbanku da DPO akwai wani da ya san an gan su kafin a kama su sun gudu?"

"Aa." Tasleem ta furta da sauri.

"Toh kinga idan ma an bada wannan hujjar zamu ce a kawo shaida, wacce kuma babu ita ba za a same ta ba."

Shiru dai Tasleem ta yi, Futuha ta zubawa Tasleem idanu, so take ta kammala wayar don ta labarta mata abin da Antin ta ce.

"Anti toh dan jira zan kiraki."

Daga nan suka ajiye waya, ta labartawa Futuha yanda suka yi. Tun ma kan akai aya Futuha ta hau girgiza kai.

"A'a, a'a, Tasleem kar ku yi haka. Nidai Futuha babu hannuna ciki. Ba fa sunansu kadai za a Sata ba kenan har da na gidanmu. Nikam ba za'a yi haka da ni ba gaskiya, count me out!"

Tasleem ta harareta kawai sai ta yi shiru ba ta ce uffan ba. Futuha ta zubamata idanu, ta san halin muguntar Tasleem, shirunta na nufin abubuwa da dama.

"Ina fatan dai ba kina son cemin za ki haWa kai da Anti Jannat ku aikata wannan babban kuskuren ba?"

"Sai aka ce maki bani da hankali ko? Mtsw."

Ta ja mata tsaki ta mike ta nufi dakin Anna amma ta gama ?udurtawa a ranta babu fashi. Idan har ?imar ita kanta ?ar tiktok Futuha zai taSu a zage ta a idanun duniya toh wannan daidai ne. Gwara ma su yi hakan kawai.

***
Mami ta taushi Ummita dakyar ta samu ta yi shiru, ta yi musu ?ar nasiha sannan ta fito. Kai tsaye dakinta na nufa ta dauki waya ta kira Hajiya Lubna. Komai dake afkuwa ta zayyane mata. Ta kara da faWin.

"Yarannan sun tada hankali lallai sai dai a zubar da cikin Ummita, kinsan dai yadda muka yi da Sadik Wizzy. Ina tsoron su kwatanta wani mugun abun."

"Haba Maryam, sai ka ce ba ke kika haife su ba. Ba za ki yi musu jan ido ba? Wai ni Maryam duk ba wannan ba, ina aka kwana batun kai Humaira wajen Babandi?"

Mami ta sauke ajiyar zuciya gami da ?ara gyara zaman wayar.

"An kashe wannan zancen, gobe zan kai ta. Na fi so a yi a ?are, na gaji ba zan iya ci gaba da wannan pretending din ba. Idan an hana ta auruwa a tura ta bariki kawai mana ba shikenan ba? Na tsani wannan Fadeel mai ba?in nacin tsiya, Babandi ya tabbatarmin muddin dai bai fice a rayuwarta ba to lallai shi zai rusa komai. Mun kasa jefa mata ?iyayyarta a zuciyarsa kamar yanda ita muka jefamata, ba na nasa kaWai ba har na dukkanin wani namijin da zai furta mata kalmar so. Kamar kuma yadda muka yi wa FATIMA har ya zamo silar rabuwarta da Yusuf. A ?arshe kuma muka zama ajalinta ta hanyar yi mata turen aljani ya kashe ta."
Wannan zancen ne ya yi dirar mikiya a kunnuwan Futuha wacce ta nufo Mami don sanar da ita yanda suka yi da Tasleem, ta tsaya cak a ?ofar Wakin cikin wani irin kakkarwar jiki da zufa.
Juyowar da? Mami za ta yi ta ga mutum tsaye cak a bakin ?ofa, ba ?arama razana ta yi ba wannan ya sanya ta ajiye wayar cikin rawar murya ta ce.

"Ke kuma me ya kawoki nan?"

Futuha ta karasa shigowa dakin sosai har lokacin bakinta a hangame saboda tsananin mamakin da ya gama baibayeta.

"Mami, duk ke kika aikata waWannan abubuwan?"

Cikin sauri Mamin ta ?arasa ta rufe ?ofar Wakin, ita dai Futuha bin ta take yi da kallo har lokacin kamar a ranar ta soma ganinta a duniya. Cikin kausasshiyar murya ta amsa.

"Eh ni ce, na aikata kuma ina kan aikatawar, ina kuma gargadinki da babbar murya! Bar ganin kin fito daga tsatsona na rantse maki matukar kika yi gangancin tonan asiri koda a wurin yan uwanki ne sai na manta da ni na haifeki, zan iya daukar kowane irin mataki muddin dai bu?atana za ta biya."

Futuha ta jinjina kai ta kasa ma cewa uffan don gani ta yi tamkar wata Mamin ce daban a gabanta. Sai kuma ta daure ta hadiye fargabanta ta ce.

"Mami, kenan duk wannan kauna da muke gani kamar kin fi yiwa su Humaira a kanmu duk ba gaske ba ne? Har fa kidnapping din da aka yi naji kin ce ke ce."

Ta juya tana wani mugun murmushi ta karasa ga madubi tana kallon kanta.

"Wawaye, ina ku ka taSa gani ko ji uwar da ta so Wan wani sama da nata? Babu ita kaf faWin duniyarnan. Idan ma akwai toh ni Maryam ba na cikinsu."

Sai ta ?ara sakin murmushi mai haWe da ?ar dariya.

"Tun auren Yusuf da Fatima, nake ?unshe da ba?in ciki a zuciyata, kakkarfan shaidar da aka yimin a garinmu da ma makwaftan da muka zauna da su a garin nan kafin rasuwar mahaifina na cewa ina da ba?in kishi kuma har akan kishin ne na taSa marin (wani Wan uwana da mahaifina ya so na aura) a bainar jama'a, na zazzagi uwa da ubansa kawai don ya ambatamin sunan tsohuwar budurwarsa kuma yar uwata da aurensu bai yiwu ba yana mai yabonta a kan idanuna. Tun daga wannan ranar ne na fasa aurensa. Ba shi kadai ba, na rabu da mutane da dama saboda kishi, saboda tsanar da na yiwa kishiya, mahaifina ya taSa neman aure na wanki ?afa har gidan da ya je nema na Sata sunansa kuma aka fasa auren. Ba?in shaidar da na samu sanadiyyar zazzafar kishi ya sanya da Yusuf ya shigo rayuwata matsayin saurayin da bai taSa aure ba, ya shiga zuciyata sosai. Na sa a raina ba zan taSa nunamasa zazzafar kishina ba saboda a lokacin labarin komai da na aikata a baya ya je kunnensa ta wurin munafukai, wannan ta sanya ya yimin gwaji kala-kala kamar ya yimin wasan yana da mata auren haWi, yana da budurwa da dai sauransu. Ni kuma na danne bana nuna masa Sacin raina har sai da ta kai ya ?aryata zantukan mutane a kaina. Amma fa duk radda ya yimin irin wannan idan na koma gida ranar ko tsinke ba zan Wauke da sunan aiki ba, kuka kuma zan yi shi. Babu wanda ya isa ya taSa ni a ranar ya sha. Mahaifina ya rasu dab da aurena da Yusuf. Bayan aurenmu babu irin faWi tashin da ba mu sha ba saboda rashin kuWi. Soyayyar da nake yiwa Yusuf ta sanya ban taSa gujemasa ba daidai da kwayar zarra. Kasuwanci iri iri babu wanda bai yi ba har siyar da kayan miya, gwanjo, da dabino. Kowanne sai an fara rimi-rimi sai lamarin ya Saci."

Mami ta haWe girar sama da ta ?asa ta juyo tana duban Futuha dake tsaye tana sauraronta ta cigaba da magana.

"Mahaifin Ummita ya fi mijina rufin asiri sosai, shi mutum ne mai arzi?i, matarsa duk sabgar dangin miji ta fi kowa gayu da kuma kyauta saboda mijinta yana da kuWi. Ba ta da ta?ama balle wani abu wai shi girman kai, wannan kyawawan Wabi'unta da na tsana, da su ne ta siye zu?atan uwar mijina kafin ta rasu, ta yi bake-bake a wurin yan uwan Yusuf, ba a ganina da mutunci sai ita. Duk yawan kirkina saboda mijina ba shi da kudi sai na zama tamkar mujiya. Eh uwar mijina tana sona amma soyayyar da take yiwa Jamila ya wuce gejin nawa. Saboda tsabar yanda tsanar Jamika ya rufemin idanu har gani nake yi ba a nunawa yarana kauna a lokacin alhalin ita ko haihuwar ba ta samu ba daga ta samu cikin sai ya Sare. Haka na jero yara biyar Mubarak,Yassar, Dawud, ?assim da kuma Ke. Wannan? lokacin ne kuma Yusuf ya zo min da labarin ?ara aure bayan mutuwar mahaifiyarsa, a sannan kuma ba laifi asirinmu a Wan rufe yake. Yusuf har shago yake da shi a kasuwa yana siyar da kayayyakin agogo wanda ?aninsa Muntari ya buWe mishi. Wannan ma ya ?ara tsananta tsanar Jamila da Muntari a zuciyata ganin wato dai arzikinsu muke ci, da azumi haka Muntari ke sauke mana kayan abinci, da sallah, Jamila ke zuwa ta kawomana kayan fitar sallah wannan abu ya tsayamin a ?ahon zuci. Maijidda ita ce macen da ta soma lura da tarin ?iyayyar da nake yiwa yar uwarta, akwai sadda ta taSa ganina muraran ina yiwa Jamila barbaWen magani a abinci wanda daga shi ne ta tsane ni ta kuma ce Jamila ta yi hankali da ni.
? Toh zuwan da Yusuf ya yi da batun ?ara aure ya yi mugun Wagan hankali amma damuwa ko ta Wigo ban gwada masa ba, a farko da na Sata rai, sai ya rude da rarrashina, sai kawai na fashe da dariyar ba?in ciki na nunamasa tsokana ce kawai amma nikam bani da matsala da aurensa. Da wannan ya auro Fatima wacce ya haWu da ita a kasuwa ta rako Dadarsu siyayyar kayan auren dan uwanta Umar. Shikenan soyayyar ta kai su ga aure. Anna ba ta tare da ni a sannan saboda mijina ba shi da kudi babu wurin da zamu ajiye ta, ita kanta a sannan zagina take yi wai don me zan ma?ale nace sai Yusuf da ba shi da ko keken hawa. Nidai son da nake yi masa ya hana ni karSar ?orafe ?orafenta. Ba ta damu da zuwa gidana ba a lokacin.
Aka yi auren Fatima da Yusuf, jininta ya hadu da Jamila. Madadin ni da muke dan shiri da Jamilar a baya, sai suka dinke da Fatima suka zama tamkar wasu ?awaye, a sannan ina da cikin Tasleem, na kai zuciyata nesa na danne da taimakon shawarar sabuwar ?awata Lubna da muka hadu a wurin wani bikin tsohon ubangidan Yusuf na kasuwa, mijinta mai arziki ne lokacin yana rike da matsayin Chairman. Da taimakonta na san Boka Babandi, muka ni?i ?afa daga nan har Katsina wajensa ba tare da sanin Yusuf ba. Na samo magungunan hana Fatima daukar ciki muka dawo.
Cikinta na farko kuwa ya bi rariya, ni ce mai jinyarta da nuna mata ?ololuwar kulawa. Dadarta koda ta zo ta dinga sanyamin albarka da yabona. Yusuf kuwa tamkar ya haWiyeni ganin a lokacin ko arba'in din Tasleem ban yi ba na haihuwa amma ina fama da kula da Fatima, wannan dalili ya siyomin sabuwar kauna a zu?atan yan uwan Yusuf.
? Kamar kuma a mafarki ina dauke da karamin cikin Raihana sai ga Fatima da ciki har watanni biyar ya soma fitowa a jikinta, ba karamin firgita nayi ba da na gani saboda ko kadan ban ga wasu alamomi ba. Kuma na rasa yanda aka yi ko a hira ba ta sanar da ni ba. Hankalina ya yi mugun tashi, sai da na kai zuciyata nesa sosai kafin na iya danne damuwata. Ga wani irin soyayya da Yusuf ke nunawa Fatima har a gabana wanda nake ji kamar na sha?e su duk biyun na huta. Ganin haka ni da Lubna muka ?ara mi?ar hanya wurin Babandi, anan ne na je masa da bu?atar jefa tsanar Yusuf a zuciyar Fatima yanda ko sunansa aka ambata sai ta ji haushi. Babandi ya ban tabbacin ba ma Yusuf ba, kowane namiji sai ta tsane shi a rayuwarta muddin ya haWa ta da wani arnen aljani. Da wannan na tattaro duka chanjina na ajiyemasa. Muka rabu da zummar zan ga aiki da cikawa, ya kuma ban wani haya?i yace duk sadda ta shiga halin ?unci da kuka marar iyaka na yi mata haya?in. Wannan zai ?ara tasirin tsanar a zuciyarta. Da wannan muka rayu, Yusuf ya shiga tashin hankalin sauyin Fatima. Akwai radda ta taSa sha?e masa wuya dakyar aka SamSare ta sai da na nemi taimako a waje, daga wannan ne kuma ya aikawa Dada sa?o ta zo takanas daga Nijar aka tafi da Fatima saboda ta rantse muddin aka bar ta ta cigaba da rayuwa a gidan za ta kashe shi ko kuma ta kashe kanta. Na yi kuka sosai kamar raina zai fita a gabansu, na ce su kyale ta ayi mata magani a nan idan har larura ce, Dada ta dinga rarrashina ta ce gwara ta tafi da ita. Daga wannan ranar ne na rabu da Fatima, rabuwar da har gobe ba ta ?ara tako Nijeriya ba. Wannan abu ya yimin masifar dadi, cikina nada watanni shida, Jamila ta haifi Wiyarta mace mai sunan mahaifiyar Jamila, Rahina suke kiranta da Ummita. Sun yi gagarumin sunan kashe kudin da naji tamkar na dora hannu a ka nayi ihu da kuka? ina ji inama Yusuf keda kudin Muntari. Da wannan na soma tunanin duk runtsi sai dukiyar Muntari ta zama rabon Yusuf watarana."

Mami ta numfasa ta karasa ta zauna gefen gado, ganin haka Futuha itama ta nemi wuri ta zauna, wasu abubuwan za ta iya tunawa wasu kuwa ba ta da wayo. Ta dai san Mubarak na yawan yabon mahaifiyar Humaira da kaunar da ta nunamasa, yayinda su Yassar suka tsaneta saboda tsanar da ta yiwa Abbansu. Maganar Mami ya katse tunaninta.

"Haka rayuwar ta cigaba har na kusa haihuwa, Yusuf gaba daya ya rame ya tashi hankalinsa saboa Fatima, ya kai mata ziyara har sau biyu daga nan ne hankalina ya yi mugun tashi, wato soyayyar da Yusuf ke yiwa Fatima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login