Showing 6001 words to 9000 words out of 189325 words

Chapter 3 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

193

dai tana son Ibb Gusau.

"Ke malamin fa ?arshe ne wallahi, ya haWu ba zan nuna masa komai ba. Nidai fatana Allah yasa ya karSi tayina ya aure ni. Wallahi zan jure dukkan wulakanci muddin zai yarda ya so ni. Yau in sha Allahu sai na nemo lambar wayarsa."

"Lallai, kina ruwa kusa da breaker." Cewar Tasleem.

Fuska dauke da damuwa Futuha ta amsa.

"Ai na yi ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nisa ma cikin ruwan Tasleem, ki dai yi fatan kar Allah ya jarabceki irin yadda ya jarabtan."

Tasleem cike da mamaki ta ce.

"To tsaya, don iskanci kwanakin nan da wa kike waya kike kashe murya kina furta kalaman so?"

Yamutsa fuska Futuha ta yi.

"Mujahid ne, wallahi akan dole nake kula shi, shi ke fa taya ni da attendance da ma test. Kinga kuwa dole ce ta haifar da shiga lamarinsa. ?an taya ni na ci jarrabawa ne."

Suka she?e da dariya. Ba jimawa suka fice zuwa falo.

Ita Tasleem nursing take karanta duk ta fi su kwakwalwa da basira, tana da kokari sosai shiyasa wasu lokutan take samun alfarma daga Abba koda zai yi hukunci ba ya tsaurara mata, yayinda ita kuwa Futuha ke karantar Mass Com, ba laifi tana da kokari sai dai matsalar tun zuwan wani matashin malaminsu makarantar ta susuce ta zama shiritacciya. Wannan yasa lokaci guda ta kwaso C.O a zango na biyu a aji na biyu a makaranta, hakan ba ?aramin Sata ran Abba ya yi ba. Shi mutum ne da ya tsani asarar kwandalarsa a abinda ba zai kawo mishi ribar komai ba sai asara, hakanan mutum ne mai son abin hannunsa sosai, dakyar Mami ta shawo kansa ya aminta da tura Mubarak karatu, ya kuma ce daga kansa ya rufe, sauran kowanennsu sai dai ya yi a jami'o'in Kasarnan.

Dawud na ajin karshe a jami'a inda yake karantar Accounting, Yassar wanda tare suke tafiya da Dawud din adalilin maimaicin aji da Dawud ya yi a sakandire, shi kam Bussiness ya ke karanta, su biyun tare suke da Futuha a jami'ar Bayero. Sai ?asim dake karantar fannin Kasuwancin shima dai inda yake aji na uku a jami'ar Maitama Sule Kano.

Wannan kenan.

Humaira jin Wakin ya yi shiru ta buWe idanunta, ajiyar zuciya ta saki tana mai jinjina wannan rayuwa ta Futuha, shakka babu ta Worawa kanta wahala, koda dai faWan da ba ruwanka, daWin kallo gareshi. Mikewa ta yi ta nufi banWakin bayan ta Wauki zanin wankanta da brush. Sai da ta wanke jikinta tsaf kafin ta fito ta soma shiri cikin doguwar rigarta ?ar kanti ruwan madara, tana daga cikin suturun da Kawunta ke siyamata. A dai fannin sutura daidai gwargwado itama tana da su, sai dai ace ba wasu masu tsada ba ne, ba kuma masu kyawun gaske ba ne idan an haWa da na su Tasleem da ta gansu a jikinsu a kwana Wayan nan. Tana cikin kwashe shimfiWarta sai ga Ummita ta shigo da sauri, ganinta ta saki fuska sosai.

"Au Humaira ashe kin tashi, kinga mu ma makaranta za mu wuce. Mami tace idan kin kammala ga abin kari can an rufemaki a kicin, idan ma ba ki gani ba ki tambayi Ladidi mai aikin Mami tana falon tana gyara."

Duka wannan zancen tana yi ne lokaci guda da sauri tana bincike dirowarta, littafi ta zaro ta dauki jakar makarantarta sai safarta a hannu da takalmi ta kama hanyar fita.

"Toh, sai kun dawo."

FaWin Humaira, Ummita ta amsa ba tare da ta tsaya ba sakamakon hon din mota da ake faman dannawa. Ganin haka yasa Humaira ?arasawa jikin windon wanda ake iya hango farfajiyar gidan, ganinsu tayi gaba Waya a motar sai Tasleem dake tsaye a waje rike da ?ugu, Ummita na karasawa ta hau ta da masifar wai tana Sata musu lokaci.

"Allah ya baku hakuri."

Ta ji Ummitan ta fadi sannan ta shige motar da sauri, tsaki Tasleem ta ja ta bita da harara sannan itama ta faWa ciki, direban ya ja suka fice. Ajiyar Zuciya Humaira ta saki ta bar jikin windon, mamaki fal a ranta na Wabi'un ?an matan. Ta lura ba su san wani abu wai shi kara da mutunci ba, haka dai ta ture zancensu ta hau gyaran Wakin. Abin ban haushi a saman gadon Futuha daidai da Wan kamfenta da ta cire anan ta bar shi a ajiye, aikuwa haka ta tsallake gadon, ba ta yi karambanin gyara musu gadajensu ba, da ace dai Ummita ba ta gyara nata ba to tabbas wannan kam za ta gyara mata, ita din mutum ce mai mutunta DAN ADAM.

Fita waje ta yi, falon babu kowa hakan yasa ta nufi hanyar kicin da ta nakalceshi tun jiya da Ummita ta tattara kwanukan abinci ta nufi ciki. Anan ta iske wata mata da ba za ta girmi Mami ba tsaye tana goge gas nan ta fahimci ita ce Ladidi. Ta gaisheta a ladabce, matar ta amsa fuska a sake.

"Ba?uwarmu Humaira ko? Sannunki da zuwa, ga abin karinki can."

Ta fadi tana nuna mata wani tireda aka Wora filet da kofi sai kayan shayi da flask a kai. Humaira ta murmusa.

"Nagode, amma zan sharo dakin sannan na ci."

"Ai da kin bar shi, idan na kammala da nan sai na share."

Girgiza kai Humaira ta yi.

"Babu komai kar ki damu zan yi ai ba wani girma ne da dakin ba."

Ladidi ta amsa da toh gami da yi mata sannu. Tsintsiyar ta nunamata da makwashin shara, ta dauka ta nufi dakin. Sai da ta kammala tas kafin ta koma ta wanke hannu ta dauki abin karin ta koma daki don ba ta jin za ta iya ci a falon. Bayan ta kammala ne ta fito da niyyar maida kayan kicin suka yi karo da Ladidi.

"Yauwa, ki je inji Alhaji wai za ku yi sallama da Kawunki zai wuce."

Ladidi ta karSi kayan hannunta ita kuwa jin haka jikinta ya yi sanyi, ta koma dakin ta dauki karamin mayafinta ta yafa a kai. Falon Abban ta nufa, Kawun ne kadai a ciki ya yi shiri tsaf na tafiya, sallamarta ya sanya shi dubanta. Ta dur?usa ta gaida shi, ya amsa sannan ya ce.
"Toh Shatu, ni zan koma. Ina fatan zaman nan zai maki dadi fiye da rayuwar da kika yi a Maine. Ina kuma ro?onki da ki zauna da kowa lafiya, kamar yadda suka karSeki da hannu bibbiyu, kema ina son ki rike su haka. Gidan mahaifinki ne, nan Win dai shi ne gatanki, ba ki da sama da nan. Sannan don Allah ki zama mai hakuri, na sanki sarai muddin aka taSo ki ba? kya kai zuciyarki nesa. Abu na gaba, kar ki sake ki bada kofar da za'a ga wallenmu, a ga kamar mun gaza a wurin ba ki kyakkyawan tarbiyya a iyaka zaman da kika yi hannunmu. Sannan addu'a, ki yawaita addu'a da ibada in sha Allah sun ishe ki."

Humaira wacce tuni fuskarta ta yi jage-jage da ruwan hawaye ta sa hannu ta share su. Gani take yi tamkar shikenan fa za ta yi nesa da asalin garin da aka haifeta, shi kenan ganin Kawu da Tanti Hafsatu matarsa? zai yi wuya a gareta. "Nagode Kawu, in sha Allahu zan kiyaye abin da ka ce. Amma ai Abba zai dinga bari na naje maku wataran ko?"
"Me zai hana na bar ki Mamana?"
Jin maganarsa gaba daya suka dub shi, sam ba su san ya shigo falon ba balle kuma tsayuwar da ya yi a bakin? ?ofar da za ta sada shi da sashinsa na ainahi.? Ya karaso da murmushi saman fuskarsa ya zauna, ta gaishe shi, ya amsa.
"Ban maki al?awarin nan kusa ba, amma da yardar Allah duk sadda na tashi aurar da ke, zan kai ki har Maine ki kwana biyu. Nidai fatana yanzu shi ne? ki saki jikinki ki zauna da mu bisa kauna. Kin ji ko?" Ta gyaWa kai tana murmushi mai dauke da kunya jin wai Abbanta ya ambaci aure. Ita duka nawa ma take yanzun a shekarunta goma sha huWu? Koda dai, akwai sa'anninta su Murja, Fatsima da ma sauransu wadanda duka an aurar da su a can. Tashi tsaye da Kawun ya yi ne ya maido ta hayyacinta. Ta mike itama, Kawu suka yi sallama da Abba. Daidai nan Mami ta shigo da sallama, tana sanye da dogon hijabi har ?asa, gaida Kawu ta yi sannan ta yi mishi sallama. Sai a sannan Humaira ta gaishe ta. Humaira ta takawa Kawu har wurin motar Abba inda direban Abban zai kai shi tasha. Tana hawaye haka ta tsaya har Kawun ya shiga motar, hannu ya Wago mata itama haka har suka fice daga gidan. Ji ta yi zuciyarta ta yi wani irin tsinkewa, haka kurum ta ji wani irin tausayin kanta ya kama ta. Kanta Abba ya dafa da muryar rarrashi ya ce. "Haba Mamana, kukan fa? Ya isa haka, ba fa rabuwa ku ka yi kenan ba, in sha Allahu zumuncin ba zai yanke a nan ba matukar akwai rai da lafiya,? ki kwantar da hankalinki nan ma gidanku ne." Ta gyada kai, daga haka suka shige gidan. Mami dake tsaye a windon falon tana kallonsa, itama juyawa ta yi ta koma Wakin Abban hawaye a saman fuskarta wanda ita kaWai ta bar wa kanta sanin ma'anarsu.
A falon Abban suka zauna yana fadin, "Bari dai nayi hira da Wiyata kafin na fita aiki ko?" Ta yi murmushi har sannan yatsunta na saman fuska tana goge ruwan hawaye.
"Ba ni labari toh, meyasa ba ki shiga makarantar boko a can ba? Kawunki dai ya cemin kina zuwa islamiyya har kin yi sauka, na kuma ji dadin hakan."
Ta gyara zama ta amsa a nutse.
"Dada ce ta ce ba zan je ba saboda koda na fara ba lallai na ?arasa ba. Ta ce kuma faransanci ne."
Abba ya yi shiru, ya gane sarai manufar Dada, wato dai ta san cewa ko ba jima ko ba dade ranar nan za ta zo da Humairar za ta dawo hannunsa, sai dai ya so ace ko na faransancin ne ta yi, da irin haka biyu babu. Ya tuna shawarar da Mami ta ba shi a daren jiya da suke maganar karatun Humairan.
"Zai fi dai ka sanya ta a inda za ta koyi sana'a koda kuwa na girke-girke ne, kasan can idan ma ta yi karatun faransanci ne, nan kuwa turanci ake. Zai iya ba ta wahala."
Toh shi Win ma dai ya ga hakan ya fi mishi sau?i, yanzun ma dubunnan da yake fitarwa na karatun yaran kaWai sai godiyar Allah kawai, ina kuma da ace ya sanya Humaira wacce ya tabbatar kafin ta fara sai an yi mata lesson a gida sosai, Waukar karatun ne ma abin tunani, bai san ya kaifin kwakwalwarta yake ba.
"Abba."
Ya tsinci muryarta wanda? hakan ya katsemishi tunani.
"Na'am Mamana."
"Abba meyasa ba ka taSa zuwa ka gan ni ba? Meyasa ko a waya ba ka damu da kira mu gaisa ba idan ma aiki ne ya tsare ka?" Ya tsare ta da ido, yanzun ya gama raina kaifin kwakwalwar yarinyar, sai dai ya sha mamakin tambayoyinta duk kuwa da ya sani lallai ne dama watarana ta yi mishi su. Sai dai bai tsammace su nan kusa ba. Dogon numfashi ya ja ya furzar.
"Kiyi hakuri Humaira, eh na yi maki laifi amma hakan ba wai yana nufin ban damu dake ba ne. Sai dai nayi hakan bisa al?awarin da na Waukarwa mahaifiyarki wanda hatta da bayan mutuwarta ban karya shi ba." Cikin sauri ta ce.
"Wane al?awari?" Ya yi shiru sai kuma ya Wago da niyyar magana, muryar Mami ta katse hanzarinsa.
"Wai nikam dai yau Abban yara ba ka da niyyar fita ko? Gashinan har goma ta gota."
Suka dubeta, a Sangaren Humaira ji ta yi gaba Waya zuwan Mamin bai burgeta ba, sai da aski ya zo gaban goshi tana shirin ta san ta ya ya aka haihu a ragaya lokaci guda kuma Mami ta yi mata katsalandan. Mami kuwa ganin hankalin Humaira ba ya kanta sai ta girgizawa Abban kai cike da damuwa. Abba shi din ma jinjina kan ya yi, ya fahimci manufarta. Don haka ya dubi Humaira da murmushin ya?e.
"Af, kinga na sha'afa har lokaci ya ja, kar ki damu Mamana, muna tare ai yanzu, a kowane lokaci idan na samu dama da kaina zan yi kiranki mu yi hirar nan kin ji ko? Yauwa Maminki ma ta ba da shawarar a sanyaki a makarantar koyon girke-girkenku na zamani, ina fatan za ki so hakan?"
Duk da yanayin rashin jin dadin da take ciki sai da ta yi farin ciki da hakan. Dama tana da son girki, ko a can gida ita ke yiwa Dada dahuwa daga lokacin da ta soma zama budurwa. Ta kuwa saki fuskarta har wushiryarta na fitowa muraran.
"Eh Abba ina so." Abba ya dubi Mami suka yi murmushi, Mamin ta karaso ta dubi Humaira.
"Yauwa ?ar Abbanta, kin ga da girki adon mace ce. Kuma na tabbatar za ki iya sosai idan kika mayar da hankali. Ana samun alheri sosai da girki. Kar ki wani damu idan ba ki yi boko ba, da yawa babu bokon amma sun samu ci gaba ta fanni da dama a rayuwarsu." Humaira ta jinjina kai, tabbas haka ne don ta ga mijin Mammati wata ?ar uwarsu a Maine, shi ma babu bokon amma yanzu kaf ?auyen nasu babu mai kuWinsa. Idan ya zo hutu da yaransa kowa sai ya san ya zo saboda alherin da yake yi musu.
"Ki je ciki nasan zaman da kaWaici ke kadai, ki sa Ladidi ta kunna maki kallo a wayarta sai ki yi." Ta fadi hakan saboda babu wuta, ?a'idar Abba tun sha biyun dare ake kashe masa inji, sai ko idan aka ci sa'a Kedco sun hasko wuta.? Humaira ta fice a falon bisa bin umarni.?Bayan fitarta Mami ta ?arasa ga Abba fuska dauke da damuwa.
"Ya haka? Kana son ka karyawa yarinya zuciya daga zuwanta? Ko kuwa so ka ke ta ri?i mahaifiyarta da mugun zato a ranta alhalin ba ta ji ba ba ta gani ba? Don Allah kar ka fara, kar ka yi wannan kuskuren. Tabo ne da yaro kan yiwa gurguwar fahimta."
Abba ya numfasa.
"Hakane, sai dai ki sani ba karamin taimakona ki ka yi ba don ba ki da masaniyar abin da zan ce a sannan. Na gama iyakar nazari ban san ?aryar da zan shirga don rufe zancen ba. Na gode maki mace ta gari."
Ya karashe yana jifanta da murmushi, ta rausaya? kyawawan idanunta tana maida mishi martani.
"Nima na gode da wannan yabon, muje ka shirya lokaci na ?urewa. Idan ka dawo ni kuma kafin nan na bincika wurin wacce ya dace a kai Humaira ta fara daukar darasi."
"Hakane, amma zan fi so ta gama shiga ta san ?an uwana. Kafin a durfafi wannan."
Mami ta Wan yi jim sai kuma ta amsa da toh. Bayan shigar su Wakin yana cikin shiri ta sanyo zancen kaya.
"Ka ga ya kamata a Wan Winka mata suturu ko ba yawa, mutumin da ya zo daga ?auye na tabbata ba wasu kayan kirki ne da ita ba."
"Ke dai wato burinki kawai na karya bakin aljihu, toh wannan na jikinta ba sutura ba ce? Kin fi kowa sanin ba na son kashe-kashen kuWi ko?" Ta yi ?ar dariya, an zo wajen. Ai idan har batu na fitar da kuWi ne toh nan suke kai ruwa rana, a karshe dai hakanan ta ke cin nasara a kanshi, kafin ya botsare akan jima.
"Haba Abban yara, Humaira fa uwa guda ce, idan ba ka yi mata ba wa za ka yiwa?" Ta ?arashe murya a narke kamar wata matashiyar budurwa, hakan ya tuna mishi zamanin tashen soyayyarsu. Ya yi dariya gami da girgiza kai.
"Maryam kenan, ke kam ba a kayar da ke a magana. Shikenan idan na dawo zamu ga yadda za'a yi. Na fita ai ko?"
"Eh ka fita kam, Allah ya kara buWi." Ta ba shi amsa tana dariyar itama.
Ya amsa da amin.
***
Washegari kuwa Mami da kanta ta bada aka siyowa Humaira atamfa da leshin sai kuwa kananun kaya dogayen riguna duka dai ba masu yawa ba, hatta da takalmin shiga taro ?afa biyu da mayafai kala uku sai da Mami ta siya mata, ba kuma ta tsaya anan ba sai da aka haWo da kayan shafe-shafen mata da na kwalliya da kuma undies.
Abba ya kalli kayan sannan ya kalli Mami.
"Yanzu dukkan kayan nan a dubu talatin?"
Mami ta Wan bishi da hararar wasa.
"Au, ka yi zaton kowa irinka ne? Wannan dai ya fi ?arfin abin da ka bayar, Mami ta cika ta siyawa Wiyarta. Wanda ka bayar ma mun gode."
Ya yi ?ar dariya.
"Maryam mai halin girma, ai shikenan, wannan tsakaninku kun fi kusa. Allah ya saka da alheri." Ta amsa da amin.? Sannan ta umarci Ummita dake zaune wadda ita ce ta dauko kayan zuwa sashin Abban akan ta Wauka ta ba Humaira na shafe-shafen, suturun kuwa ta sa a leda Humairar ga shirya su kai wurin telansu.
Ummita ta amsa da toh, sannan ta kwashi kayan ta fice.
A falon Mami kuwa, Tasleem ce zaune a gefe daga ita sai vest sai kuwa wandon makarantarta da ba ta cire ba, zaune take tana cin Wan wake tana ba su Raihana labarin wata ?ar ajinsu Suhaima da kusan kullum ta Allah babu ranar da ba sa taWinta. Sosai ta tsayawa Tasleem Win a ?o?on rai, a cewarta yarinyar ta fiye rawar kai, ga nunawa sauran Walibai kamar ta fi uban kowa ?o?ari. Tasleem ta cusa loma a bakinta sannan ta dube su.
"Kun san yau wallahi ta ci arzikin Babandi da ya shiga tsakaninmu amma da sai na gwabje bakinta. ?ar iskar yarinya ta dubi tsabar idona ta ce wai ina mata katsalandan a harkokinta saboda kawai tana yin tutorial din sanya kai na ce ita kanta ba ta gane ba shikenan fa ta tasomin, su kuwa ?an korenta su Teema Small saboda na taSa Hajiyarsu me zuwa da mota nan suka goyi bayanta."
"Ke dai Tasleem ina raba ki da nuna bakin cikinki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login