Showing 90001 words to 93000 words out of 189325 words

Chapter 31 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

238

ya kira Sister dinsa Hannatu tana hanyar zuwa."

Gaba Waya ta manta da wani batun zuwansu, Mami kuwa haWe rai ta yi ba ta ce uffan ba har sai da Raihana ta ?ara magana.

"Ki je ki Wan sauya kaya don Allah. Kar ta ganki da Tshirt."

Ladidi ta yi dariya Humaira kuwa ta maka mata harara ta rasa dalilin kuma da aka yi ta Wan dawo da jin haushi-haushin Fadeel, sai lokacin kuma Mami ta yi magana.

"Toh uwarta, ke kuma Humaira meyasa ba ki faWamin kina da ba?uwa yau ba?"

Cikin sanyin murya da kuma rashin jin dadin Satawa Mamin rai da ta yi ta ce.

"Kiyi hakuri Mami, gaba daya na manta ma ya faWamin."

Mami ta sauke ajiyar zuciya, ta sauya yanayinta na farko sannan a sanyaye ta ce.

"Ai shikenan, ba don girkin da ake na Futuha ba da sai dai ta zo ba a yi nata tanadin komai ba kenan. Ladidi ?aro shinkafar nan kafin ki wanke."

Ladidi dake shirin wanke Wanyar shinkafa ta zuba a ruwa ta amsa da toh, sai da ta ?ara ruwan tukunyar sannan ta ?ara awon shinkafar da ajiye. Raihana dai ta tsaya jiran Humaira ta dage lallai sai ta sauya shigar jikinta. Mami ba ta sa musu baki ko kadan ba, Humaira har haushin Raihanar ta dinga ji saboda irin wannan nacin ba ta ko fuskantar yanayin fuskar Mamin.

"Ki rabu da ni don Allah." FaWin Humaira cikin haWe gira. Sai lokacin Mami ta sa baki ta hanyar bin Humaira da murmushi.

"Aa Humaira, da gaskiyarta. Maza je ki sauya suturar jikinki. Bai kyautu ba?uwarki ta ganki a hakan ba. Jeki."

Ganin yanayin Mamin har a sannan ba ta gamsu ba, amma ta bi umarninta suka fice da Raihana zuwa nasu Wakin. Ta iske Raihanar ta fiddo mata wata atamfarta purple mai ratsin fara da ba?i, ta kalle ta. Raihana ta murmusa.

"Ya aka yi? Da magana ne? Ko na sauyamaki kayan?"

Guntun tsaki Humaira ta ja.

"Ke dai yadda kika damu da wannan Fadeel din da ma ke kika aure shi."

Raihana ta ji ba dadi jikinta kuma ya yi sanyi, tana tunanin Humaira ta fara sauyawa daga lamarin nata da na Fadeel sai ta ga abin ba haka ba.

"Allah ya huci zuciyarki tawan." Ta fadi tana ri?o hannun Humaira, sai itama ta ji ba dadi.

"Shikenan. Bari na watsa ruwa na sauya ko don ke."

Sosai Raihana ta ji dadin kalamanta. Ta yi dariya.

"Toh."

Daga haka ta fice ta bar Humairar da shiga bandaki.

***
Murja tana zaune gaban motar ta hakimce yayinda Hannatu da yarinyarta mai shekaru uku da ta ci suna Husna suke a baya zaune.
Tun da Murjar ta ji inda Hannatun ta nufa ta kafe akan sai ta bi ta, a farko Hannatu ba ta so ba don tana da labarin irin son da Murjar ke yiwa Fadeel daga bakin Kausar. Shi Fadeel dayake bai Wauki maganar da muhimmanci ba ya sa bai ce mata komai a kai ba. A karshe dai ganin yadda Anti Amarya ta nuna ta yi na'am Murja ta raka su ya sa itama Soye nata rashin yardar suka tafi tare ba da sanin Fadeel ba.
Karfe biyar na yamma suka shiga gidan. Raihana ta tare su da fara'arta zuwa ciki. Murja sai raba idanu ta ke ta ga inda Humaira za ta Sullo kuma ta ga yanda ta sauya. Ummita itama ta fito suka gaisa da su, nan suka jajanta musu da addu'ar Allah ya kiyaye gaba. Ba ta amsa ba sai ta mike sakamakon idanunta da suka cicciko da kwalla ta nufi daki.

A duniyarta yanzu babu abin da ta tsani ta tuna kamar abin da ta faru gareta a hannun Kidnappers. Gani take duk ranar da aka Waura mata aure da Sahabi babu abin da zai hana shi gano komai, Abba ya yi niyyar sanar da shi amma Mami ta nuna kar ya yi hakan. Ita kuma a karan kanta ta rasa ta ina za ta fara gayamishi. Ga wata sabuwar kauna da yake nunamata tun bayan fitowarsu duk domin ya kwantar mata da hankali.
Ganin da ta yi Humaira na Wakin, ta yi saurin share fuskarta ta dubeta fuskar a Wan sake duk da ba kamar can baya da take Ummitarta ba.

"Sun ?araso su na falo. Ki je ku gaisa, mace mai kirki da ita."

TaSe baki Humaira ta yi.

"Toh." Shi ne abin da ta iya cewa, daga haka ta sa kai ta fice. Bayan fitarta Ummita ta tura kai a filo ta yi kuka mai isarta tana mai tausayawa kanta. Wannan ba?in ciki na keta alfarmarta da aka yi ta kasa gogeshi daga kirjinta, ta dai san an gogamata ba?in fentin da har abada ba za ta iya gogewa ba. Amsar da ta kasa ba wa kanta har yau shi ne, wane ne wanda ya sa a yi kidnapping dinsu.

*_Ba don kar asirinmu da na Boss Winmu ya tonu ba, da sai na nemi aurenki na killaceki saboda kin haWu ?arshe._*

Ta tuna wannan ?azamin zancen da ya fito daga bakin Wizzy a sadda yake kam ganiyar raba ta da mutuncinta. Kenan dai akwai wanda ya sanya su wannan aika-aikar. Waye shi? Kuma a ina yake? Allah ne kaWai masani. A karshe dai ta yakice wannan tunanin ta mike ta shiga bandaki.

***
Hannatu ta dubi Humaira har ta ?araso ta zauna tana mata Wan murmushi. Murja kuwa kallon Humaira kawai take yi cikin tafarfasar zuciya tana mai kuma cin alwashin ganin bayanta. Babu wani abu da ya sauya daga kyawunta wannan ne ya ?ara wa Murja ba?inciki a ?asan rai. Ta kauda fuska tana amsa gaisuwar da Humaira ke yi mata a yatsine. Ita kuwa Humaira mamaki take na dama Murjar ta san Fadeel amma sai ta bar wa cikinta ba ta tambaya ba. Hannatu ta saki jikinta ta yi ta jan Humaira da hira, kasancewar da Raihana a falon ta samu ?ar tayi, tun dai Humaira ba ta saki jiki ba har sai gatanan ta soma murmusawa ha?oranta na bayyana.

Raihana ta kawomusu abin motsa baki da kuma abinci. Husna ta ma?alewa Humaira tana mata hira iri iri na yara. Itama ta dinga biyemata. Can dai Murja ta kasa jurewa ko Mami ba ta tsaya sun gaisa ba ta amsa wayar ?arya sannan ta dubi Hannatu.

"Ni zan wuce sai kun taho. ?awata ce ta zo."

Suka dube ta har Raihana da ta fahimci sauyin fuskar Murjar da irin harare-hararen da take wurgawa Humaira jifa-jifa.

"Shikenan, sai mun taho."

Ranta ya ?ara Saci, wato dama so take ta tafi Win don haka ta dauki jakarta ko sallama ba ta tsaya yi da su ba ta fice a fusace.

Ba jimawa kuwa da fitarta Mami ta fito cikin shirin fita. Daga ganin yanayinta sauri take kuma fuskarta ya nuna rashin nutsuwa. Hannatu ta gaida ta, ta amsa da Wan sauri. Ganin haka Raihana da Humaira suka tarbi Mamin da neman ba'asi. Guntun tsaki ta ja fuskarta dauke da tsantsar damuwa.

"Wajen Tasleem zan je, sun yi dambe da wannan Fauziyar shi ne fa jini ya Salle mata amma sun wuce asibiti."

Hankalinsu su din ma ya tashi. Suka nuna za su bi ta amma fir ta ce aa su zauna da ba?uwarsu sannan ga Futuha dake hanyar zuwa kada a bar gidan babu ?an tarbarta. Dole suka jajanta suka dawo ga Hannatu aka cigaba da hira. Ba ita ta bar gidan ba sai bayan Magriba. Ta kuwa ajiyewa Humaira leda babba ta kayan kwalam sai ko turarukan da ta yo mata tsarabarsu. Firr Humaira ta ?i karSa sai da?yar sannan ta yi godiya. Lokacin itama Ummita ta fito falon, tare suka yi mata rakiya har gaban motar da suka zo cikinta.

***
Karfe takwas da mintoci sai ga Futuha a gidan, tun yamma ta sauka a garin tana gidanta, ?asim ne ya kai musu girke-girken da aka yi musu. Ta shigo gidan gaba Waya jikinta a mugun sanyaye. Matasan samarin duka suna falo aka tarbe ta da murna, su Humaira su din ma duka ana zaune ana kallon film din Krissh da ake haskawa a mbcbollywood. Ganin yanayin yadda take amsa musu hirar ya sanya Yassar dibanta dakyau.

"Are you okay?" Ta yi murmushin ya?e kai ka ce ba Futuhar nan ba ce mai Wora hotuna iri-iri da murnar zuwa Dubai a tiktok.

"Yes. Mamin ba ta dawo ba?"

"Ta dawo tana Waki."

FaWin Raihana. Ta kuwa nufi Wakin, ban da gaisuwar su Humaira babu wani jimamin da ta yi musu na abin da ya faru. ?amshin turarenta da ya cika falon ne ya sanya Ummita jin kanta na juyawa, ta ji tamkar hanjin cikinta ke kaWawa. Da sauri ta mike ta yi dakinsu, kafin ta ?arasa shigewa banWakin wani amai ya tahomata wanda sai da ta amayar da duk abincin da ta ci a ranar. Humaira da Raihana wadanda suka biyo bayanta ganin irin mi?ewar da ta yi ta bar falon suka tsaya cak cike da fargaba mai tsanani su ke bin ta da kallo. Raihana ta karasa cikin sauri bayan fitowar Ummita daga banWakin ta ri?e ta.

?? "Lafiya? Meke damunki?"

Ummita ta yamutsa fuska kaWan.

"Ban sani ba, kawai dai na ji zuciyata tana tashi."

"Allah ya sauwa?e, ki Wan kwanta ko za ki ji dadin jikin." Fadin Humaira cikin dauriya da ?aryata zuciyarta har da jan istigfari bisa sa?e-sa?en da ta jefa mata. Ummita kuwa Wan murmushi ta yi.

"Kar ku damu, kalau nake. Naga duk kun yi wani sukuku da ku."

Cikin kokarin basarwa Raihana ta zauna gami da jan guntun tsaki.

"Ai dole, ga Tasleem can kwance asibiti dakyar aka tsaida jinin. Wai kawai saboda ta kama Fauziyya na waya da tsohuwar budurwar Yaya Hamza kuma ?ar uwarta tana ba ta labarin rayuwar ita Tasleem din da Yaya Hamza shikenan fa daga cacar baki sai cibi ya zama ?ari. Nima Mami naji tana ba Anna labari. Yanzu dai Maman Hamza ta ?i zuwa ko duba Tasleem ta ce wai kashe mata Wiya ta so yi."

Humaira ba ta ce uffan ba, domin tun dawowarsu ta ?ara jin Tasleem ta fice a ranta, ta kuma ?udurta ban da dai gaisuwa ta musulunci to fa babu abin da zai sa ta cigaba da tura kai ba kwarjini wurin waWanda ba za su taSa kaunarsu ba. Ko kaWan Tasleem ba ta wani nuna farin cikin dawowarsu ba, ita kuwa me zai sa ta cigaba da shiga sabgar wacce ba ta yin ta?

"Allah Sarki, Allah ya kawomata da sauki."
Cewar Ummita sannan itama ta ja bakinta ta yi shiru.

***
Yanayin da Futuha ta shigar wa Mami ne ya sanya ta Wago kai daga wayar da take amsawa har da hawayenta. Cikin wani sauri ta sallame wayar ta mi?e, Futuha ba ta kawo komai ba ta ?arasa da sauri ta rungumeta ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Mami wacce ta ji kirjinta ya yi wani irin bugu da ?arfi ta Wago kai da azama ta kalle ta har hannuwanta a rawa.
"Ke mene ne ya faru ne? Ina Yakubun?"

Gaba Waya ta ruWar da cikin Mami wanda ta ji har wata ?ar ?ara ma yake yi.

"Mami ?arya yake yimin, ashe matarsa tana gidansa cikin wata irin ?as?antacciyar rayuwa?"

"Toh ina ruwanki da ita! Ke ba kanki kika sani ba?!"

Yadda Mamin ta yi furucin a zafafe ya sa Futuha shiru tana kallonta da Wan mamaki saman fuskarta, kamar dai ba Mamin da ta saba karo da ita ba. Sai kuma ta tuno labarin ?anmatancin Mamin da Anna ta ba su, mace ce da a tarihin soyayyarta ba ta taSa kallon mai mata balle ta ji zuciyarta za ta iya Waukar zaman kishi da ita ba, har tana jinjina mamakin zaman da ta amince suka yi da Fatima ta kuma ?aunace ta. A baya dai Mami ba ta san kowa da komai ba sai kanta da kuma nata. Wannan tunanin da Futuha ta yi ne na tsohon tarihin Mamin ya sanya ta sauke ajiyar zuciya lokaci guda kuma mamakinta na farko ya gogu tas daga kwanyarta.
"Nifa ba wannan ?aryar ce ta tada hankalina ba, tun kafin mu dawo likita ya bayyanamin ina da ciki bayan ?ar rashin lafiya. Na bar abin na Soye ban sanar mishi ba akan zan ba shi labari mai dadi, sai yau da muka dawo ne nake sanar da shi toh kawai sai ya sauya fuska. Ya kuma rantsemin shi bai aure ni don na haifarmasa, daga uwargidansa kawai yake da kwaWayin samun yara. To fa shi ne da faWa ya kaure tsakaninmu, ya ce na zubar ni kuma na ce ba zan zubar ba tunda ba shege ba ne, kawai Mami sai ya ja hannuna ya kai ni Sangaren Uwargidansa. Nayi mamakin ganin ashe yaransa takwas har da budurwar da za ta yi sa'ar Raihana. Komai nata ya ci uwarsa a falon. Goyon Wa take yi ma, a gabanta da na yaran ya nunamin yaranta sun ishe shi ba ya kaunar haihuwa daga kowace mace. Ya kuma aure ni don ya ci duniyarsa ganin da ya yi ni ?ar rawa ce wai a Tiktok na kuma san ta kan rayuwa sai ya Wauka zan san dabarun family planning kafin aure."

Kawai sai ta fashe da kuka. Mami zuciyarta har wani tafarfasa yake yi. Ta ji kukan Futuhar tamkar yana ?ara tafarfasa ?wa?walwarta don haka ta dakamata tsawa.

"Ya isa! Nace maki ya ishe ni haka! Haba! Da wanne ku ke son na ji? Da mummunan albishir din da Babandi ya faWamin ko kuwa da hargitsinku?! Ke ba za ki iya cin uban shege ba?! Ba za ki iya yadda za ki yi ki ga kin fitar da yar iska daga gidanki ba?! Shashasha kai marar wayo!"

Tana kaiwa nan ta nemi bakin gado ta zauna kirjinta na dukan tara-tara tana maida numfashin gajiya. Futuha kuwa ai sai ta ?ara yin mutuwar tsaye don mamaki. Toh Mamin nan dai ta tabbata ita ce ainahin Mamin can baya lokutan yanmatancinta, ita ce Mamin da Anna ta yi mugun kewarta. FaWa, zagi kuma duk akan kishi? Yau Mami dai da bakinta ta mata iznin daukar kowane mugun mataki ne akan kishiyarta da mijinta. Futuha ta juya cikin sassarfa tana kukan har lokacin ta fice zuwa Wakin Anna.

Mamin kuwa sai bayan da kwanyarta ta Wan samu nutsuwa, tashin hankalin dake ?asan ranta ya Wan lafa sai ta soma tunano irin maganganun da ta faWawa Futuha. Ta lumshe idanu ta ja guntun tsaki. Ta san yarinyar dole mamaki ya kashe ta, amma ita ta san azabtuwar da take yi ko kuma ta yi a shekarun baya da suka gushe. Ta tsani kishiya tsana mafi munin gaske.

'Ciki har da Fatima?'

Wani Sangare na zuciyarta ta watso mata wannan tuni. A fili ta Waure fuska tamau, idanunta nan da nan suka kaWa tsabar masifa da kuma abin da ta tuna na daga rayuwar Fatima da Yusuf a baya.

"Har da Fatima." Ta furta a zahiri, can kuma ta mi?e ta shiga banWaki ta wanke fuskarta. Sai bayan ta dawo daidai ne sannan ta fito zuwa Sangaren Abba. Ta iske shi zaune yana kallon labarai, itama wuri ta nema ta zauna da wani irin sanyin jiki.

Abba ya maido hankali gareta.

"Maryama, na ganki wani iri, Futuhar ba su dawo ba ne?"

Mami ta girgiza kai.

"Sun dawo, tana wajen Anna ma suna gaisawa."

"To ko jikin Tasleem din ne? Ni me ma ya faru ne da ita ta yi rauni?"

Ko kusa ba ta sanar da Abban gaskiyar abin da ya yi sanadin kwanciyar Tasleem din a asibiti ba. Ta sani muddin ya ji to faWa zai yi wannan ya sa ta gyara batun.

"Zamewa ta yi ta faWi a banWaki. Amma ai da sauki tunda jinin ya tsaya."

Jinjina kai Abban ya yi.

"Allah ya raba su lafiya. Sai ta ?ara kula."

Ta yi shiru tana kallon gefe guda ta kasa amsa mishi, ya ri?o hannunta cike da kulawa murya a tausashe ya ce.

"FaWamin, meke damunki?"

?asa ta yi da idanunta sai hawaye, suka zubo saman hannun Abba da ya Wora bisa nata. Nan da nan ya ?ara shiga tashin hankali.

"Kinsan bana son kuka ko? Taimaka ki faWamin damuwarki Maryam. Zuciyata ba za ta Wauki wani sabon tashin hankalin ba bayan wanda na fuskanta kwanakin nan."

Ta jinjina kai ta dube shi.

"Abban yara tunanin yarannan ya kasa barin zuciyata ta huta. Tun dawowarsu zan iya ce maka Ummita har yau ta ?i dawowa cikin nutsuwarta. Yarinya mai fara'a da son jama'a marar hayaniya, ta koma wata iriya. Babu doguwar magana balle hira, koyaushe zaman tunani da shiru. Wannan abu yana damuna matu?a."

Shima Abban hakan da ta faWi sai ya ?ara taso mishi da nasa damuwar.

"Hakane Maryama. Toh a shawarce me kike tunanin za'a yi? Mece ce mafita?"

Mami ta numfasa.

"Mafita a samar mata abin da zai dawo da walwalarta. Abin nufi, madadin lokacin da aka sa na aurenta da Sahabi, me zai hana a yi mishi magana idan sun shirya kawai ya kawo lefe a sanya bikin nan da kamar sati biyu?"

?an jim Abba ya yi cikin hali na tunani. Sai kuma ya ce.

"Kina tunanin idan an yi hakan ba a tauye ta ba kuma. Bana jin yarinyar nan ta samu nutsuwar da za ta karSi aure a yanzu. Kada ki manta fa, keta haddinta aka yi ta ?arfi. Aa Maryama, mu dai yi hakuri tun da abinda ya rage cikin shekarar bai wuce watanni biyar ba, ki jira mu ga abin da Allah zai yi a gaba."

Ba haka ta so ba sam, ba kuma ta taSa tunanin Abban zai watsamata ?asa a ido ba. Kai ta mance rabon ma da ta bada shawara irin haka dangane da abin da ya shafi yaran ya musanta. Ganin sauyin dake saman fuskarta ne ya sa Abban ?ara ri?o hannunta ya Wan matsa.

"Kiyi hakuri Maryama, ba fa watsa maki ?asa a idanu nayi akan al'amarin yaranki ba. Aa, ki dai daure na sani da zafi ka dinga ganin Wanka cikin yanayi mai firgitarwa. Amma a shawarce, me zai hana ta je Bichi ko sati biyu ta yi kinga za ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali."

Daure fuska Mami ta yi.

"Shikenan, Wauke ta a yau ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login