Showing 108001 words to 111000 words out of 189325 words

Chapter 37 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

217

amsa da toh kawai, bayan fitar Futuhar ta girgiza kai. Mamakin wannan rayuwa ta yaran Mami take, tabbas albasa ba ta yi halin ruwa ba, da ace sun biyo Mami hatta da girkin ba su da matsalarsa. Ta rasa menene ribar Wiya mace idan ta zauna har ta yi aure ba ta iya girki ba. Banda shiriritar Futuha, ta gwammace a koyawa Hafsatu girki ta cigaba da yi mata bauta ita kuwa ta zauna ta mi?e ?afa. A ?arshe dai ta watsar da tunane-tunanen da ta tabbatar ba za su yi mata wani amfani ba ta cigaba da ambaton sunayen Allah har aka kira sallar isha'i ta gabatar ta kuma haWa da nafila ta yi addu'a anan ma sannan ta ninke dardumar ta fita, abincin sam bai yi mata ba. Shinkafa ce dafaduka ta dai ji kaji wadanda daga ka kai saman hancinka sai ?arni ya bugeka, da sauri ta mayar ta ajiye. Sanin da ta yi idan ta zauna sai ta kwana da yunwa ne ya sanya ta daukar indomie kanana biyu ta dafa ta ci ta sha ruwa.
Saita alarm ta yi ya tashe ta karfe uku, dakyar ta tashi saboda ba ta saba ba ga bacci dake neman fin ?arfinta, sai da har uku da rabi ta buga sannan ta iya mi?ewa firgigit tana ambaton sunan Allah. Hakan ya ba ta wani ?arfi ta kuwa Wauro alwala ta dawo ta yi nafiloli ta karanta al?ur'ani bacci na Waukarta, dakyar ta daure ta yi sallar asuba sannan ta kwanta anan bacci mai karfi ya kwashe ta.
Sai wuraren takwas na safe ta tashi ta yi wanka ta shirya tsaf ta dora hijabinta ta nufi kicin. Ta sani mutanen gidan ba sa tashi da wuri, maigidan kansa sai ya kai goma bai fita ba. A kicin ta tarar da Hafsatu na zaman jiranta har ta yi gyara ta wanke kwanuka. Suka gaisa fuska a sake, nan suka shiga haWa kayan kari, kasancewarta babbar mace kuma mai basira tana hankalta kwarai da yanda Humaira ke sarrafa girkinta. Suyar dankali da agada suka yi sai ko sauce da ta haWa, sai ruwan shayi da ya ji citta da kanumfari. Sai ko farfesun nama da ta yi da ya ji kayan lambu. Kicin din ban da ?amshi ba abinda ke tashi, komai ta yi daidai gwargwado yanda ta tabbatar ba za'a yi almubazzarancinsa ba. Hafsatu ta fita da shi zuwa dinningtable na Futuha, ita kuwa Humaira bayan ta zuba wa Hafsatu ta Webi nata ta yi Waki don ba za ta iya jurar har sai su Futuha sun tashi ta karya ba saboda yunwar da ya addabe ta, a ranar kuma ta tashi da wani irin karfin jiki da walwala. Ta ?ara gas?ata cewar Fadeel, babu abin da ibada ba ta Waukewa na daga damuwa da ma ?uncin zuciya. Hamdala kawai ta ke yi bisa yanayin da ta tsinci kanta a ciki.

***
A Sangaren Fadeel kuwa, sosai suke shirin bikin Ibb da Dakta Salma wanda bai fi sati ya rage a yi ba. Abokansu duk wanda ya ji zancen auren Ibb sai ya tambaya ko an yi na Fadeel? Amsar dai bai wuce nan kusa shima zai yi ba. Kamar koyaushe a kwanakin nan, yau ma su na tare bayan ya raka Ibb wurin Dakta Salma jin tsarin events din da za ta gudanar, Ibb sai faman mita yake yi mishi akan kawai ya kai kudi a sanya aurensu lokaci guda shi kuwa murmushi kawai ya ke yi. Girgiza kai Ibb ya yi.

"Fadeel na sanka, kana da ?o?ari sosai gun Soye damuwa, ba ka fiye son Worawa mutane nauyin damuwarka ba, amma ba yanda ka iya, mun taso tare kuma kai Win aminina ne dan uwana na maka sanin da wani mafi kusa da kai Win bai yi ba. Yanzu a ture zancen wasa, please and please ka yi abin da muke da tabbacin yiwuwarsa, idan yin a yi, idan barin a bari."

Tu?i yake yi amma sai da ya Wan juyo ya dube shi.

"Ban fahimceka ba. Me za a bari?"

Ibb ya kauda fuska yana Wan shan ?amshi.

"Auren mana, ko dole ne sai ita? Lamarinta ya fara kai ni bango, ita ba ?ar kowa ba a ?asarnan sai ji da kai da ta?ama. Matan da suka fi ta sun nuna su na yi da kai sun kuma nuna sun ji sun gani kowane yanayi ma a tafi da su amma ka nace mata, ka ma?ale sai ita. Haba Fadeel, yaushe duk wannan zai wuce? Har yanzu kana da hope din cewa za ta amince da aurenka da bakinta?"

Fadeel bai ce komai ba, amma zuciyarsa zafi take. A duniya bai taSa yin so ba sai akan Humaira, kuma da son ya tashi kama shi, sai ya yi mishi wani irin kamun dabaibayi wanda ko ya ?i ko ya so, hakanan zai rayu da shi. Bai dai san abin da gaba za ta haifar ba.

"Ban iya ?iyayya ba, kamar yanda ban iya soyayya ba ka san da haka ko? Meyasa ka ke tunanin akwai ranar da zan iya ha?ura da Humaira alhalin ba ta yimin laifin da zan ?i ta ba har yau? Ko ka yi zaton ta taSa wula?antani ko zagina? Toh Humaira ba ni ta wula?anta ba, soyayyar da na furta ina yi mata ta wula?anta, amma na yi mata uzurin kasancewarta daga jinsin Dan Adam wanda muka riga muka san ajizancinsa. Ka yi hakuri, na sani kana jin babu dadi yadda ake maka ?orafi akan aurena har da masu nemana da sharri. Please ina son ka toshe kunnuwanka daga garesu. Duk radda ni Fadeel na furta maka cewa na bar Humaira, toh ka sani ina nufin rabuwa ta har abada, amma yanzu bana jin ko SurSushin hakan a zuciyata. Ba na jin kuma wannan mafarki naka mai tabbatuwa ne saboda ba ta yimin kamun wasa ba. Ka bi wannan Wan uwannaka da addu'a Ya Sheikh, komai zai zamo tarihi fa in sha Allahu."

Harara Ibb ya wurga masa jin ya ambace shi da sunan zolaya, Fadeel kuwa murmushi ya yi mishi yana ?ara yi mishi kirari da Angon Salma. Nan kuma ya saki fuska aka bar maganar gaba Waya.

***
Cikin hukuncin Allah, a kwana a tashi har tsawon lokacin da su Abba suka ?ara ro?ar alfarma a yi bikin Ummita da Sahabi ya kusa cika, a sannan Humaira ta tattara ta bar gidan Futuha adalilin mijin Futuhar da ko kallo suke sai ya dinga kiran Humaira wai ta fito su yi kar ta ?umshe a Waka. Ko kuma ya yi ta santin girki yana fadin ai kaf gidan su Futuha ta fi su iya girki, Futuha tun tana ya?e har ta zo ta kasa jure Sacin ranta ganin tashi guda ya siyo wani rantsetsen leshi dan dubu arba'in ya kawo wa Humaira matsayin ladan girki da take yi musu. Anan ne gaba daya ta sauya fuskarta ta ce Humaira ta tattara ta koma gida, ta sa direba ya kai ta bayan ta karSe leshin. Ba tare da sanin cewa ita Humaira hakan ya fiye mata komai dadi ba don dama ta gaji da zaman gidan, dadinta daya bai wuce na ibadar da take yawan yi yanzu ba sosai, kuma abin mamaki koda Fadeel ya kira ta ta rage jin wannan tsanar da Sacin ran sai dai ba yabo ba fallasa.

Tashin hankalin daake gudu dai shi ne ya afku, Abba ya zaunar da Sahabi da wani Kawunsa a dakin ba?i ya sanar da su abin da ke faruwa. Sahabi da yake jin wai wai a gari bai yarda ba ji ya yi har wani jiri na neman kwashe shi daga zaune. Kawunsa kuwa ya jinjina lamarin, ya kuma yi addu'ar Allah ya sauki Ummitan lafiya a karshe ya ce idan ta haihu ta yi aure ban da Sahabi don tuni dama sun yi mishi mata ganin ana ta yawo da hankalinsu akan Ummita. Sahabi ya kasa cewa uffan, idanunsa sun kaWa. Tsakani da Allah yake son Ummita, ya kuma so aurenta, amma bisa gargadi iyayensa ga Kawu, matukar idan sun je ta tabbata ciki ne a jikin Ummita toh lallai su faWi hakan. Sun kuma yi barazanar saSawa Sahabi muddin ya musa zancen. Da wannan aka ?ulle mishi baki ya kasa cewa komai. Sai ma da zai tafi ne ya ro?i arzi?in ganin Ummita, nan Abba ya ba shi hakuri gami da nunamasa ba za ta iya jure ganinsa ba. Ya yi hakuri dai ya bi umarnin iyayensa. Daga wannan Sahabi ya ja jikinsa suka bar gidan bayan Abba ya dam?a musu dukkan wani abu da suka kawo da sunan aure.

Ummita na Waki ban da kuka babu abin da take yi, Humaira wannan karon ta ma kasa rarrashinta, ga ciki ya fito ras ana gani kasancewar bai fi watanni biyu ya yi mata saura ta haihu ba. Ta shiga watanni bakwai cif. Ita kanta Humairar hawayen take yi tana gogewa. Ta dai tabbata shikenan Sahabi ya rabu da Ummita duk kuwa da irin dogon wayar da suke yi da soyayyar da suke nunawa juna.

"Kaddararki ce Ummita, kiyi hakuri mu rungumeta da hannu bibbiyu. Watarana komai zai zama tarihi."

Ta girgiza kai.

"Humaira na sani ?addarata ce, amma wallahi Humaira na tsani cikin jikina da abin da ke cikin. Ba zan taSa sonsa ba. Humaira duk sadda cikina ya yi motsi ji nake kamar na Wauki wu?a na caka a cikin abin da ke cikin ya mutu gaba daya koda ace nima nawa ajalin kenan. Allah ya isa, Humaira ba zan taSa yafewa azzaluman nan ba. Har gobe mummunan fuskokinsu na nan a kwakwalwata, wallahi yau idan Allah zai nunamin su, sai na raba su da numfashinsu."

Hawaye sosai itama Humaira take yi, balle kuma Raihana wacce shigowarta kenan dakin sanye da Uniform ta dawo daga makaranta ta tsinci labarin fasa auren Sahabi da Ummita kwata kwata a bakin Mami, kuka sosai take yi sanin irin kaunar da suke yiwa juna. Ta karaso ta rungume kafadar Ummita tana kuka tamkar ranta zai fita ta ma kasa magana. Sai Humaira ke aikin rarrashinsu cikin ?arfin hali duk da itama hawayen ne ke zubomata.

"Humaira! Raihana!! Kuna ina?!"

Jin muryar Mubarak yana kiran sunansu murya a sama ya sanya su duban juna kafin su fito zuwa falon gaba daya ban da Ummita da ko motsi ta kasa. Kirjinta ne kawai ke dukan tara-tara, zai wahala ta yi mafarki bai afku ba, tana tsoron kuma yanzun ace mafarkin nata ne ya tabbata. Sai ta hau ambaton Innalillahi a ?asan ranta.

Ba Mubarak ne kaWai a falon ba, har da Mami da Abba wanda bai je kasuwa ba saboda lamarin fasa auren Ummita sosai ya taSa ransa, dama kuma ya san da zuwan ranar, amma babu yanda iya.

"Kai Mubarak, mene ne haka kake ihu a gida?"

Mubarak da idanunsa suka kaWa gaba daya ba cikin nutsuwarsa yake ba, daga shi sai singilet da wando three quarter, fuskarsa ta yi jazur abinka da farin mutum. Waya kawai ya mi?awa Abba, Mami da su Humaira har su na rige rigen zuwa le?a saman wayar. Rubutu ne a ka yi dogo, headline din rubutun mai jan hankali sai ko rubutun.

GASKIYA TA YI HALINTA...
Rahina Sani da Humaira Yusuf wadanda kwanakin baya ake tunanin sace su aka yi, a yanzu gaskiya ta yi halinta. Yan matan sun bi samarinsu ne yawon sharholiya inda a karshe har Waya ta zubar da cikin da ta yi yayinda Wayar kuwa Allah ya tona asirinta cikin ya ?i zubewa tana nan yanzu haihuwa yau ko gobe. Bincikenmu ya tabbatar da cewa ba sace su aka yi ba, dama ?an hannu ne suka bi abokan watsewarsu ganin asirinsu zai tonu ne ya yi sanadin da suka haWa baki suka yi ?aryar an sace su. Tabbas inda ranka ka sha kallo da mamaki!
Sakin wayar Abba ya yi har yana taga-taga zai fadi, da taimakon su Mami dake kusa da shi ya samu ya zauna a kujera mafi kusa saboda rawar jiki. Humaira kuwa zuciyarta ke wani irin tafarfasa ranta idan ya yi dubu ya Saci, waye wannan ke kokarin Sata musu suna a idon duniya? Mene ne ribarsa?

"Wannan wace irin rayuwa ce? Daga wannan sai wannan? Waye da wannan aikin? Kai Mubarak a ina ka samo mummunan labari haka?"

Duka wannan zantukan Abba ke yinsu lokaci guda cikin rawar murya mai nuni da zallar Sacin rai. Mubarak da ya dauki wayarsa ya amsa.

"Abba ina zaune naga an turo group din da nake har da masu bibiyata ta inbox su na tambayar ko dagaske ne. Da na duba naga an yi forwarding sama da sau hamsin. Wannan ya sa na fahimci koda ace ba a jima da baza labarin ba, toh ya samu karSuwa ainun."

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! A duniya ba ka sanin cewa kana da ma?iya sai irin hakan ta kasance. Ina so maganar nan ta tsaya iya mu da wadanda suka sani a gidan, koda wasa kar a faWawa yarinyarnan ko don yanayin da take ciki. Mu rufe duk wata ?ofa da za ta tsinci labarin. A karSe wayarta, ku kuma ku kiyayi tayar da zancen a gabanta. Ni kuma in sha Allahu sai inda ?arfina ya ?are wajen ganin an bi maku hakkinku, koda ace abin da na mallaka zai ?are sai na sanya an bincikomin me wannan aika-aikar an hukuntashi ya kuma faWi dalilinsa na aikata wannan abu."

Kowa a wurin ya gamsu da batun Abban, Mami kuwa tunani kawai take yi na waye wannan da ya fi ta nuna ?iyayya ga yaran? Fatanta kar ya kasance wacce take zargi. Ta sani tunda har Abba ya ci akwashin Waukar mataki akan al'amarin to fa babu fashi.

Da wannan aka kashe zancen amma fa ran kowa a Sace, koda su Humaira suka koma Waki, sun tarar Ummita ta shiga bandaki wannan ya sanya da sauri ta Wauke wayarta ta kashe ta jefa a sif, da Ummitan ta fito ma babu wani a cikinsu da ya nuna mata komai. Ita Win ma ba ta lura da yanayinsu ba balle ta mayar da hankali, damuwar rashin Sahabi ya rinjayi komai. Tana bu?atar ganin ta samu nutsuwa ko ya ya ne, tana tsoron ciwon da damuwa za ta haifar mata. Wannan dalilin ne ya sanya ta jin tsoron tambayarsu dalilin kiran da Mubarak din ya yi musu, sai ta zaSi yin shiru gami da kwanciya ta hau jan carbi.

***
Wasa-wasa sai ga zance ya yaWu a duniya. Abinka da soshal midiya masu jran ?iris sai ga labari salo-salo ana juyawa har da masu fitowa su na ?ara nasu gishirin su na ?ara yaWawa. Abin mamaki da tsoron shi ne har asalin su Humaira da Ummita na kasancewarsu yaran ri?o a gidan da suke haka aka dinga yaWawa ana faWin watakila musguna musu ake yi ya yi sanadin shigarsu karuwanci yayinda a wani gefen wasu ke cewa mai yiwuwa son duniya ne ya kai su ga faWawa halin da suka tsinci kansu. Har da kuma wadanda suka ce koda ace ba karuwancin suka fita da zummar yi ba, zai iya yiwuwa sun yi ne domin su samu ma?udan kuWaWe amm a ?arshe abokan ta'addar nasu suka cutar da su ta hanyar yi musu fyaWe. Labaru dai iri-iri akan bayin Allahn nan biyu Humaira da Ummita babu irin wanda bai yaWu ba. Mafi rinjaye sun fi aminta da cewar da haWin bakinsu aka sace su hakan ta kasance. ?alilan ne masu tsoron Allah wadanda ba su yarda da wannan labaran ?anzon kurege da ake ta fafutukar yaWawa ba.
? Tsintar wannan labari a wurin dangin Ummita da ma Humaira sam bai zo musu ta daWi ba. Hankali tashe Anti Maijidda ta diro Kano, ko kaWan ba su da labarin wai Ummita na da ciki, a hakan ma ba ta amince ba sai da ta zo don kanta ta ga Ummita da tulelan ciki, wannan ba?in ciki yasa har suma ta yi ta kuma ti?e lallai sai dai Abba ya ba ta Ummita su tafi. Mami kuwa tashin hankalinta bai wuce na wayar da Wizzy ya ?ara yi mata bayan bayyanar labarun da ake ta yayatawa ba akan lallai Ummita na haihuwa ta ba shi Wansa yana so zai kai wa gyatumarsa idan kuwa ta saSa zai iya tona asirinta. Wannan dalilin ne yasa itama ta kafe akan Ummita ba za ta tafi ba.

Anti Maijidda ta fusata ainun ta dubi Mami da hawaye jage-jage saman fuskarta tana kai nunata da yatsa.

"Ke Maryam! Ni ba sakara ba ce ki dube ni dakyau! Idan idanun kowa ya rufe ba a ganin aibunki ni kuwa Maijidda ko ruwan teku za ki shiga ki wanke jikinki ki fito ba za ki taSa sauyawa daga yanda nake kallonki ba. Don haka tun wuri ki fita idanuna na runtse, idan kuma ke kika yi na?udar Ummita a yau sai ki hana ni tafiya da ita mu gani!"

Jin haka sai kawai Mami ta sa kuka sosai, Abba ransa ya Saci yayinda Ummita ta kwantar da kai a kafaWar Humaira tana nata kukan.

"Hajiya Maijidda ina ganin ?imarki kuma albarkacin Jamila da abin da ta haifa ya sa ban taSa Waga idanu na faWamaki maganganu ba. Ko ba komai kina ganina da wannan girman, amma fa ba zai yiwu ace koyaushe ki zauna kina kushe Maryama ba. Haba, duk ?o?arin da take yi akan Ummita bakya gani? Meyasa kike nema ki yanke zumuncin da ke tsakanina da Wiyar Wan uwana? Ke a ganinki idan ace yau Maryama na cutar da ita zan zuba idanu ne nayi shiru? Ni ga sakarai?"

Mami ta Wan dube shi ta gefen idanu kawai, yayinda Maijidda ta ji zafin maganganunsa.

"Alhaji Yusuf, na ji Maryam ba ta cutar da Ummita, amma yau idan har ni na isa da Ummita matsayin yaya ga mahaifiyarta ina neman alfarma a wurinka ka bar ni na tafi da ita Bichi. Ka ga dai yadda abubuwa suka rincaSe, sunanmu gaba daya ya gama Saci, ba naku ba, ba kuma ga namu ba ?an uwan mahaifiyarta. Don haka ina? ro?on arziki ka bar ni na wuce da ita."

Ummita ko kusa ba ta gane Sacin sunan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login