Showing 183001 words to 186000 words out of 189325 words

Chapter 62 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

225

kanka a madubi dai ka ga yanda kake ?ara zama wani handsome guy."

Murmushi ya yi.

"Ni fa na ga alama nan gaba sai na dinga thinking twice kafin na furta wata kalmar ta English a gabanki."

Ta yi dariya gami da rungume shi.

"Kai ne malamin ai, ba don kai ba ko zo na kashe ki da turanci ban iyaba. Thanks to you da ka daukarmin malamar karatu ka kuma yi kokarin ganin na goge sosai ina mu'amala da Walibaina na girki na kabilu iri daban daban."

Shima rungume ta ya yi. Ta lumshe idanu cike da shau?i, Fadeel ya yi mata komai, bai bar ta da wahalar karSar odar girki ba sai da ya tabbatar ya samar mata wuri na musamman a bangaren gidan an gina mata katafaren kicin da ma aji wanda za ta dinga koyar da dalibai masu son koyon girki a ciki. Tana da yara ?an aiki wadanda aka yiwa tshirt ruwan hoda a bayansu an rubuta Deelsha's Delicacies. Komai na su akwai tambarin wannan sunan a jiki, sunan Humaira ya karaWe ba ma iyaka Kano, kusan wurare da dama a faWin Nijeriya an san da ita.

Daren dai haka suka raya shi tamkar wasu sabbin ma'aurata, koyaushe Fadeel ji yake kamar ana ?ara rura wutar ?aunarta a zuciyarsa. Har Ibb da Dakta Salma sun saka musu sunan Laila da Majnun sun gaji da kira sun ha?ura.

***
Bugun ?ofar take yi da ya firgita Futuha. Yakubu ya dube ta.

"Waye haka? Dama kina yin ba?i ne idan bana nan?"

Ta yi saurin girgiza kai a tsorace.

"Wallahi aa, nima ban san waye ba." Ta fadi ?irjinta na bugu da sauri-sauri. Ya yi kwafa ya mi?e daga kwanciyar da ya yi saman doguwar kujera ya shuri takalmansa ya nufi kyauren ya bude, ba don ya ja gefe ba saura ?iris Mami ta faWa kansa. Ganinta ya sanya shi sauya fuska sosai.

"Sannu Yakubu, ashe kana gidan." Futuha jin murya kamar ta Mami ya sa ta fitowa daga falon da sauri. Ita din ce kuwa. Ta dubi Yakubu dake watsawa Mamin kallo kai ka ce wani abin ?yamar ya gani. Ta maida idanunta kan Mami bakinta har rawa yake wurin tambaya.

"Mami, lafiya kuwa kika dawo?"

Sai ta soma kuka.

"Na rasa muhalli Futuha, na rasa wurin kwana don Allah Yakubu ka amince yau kaWai na kwana anan idan ya so gobe sai na yi sammako na fita neman gidan haya."

"Ba zai yiwu ba gaskiya Hajiya, gidan nan na gina shi ne domin ni da matata, ban yi gurbin kowa a ciki ba har ke da kike mahaifiyarta don haka ki yi hakuri ki bar nan kar ki Satan rai a daren nan."

Cike da takaici Futuha ta dube shi.

"Haba Yakubu, mahaifiyata ce fa. Don ta ro?i alfarmar kwana guda a gidannan ba za ka iya yi mata ba?"

Ya kalle ta a wulakance.

"Ai ni bani da karfin zuciya irin na Abbanki da zan bar uwar matata ta rayu da mu tsawon shekaru. Wato na ciyar da ita kuma na ci da Babarta? Toh ba zan yarda ba wallahi, daga ke har ita yanzu sai na tattaraku ku bar gidannan."

Ran Futuha ya kai karshe wurin Saci, wato Yakubu ya kai matakin ?arshe a fagen rashin mutunci. Uwa uwa ce ai duk lalacewarta, sai kawai ta ji ta tunzura ta mance da duk wani gargadin Abba.

"Toh matukar Mami ba za ta kwana a gidannan ba nima ba zan zauna ba zan bi ta mu tafi."

"Ni kuma muddin kika taka ?afa kika fita a gidannan kin fita kenan a bakin aurenki!"

Daga haka ya koma ciki bayan ya watsawa Mami kallon banza, ita kuwa kuka kawai take yi tana girgiza kai cike da tunano alkhairan Abba. Ashe ba ?aramin namijin ?o?ari ya yi mata a baya da ya aminta ta rayu gida daya da Annarta ba, ko sau daya bai taSa nuna wani bacin rai ba balle ?yamar al'amarin? Har Futuha ta juya ta koma ciki ba ta ma ankara ba, can ta dawo yafe da mayafi sai jaka. Mami ta girgiza kai.

"Babu inda za ki je. Nima yanzu idan na fita ban san gidan da zan shiga na kwana ba. Ki yi zamanki tunda ya ?i aminta na kwana a gidannan, zan nemi wani wurin."

Haka suka tsaya jayayya, a karshe dabara ta faWowa Futuha, nan da nan ta fiddo wayarta ta kira Baba Amina. Cikin kuka ta shiga ro?on alfarma a gareta a kan Mami. Ta bata labarin yanda mijinta ya dage akan kwanan Mamin, ga kuma dare ya tsala babu inda Mamin za ta je. Zuciya ta musulunci ya sanya Baba Amina ta duba girman Allah da Futuha ta haWa ta da shi ta aminta, ta ce Futuha kar ta sake ta fito, ta dai saka Mamin shiga koda makwaftansu ne za ta aiko babban Wanta ya dauke ta a mota. Godiya sosai Futuha ta yi, tana sane ta fasa kiran Anti Maijidda da ta yi niyya da farko, ta san ko giyar wake Mamin ta sha, ba za ta lamunci wata alfarma daga Anti Maijidda ba. Batun Baba Aminar ma ta so nuna ba za ta je ba, sai da Futuha ta nuna bacin rai sannan ta sassauta. Tana nan makwaftan har dai Wasilu Wan mijin Baba Amina ya zo, ta sha jinin jikinta ganin dalleliyar motar da aka turo a dauke ta cikinsa. Haka ta yi lamo sanyin AC na bugata da tunanin ina mijin Baba Amina ya samu kuWaWe haka har ya mallaki motar nan? Ba ta ?ara shan mamaki ba sai da ta ga madadin a nufi unguwar Jakara sun karya kwana sun shiga rijiyar zaki gaban wani dan?areran gida, gaba daya unguwar shiru babu ko ?arar inji sai hasken fitilun solar daga kowane gida. Haka aka wawake ?aton gate suka shiga.

Baba Amina ta karSe ta babu yabo ba fallasa, ta bada umarni ga babbar jikarta Yusra akan a nunamata masaukin ba?i. Daga haka ta wuce wajen mijinta. Hatta abinci sai da aka kai mata ta kuwa ci hannu baka hannu kwarya. Sai kuma ta mike ta shiga ta wanke jikinta ta mayar da kayanta. Ta kwanta babu tunanin ko ramuwar salla tana kallon fankar dake wulwulawa a dakin, wai yau ita Maryam ita ce ta ke cin alfarmar waWanda ta raina take ?yamata? Yau dai Baba Aminar da ta saba yi mata kyautar kwancen kayanta da kuma tsoffin kujeru idan ta tashi sauyawa, ita ce a wannan daular? Toh ita kuwa Baba Amina sana'ar me mijinta ya samu haka? Yaushe ma ya bar koyarwar da ta san yana yi a baya?

Sai kuma ta hau tunanin inda za ta nufa daga nan, ita har ga Allah abin kunya ne ta je kauyensu a haka. Toh amma kuma ai da wannan kunyanda tozarcin da take fuskanta gwara ta koma ?auyen. Wata zuciyar ta shawarce ta, sai kuma ta girgiza kai.

"Allah ya yimin tsari." Ta bayyana a fili. Ita dai gwara ta samu koda na mota ne ta je can Auyo wajen Hajiya Lubna ta karSi kuWaWenta.

***
Da sassafe ta ji an banko ?ofar an shigo, ta mi?e firgigit, Baba Amina ce fuskarnan tamkar an aikomata sa?on mutuwa. Mami ta mi?e zaune tana mutsistsuka idanu.

"Maryam, gari ya waye, ki tashi ki tattara ki bar min gidana. Jiya albarkacin Futuha ki ka ci saboda mu mutanen arziki ne mun san darajar aure da ma Wan adam, ba za mu lamunta ki je ki kashe auren ?armu ba saboda tsabar rashin hankali irin naki. Ki gaggauta shiri don dai abin kari ba zan hanaki ba, za'a kawo ki ci ki gaggauta tafiya."

Tana kaiwa nan ta fice ta banka ?ofar, Mami ta mike tana haWiyar yawu ma?wat, wani abu ne tokare a ma?ogwaronta, wannan cin kashin da take fuskanta da me ya yi kama? Tana nan zaune tana tufka da warwara gami da sharce hawaye Yusra ta shigo da sallamarta ta gaisheta sannan ta ajiye tiren dake hannunta ta dauki na? na jiyan da ta shigo da shi, har za ta fice Mami cikin sauri ta dakatar da ita da cewa ke. Ta dawo ta tsaya.

"Sunana Yusra."

"Ok Yusra, dan taimakamin da kwatancen gidan Raihana."

Yusra babu abin da ta sani akan Mamin, amma daga yanayin yanda Baba Amina ke nuna rashin son ba?uncinta sai ta ji shakkar sanar da ita. Lura da hakan sai Mami ta murmusa kadan.

"Ni mahaifiyarta ce."

Ta sha mamakin jin wannan furuci, wato ita ce Mami? Maman Anti Raihana da take da labarinta? Tabbas ta san labarin komai amma a fuska ba ta san wace Mamin ba. Girgiza kai Yusra ta yi.

"Kiyi hakuri sai na tambayi Baba idan ta amince shikenan."

Sauke ajiyar zuciya ta yi. Ta san Amina ba za ta wani aminta ba sai ta sauya dabara ta ce ta bar shi kawai. Gwara ta yi amfani da lambar wayar Raihanar da ta karSa hannun Futuha.

***
Hakanan ta fito daga gidan Baba Amina, mijin Baba Amina har dubu ashirin ya Wauka ya ba ta, ta karSa ta yi godiya tana tuna sadda mijinta Ke musu idan sun shiga matsalar da ta fi ?arfin aljihunsu.

Wurin masu siyar da waya ta nufa ta samu waya ?arama secondhand ta sanya layin da Futuha ta ba ta sannan ta shiga neman layin Raihana.

Sau uku ta yi ?ara aka Waga, muryar Raihana ta doki dodon kunnenta.

"Raiha, ni ce Maminki."

Ta ji Wif na Wan lokaci an dauke wuta ta ma yi zaton ko ta tsinke can sai ta ji Raihana cikin muryar kuka ta amsa.

"Mami."

Ko ya uwa ta kai ga lalacewa uwa ce, kaunar Mamin da kewarta da take kwana da tashi da shi wannan karon ma shi ya cika mata zuciya. Koyaushe cikin addu'a take akan Allah ya shirya mahaifiyarta kar ya dauki ranta ba tare da ta tuba ta nemi yafiyar wadanda ta cutar ba.

Itama Mamin cikin hawayen ta amsa.

"Naam Raihana. A ina zan sameki ina so zamu yi magana."

Nan da nan Raihana ta yi mata kwatancen gidanta cikin rufewar idanu. Ta manta dakyar ta samo soyayyar uwar mijinta da ma danginsa wanda kyautatawarta garesu da ma kyawawan dabi'un da suka ga ya sha bamban da na mahaifiyarta bayan sun mata? gwaji iri-iri yasa suka yada makaman, suka kuma ri?e ta da mutunci.

Mintoci kalilan sai ga ta a gidan. Raihana ta fito ta buWemata suka shiga ciki tana danna hawayenta ganin yanda Mamin gaba daya ta sauya kamar ba ma'abociyar ?amshin nan da saka manyan suturu ba. Allah ya taimaka mijinta ba ya gidan ya ma yi tafiya Abuja. ?anwar mijinta da suke tare kuwa tana makaranta. Dama Afnan da Yazid suna can gidan Abba ba su dawo ba. Bayan sun zauna sai da ta fara kawomata abinci da ruwa ta kara ci don a gidan Baba Amina ba ta ci a nutse ba sannan ta soma magana.

"Mami, kece kika zama haka?"

Ajiyar zuciya Mami ta yi gami da girgiza kai tana bin gidan Raihana da kallo, babu laifi ya tsaru sai dai har yau a yaranta ba ta ga wanda ya samu gida irin na Humaira ba, yanzu kuwa ko ya ya gidan yake? A can baya ma ba za'a haWa shi da wannan ba ballantana kuma yanzu da ta ji wai yaranta a kamfanin mahaifin Fadeel suke aiki. Ta sani arziki kam zai ci uban na baya. Shirun da ta yi ya sanya Raihana Wora zancenta.

"Mami don Allah wannan hali da kika tsinci kanki ciki ya ci ace zuwa yanzu ya isheki ishara. Kin yi komai don ganin rayuwar yaranki ta inganta, amma ki sani yaranki kaf babu wanda bai ci arzikin Humaira ba. Humaira ita ce silar da Fadeel ya nemawa su Yaya Yassar aiki a kamfanin babansa. Humaira ta kasance mai kyautata mana, koyaushe cikin kawowa yaran tsarabe-tsarabe take a duk sadda ta je Umarah ta dawo."

"Har Umarah ta je?" Fadin Mami idanu waje, Raihana ta yi murmushi.

"Yes Mami, ta je kuma ta kai su Abba, ya kuma kai Kawunta. A yanzu da nake maki magana Humaira sai ta siyar dake da harshen turanci, ta zama babbar mace kuma majingina ga ?an uwanta. Ta na da babban ajin koyar da girke-girke a gidanta wanda Fadeel ya gina mata hakanan tana cigaba da karSar oda. Batun da nake maki da yanzu a wannan satin za'a yi hira da ita a babban kamfanin gidan rediyon BBC dake Abuja amma yanayin laulayin cikin da take fama da shi kuma ta kusa haihuwa shi ne dalilin da aka Waga. Mami babu riba Waya da kika ci, Ummita dai ta kammala karatunta aiki ne kawai Ridwan bai aminta da shi ba hakan yasa ni da ita muka kafa kasuwanci don nima kakar su Yazid ta ce ba ta amince nayi aiki ba. Yanzu ki duba ki gani, da bazarsu yaranki suke taka rawa, ban yi niyyar faWawa Futuha yanzu ba amma ke dai zan fadamaki ko hakan zai sa ki kara gane kuskurenki Mami, ki kuma sani cewa dagaske Humaira da Ummita masoya ne a garemu. So suke su taimakawa Futuha ta kafa kasuwanci, kuma a yi magana da Abba akan ya gargadi mijinta shima a nema mata gafararsa don ya huce daga zafin da ya dauka da ita kuma duk saboda ke. Har gobe ina bakin cikin abinda kika aikata Mami wanda ya yi silar rasa Tasleem, an neme ta sama ko ka ?asa an rasa. Babu wanda ya ji ko kuma ya kara ganinta, ba mu san duniyar da ta ke ciki ba, ba wanda ya san rayuwar da ta jefa kanta ciki. Mami ko domin lahirarki ina ro?onki akan ki nemi afuwar wadannan bayin Allahn. Ki sauya sabuwar rayuwa ki zauna lafiya da kowa."

Mami hawaye take fitarwa sosai, ta ji za ta gyara, ta yarda wanda ya fika ya fika har abada, wannan daukaka ta Humaira ba karamin taSa ranta ya yi ba, wato duk haukar da ta yi ta ?are babu abin da hakan ya sauya. Zuciyarta ta cika da tunanin Tasleem, ko ina ta ke? Wace kalar rayuwa ta faWa?

"Shikenan, zan gyara komai amma yanzu ki bani wani abu zan je Jigawa ganin Hajiya Lubna, akwai kuWaWena a hannunta, su zan karSo sai na dawo na kama gida na fara sana'a."

Mamaki ya cika Raihana.

"Mami ba ki yi maganar neman gafarar su Abba da Humaira ba."

Ta dan runtse idanu tana dan jin zafi da radadi, kamar ta ta je ta durkusa wajen wadanda ta raina a baya neman gafararsu? Ba ta jin dai a yanzu za ta iya sai dai ko nan gaba. Don ta kwantarwa da Raihana hankali sai ta gyada kai.

"Zan yi hakan, yanzu dai ina bukatar kudi daga wajenki zan je ga Hajiya Lubna."

Raihana ta dan ji sanyi, za ta so dai Mamin ta aiwatar akan kari ba wai ta ja lokaci ba.

"Toh, amma kinsan inda gidansu yake a can?"

Sai a nan ta tuna wautarta ma.

"Aa, sai dai nasan sunan Babanta, Lawal Mai Ashana kinga za'a iya samun wanda ya san shi."

"Wannan ba dabara ba ce Mami, bari na kira Anti Laila, ai muna zumunci da ita tun ba Humaira ba da ba ta yarda Malamarta ba ta girki."

Ita dai uhm kawai ta ce amma bayan haka ba ta ce komai ba, ta yarda tsanar da ta yiwa Humaira a baya ba Wan kaWan ba ne? don har yanzun idan ana maganarta ita dai jin ta take babu yabo ba fallasa a zuciyarta. Ta dai yarda kuma ta aminta sun fi karfinta har abada.

Raihana sai da ta ba ta kaya ta sauya, kasancewar ta fi ta tsawo ma sai da kayan suka yi Wan shari ?asa musamman dayake Mamin ta rame.? Ta haWamata da sabbin atamfofi har biyar da mayafai cikin na siyarwar su daga nan ta bata dubu hamsin. Koda ta raka ta har gate sai da ta ksra rungumeta tana kuka kamar kar su rabu, ta ro?i Mamin gafarar duk wani bacin rai da ta taSa shiga sanadinta, Mami ta girgiza kai tana nata hawayen.

"Ba ki yimin komai ba Raihana, idan kin ma yi na yafe. Nima ki yafemin."

Ta ce itama babu abinda Mamin ta yi mata, ta kuma bi ta da ro?o akan ta nemi gafarar da ta ce ta yi kar lokacin ya ?ure. Ta amsa da toh suka rabu akan zasu yi waya.

***
Da kwatance ta isa gidan su Hajiya Lubna. Ginin sumunti fentin duka ya goge, kana gani dai ka san ya kwana biyu a duniya. Cikin gidan ma ta soma karo da awakai da matan ?annan Hajiya Lubna ke kiwo, mutanen da a baya Hajiya Lubna idan sun je wurinta take nuna musu ta?ama da isa, ko gaisuwarsu a wulakance take amsawa. Bukatunsu kuwa hakanan za su yi ta shelar zuwa ana jeromata su sai sun ci sa'a dakyar take taimakawar. Haka Mami ta daure zuciyarta tana toshe hanci saboda ruwan da ya cakuWe da kashin awakan yana tashin samami. Ta shiga da sallama, matan gidan duka su na tsakar gida, mai tankaWen tuwo tana yi, mai daka daddawa tana yi sai kuwa wasu a gefe suna kitso. Can kuma yara na wasa da kasa sun yi dama-dama da jikinsu. Suka amsa sallamarta su na mata kallon ba?uwar fuska.

"Wajen Hajiya Lubna na zo."

Suka kalli juna suka yi wata iriyar shewa gami da fadin warr! Ita abin ma sai ya ba ta haushi.

"Lafiya? Ko ba nan ne gidan ba?"

"Aa, maida wukar meye na fusata? Nan ne mana. Amma ai mun ji kin ce Hajiya, koda dai ba a sauyawa tuwo suna ko?"

Wacce ta fadi hakan ta karashe cikin shakiyanci.?

"Kema dai Sa'ade akwai ki da wata magana, toh ai yanzu ko hanyar jirgi bana jin Luba za ta tuna, ke kam dadin ya kare an dawo asali an zauna babu cas ba as!"

Mami ta bude baki za ta tarewa aminiyarta ta ji muryarta tana sallama. Ta juya da sauri ta dube ta. Sanduna ne guda biyu take dogaraws ta shigo, ta yi mugun rama da duhu. Wata ?ar leda ce a hannunta ba?a. Ganin wata kamar fuskar da ta sani ya sanya ta yin shiru tana nazari.

"Ga nan Hajjaju ta dawo, sannu da zuwa."
Fadin Sa'ade. Suka kwashe da dariya, Mami kuwa karasawa ta yi da sauri ta rike hannunta daya.

"Hajiya Lubna! Ke ce kika zama haka?"

Sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login