Showing 21001 words to 24000 words out of 189325 words

Chapter 8 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

200

kunya."

"Toh naji, ki yimin hotonsu na miki alkawari ina kalla zan goge, nima zan aikomaki da hotona nikam ko ace ba ki goge ba ba zan damu ba saboda ina maki son da nake jin cewa komai na jikina mallakinki ne koda ba mu yi aure ba. Uhum?"

Humaira ta dafe kirji, yanzu kam ta fahimta, ta gane komai. Nan da nan ta nemi gajiyar da ke Wibanta tana tafiyar rangaji ta rasa, da wani irin azama ta daga labulen dakin ta fada ba ta ko tuna da sallama ba. Raihana da ke fuskantar madubin dakin rike da waya tana videocall da wanda ta kira Baby, ta hango Humaira ta cikin madubi, ba ta san lokacin da ta kashe kiran gaba daya ba gami da saurin ajiye wayar saman madubi. Cikin rawar baki da danne firgicin da ta shiga na irin kallon zargin da Humaira ke watsa mata ta ja guntun tsaki tana kama gefen bedsheet wanda tuni ta kammala gyaransa amma ta hau kara cusawa.

"Ke kuma Malama kawai sai ki faWomin haka babu sallama babu komai?"

Humaira ta karasa, ita ban da haushin Raihana da ta ji, har da wani irin bakin ciki da tsanar saurayin da Raihanan ta yi waya da shi ta ji. Ta yarda ba su ga maciji da yan uwanta, amma fa tana kaunarsu kuma tana ji a jikinta sai inda karfinta ya kare matukar ta ga Wayansu zai cutu. Don haka tana zuwa saitin Raihana ta fizgo hannunta suka kalli juna, Raihana har sai da ta yi taga-taga za ta fadi kafin ta warce hannunta a tsorace, da karfi ta ce.

"Ke kuma Malama wai mene haka? Me na yi maki za ki nunamin hauka?"

Ta fadi ne cike da karfin hali domin a tsorace take, tana gudun ace aljanun Humairar ce suka tashi. Humaira wacce idanunta har sun rine tsabar bacin rai ta kalleta sosai.

"Raihana kina da hankali kuwa? Kin san me kike shirin aikatawa kanki? ?angare masu muhimmanci da girma a jikinki wani jakin banza ya ke so ki tura masa? Kina hauka ne? Wannan saurayi ne da za ki kula? Toh wallahi muddin kika yarda kika aikamasa kin gama cutar da kanki har abada, balle kuma akai ga ya nemi ku hadu da shi a waje. Ina iliminki ya tafi? So ba hauka ba ne ki bude idanuwanki ki fidda baragurbi cikin rayuwarki."

Raihana da tun da ta fahimci dagasken Humaira ta ji dukkan hirarsu sai ta hau borin kunya ga zufa na yankowa saman goshinta har yana ji?a sumar dake kwance a wurin.

"Me kike nufi? Ni ba ni da hankali ne da zan tura masa? Ko kin dauka shashasha ce ni? Toh ni nasan yanda nake tafiyar da ire-irensu don haka ki rabu da ni. Wannan rayuwata ce. Zan gudanar da ita ne yanda na so. Bai shafeki ba."

Humaira ta yi shiru, can ta nisa za ta kara magana wayar Raihanan ya hau kara, aikuwa da azama ta nufi wayar har tana ture Raihana. ?agawa ta yi ta sa a kunne, Raihana na son dakatar da ita amma tana tsoron kar ta sha duka a hannunta.

"Sweetheart na ji shiru, muna waya..."

"Ba ita ba ce, wannan yayarta ce. Zan kuma yi maka gargadi da babbar murya. Wallahi wallahi ka kara gangancin neman yar uwata da tura maka wani hoto na sassan jikinta sai na nunamaka ba kowace mace ake taSawa ba a sha ba. Sai ka raina kanka. Banza dan akuya kawai! Tirr da matasa irinku wadanda ba su ajiye komai a cikinsu ba sai tsabar iskanci da baWala. Mu zuba ni da kai mafashi ya fasa!"

Ba ta saurari me zai ce ba ta datse kiran ta wurgawa Raihana wayar tana jifanta da muguwar harara, Raihana dai kasancewar ta yi amannar wannan jinnun Humairar ne ke magana ba ita ba, ta kasa kataSus sai rawar jiki tana ji kamar ta saki fitsari a gefe guda tana jin bacin rai da tsanar shiga hanci da kudundunen da take mata amma ba dama ta yi magana, ta kuma sa a rai za ta yi duk yadda za ta iya ta ga ta ba shi hakuri kar ya kai zancen Humaira zuci.

"Idan kin kammala wayar ashararancin sai ki yi sauri ki kammala aikin Mami na jira. Shashasha da ba ta san ciwon kanta ba."

Daga haka Humaira ta ja tsaki ta fice cikin zafin rai. Wayar Raihana na ta ?ara amma ta kasa Wagawa don gani take yi da zarar ta Waga aljanun Humaira za su isar mata da sa?o ta kuma dawowa, wannan karon kam ta sani lugudar ta za ta yi mata. Hawaye na zubomata tana ci gaba da gyaran dakin, hawayen na bakin cikin abin da Humaira ta yi mata ne, tun da take samari a duniya ba ta taSa yin wanda har a zuciya ta ji tana mishi son aure ba irin Musaddam, yanzu ga shi nan ta Sata mata shirinta. Tana mishi so da zuciya daya wanda take jin ko mene ne za ta iya yi a kansa. Don haka a gaggauce ta share dakin ta fice zuwa bangaren Anna domin ta samu damar ba shi hakuri sosai.
Ai kuwa duk kalar hakuri da karyar taSin hankalin da ta dorawa Humaira duk domin ya aminta da ita ya kasa, cewa ya yi shi din son da take mishi bai je ko'ina ba tunda har za ta bari wani ya ji sirrinsu. Raihana kamar ta mutu don bakin ciki, ta tsinewa Humaira ya fi a ?irga.

Ita kuwa Humaira umarnin Mami ta cika ta sanya turaren wuta a dakin ta fice nasu dakin. Koda Ummita ta nemi sanin abin da ya jefa ta cikin ?unci, cewa ta yi babu komai. Har ta yi wanka ta shirya ba ta cikin walwala.

Misalin karfe takwas da mintoci Mubarak ya iso gidan. Su Muhsin suka cika gidan da Oyoyo, Tasleem su ma duk yanda su ke ganin yayannasu da shige musu hanci da kudundune sun yi murna da ganinsa. Humaira na gefe tana murmushi ba ta karasa ba tana karemishi kallo. Shi kam kammaninsa da Abba har ta Saci, shima dai ba ya kama da Mami, sai ko ba?i da laushin gashi irin na yan uwansa da ya dauko. Kansa cike taf da suma ya tara. Bayan ya zauna ganin Ummita ta karasa ta gaida shi ya amsa cikin sakin fuska ne ya sa itama karasawa su gaisa. Ya nunata da yatsa ya yi shiru alamar dai so yake ya tuno wani abin. Can kuwa ya ce.

"Humaira, right?"

Ta dai fahimci so yake ya tabbatar ko haka sunan ya ke sai ta gyada kai. Su Tasleem suka kwashe da dariya, ya tambayi dalili suka amsa da ba komai. Mami ta fito fuskarta cike da fara'a, ganin mahaifiyarsa ya mike tsam ya karasa ya dan rungumo kafaWarta, ta dan tureshi tana murmushi.

"Ba ka girma ko?"

Ya kuwa kara marairaicewa.

"Girma fa kika ce Mami, yaushe rabonki da ni don Allah?"

Har lokacin murmushin take yi ta amsa.

"Amma ai ana waya da videocall ko?"

Da wasa ya sake ta ya juya.

"Shikenan bari na koma inda na fito tunda kin ?oshi da ganina."

Da sauri ta ri?o rigarsa har duka falon aka dara. Ya ja hannunta suka nufi bangaren Abba su na hira.

Abba ya yi murna da ganin Wan nasa, ya kasa rufe baki. Nan suka hau taSa hira karshe kuma Abban ya ce ya je ya kimtsa ya ci abinci tukunna. Da wannan ya mike ya fita, daga uwa har uban suka zuba mishi ido cike da kauna kowannensu kuma da abin da yake ayyanawa a ?asan rai.

***
Zaune yake a babban falon dake cikin Airport din Abuja, ya kalli agogon dake Waure a tsintsiyar hannunsa mai cike da gargasa ya fi a ?irga, ya maida duba saman wayarsa yana latsawa. Cikin sa'a kuwa ya ji muryar ma'aikaciyar ya karaWe wurin inda take umartar fasinjojin da za su je Kano akan su nufi ciki. Ya mike kuwa don dama abin da ya zaunar da shi kenan. Hannunsa Waya ri?e da trolley Winsa yana ja, tafiya yake da sassarfa. Bayan komai ya kammalu jirginsu ya Waga. Isar su keda wuya, ya yiwa abokinnasa IBB GUSAU waya. Kafin ya kai ga magana ya ji saukar muryarsa daga gefe.

"Barka da zuwa."

Juyawa ya yi yana dubanshi da idanunsa dake Soye cikin wani arnen ba?in gilashi, sai kuma ya ja guntun tsaki yana Wan murmushi, lokaci guda ya ba shi hannu suka yi musabaha kafin su rungume juna suna cike da farin ciki. Bayan sun saki juna da mamaki ya ga idanun Ibb sun kaWa, nan da nan ya daure fuska.

"Ok, hakan na nufin ba ka yi murnar ganina ba kenan na koma inda na fito ko?"

Girgiza kai Ibb ya yi ya sa hannu yana karSar trolley dinsa yana fadin.

"Hakan ba zai taSa faruwa ba, in sha Allahu ka dawo kenan. Tafiyar kuma daga ni har Alhaji ba za mu ?ara bari ka yi irinta ba. Shekarun da ka yi sun isa hakanan."

Ya shafi sumar kansa bai ce komai ba ban da baki da ya Wan taSe ya yi gaba kai kace ya san inda mazaunin motar amininnasa ya ke. Ibb da murmushi ya mara mishi baya. Suka jera su na gifta filin wurin, Ibb ba gajere ba ne, amma fa duk tsawonsa bai kama ?afar abokinnasa ba, kusan su biyun duka sai ka rantse ba su ne suka gama yiwa juna murmushi da runguma ba, tafe suke su na kallon hanya kai ka ce ba su san juna ba, duk inda suka gifta sai an bi su da kallo, ?an matan dake wurin kuwa ji suke inama inama, inama za su yi nasarar samun sa'a a cikinsu Waya ya yaba, da sun tabbata masu sa'a. Shi yana sanye da ?ananun kaya yayin da Ibb ke sanye cikin manyan kaya dinkin babbar riga har da hula kai kace wani Ango.

"Ina ka nufa?" Ya yi tambayar fuska a haWe a sadda Ibb ya murza sitiyari ya nufi gate din Airport din, shi ma ba tare da ya kalle shi ba ya amsa.

"Ka fi kowa sanin inda ya dace mu soma manufa. Tushiya masomin dawa."

Girgiza kai ya yi.

"No Ibb, i am not ready for it, muje ka kai ni hotel. Hakan na fi bu?ata. Please."

Ba musu Ibb Gusau ya amsa da Alright, ba ya so fadi tashin da ya jima su na yi da Alhaji ya tashi a tutar wofi, ai an yi mai wuyar da suka samu ya dawo garin. Don haka kai tsaye Bristol Hotel ya kai shi ya kama mishi masauki, da wani irin walwala da annuri dauke saman fuskarsa ya fito ya rabu da shi ya kama hanya don ya je ya ba Alhaji kyakkyawan albishir. Lallai ya san da zuwan Wan nasa, amma bai taSa kawo wa a rana irin ta yau ba da ake shagalin bikin ?aninsa mafi soyuwa ba a rai.
Kasancewar gidan cike yake da jama'a ?an uwa, makwafta har ma da abokan arziki ne ya sanya Ibb zagayawa ta Sangaren Alhajin ya shiga ainahin falonsa na karSar ba?i. Kamar yanda ya yi tsammanin hakan ya tarar, wato dai Alhajin ba shi Waya ba ne a falon, yana tare da babban yayansa Baffa Gidado sai Wan gidan Baffa Gidadon, HarWo. Sai ko ?annensa guda biyu dake zaune? su ma a gefe ana Wan taSa hira, kallo Waya za ka yiwa fuskokinsu ka fahimci su na cikin annashuwa. Sallamarsa ce ta katse hirar tasu wadda ke gudana da harshen fulatanci, suka dube shi gaba daya, ya karaso yana ?ara mi?a gaisuwa a karo na biyu domin dazun daga gidan ya fita. Alhaji ya amsa gaisuwar yana bin fuskar Ibb da kallo ganin yadda yake wata irin fara'a na musamman wadda rabonsa da ganin kwatankwacinta tun a baya kafin afkuwar wasu lamura marasa daWi. Ganin bakin Ibb na ta motsi amma ya kasa magana ya sanya Alhaji mi?ewa tsaye wannan karon kirjinsa bugu yake da sauri-sauri.

"Muje." Shi ne kawai abin da Alhajin yace, aikuwa kamar jira yake har da tuntuSe a kokarinsa na bin bayan shi. Wata ?ofa suka bi wacce kai tsaye main parlour din Alhajin na cikin gidan suka faWa. Ko zama Alhaji ya kasa hakurin yi su na karasawa tsakiya ya juyo gaba Wayansa.

"Ibrahim, ya ake ciki? Meke faruwa?"

Madadin ya amsa sai kawai ya rungume Alhajin kafin ya sake shi yana dariya.

"Mafarkinka ya tabbata zahiri Alhaji."

Alhaji hannunsa har rawa yake ya kama kafaWun Ibb har idanunsa sun cicciko da kwalla.

"Ya..ya..ya..da..wo?"

Ya yi maganar da rawar murya, jinjina kai Ibb kafin ya amsa.

"Eh, FADEEL ya dawo."

Alhaji ya sauke nannauyan ajiyar zuciya.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah. Yana ina yanzu? Muje ka kai ni na gansa."

Ibb zai musa amma babu dama domin dagasken dai ba abin da Alhaji zai saurara. Don haka sai kawai ya juya, Alhaji biye da shi suka fito. A farfajiyar gidan suka yi kiciSus da Ango Fu'ad wanda shigowarsa gidan kenan daga Hotel din da abokan karatunsa suka sauka. Ya karasa ganin irin rawar jikin da Alhajinsu ke yi, ga Ibb na kokarin buWe mota.

"Alhaji, fita za ku yi ne?"

Alhaji ya dafa kafaWarsa fuska a sake ya ce.

"Maza shiga mota." Ba musu ya zagaya ya shiga har sannan fuskarsa dauke da mamaki, ya kuma kasa tambaya. Ibb bai ko hana Alhaji wannan yun?uri ba don ya sani Fadeel zai yi farin ciki kwarai da ganin ?aninnasa.

***
? Ya yi wanka ya shirya tsaf cikin riga body hug fara ?al sai blue jeans. Yana zaune yana kurSar ruwan shayin da aka kawo mishi, hankalinsa kaf yana wajen Mahaifinnasa, wata zuciyar na ce mishi ya je ya gan shi, wata kuma na kwaSarsa. A hankali ya ajiye mug din dake hannunsa ya jingina kai jikin kujerar yana mai lumshe idanunsa. Dogayen gashin idanun suka kwanta luf saman fatar wurin. Ji ya yi ana buga ?ofar, ya buWe su kafin ya mi?e. Yana da tabbacin Ibb ne. Hakan yasa koda ya bude bai tsaya kallonsa ba ya juya ya koma cikin Wakin gami da faWin.

"Wato gadina ka koma kenan?"

"Muhammadu." Ya tsaya cak a tsakar Wakin, kaf duniya mahaifinsa kaWai ke kiransa da ainahin sunansa, da hanzari ya juyo, tuni lumsassun idanunsa sun kaWa. Alhajin ya taho da sauri ya rungumeshi, shi kuwa ya tsaya kamar wanda aka dasa a wajen ya kasa motsi. Fu'ad da bai san wainar da ake toyawa ba sai yanzun, kawai kuka ya sanya tsabar murnar ganin yayannasa da ya nisanta da su saboda wasu dalilai. Ya karaso da sauri ya haWa daga Alhajin har Fadeel ya rungume yana kuka. Duk jarumta irin ta Fadeel sai kawai ya ji hawayensa sun zubo. Suka saki juna Alhaji da kansa ya sa hannu yana share masa hawayen.

"Ashe da raina da lafiyata ban mutu ba zan ga wannan rana? Alhamdulillah."

Abin da Alhajin ya furta kenan. Fadeel ya yi murmushi da gefen kumatu yana dafa kafaWar Fu'ad.

"Ango, har ka girma za ka yi aure."

Suka yi dariya har Ibb, Fu'ad kuwa yan sunkuyar da kansa gami da shafar ?eya. Nan fa Alhaji ya matsa akan lallai sai ya tattara sun tafi gida da shi. Anan ne kuma ya tamke fuska kwarai, ya koma Fadeel Winsa na ainahi.

"Muddin tana gidan nan ba zan iya shiga ba. I am sorry Alhaji."

Jin haka Fu'ad da Alhaji suka kalli juna suka yi murmushi. Shi sai a lokacin ma ya ji nauyin Fu'ad din, wai uwarsa yake ikrarin ba zai shiga gidan idan tana ciki ba.

"Yaya Fadeel, Mama ba sa tare da Alhaji, tayi wani auren a garin Kogi. Sai dai ko Anti Amarya our new Mum."

Sai Fadeel ya kasa cewa komai, ya maida dubansa ga Alhajin, ya gyaWa masa kai don ya ?ara tabbatar da abin da Fu'ad ya faWi.

"Yanzun ka shirya bin mu?"

Ya jinjina kai yana murmushi. Ibb tuni ya soma haWa mishi shirginsa. Fu'ad ya karSi akwatin suka fito baki Waya, suka yi mota yayinda shi kuma Ibb ya tsaya a reception.

Isar su gidan kai tsaye suka nufi sittingroom wajen su Kawu Gidado, sai dai tuni sun fice masallaci gabatar da sallar La'asar. Koda dawowarsu ganin Fadeel gaba Waya dakin ya kaure da murna. Magana dai ta bazu a gidan Fadeel ya dawo, babban Wa namiji a wurin maigidan. Nan fa mata gwaggonninsa ?an uwan mahaifinsa kowa ya fito zuwa falon. Murna kam ba a magana. Yayyunsa mata waWanda kaf dinsu su na da aure sai guda Waya bazawara da aurenta ya mutu take zaune a gidan da yaranta, su din ma kowaccensu ta halarci falon. Kallonsu kawai yake yi yadda kowacce ke haba-haba da shi, murmushi kawai ya ke yi don ba shi da tabbacin ko abin nasu ya kai zuci ko aa. Sanin da ya yi musu daban a baya, ba shi da masaniya akan yanzu.

***
? Raihana ce zaune a can lungun gadon Tasleem ta ma?ure a gefe tana zuba kuka ga waya saman kunnenta. Musaddam take ta ba hakuri adalilin ya ?i ya huce tun sadda Humaira ta gasa mishi zafafan maganganu. Ya kuma ci alwashin ko don ya nuna wa Humaira ba ta isa ta tsaida shi daga abin da ya yi niyya ba, sai ya kusanci Raihana ko ta ?arfi kuma ya yi hotuna don ya shayar da ita mamaki. Yana sane da gangan ya ?i ya huce saboda kawai ya ?ara fahimtar irin matowar da Raihanan ta yi a kansa.

Sati Waya kenan da dawowar Yayannasu amma ko kaWan walwalwarta ba ta dawo daidai ba ga wani irin tsanar Humairar da take ji a ?o?on rai amma shakkar kada ta tona mata asiri da ma tsoron ita kanta Humairar ya hana ta labartawa koda Tasleem ce balle Futuha. Sai ?awarta da ta ba labarin, ita kuwa ?ara hure mata kunne ta yi akan kar ta yarda wata can bare ta raba ta da abin sonta. Da wannan huWubar da kuma mahaukacin son da take yiwa Musaddam idanunta suka rufe ruf. A wannan yanayin walwalarta ba ta dawo ba sai da ta tabbatar ya ha?ura bisa al?awarin za ta zo gidan su Munirat su gaisa.

Humaira ta shigo Wakin daidai sadda Raihanan ke fadin. "Shikenan zan zo goben idan har ganina zai samar maka da nutsuwa."

Wannan kalmar ta daki zuciyarta, sai dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login