Showing 66001 words to 69000 words out of 189325 words

Chapter 23 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

212

sam ba ta burgeshi tun sadda Alhaji ya faWamasa sa?onta.

"Yauwa."

Daga haka ya maida hankalinsa ga Kausar suna hirar aikin Fu'ad da babu hutu. Ita kuwa Kausar hakan ba karamin dadi ya yi mata ba, ta gama lura da irin matowar da Murja ta yi a kan Fadeel, ta kuma sani zai wahala ta same shi tunda sam ba ta gabansa. Murja ta sha?a, saukowar Anti Amarya daga saman bene ya sa ta mikewa. Fadeel ya gaisa da ita. Ta mi?awa Murja kudin tana fadin.

"Ina daWa ro?onki, na san halinki kar ki je ki zauna don Allah Murja. Kina karSar snacks din ki biya ki dauko cake."

Ta amsa da toh, ji take inama direban gidan ba ya nan sai ta ce Fadeel ya kai ta. Amma tun dazun yana waje ita yake jira. Fadeel kuwa yana jinsu amma bai sa baki ba. Ba ya son ya za?e akan lamarin Humairar har su shinshino wani abu babu ma kamar Murjar da bai gama yarda da ita ba.

***
Ta tsaya daga ?ofar gate din gidan tana ?arewa gidan kallo, yamutse fuska ta yi. Eh ba laifi su na da rufin asiri amma ko daga waje bai kama ?afar gidan su Fadeel ba. Ta karasa ta yiwa Maigadi sallama ta kuma faWi abin da ya kawo ta, iznin shiga ya yi mata kai tsaye don dama yana da masaniyar sana'ar Humairar.

A sadda ta karasa ciki Humaira na zaune tare da su Raihana a falo bayan gama yi mata kwatance a waya, ta sani ba za a Wau lokaci ba za ta karaso tunda a sanda suka yi wayar tana kusa da su.
Sallamarta ya sa gaba daya suka dube ta. Ba laifi tana da nata tsarin daidai gwargwadod. Abaya doguwa ce a jikinta sai mayafinsa, sai ko wani ?aton gilashi da ta rufe kwayoyin idanunta da shi. Tunda ta shigo falon ya karaWe da ?amshin turarenta mai ?arfi irin wanda ya zama haramun mace ta fesa ta fita da shi. Suka tarbe ta da hannu bibbiyu aka gaisa. Humaira har da kawomata ruwa da ragowar snacks din ta ci. Kasancewarta wayayyiya ta sake da su aka Wan taSa hira har Mami ta fito suka gaisa da ita. Murja ta yaba kwarai da tarbar da aka yi mata, ta kuma ji a jikinta Fadeel ba zai so Humaira ba, ba ita ce wacce yake so Win ba don dai wannan din ba wata babba ba ce ba za ta wuce shekaru goma sha biyar ba.

"Kina da page a instagram ne?"

Humaira ta gyaWa kai da murmushinta har wushiryarta na bayyana.

"Eh akwai."

"Mene sunan?"

Nan fa daya, ta sani furtawar ne aiki ba ta iya ba sosai. Raihana ta karSe zancen ta fadi. Murja har sai da ta Wan kalli Humaira sannan ta kalli Raihanar da murmushi.

"Ok zan yi following dinki. Na ji dadin ganinki na kuma ji dadin Wandanon snacks dinki duk da daman na san Wandanon. Akwai Wan uwana Yaya Fadeel yana kawomana sosai. Ta wajensa muka sanki."

Murjar ta fadi tana mai ?urawa Humairar idanu don ta ga yanayinta, so take dai ta samu tabbacin babu komai tsakaninsu. Raihana kuwa Wan jim ta yi a ranta tana tunanin wane Fadeel din? Kodai Fadeel wanda ta sani ne, tabbas ya faWamata yana odar snacks din Humaira ta hannun wata Antinsa. Ko shi din wannan ke nufi? Idan kuma hakane ita wace ce a wajensa? Ta maida dubanta ga Humaira don ta ga yanayinta, sai ta lura ko kadan ba ta sauya daga murmushin da take yi ba, sai dai jin sunan kamar jikinta ya dan yi sanyi.

"Allah Sarki, na kuwa gode sosai." Abin da ta ce kenan, wannan ya sa Murja kuma sakin jikinta sosai. Lallai wannan ba ita ce Humairar da Fadeel ke mutuwar so ba, wannan da alama ba ta ma san da zamansa ba. Dama ya ce ba shi ke yin odar da kansa ba. Yanzu kam ta yarda. Murja ba ita ta bar gidan ba tsabar shagala da ta yi suna ta kwasar hira da su musamman Raihana wacce ta fi su sanin mutane, kusan ma akwai ?awayen Raihana na makaranta wadanda duk Murjar ta san su hakan yasa hira ta musu dadi sai da Anti Amarya ta kira wayarta tana faWan jimawarta ba shiri ta mike, su Humaira kuwa har mota suka raka ta da ledojin. Murja ta karSi lambar Raihana da zummar a dinga gaisawa duk da ta girme musu don za ta yi sa'ar Tasleem.

***
Sadda ta isa gidan har yara sun fara zuwa ?an party. Ta karasa Anti Amarya na mata faWan dalilin jimawarta. Hakuri ta ba ta, ganin Fadeel a wurin wanda ke cin abinci a nutse saman dinning ta ce.

"Wallahi hira muka sha da su Humaira, mutanen gidan akwai kirki kar ki so kiga kamar kada a rabu."

Fadeel ya ji maganar har ransa, ya kuma ji dadi sosai. Bai dai ko Wago ya kalle ta ba. Yana ji dai tana ta ba Anti Amarya labari ita dai ledojin ta hau buWewa tana kallon snacks din. Koda ta dandana sun mata dadi kwarai. Nan aka shiga sanya wa a takeaway ana rufewa, Kausar na nan ana aikin da ita.

An gudanar da party cikin armashi, yaran Daddy da Mommy ne suka cika gidan don Anti Amarya sam ba ta barin mara shi ya raSe ta. Yawanci duk abokan makarantar Abdul din ne sai ko makwaftansu. Hatta a yaran yan uwanta ba kowa ta gayyata ba.

***
?angaren Amare kuwa, Amarya Futuha an ci amarcin sati daya cif ko ?ofar gida ba ta le?a ba. Hotunansu ita da mijinta kala-kala babu wanda ba ta Worawa a Instagram, shi kansa Angon hakan na mishi dadi kwarai bai taSa hanata ba. Tunda ta zo ba ta taSa sanya Uwargida a idanunta ba, karshe ma sai Ango Yakubu ke sanar da ita ta yi tafiya Saudia ita da yaranta. Futuha tun da ta ji haka duk sai ta matsa mishi akan ita ma ya dace su tafi hutun honeymoon Dubai. Hakan ya yi mishi dari bisa dari, a lokacin ji yake ko nawa ne zai iya kashewa Futuha saboda dadin angoncin da yake kwasa. Ba Sata lokaci aka soma shirin yi mata passport da sauran abubuwan da ya kamata ma tafiya. Sai bayan kammaluwar komai sannan washegari ta yi nufin zuwa gidansu ziyara da kuma sallama.

A Sangaren Tasleem ma, babu laifi Hamza na iyakar kokarin faranta mata, sun ci soyayyarsu yanda ya kamata, ba ta dora koda ruwan zafi daga gidan iyayensa ake kawomusu abincin safe zuwa dare. Sai da ta yi sati cif sannan suka kara shiga ta gaida Mahaifiyarsa da abokan zamanta su uku. Gidan dai babban gida ne mai tarin yara da jikoki. A ranar har gidajen facalolinta sai da ta shiga, wasu sun kata tarbar kirki yayinda wasu kallon tara saura suka dinga yi mata. Haka tattara ta dawo gida.

A ranar da suka yi waya da Futuha take ba ta labarin tafiyarsu Dubai hankalinta ya yi mugun tashi, ji tayi inama ita ce ta samu wannan damar. Ciki-ciki ta yi mata murna, dama tana jin haushin hotunan da take karo da su a media na Futuhar da mijinta yanda kowa ke santin kyawun da suka yi. Futuha ta ce ta shirya za su zo har gida su yi mata sallama. Ba ta ma iya amsawa da toh ba ta katse kiran gami da jan tsaki. Ya yi daidai da shigowar Hamza falon, hannunsa rike da ledoji ya yi mata siyayyar kayan sanyi da kaza. Har ya karaso kusa da ita ba ta san ya yi ba tsabar ta lula duniyar tunani. Sai da ya ajiye ne ya dan zunguri kafaWarta kadan. Ta dubeshi, murmushi tattausa ya sakar mata, itama ta bishi da na ya?e. Rungumo kafaWarta ya yi.

"Tunanin me kike yi ne haka? Har na shigo da favourites dinki amma ba ki lura ba?"

Ta kai duba ga ledojin dake ajiye, har gumin sanyi Waya yake, sai ta ji ta kasa farin ciki da abin da ya ajiye din duk da cewa a baya har so take ya kawo su ta dinga tsalle kenan tana rungumeshi. A yanzun kuwa ko Wigon annashuwa ba ta yi ba. Sai jikinsa ya yi sanyi, ya kamo yatsun hannunta.

"Wai me ya sauyamin ke haka? Ko bayan fita na kin yi ba?i ne?"

Dama kiris take jira ai sai ta tunzura ta yakice hannunta.

"Me kake nufi?! Na yi ba?i sun zugani ko sun Satan rai? Yan gidanmu kake nufin sun zo ko ?awayena?! Au zargina kake yi akan wani zai iya zuga ni akanka? Ai ba sai an zuga ni b, ni mai zuga kaina ce!"

Gaba daya ya razana, ya yi jim yana kallonta, a iya saninsa babu inda maganarsa ta kai nan. Me ya kawo batun zuga kuma ana zaune kalau? A ina ya ce hakan?

"My Noor, me ya kawo zancen zuga? Ban gane inda kalamanki suka dosa ba?"

Sai a sannan ta Wan dawo hayyacinta. Ta ja guntun tsaki ta zauna. Nan da nan kuma Hamza ya Wan sauya fuska.

"No please, zan dauki komai amma ban da raini, ina maki warning na farko da karshe, bana son tsaki. Kar ki kuma."

Ba ta ce komai ba face turo bakin da ta yi, sai ya ji ma gaba daya ta Sata masa rai kawai ya mike ya yi daki. Ta bishi da harara, ita ta sani ko wannan motar tasa zai siyar ba zai ishe su su je Dubai har su kashe kudade irin wanda Futuha zasu kashe ba. Ta san muddn Futuha ta yi wannan tafiyar to fa kanta zai fasu, za ta ?ara jin wani girman kai har ma ta dinga yi mata fi'ili iri-iri. Don haka hankalinta ya tashi, ga babu yadda ta iya, nata mijin ba ta tunanin ma ya taSa taka farfajiyar Airport balle ya shiga jirgi. Ta ja tsaki karo na biyu. Madadin ta kwashe ledojin da ya kawo ta adana komai koda ba lokacin za ta sha ba, kawai sai itama ta bar su anan ta shige nata dakin ba ta ko bi ta kansa ba don har sannan zuciyarta zafi take yi, hassada mugun ciwo ne.

***
Tun karfe goma Humaira ta je kasuwa yin cefane bisa umarnin Mami wacce ke ta shirin tarbar Futuha da za ta zo. Tana dawowa kicin kawai ta shiga ta soma shirin girki, tuwon semovita miyar kuSewa danya wanda ya ji nama da busassan kifi, shi Futuhar ta ce tana muradi sai ko lemun kwakwa. Wuraren karfe Waya ta kammala komainta jera a saman tire ta kai falon ta ajiye. Daga nan ta koma dakinsu. Ita ko kusa ba ta wani zumuWin ganin Futuhar kamar yanda su Ummita ke yi. Tun dawowarsu daga makaranta jin ance tana hanyar zuwa suke faman rawar ?afa. Ai kuwa ko awa Waya cikakka ba su yi da dawowa ba sai ga mota direba ya kawo ta har farfajiyar gidan. Da gudu Raihana ta fice tarbar yar uwarta, itama Ummita ta mara mata baya a nutse take tafiya. Humaira sai ta ja guntun tsaki ta cigaba da danna wayarta tana ganin sabbin likes da comment da sabon hotunan da ta dora na girke-girke suke samu. Ta shagala sosai sai ji ta yi an warce wayar, ta juya da sauri. Raihana ce. Dariya ta yi mata.

"Ki taso inji Mami ku gaisa da Futuha. Ashe Dubai za su wuce da mijinta sati na sama."

Ta Wan yi murmushi, ba ta fiye son kushe su a gaban Raihana ba don haka ta taya murna a fili.

"Kai amma na mata murna, Allah ya kai su lafiya. Muje toh. Bani wayata kuma."

Raihana ta mika mata suka yi dariya. A falon ta iske Futuha zaune, masha Allah ta ?ara ?iba da kyau, kumatunnan har wani kyalli suke yi. Wani arnen leshi ne a jikinta fari da ruwan toka ya sha aikin stones sai faman baza ?amshi take yi, hira sosai take yi da Mami. ?assim ma na zaune banda Yassar da Dawud wadanda sula tafi Camp a can garin Jigawa. Humaira ta karaso ta gaida ta, ta amsa mata tana yamutse fuska kaWan daga nan ta maida hankali ga uwarta su na cigaba da hira. Humaira wacce dama ta san a rina kawai sai ta mike ta saci jiki ta koma daki, Ummita ta mara mata baya.

"Ke kuwa daga gaisuwar sai ki taho?"

Harara ta dan watsa mata.

"Idan na zauna me zan mata? Goyata zan yi? Ai dai kinga yanayin amsar gaisuwar da ta yimin ko? Toh ni kuwa marar zuciyar ina ce da zan tsaya?"

Ajiyar zuciya Ummita ta yi.

"Allah ya kyauta, kinsan Allah na yi zaton aure zai sauya su, amma naga har yanzu da sauransu."

TaSe baki Humaira ta yi ta ce.

"Toh yaushe ma aka yi daren? Ke ta dai samu duniya ne kawai shiyasa abinta ya ?ara gaba. Nifa kinsan ba abin da ke ban mamaki face irin yadda matarnan ba ta yiwa kanta faWan ta nutsu ba take faman Wora hotunanta a media. Shi ma mijinnata soloSiyo da ya biyemata."

Ummita ta kama baki har da Wan waigawa ta ga ko babu wani a kusa da ya ji kalamin Humaira.

"Kinga ki rufamana asiri. Mutum ba shi ya ga zai iya ba? Kar ki manta har da shi din Ogan nata ake wannan taSargazar kinga kuwa abu nasu maganin a kwaSe su. Wayewar yanzu ce ta shirme ta zo da haka."


Dariya Humaira ta yi.

"Kenan kema haka za ki yi da Sahabinki ko?"

Duka ta kai mata a cinya.

"Allah ya sauwa?e, mu aurenmu ko party ba zamu yi ba, walima kawai a cikin gida ta isa. Albarkar auren muke nema. Hum, nifa yanzu duk ya dameni akan zai turo a sanya rana kafin nan da shekara idan mun kammala nayi Candy a yi auren. Wallahi kwanakin nan duk akan hakan muke ta rikici. Na rasa yanda zan Sullo masa."

Humaira ta mike zaune sosai. A duniya ta tsani ta ga Ummita cikin damuwa ko na sakan, don haka ta ce.

"To me kike jira? Me zai hana ki ba shi wannan damar? Kina sonsa yana sonki fa. Kuma sa rana ba shi ne auren ba, don Allah ki yi shawara da Mami tunda kinga ta san da zamansa, na tabbata za ta goyi da bayan ya turo."

Ummita ta zubamata idanu ta yi shiru cike da damuwa, ga mamakin Humaira kuma sai kawai ta ga hawaye sun soma zuba daga kwayar idanunta.

"Lafiya? A maganata akwai wacce ta maki zafi? Kiyi hakuri don Allah kinji?"

Girgiza kai Ummita ta yi,

"Ko Waya Humaira, ke ce dalilin da yasa na kasa ba Sahabi damar turo iyayensa. Wallahi bana jin dadin mafarkaina a kanki kwanakin nan. Humaira na damu da rashin bada ?ofa ga kowane saurayi ya nemi aurenki da kike yi. Ba na so na yi aure na bar ki a wannan halin. Gaba daya na damu."

Shiru Humaira ta yi, toh ita da kamar abin yana damunta kamar kuma ba ta damu ba. Ta ma kasa fahimtar komai sai kawai ta dubi Ummita a sanyaye.

"Kin manta ke ce me nusar da ni idan na Sata? Ke ce me ?arfafamin gwuiwa akan imani da Allah a irin wadannan lokutan? Toh ki sani, har ga Allah ba na jin son kowane namijin ba balle na ji son auren a raina. Hakan ba yana nufin wata matsalar ba, ki kaddara lokaci ne, duk sadda na ji son wani a raina, watakila..."

Sai kuma ta ma rasa me za ta ce, kawai sai ta sunkuyar da kai ta ri?e hannun Ummita cikin nata. Karon farko da ta ji tana hawaye, hawaye mai dalili ba wanda ta saba yi a irin gaSar nan babu dalilin ba. Ummita sai ta ji tausayinta ya lulluSe ta, Humaira ai itama da zuciya a kirjinta. Dole akwai abin da ke damunta amma ba ta faWa, ba ta magana sai dai ta yi shiru idan sun taso da zance ta maida su wasu cali cali.

"Ki tayani addu'a Ummita, ina da damuwa amma ban gama gane kan damuwar ba. Ina da abin faWi, amma zuciyata na kwaSa ta a koyaushe akan bai kai abin magana ba nayi shiru kawai. Na rasa meke damuna, idan na ce zan zurfafa tunani sai jikina ya hau rawa, kaina ya hau sarawa. Watakila iyakar abin da zan iya faWa kenan. Nidai ki dinga sanya ni a addu'a."

Ummita ta Wan rungumeta suna kuka. Kowannensu da kalar tunaninsa, dakyar suka rarrashi junansu suka share hawayen.

Sai kuma Humaira ta cigaba da karfafa mata gwuiwa akan ta bari Sahabi ya fito a yi magana. Ta kara da fadin.

"Kinga itama Raihana zan ce ta amince ta bar Imran ya turo. Shikenan sai ku bar min gida na huta."

Ummita ta harareta, ita kuma ta yi dariya tana kokarin danne radadin ciwon kan da take ji gudun kar ta kefa Ummita a wata sabuwar damuwar. Koda Ummita ta fita don amsa kiran Mami wacce ta turo Muhsin, sai ta zame ta kwanta ta runtse idanu tana tauna maganganun da suka yi da Ummitar, hannuwanta ri?e da kan da ke faman sara mata. Tana nan kwance har bacci ya sure ta, Raihana ta zo ta tashe ta akan ta je Mami na kira. Ta ci sa'a zuwa lokacin ya rage ciwon, don haka dankwalinta da ya zame ta maida ya rufe kan ta fita. Anan fa Mamin ta mata umarnin ta shirya za ta bi Futuha don ta taimaka mata da girki abokan mijinta za su je gidan nan zuwa jibi. Kamar ta cewa Mamin a bari mana sai jibin ta je ta dawo, amma ba ta son jan musu da ita kawai sai ta ce toh. Ranta na zafi haka ta shirya ta bi Futuha suka tafi. Tana ji Futuhar na yiwa Tasleem waya wai gatanan a hanyar gidanta, ita dai ba ta ce mata uffan ba sai kallon window da take yi zuciyarta na zafi, wani sashi na zuciyar na kokarin ce mata Mami ba ta kyauta mata ba yayinda wani gefen ke kwaSarta yana nusar da ita irin kirki da mutuncin Mamin. Bai kyautu ta munana mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login