Showing 93001 words to 96000 words out of 189325 words

Chapter 32 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

221

kai ta sai Maijidda ta zuba ruwa a ?asa ta sha tunda ta ga gazawata a kula da Ummita. Nagode."

Tana kaiwa nan ta zame hannunta cikin na Abban ta soma kokarin mi?ewa tsaye. Ya yi saurin dakatar da ita.

"Haba Maryama, to kiyi hakuri naji na yi laifi a kalamaina. Ba zan kai Ummita ba face da izninki. Kiyi hakuri, shikenan? Yanzu me kike tunanin za'a yi don sama mata nutsuwa?"

Ta sauke ajiyar zuciya.

"Tunda har shawarar da na bayar bai yi ba, toh na fi tunanin ka bayar da kudi muje da su ukun nayi musu ?ar siyayya sai kuma ita Humaira da ka riga ka san matsalarta akan maza. Ganin wannan abu da ya afku ga Ummitan ya ?ara sanyawa ta tsani al'amarinsu. Daidai da Fadeel din da muke murnar ta soma sakin jiki da shi suna ?ar hira yanzun ko muryarsa ba ta wani son ji. Tun wuri gwara a yi mata maganinsa. Na kuma fadamaka labarin wani mai magani, idan har ka amince sai na kai ta a karSo a gani ko za'a dace."

Abba ya kurawa Mami idanu, a duniya bai taSa ganin matar da ba ta damu da nata ba sai na wasu. Ba ruwanta da damuwar yaranta sai abin ya ci tura. Matar da Wiyarta ke kwance a gadon asibiti amma ba ta ko zancenta, burinta ta samar da farin ciki ga yaran wasu. Kaunarta ya ?ara mamaye zuciyarsa, ya ri?o hannuwanta ya sumbata sannan ya sakarmata murmushinsa da ya san yana daga cikin abin da yake ?ara dulmiyar da ita cikin kogin sonsa. Ita kuwa sai ta Wan kauda kai tana murmushi.

"Ina kaunarki Maryam, Allah ya yi maki albarka ya bar mu tare. Kin cikemin gurbin mace hudu a duniya. Babu abin da zan ce maki sai fatan alheri. Yanda kika ce haka za'a yi, gobe ki shirya zan baku kudi, ku fara da siyayyar, koda zuwa jibi ne kuma sai ki kai Wiyartaki wurin mai maganin. Ina fatan hakan ya yi maki?"

Har lokacin tana murmushi ta gyaWa mishi kai.

"Ya yi ranka ya daWe. Fatanmu Allah ya maidowa yaranmu farin cikinsu."

Cikin jin dadi Abba ya amsa da amin amin.

***
Washegari kuwa hakan aka yi, tamkar ba Mamin da Tasleem Wiyarta ke kwance gadon asibiti ba, tamkar kuma ba wacce Wiyarta mace ta farko ba (Futuha) ta kawo mata ?orafin tashin hankalin da take ciki. Daga fuskarta za ka fahimci kamar a duniya ba ta da wata aba wai ita matsala ko kuma damuwa. Ta saki ranta suka zagaye shoprite da su Humaira da Raihana. Ummita sosai kuwa ta sake Win kamar yanda Mamin take bu?ata, su kansu sun ji dadin yadda yanayinta ya sauya. A Sangaren Ummitan kuwa, ta tabbatar domin ta saki jiki ne aka yi duk wannan shiri hakan ya sa ba ta watsawa Mamin ?asa a ido ba, ta daure ta yakice damuwarta ta saki jiki. A Sangare guda shima Sahabi na nashi iyakar kokarin ganin ya faranta ran abar kaunartasa. Wannan ma ya yi tasiri kwarai a zuciyarta amma har lokacin wannan ba?ar ranar ta ?i Sacewa a tunaninta da mafarkanta. Su ne har gidan Hajiya Lubna, sun Wan jima tare da yaranta a ?asa inda Mami ta haye saman kafin daga bisani ta sauko su wuce.

"Mami ba zamu le?a Anti Tasleem ba?" Cewar Raihana. Mamin ta yi shiru. Ganin haka sai Ummita ta sa baki.

"Mami don Allah muje a duba ta."

Humaira kuwa uffan ba ta ce ba, asalima kallon shuke-shuken dake farfajiyar gidan Hajiya Lubna kawai take.

"Shikenan, muje. Yarinyar ce ta ban takaici, kina da ciki don sakarci ki tsaya wani faWa akan kishin banza da wofi."

Su dai babu abin da suka ce. Humaira ta buWe bayan mota ?arama ?irar KIA da Abba ya tsiya ta shiga. Mami ta Wan bita da kallo sai kuma ta murmusa ba ta ce uffan ba. Ta dubi Hajiya Lubna.

"Shikenan Hajjaju, sai mun yi waya."

?ar dariya Hajiya Lubna ta yi.

"Toh Hajiya Mamin yara. A gaida Tasleem din ki ce mata ta sha kuruminta zan zo."

"Ai shikenan. Za ta ji."

Daga haka suka yi sallama.

***
Malamin ya yi shiru yana duban ?asa, can kuma ya Wago ya kalli Murja ya girgiza kai.
"Abin da kike so ba zai taSa kasancewa ba."
Wani malolon ba?in ciki ya turnu?e zuciyarta. Da?yar ta haWiyi miyau mai Waci ta ce.

"A yanzu kake nufi ko har a gaba? Kenan Humaira ba za ta kasu ba?"

Malamin ya yi ?ar dariya.

"Wane mutum! Inji mutuwar. Ai Hajiya Murja babu wanda ba zai mutu ba. Kuma ni da na isa na duba mutuwar wani ai da nawa zan fara dubawa. Abin nufi kina son ta mutu kada ta auri Fadeel din ko? Toh hakan ba zai taSa yiwuwa ba."

Ji tayi wani abu mai nauyi ya tsaya a ?ahon zuciyarta. Malamin ya zubamata idanu, ya lura ba ta saduda ba don haka ya sauya zancen.

"Amma fa idan kina so za'a iya nakasata rayuwarta. Zamu iya nakasta ta gaba Wayanta. Amma da sharaWi, matukar aikin bai ci ba, zai dawo kanki. Kin amince?"

Ba tare da dogon tunani ba ta amsa.

"Eh na amince."

"Murja, ko za ki yi shawara?"

Ranta ya Saci sosai.

"Wancan karon haka ka ce min, wannan karon ma kana nema ka tauye ni da faWin haka ko? Toh yanzu ba shawarar da zan yi, ga kudi nan ka yi duk abin da ya kamata."

Ta bude jaka ta ciro bandir na dubu ta dire mishi.

Ya yi murmushi.

"Shikenan, ni nawa aiki. Sauran ke za ki yi da kanki. Dole kina bukatar zuwa inda ita yarinyar take. Ki je ki dawo nan da kwanaki uku."

Murja ta ji kwanakin tamkar watanni a wurinta. Tana jin zuciyarta za ta iya bugawa na yanda Fadeel ke rawar ?afa akan Humaira, kullum ya zauna da Hannatu a falon Anti to fa hirarta ne kawai.

"Babu wani aiki da za ka yimin akan Fadeel?"

"Aiki kai, ga wannan layar ki tabbatar kin saka a ?ar?ashin katifarsa, muddin ya kwana ya tashi ki Wauke ki binne. Wannan kwallin kuma ki zizira ki tabbatar kun yi ido hudu."

Ta yi murmushi, duk da cewa ta yi abubuwa da dama ba ta yi nasara a kan Fadeel ba amma hakan ba zai sa ta karaya ba. Ta karSa ta sa a jaka ta mishi sallama ta tafi zuciyarta sol.
***
Misalin ?arfe bakwai da mintoci ne, Fadeel ne zaune a falon Alhaji tare da Hannatu da Alhajin. Wannan damar Murja ta yi amfani da shi wajen kokarin ganin ta ?addamar da shirinta, sai da ta fakaici idanun su Khadija da Abdulmaleek wadanda suke kallo ta nufi Sangaren Fadeel.?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? Sai dai ta yi mugun mamakin jinsa a gar?ame da mu?ulli. Ta ciji leSSa don takaici kamar ta haWiyi zuciya ta mutu haka ta ke ji, sai kuma ta tuno duk abinsa da safe yana barin mukullin Wakin ya fice don a yi mishi gyara. Wannan ya sa ta yi murmushin mugunta ta juya tana mai kara cin alwashi.

***
Futuha na zaune tana faman cika da batsewa kamar ta fashe, Alhaji Yakubu ya shigo fuskarnan a murtuke ya zauna yana dubanta gami da jefamata ledar dake hannunsa.

"Idan har kina son mu cigaba da rayuwar farin ciki da ke, to ki gaggauta shan magungunan nan, an tabbatarmin zasu yi sanadin zubewar cikin dake jikinki. Idan kuwa har ki ka ?i, kika dage sai kin haihu da ni, toh shakka babu ba?ar rayuwar da za ki fuskanta sai kin sha mamakinsa. Sannan rashin bin umarnina zai yi sanadin da zan yi aure."

"Wallahi ba zan sha ba! Idan kuma aure ne ka yi idan ka isa! Kuma wallahi ka ji na rantse maka matukar ka ce za ka wulakantani ba zan zauna ba sai dai ka sakeni!"

Ya yi wata muguwar kyakyacewa da dariya. Ya nunata da yatsa.

"Ke Futuha, ba ki da hankali ashe? An fadamaki ni Yakubu zan saki mace? Ai babu wannan ranar a duniyata. Zaman aure da ni ya zamar maki dole. Koda bakya so kuwa sai kin zauna da ni. Na dai fadamaki, muddin rayuwarnan mai dadi da na WanWana maki kina so ya Wore, to sai kin bi umarnina. Idan kuwa kin ?i zan auro..."

Sai kuma ya yi shiru yana jinjina kai duk a kokarinsa na shanye sirrin dake ransa. Tun su na Dubai ya yi wani irin sabo da Winkewa da Sa'a ?ar Snow, kullum yana shafinta yana jifanta da likes da kuma chatting da suke yi a Soye. Tsantsar kalaman iskanci da ma hotunan tsiraicin da take turomasa ya yi mugun hargitsa shi, ba ya fatan ya kusanci zina amma ya sha alwashin aurenta. Ta kuma amince sannan ta ba shi lokaci ya gama cin angoncinsa kamar yanda ta bu?ata. Ya fi kowa sanin ?ar tsamar dake tsakaninta da Futuha, ya tabbatar idan zancen ya fasu to fa ba za su kwashe da dadi ba hakan ya sanya shi zaSar yin shiru.

"Ka auro wa?! Ka faWamata ko ma wacece don ubanta ta yi kaWan ta shigo gidannan!"

Ya mike ya watsamata harara.

"Saboda ke kika haife ni kenan? Titse ni za ki yi na faWamaki ko? Toh sai ki yi da wani."

Yana kaiwa nan ya kama hanyar fita, aikuwa ta yi tsalle ta dire gabansa idanunta har sun kaWa tsabar kishi da Sacin rai, cakumar wuyan rigarsa ta yi tun ma ba ta kai ga furta ?ala ba ya cire hannu sai ji kake tas a saman fuskarta.

"Ke! Ashe iskancin naki ya kai haka? Ni kike cakumarwa wuya?! Wannan ya zama na ?arshe idan kika ?ara mugun gangancin nan sai na nunamaki ba ki da wayo! Banza marar tarbiyya ?ar rawar Tiktok kawai! Mtsw."

Yana kai wa nan ya fice yana gyara zaman babbar rigarsa, dama dawowarsa kenan daga wurin ?ar Snow, don dai kalamai da rungume rungume wadannan ya sha su kamar ba gobe, ita ta yi mishi rakiyar siyan magani kafin ya maida ta gida da siyayya mai yawa sannan ya dawo gidan.

Futuha ta yi kuka mai isarta tamkar ranta zai fita sai dai ta ?udurta a zuciyarta Alhaji Yakubu bai isa ya wulakanta ta ba. Sai ta Wauki mummunan mataki a kansa kamar yanda Mami ta ba ta shawarar ta kwaci kanta da gidanta, to kuwa za ta ?wata ta ?arfin tsiya. Gama tunaninta kawai ta ciri waya ta kira wata tsohuwar aminiyarta Aneesa Jafar. Matar aure ce amma tantiriyar ?ar duniya ce domin ko a rayuwarsu ta makaranta tana cikin masu neman soyayyar Sir Ibb duk kuwa da auren dake kanta. Ita din shaida ce a yanda take juya mijinta a gida hakan yasa ta yanke shawarar tuntuSarta. Tun sadda ta yi aure ba ta ?ara nemanta ba saboda a ganinta ajinta ya fi nata, sai a yanzun da bu?atarta ta taso.
Kasancewae Aneesa ta iya barikanci, ko kusa ba ta nunamata komai ba suka gaisa hannu bibbiyu. Sai kuma Futuha ta warware mata damuwarta. Dariya Aneesa ta yi kafin ta amsa.

"Ai wannan ba matsala ba ce yar uwa, amma ki yi yanda yace. Ke banda abinki mene ciki don kin zubar da cikin wanda ya nuna ba ya son haWa zuri'ar da ke? Kuma wallahi kika yarda kika haihu da shi to ina mai tabbatar maki nan da nan za ki lalace ki zama wata daban. Ki daurewa ranki ki zubar da cikin idan ya so ki kawo kudi mu san hanyar da zamu bi ki mallake shi, yanda ko tsinke bai isa ya tsallake ba matukar ba ki yi mishi izini ba."

Cikin sanyin jiki da kuma Wan nutsuwar da Futuha ta samu ta ce.

"Toh Aneesa. Ni dama tsoron mutuwa nake, kada na sha na mutu naji ance masu zubar da ciki mutuwa suke yi."

"Mutuwa ai sai lokaci ya yi, nidai ina ba ki shawarar ki zubar kuma ki je ki yi planning abinki hankali kwance. Matukar dai kina so mu cimma burinmu."

Ta sauke ajiyar zuciya ta jawo ledar magungunan sannan ta ba Aneesa amsa.

"Shikenan, yanzun nan zan sha. Nagode Aneesa, zuwa gobe duk yanda ake ciki zan kiraki mu ji abinda ya dace a yi."

"Shikenan, sai na ji ki."

Daga nan suka yi sallama. Ta ?urawa magungunan idanu, a wata farar takarda suke, ta yi shiru can kuma kamar wacce aka tsikara ta mike ta dauko gorar ruwa ta bude, ta zazzaga magungunan a hannunta ta shanye su tas sai jiran sakamako.

***
Tana kwance tana juyi yayinda yan uwanta duka ke bacci abinsu. Ta mike zaune ta yi shiru, tashin zuciya take ji sai dai ta rasa yanda za ta yi ba ta kaunar ta yi amai motsin yun?urin ya tashe su. Zuwa lokacin ta soma shan jinin jikinta, tsoro da firgici ya soma shigarta. Bai fi kwanaki uku watan da suke ciki ya mutu ba amma har yau babu labarin ganin al'adarta. Tsoro iyaka Ummita na cikinsa. Ta kasa jurewa tashin zuciyar da take ji sai ta bude dakin ta fita da sauri zuwa falon bandaki, nan fa ta shiga kelaye amai kamar hanjin cikinta za su zubo. Duk wani kayan kwalam da ta ci a ranar sai da ta dawo da shi. Ta kammala ta wanke fuska ta gyara wurin, ta kuma Wauro alwala ta dawo falon ta zauna. Sai kawai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ga wani irin mugun sanyi da ya lulluSe ta lokaci Waya. Ba ta son koda tuna kalmar da take tunanin shi ya zama damuwarta balle har ta furta.

'Idan ya tabbata haka din ne ya za ki yi da Sahabi?'

Zuciyarta ta watso mata tambayar, ta rike kai sai kawai ta fashe da kuka sosai. Ba ma Sahabin kawai ba, ta ina za ta soma karSar wannan ?addara na rainon cikin da ta same shi ta hanyar fyaWe? FyaWen ma daga Wan ta'adda?

Tana wannan kukan mai tsuma zuciya ba tare da sanin irin ?arfin buWe muryar da ta ke yi ba har sai da ta ga hasken fitila a falon an kunna saboda akwai wuta. Mami ce, kafin Mamin ta ce wani abu sai ga Humaira a gigice ta fito itama. Kusan lokaci guda suka ?araso gareta.

"Mene ne ya faru Ummita?"

Humaira ta tambaya jikinta har yana rawa nan da nan itama ta soma hawaye ba tare da sanin ainahin dalilin kukan yar uwarta ba.

Ummita ta rungumeta tana kuka sosai.

"Ciki Humaira, Humaira zan haifi shege."

Da karfi kuma cikin daga murya Humaira ke girgizata kamar zararriya tana fadin.

"Wa ya fadamaki kina da ciki? Karya ne! Karya ne ba ki da ciki!!"

Mami ta dago Ummita.

"Wa ya fadamaki wannan mummunan labarin? Kin ga wasu alamomi ne?"

Mamin ta fadi nata hankalin itama a mugun tashe, nan da nan cikinta ya duri ruwa. Cikin sheshsheka Ummita ta ce.

"Ma..ma.mi, amai nake ta yi."

Ajiyar zuciya Mamin ta sauke.

"Haba Ummita, amai kuma sai aka ce maki yana nuni da cewa kina da ciki kenan? Amai ai alamun cutuka ne da dama, ba lallai sai ciki ba. Lokacin al'adarki ya yi ne?"

"Eh Mami, har ya wuce."

Gaban Mami ya buga da ?arfi, Humaira sunan Allah ta shiga ambato sakamakon ji da ta yi tamkar an zare mata wani laka na jiki. A durkushe take amma kuma jiri ne ke kwasarta. Tana ji tamkar a mafarki ake wannan diramar ba a farke ba.

"Maryama, meke faruwa ne?"

Suka juya gaba daya, Abba ne sanye fa jallabiya a tsaye a Wan rikice, ya tako ya ?araso ganin Ummita na kuka ya sanya shi ?ara jin rashin nutsuwa sosai.

"Ummita, meyafaru kike kuka?"

Mami ta yi saurin share hawayen da suka zubomata, ta mi?e tsaye.

"Babu komai, ba ta jin dadi ne. Humaira ku shiga ciki. Ki kwantar da hankalinki gobe idan Allah ya kaimu zamu yi test a gani."

Bayan wucewarsu Abba wanda ya daskare a tsaye cikin wani mugun faduwar gaba ya ce.

"Maryama, meye hakan kuma? Na kasa gano bakin zaren wannan tattaunawar da tsakar dare?! Me kike son ki ce?"

Gaba daya ma Abban ya diririce ko kadan ba ya cikin nutsuwarsa.

Mami ta dafe hannunsa.

"Babu komai Abban yara, muje zan maka bayani."

Zai ?ara magana ta hana shi ta hanyar ro?onsa akan su tafi dare ne kar a ji sai kuma ya hadiye maganar ba musu ya yi gaba zuwa Waki ta bishi a baya bayan ta kashe fitilun falon.

Ya ji zancen tamkar saukar aradu, nan da nan ya dafe kansa.

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Maryama wannan mummunan labarin da me ya yi kama? Tashi tashi muje asibiti yanzu a dubamin ita."

Mami cikin hawaye ta yi saurin dakatar da shi ta hanyar dafe kafarsa gami da girgiza kai.

"Aa Abban yara, kar muyi haka. Yin hakan tamkar tonuwar asirinmu ne. Duniya sai ta san halin da muke ciki. Ka kwantar da hankali tunda ana siyar da Pt-strip na awon ciki, gobe da safe mu bayar a siyo a auna fitsarinta don mu ga halin da take ciki. Mu yi fatan alheri da fatan kar zatonmu ya tabbata.

Ajiyar zuciya mai karfi Abba ya saki.

"Innalillahi...Ya Ilahi! Wannan ranar dame zan kirata ni Isuhu? Inama tun farkon fari ban hana Hajiya Maijidda ri?on Ummita ba tun tana ?arama, da watakila ba zan ga wannan ranar ba."

Wani irin zuciya ya tasowa Mami, ta ji tamkar ta haWiyi zuciya ta mutu. Ranta ya yi mugun Saci, wato duk hakuri da dauriyar shanye damuwa da bakin cikin RI?ON BARE da ta yi, da wannan sakayyar Abban zai bi ta? Ta so ta furzar da abinda ke ranta sai kuma ta daure kamar koyaushe ta shanye rabi da kwatan Sacin ranta ta ce.

"Wane irin rashin tawakkali ne haka Abban yara? Ka isa ka hana Allah ikonsa ne akan al'amarin Ummita? Ummita ko bangon duniya ta je idan hakan ya ?adartu a kanta sai ya afku. Ban da haka ma, kenan kana kaicon rayuwar da ta yi a hannuna? Kana kaico da irin abin da ya fada mata? Ko a tunaninka a sanadina ne aka sace su har kaddarar fyaWe ya faWa kan Ummita?"

Ta karasa zancen da wani irin kausasshen murya, ganin ya kalleta da sauri da alama zancen bai mishi dadi ba kuma bai san fassarar da za ta ba shi kenan ba ya sanya ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login