Showing 81001 words to 84000 words out of 189325 words

Chapter 28 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

223

sauke ta a gidan. Tana shiga ta zube jikin ?anwar Abba, Baba Amina? da suka saba tun a baya tana kuka sosai ana ba ta ha?uri. A lokacin ne kuma Mami ta shigo daga Sangaren Abba cikin dogon hijabinta, ta gama jin yadda aka yi da Abba da kidnappers din akan kuWin fansa. Jin muryarta su na gaisawa da makwaftan da ba su jima da le?owa gidan ba ya sa Anti Maijidda mi?ewa kamar wacce aka tsi?ara ta hau tafi raf raf har sau uku, wannan ya ja hankulan kowa kanta yayinda wasu suka shiga tunanin kodai Satan Ummita ya girgiza kwakwalwarta har haka? Mami kuwa cak ta tsaya kawai tana mai zubamata idanu. Maijidda kenan, macen da ba su taSa raSar juna da alheri ba, babu wata jituwa da ta ?ara haWa su tun bayan rasuwar Fatima mahaifiyar Humaira.

Maijidda ta soma magana murya a Wage kuma a kausashe.

"Ki zuba ruwa a ?asa ki sha Maryam! Ki tara jama'arki ku yi kiWa ku yi rawa har da juyi! Yau burinki ya cika! Abin da kika jima kina ?ullawa akan yarannan yau kin cika shi!"

Jin haka Baba Amina ta mi?e a firgice cikin kaWuwa ta fisgo hannun Maijidda.

"Maijidda ki shiga hankalinki mana! Ki yarda da ?addara ki yi imani da ita. Wannan wane irin zantukan banza ki ke yi akan baiwar Allahn da ta ri?i amanar Wiyar ?ar uwarki da amana da kulawa tsawon shekarunnan koda wasa Ummita ba ta taSa kokawa da ita ba? Wane irin ba?in ?azafi kike shirin yiwa baiwar Allahn nan?!"

Anti Maijidda ta fashe da kuka sosai tana nuna Mami da yatsa.

"Har abada ni Maijidda ba zan taSa kaunarta ba, kuma ba na jin zan yarda da ita koda ace gaba Waya mutanen duniyar nan za su taru su yi mata kyakkyawar shaida! Ba?ar azzaluma ce! Amina ni nasan wacece Maryam, ni zan ba da labarinta! Don haka idan har bincike ake son yi na gaske daga cikin gida, a soma daga kanta da kuma azzalumar uwarta!"

Wannan ?azamin furucin ya sa Mami ta fusata sosai.? Hannunta na rawa kamar yadda dukkan gaSSan jikinta suke yi ta nuna ta da yatsa, da?yar maganarta ke fita saboda zuciyar da ta taso mata da kuma ruwan hawayen da suka wanke mata fuska lokaci guda.

"Na shanye dukkan ba?a?en maganganunki na tsawon shekarunnan ba don komai ba sai domin albarkacin ?ar uwarki marigayiya Maimuna da muka yi zaman mutunci da ita! Na kuma cigaba da jure duk wani cin kashinki a dalilin Ummita jinin Maimuna ce da Naziru. Ban da haka ba ki da wata ?ima ko daraja a idanuna!"

Baba Amina da mutanen Wakin dakyar suka tsawatar aka kashe zancen inda Mami ta fice daga falon cikin ?unar rai zuwa Wakinta inda Anna ke zaune kuma tsaf ta ji dukkan abin da ya faru. Allah ya ta?aita lamarin Jannat ba ta gidan, ta fita dubiyar wata ?awarta da aka yiwa aiki a asibiti, da abin zai fi haka Saci.

Anna ta dube ta sai kuma ta yi dariya.

"Maryama kenan, wannan shi ne sakamakon bautar da ki ka yi na ri?on Ummita ko? Wannan ranar nake jira dama, ban kuma zaci zan gani nan kusa ba. Shashashar yarinya! Ga shi nan tun ba a je ko'ina ba kin kwashi kashinki a hannu. Da ace tun a farko kin ji maganata hakan da bai faru ba. Yanzu sai kiyi kuka da kanki akan duk abin da ya faru."

Mami ba ta ce da Anna komai ba, sai ta fidda hijabin da ta zumSula ta Wauki wayarta kawai ta zauna ta yi shiru tana aikin dannawa, Anna ta cigaba da zabga ruwan bala'i, da Mami ta ga abin ba na ?are ba ne, kawai sai ta fice zuwa Wakin su Raihana ta ba??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????r mata Wakin.

***
Fadeel ya farka gami da ?urawa silin idanu, shiru ya yi yana ?o?arin tunano dalilin kwanciyarsa ciwo, a hankali kuma ya juya kansa ya dubi Wakin. Ibb ne kaWai a zaune yana danna waya bai ma lura da farkawarsa ba. Ya lumshe idanunsa lokaci guda komai ya dawo kwanyar kansa, a firgice ya mi?e zaune.

"Ya Salam!" Ya faWi da ?arfi yana mai fisge drip din da aka sa mishi. Furucinsa ya sa Ibb mikewa da sauri ya nufo shi gami da ri?e kafaWunsa.

"Fadeel yi a hankali mana."

Jin haka ya dube shi da rashin kwarin jiki.

"No Ibb, kwana nawa nayi a nan? Humaira na hannun kidnappers, za su kashemin ita. Ka bar ni na je nemanta."

Daidai nan Alhaji da Daddy suka shigo. Fadeel ya mi?e jiri na kwasarsa yayinda Ibb ke Wan ri?e shi, Daddy da sauri ya tarbe shi ganin kamar zai faWi ya ce.

"Fadeel kwantar da hankalinka, in sha Allahu za'a ga Humaira."

Kawai sai ya ji hawaye sun zubomasa, wato za ma a gan ta ba wai an ganta ba? Ya girgiza kai yana kallon Daddy amma sai ya kasa magana.

Suka taimaka suka mayar da shi mazauninsa. Daddy a nutse ya karanta masa duk yadda suka yi da Abba ya kuma ?ara da faWin.

"Yanzu haka ba mu jima da waya da shi ba, ya tabbatar mana da cewar sun samu kira daga mutanen, sun kuma bu?aci kuWi. Wannan damuwar ba zai magance maka kowacce matsalar ba, addu'a da kuma sadaka ita zamu du?ufa yi. Yanzu idan ka ce za ka fita nemanta, ta ina za ka fara? Ka san a inda suke ne? Daji, cikin gari, kasuwa, ?auye, kai ko ma ba a garin suke ba gaba Waya wannan sanin Allah ne kaWai don haka ka samarwa kanka ?arfin zuciya ka dage da kai wa Allah kukanka. Babu abin da ba ya magancewa."

Daddy ya cigaba da kwantar masa da hankali har da cewa koda ace kudaden da Abban za su haWa ba za su kai ba, shi ya ji ya gani zai san yadda za'a yi a cika a bayar don su kuSuta, balle kuma shi Fadeel din wanda yake jin zai iya sadaukar da dukkan abin da ya mallaka a doron ?asa don kuSutar rabin jikinsa daga hannun azzaluman nan. Sosai ya ji dadin zantukan Daddy, da wannan ya lallaSa ya yi wanka, brush, da alwala, Ibb ya ba shi kaya ya sauya. Daga nan ya hau ramuwar sallolin dake kansa.

Bai kai ga idarwa ba sai ga Anti Amarya tare da Murja sai ko Fu'ad da ya kawo su, hannun Murja ri?e da kwandon abinci. Ta gaida su Abban sannan ta karasa ta ajiye gefen gadon. Gefe ta koma tana satar kallon Fadeel Win da a kwana Waya kawai ya zabge. Zuciyarta na wata iriyar tafarfasa.
? 'Ka yi ka gama Fadeel, na rantse maka koda ace Humaira ta fito ni Murja sai na kashe ta da hannuna. Ballantana ma ba za ka ?ara ganinta ba.'

Ta yi maganar a zuci, su Alhaji suka tafi saboda yamma ta kawo kai yayinda Ibb suka fita don yi musu rakiya. Fadeel na idarwa ya dubi Anti Amarya ya gaishe ta, ta amsa tana mishi sannu. Ido ta Wan yiwa Murja hakan ya sa ta saurin gaida Fadeel, ya amsa ba tare da ya kalleta ba.

? Nan suka zauna har sai da Fadeel ya Wan sha ruwan shayi dakyar amma sam ya ?i yarda da cin abinci, tunaninsa ko a wane yanayin Humaira take? Watakila ma ko abincin ita ba a ba su sun ci ba. Wannan ya da?ilar da shi daga ci.

***
? Sahabi saurayin Ummita kullum sai ya zo gidan ya gaida Abba da Mami, gaba daya ya komaWe ya rame tsabar tunanin Ummita. Iyaye da ?an uwansa babu wanda bai shigo jajantawa ba. Hakanan ?an makarantar islamiyyar su sun zo sun kuma yi saukar Alkur'ani akan Allah ya bayyana su. Hatta da yan makarantar su Ummita na boko sun zo har da malaman makarantar an jajanta. Aka yi addu'a suka tafi.

? Labarin dai yana ta yaWuwa don har waWanda su Abban ba su ma sani ba sun zo sun taya su jaje, da yawansu a social media suka ci karo da shi. Mubarak dake Ghana yana jarrabawar ?arshe hankalinsa gaba daya yana Kanon, ba don Abba ya ce kar ya zo ba ya zauna har ya kammala da tuni ya dawo. Hakanan su Yassar ba su zo ba. Amma sosai abin ya taSa su duk da ?iyayyar da suke yi musu.?
? ?
?? ?angaren Futuha kuwa ?ar Dubai, kasancewarta mai mu'amala sosai da yanar gizo sai ga abin nema kuma ya samu. Bidiyo sosai ta yi tana kuka ga hotunan Ummita da Humaira daga ?asa ta Wora a shafinta tana addu'ar Allah ya bayyana su a ?arshe ma har da sanya muryar shahararren Malamin nan wato Sudais yana addu'a. Koda ta Wora hankalinta kwance ta shiga duba yadda ba a Wauki dogon lokaci ba bidiyon ya yaWu, nan fa jama'arta suka fara jajanta mata su na tambayar dama Humaira mai shafin Deelsha's Delicacies yar uwarta ce? Da yawa ma wadanda ba su san Humairar ba ko shafinta sai lokacin suka dinga followinh dinta, lokaci guda shafinta ya yi jama'a fiye da dubu talatin. Hakanan shafin Ummita ma ya yi jama'a.

Raihana tana kallon duk abin da ke wakana amma ba ta magana, karshe ma sai ta kashe wayarta gaba daya ta ajiye.? Tun da Abba ya shaida musu da kuWaWen da aka ce a bayar na fansar Humaira da Ummita ta ke jin ?ar nutsuwa, ko ba komai kenan su na lafiya kuma Abban ma ya tabbatar musu ya ji muryoyinsu amma bai ce musu ga a yanayin da ya ji ba gudun tayar musu da hankula.

***
? Fadeel da Ibb suka shirya tsaf a washegari zuwa gidan su Humaira kamar yanda Fadeel din ya nema. Hankalinsa ya kasa kwanciya da zamansa a asibiti alhalin ba a ga Humaira ba, kuma bai je ga iyayenta ba. Wannan ne ya sanya su Alhaji goyamishi baya don haka ana ba shi takardar sallama ya kama hanyar gidan.

Sun samu tarba na mutunci daga Abba, Tasleem tun ganin da ta yiwa Fadeel matsayin saurayin Humaira ya zo jajantawa ta ji hankalinta ya yi mummunan tashi. Kishin nan daWaWWe na Humaira ya taso ya soma? cin zuciyarta. Har gobe akwai son Fadeel a ?irjinta, ta kuma tabbata da ace shi ta aura da yanzu wani labarin ake ba wannan ba.

Kusan lokaci guda suka shigo gidan da Fadeel anan ta gan shi, shi kuwa bangaren Abba suka nufa inda ?asim da ya yi musu iso ya raka su ciki. Fauziyya ce ta yi mata rakiya gidan, tana kuma lura da sauyin da ya zo mata lokaci guda sadda ?asim ya dawo yana shaida mata ai manemin auren Humaira ne. Ta yi shiru ba ta ce mata komai ba tana ?ara nazarinta.
? A falon ta bar Fauziyya ta faWa Sangaren Anna tana huci. Nan ta tarar da ita zaune da Jannat wacce ke zaune tana taunar gasasshiyar kazar da ta siyo suna hira da Anna kai ka ce babu wani tashin hankalin da ake yi a gidan. Ganin yanayinta ya sanya su dubanta.

? "Toh mai ciki, yau kuma wa ya taSo ki?"

Ta zauna idanunta suka cicciko da kwalla yayinda zuciyarta ke faman tafarfasa. Kwafa ta yi kana ta amsa.

"Wai Fadeel na gani ya zo jajantawa Abba fa? Har yanzu dama yana tare da Humaira? Shi ne don munafunci Humaira ta ci amanar Mami ta Soye zancen?"

Murmushi Jannat ta yi.

"Ke ban da abinki ina Humairar take a yanzu? Kina tunanin shirin na wasa ne za ta dawo, ai daga can inda take sai wata duniyar kuma ba wannan da muke ciki ba. Duk fa wanda ya samu dama ya dama.? Kuma da kike wannan maganar ba yanzu gashinan kin auri Hamza ba? Ba kya sonsa kika bari ciki ya shige ki?"

Tasleem ranta ya Wan yi sanyi jin yadda Anti Jannat ke fadin kaddarar Humaira kai ka ce ita ta rubuta hakan. Batun cikinta ya ?ara jefata damuwa, dama ba da son ranta ta samu ba kuma Hamza ya rantse sai ya yi mugun saSa mata idan ta zubar.

"Wallahi Anti idan har zan samu na auri Fadeel zan iya kashe ko nawa ne a yimin aiki a kan Hamza ya sake ni. Anti wai kin taSa ganin Fadeel kuwa da irin yadda ya haWu? Wallahi ba zan iya zuba idanu wata ta kwacemin shi ba."

Anna tsohuwar banza ta kwashe da dariya madadin ta yi kwaSa akan wannan haramcin da ake aikatawa sai ma ta ce.

"Kina da Jannat Firdausi ai babu ke babu fargaba. Yadda aka yi wancan haka wannan ma zai kasance labari."

Suka yi dariya. Can kuma Jannat ta Wan jinjina kai.

"Ko wane ne wanda ya aikata wannan kidnapping din ya yi matu?ar burgeni, da ace ina da damar ganinsa sai na mishi babbar kyauta. Sai hakan ya zo mana da nasara kuma akan gaSa, Boka ya tabbatarmin da cewa Humaira a can za ta haWu da ajalinta. Itama Ummita babu tunanin za ta rayu balle har su samu damar kuSuta su dawo. Kawai dai zan so dawowar ita Ummita, yarinyar ta iya bauta."

Tasleem ta yi murmushi.

"Nima dai Ummita ba ta yimin komai ba, ba ni da wani ?ulli da ita kamar Humaira. Wallahi Anti na tsane ta na kuma tsani duk wani mai sonta."

"Har da ni kenan!"
Suka juya don ganin mai furucin a razane. Tasleem ce ta soma? kauda kanta gami da jan guntun tsaki ciki-ciki ba tare da ta ce uffan ba.
Raihana wacce ta gama jin dukkan munanan maganganunsu? ta tako tsakiyar dakin sosai ta cigaba da magana.
"Har da ni kenan! Wannan ba Ummita ko Humaira kaWai ku ka tsana ba Anna, har mu jinin Abba. Na yi mamaki dama da Anti ba ki Wau mataki akan abin da Humaira ta yi maki a kwanakin baya ba, ashe dama ke tarkon da kika Wana babba ne? Ashe wannan damar kike jira? Kai duniya! Mutum ya ?i mutum har ta kai yana mishi fatan mutuwa? Me suka tare maku? Ku ji tsoron ranar da ha??in su Humaira zai kama ku!"

"Me kika ji ance da za ki rufe mutane da faWa tamkar kina magana da Muhsin ko Waleed?"

Jannat ta furta a ?o?arinta na shanye firgicin da ta Wan shiga, toh koda ace ba su da hannu a satar Humaira da Ummita, ai wannan Sarin zancen da suke yi zai iya jawomusu matsala tunda ana kan bincike ko yau Win da safe sai da D.P.O ya zo wurin Abba.

Raihana ta yi murmushin takaici.

"Kar ku yi tsammanin ban ji mugun ?ullin da ku ke yiwa bayin Allahn nan ba. Amma ku sani, Allah na tare da bayinSa a duk inda suke kuma cikin kowane hali. Na rantse muku, duk iya yinku, duk iya ?o?arinku, ba za ku iya kawo sanadin koda karta a fatarsu ba balle a kai ga rasa rayukansu ba face sai da iznin Allahn da ya halicce su. Ku yi dukkan kokarinku, akwai ranar ?in dillaci."

Tana kaiwa nan ba ta ko ?ara kallonsu ba balle ta ji me zasu ce ta sa kai ta fice daga dakin a guje zuwa nasu Wakin wanda suka mallaka da su Humaira a baya. Haka kawai sai ta buWe sif din kayan Humairar da Ummita ta fiddo abin da ta san sun fi so cikin kayansu ta yi ta kuka. Lamarin da ya sanya Mami hana ta kwanan Wakin sai dai nata Wakin. Ba za ta iya misalta ba?in cikin da ta ke ciki ba sanadiyyar Satan ?an uwannata. A gefe guda ga ba?in cikin kasancewar Jannat yar uwa ga Maminta ballantana a kai kan Tasleem da take ji kamar ta sha?e ta. Sai ko Anna da har ba ta kaunar ganin fuskarta a kwanakin nan tun da ta nuna ba ta wani bakin ciki da Satan yan uwanta.

***
Abba ya yiwa su Fadeel tarba na mutunci da dattako, gaba Waya idan ka ga Abba sai ya mugun ba ka tausayi sakamakon yadda ya koWe ga kuma rama.
?
"Ka yi hakuri Fadeel, in sha Allah ?iris ya rage na kammala haWa kuWaWen fansar su, lafiya kalau za su dawo hannunmu. Kai dai ka ci gaba da addu'a."

Fadeel ya ?ara yin ?asa da kai, Abban da ya ke da burin ya wayi gari ya gan shi a gabansa da zummar neman auren Humaira, su yi hira da dariya tsakaninsu sai gashinan ganin da suka yiwa juna na farko ba mai daWi ba ne ko kaWan.? Zuciyarsa ta yi rauni nan da nan kuma ya ji idanunsa sun kawo ruwa da?yar ya iya daurewa ya amsa.

"Toh Abba, Allah ya kuSutar da su."

Abban ya amsa da amin, yana son ya ce idan da yadda zai tallafa, a ba shi dama amma ba ya so Abban ya ga kamar ya mishi katsalandan wannan ne dalilin da ya sa shi jan bakinsa ya yi shiru. Sun Wan jima anan har Abban ke faWamusu cewa Kawun Humaira suna hanya daga Maine, ?asar Nijar. Suka yi musu fatan isowa lafiya a karshe dai Ibb ya soma yiwa Abban sallama kan zasu wuce ganin Fadeel kamar ma ba shi da niyyar motsawa.

Bayan fitarsu Abba ya yi tagumi cike da tunani, a yanzu duka-duka dai abin da ya haWa bai fi miliyan shida ba, ya kuma sani muddin ba gidansa da suke ciki zai siyar ba bayan motocin da ya sa kasuwa ya siyar, to fa babu ta inda zai samu cikon miliyan goma na fansar yaransa. Yana wannan halin ne Mami ta yi sallama ya amsa gami da ba ta damar shigowa. Ta shigo sanye da hijabinta ta zauna gefensa fuskarta dauke da damuwa ta ce.

"Ba?i ka yi ne?"

Ya numfasa.

"Eh, yaron nan Fadeel ne ya zo da abokinsa, ba su jima da tafiya ba."

Ta Wan yi jim sai kuma ta numfasa ta ce.
?
"Allah Sarki."

Daga haka ba ta Wora komai ba, shiru ya biyo baya kafin Abba ya girgiza kai ya ce.

"Maryam, an zo gaSar da dole sai na siyar da gidannan na cika kuWin fansar yarannan. Idan ya so sai mu koma wanda bai fi shi ba, lokaci na ?urewa sosai, kaina ya ?ulle gaba Waya, dole na tashi na nemi mai siya ko kaWan a kuWin ne aka ba ni zai isa na cika na kaiwa wadannan mutanen."

Murmushi Mami ta yi.

"Kamar ka san shawarar da na zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login