Showing 54001 words to 57000 words out of 189325 words

Chapter 19 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

246

sanyaki kafin na zo." Muryar Mamin ta katse ta. Ta mike tana mai amsawa da toh gami da share kwallar da ta cika idanunta. Bayan fitarta Anna ta ce.

"Maryama ban san irinki ba, ban san wa kike son ki burge ba. Wato har wani girki za ta fara na harkar kuWi? Wannan naki salon u?ubar ce ko kuwa dai son yarinyar ne fiye da naki yaran ya rufemaki idanu kike son ta kere su a komai ta yi musu zarra? Idan bacci kike ki farka, kin nemawa yarinya har ya zama mai arziki, a kuma yanda naji za?in miyarta ina mai tabbatar maki watarana sai ta fi ki kuWi. Tukunna ma, kuWaWen kina nufin ita za ki dinga dam?awa?"

Mami ta yi shiru na ?an sakanni har Anna ta ?ara tankawa yayinda Jannat kuwa ta ja tsaki don tana jin haushin yayarta sosai, tana abu tamkar a duniya su Humaira ta haifa ba su Futuha ba. Can dai Mamin ta yi magana.

"Ta asusuna kuWin za su shigo."

Murmushi Anna ta yi mai tarin ma'ana kafin ta ce.

"Na sanki Maryama, ni na haifeki. Kar ki zo mini da rainin hankali da wayo kinji ko? Wato ni ga sakara shi ne za ki rufe ni ruf, to ai koda ta asusunki kuWaWen suka shigo a yanda kike nunawa yarinyarnan kamar ki lashe ta, ke me iya yin hidimar ta ce ba naki ko yaranki ba. Kaiconki Maryama, lallai idan ba bi a hankali ba yarinyar nan watarana sai ta watsa maki borkono a idanu. Kina wasa da wuta."

Janant ta kalli Mami, sai kuma ta girgiza kai.

"Anna, zai fi kyau ki bar wahalar da bakinki a kan wannan saboda Wiyarki ta yi nisan da ba ta jin kira. Ita mai miji, burinta ta nunawa duniya ta fi kaunar Wa wani sama da nata yaran. Idan kin ji yanda yarannan ke ?orafin nuna halin ko in kula da take yi musu sai ki rantse ba ita ce ta yi na?udar su ba a bola ta tsinto su. Babu ma kamar su Yassar wadanda su ubansu bai sakarmusu sun ji dadin rayuwa irin na matasa sa'anninsu ba, su ba su sami wata kyakkyawar kulawa a wurin uwar ba. Ni na rasa irin wannan gidan da rayuwar cikinsa. Ba haka nake rayuwa a gidan nawa mijin ba, shi koyaushe burinsa ya wadata mu da abinda za mu huta ni da yaransa, amma tun da na rayu a gidannan har na yi aure, mijinta bana jin ya kashemin sama da dubu Wari biyar a rayuwa."

Mami ta mi?e tsaye tana duban Jannat, zuwa yanzu ranta idan ya yi dubu to ya Saci.

"Ya isheki hakanan! Ke tsabar rashin kunya har kya kalli kwayar idanuna ki faWan magana? A gidan dai da kika raina nan kika rayu sannan ko Yusuf bai kashe maki sama da kuWaWen ?aryar da kika buga lissafinsu ba, ai kin ci kin sha daga jikinsa. Ke yanzu idan da kina can wannan dajin kina rayuwa, har kin isa ki ga shi mijin da kike tutiya da shi ki aura? Ni na isheki! Nan da kike ganina kar nake, na fi ku sanin inda ke mini ciwo. Ba damuwarki ba ce kuma balle ki sani, idan har ba za ki dauke idanu daga lamuran gidana ba, ki tattara ki..."

"Maryama!" Tsawar da Annan ta bugamata ne yasa ta yin shiru tana fesar da huci mai zafi, ta kalli Anna sai kuma ta juya ta fice daga Wakin. Jannat nan ta haukacewa Anna wai Mami ta yi musu gorin zama a gidan don haka su tattara su bar mata gidanta. Anna dai ta dinga lallaSa Jannat, ta sani muddin ta bi cewarta ta bar gidan to fa komawa can wani ?auyensu dake garin Agadez ya kamata, yanda ta fito ta WanWani rayuwar daula koda ace bai kai yanda ta ke so ba, ta gwammace ta cigaba da rayuwa a nan. Ta sani babu ta yanda za'a yi shegiyar surukar zamani irin ta Jannat ta amince da zamanta a gidan Wanta. Dakyar dai ta samu Jannat ta janye ?udurinta, tsana da haushin Humaira ya ?ara ninkuwa a ?asan ranta.

***
Humaira kuwa sai ta nemi murnar da take yi na Oda ta rasa, jiki a saluSe ta yi mata dahuwar dafadukan macaroni mai busasshen kifi. ?amshinsa ya karaWe kicin Win da falo. Koda ta kammala ta haWa komai a ?aton faranti ta kai mata babu godiya ba kallon arziki, itama ba ta sa a ka ba kawai ta jya da zummar tafiya.

"Ke zo nan!"

Muryar Anna ta ji, ta runtse idanu kirjinta na dukan tara-tara cike da tunanin da wanne kuma Annar ta zo yanzu ta juya ta koma ta durkusa ba tare da ta kalleta ba. Ta soma magana a kausashe.

"?ago ki kalleni nan, ni da kike gani dai na fi ?arfinki. Mun ci dubu sai ceto, zuri'ar Mamman ?an Jika daidai nake da kowane bafillace mai ta?ama da asiri. Har mu za a gayawa asiri? Tun wuri ina gargaWinki ki fice a rayuwar Wiyata, idan ma wani mugun ?ullin aka kawoki da shi don ki shiga tsakaninta da yaranta toh ahir Winku, ni dai na fi ?arfinku balle kuma tsatsona. Ki kama kanki tun kafin na Wau mummunan mataki a kanki. ?an girkin da kike ta?ama kin iya ni mai iya juya lamarinki da shi ne, idan kuma kina da ja ki cigaba kar ki fasa. Asir dai ba za ki nunamana ba, mun saka Allah a gaba ne kawai shiyasa muka watsar. Amma muddin kika ce za ki cigaba da juya Wiyata kamar waina da shiga tsakaninta da yaranta da ta haifa da cikinta ni nan zan nunamaki iyakarki."

Tana kaiwanan ta juyar da kai tana girgiza ?afa na bala'i. Humaira ta dubi Anna dakyau, an zo gaSar da ba za ta jure ba sai ta ba ta amsa ko yaya ne. ?azafin sihiri ba za ta jure shi ba don haka ta soma magana da wani irin ?unar rai.

"Kiyi hakuri Anna, amma kalamanki laifi ne ko a wurin Ubangiji, kin yimin mummunan zato kin kuma yimin ?azafi. Lallai Ubangiji zai yi mana hisabi a gobe ?iyama. Na samu kyakkyawan tarbiyya a wurin Dada da Kawuna irin wanda nake da ya?inin ko uwar da ta haife ni sai haka. Ban san boka ba balle mugun malamin da zan je ya yi min wani mugun aiki ba, asalima ban da a fina-finai da kuma labari ban taSa karo da su ba. Wanda ya ri?i Allah, ai ba zai aikata abin da kuke yi ba. Kullum cikin zagi da aibata musulmi Wan uwanku, ni Humaira babu wani mahalu?i a duniyarnan da zan kai ya yimin aiki a kan wasu, kenan idan nayi hakan ma ban ri?i gaskiya Waya ba, ban yi imanin Allah zai iya amsamin addu'ata ba komai muninta komai kyawunta ba kenan. Ai Ubangiji ya wuce duk zatonku. Balle ma ban taSa ro?o mai muni kan kowane Wan uwana musulmi ba, kuma ba zan fara akan Mami ko yaranta ba. Tsakanina da Mami sai addu'a, ta yimin ri?on da ya sa nake jure dukkan wani abu da za ki yimin ke da jikokinki. Har abada kuma bisa darajar Mami ba zan taSa daina ganin mutuncinki ba. Kiyi hakuri idan da abin da na faWi mai zafi."

Tana kaiwa nan tuni ruwan hawaye sun wamke fuskarta, a bisa tilas ta kalli idanun babbar da ba ta ri?e girma da tsufanta ba ta gasamata maganganu. Ita ta fi Anna jin ciwon haka, sai dai haka take, ba ta iya hakuri idan aka kai ta bango musamman idan abin ya kasance ya haWu da ba?in ?azafi. Juyawarta ya yi daidai da saukar igiyar chaja a gadon bayanta, Jannat ce wacce a farko ta yi Wif don gani tayi tamkar a mafarki wai wata ?aramar yarinya na gasawa uwarta maganganu, sai da ta motsa da zummar barin Wakin sannan ta zabura ta janyo igiyar chazarta. Nan fa ta hau jibgar Humaira amma kamar ba mutum ake duka ba, ta ?i tafiya ta kuma ?i ?watar kanta. Zuciyarta tafarfasa take yi. Kallon Jannat take kawai tsakar idanu yayinda idanunta suka kaWa sosai sai ruwan hawaye. Ganin da ta yi Humairar babu ko gezau sai kawai ta hau wanke ta da mari tana zaginta. Ta yi biyu, za ta ?ara ta ri?e hannunta gam, ba ta san ya aka yi ba, ba ta kuma jin za ta iya tunanin mai kyau da marar kyau a lokacin, kawai ta ji yatsun hannunta sun sauka saman fuskar Jannat da mugun ?arfi ji kake tas!!! Ya yi daidai da faWowar su Futuha Wakin waWanda dawowarsu kenan daga shoprite cike da nishadi. Ganin abinda ya faru ne ya sa Tasleem sakin ihu mai ?ara da ya ja hankalin Abba da Mami dake a sashin Abban, suka nufo da sauri Abba ya Wan tsaya daga ?ofa yayinda Mami ta kutsa kai Wakin. Alokacin rufewar idanun Humaira har ya kainta sha?i wuyan Jannat ta dangana ta da bango, babu sautin kuka sai ruwan hawaye, Jannat ta raina kanta, ta ji ashe ba ta da ?arfi don ji tayi kamar ba iyaka Humairar ba ce ta sha?e ta ba.

"Wayyo Allahna! Ku taimaka za ta kashemin yarinya!"

Jin wannan furucin na Anna ya sa Abba danno kai cikin Wakin. Tsawa ya dakawa Humaira ba ta ko kalleshi ba. Ya kuwa ?arasa ya Wauketa da wani marin sannan ya fincike hannunta. Mami kuwa mutuwar tsaye ta yi, ita kadai ta san me take ji a zuciyarta, wannan shi ne lokacin da take gudu, ta juya da sauri ta bar Wakin. Su Futuha kuwa suka yi kan Antinsu suka rirri?e suna kuka yayinda Anna ma kukan take har da biyu saboda ganin Abban. Shi kuwa rufe Humaira ya yi da duka sai da ya ga har ba ta motsi kafin ya karasa ga Jannat yana ba ta hakuri, Jannat kamar jira take kawai sai ta fashe da kuka sosai da fadin.

"Wannan wane irin cin mutunci da zarafi ne? Da aurena da darajata da shekaru sa'ar ?anwar ?anwata ta sha?i wuyana? Wannan rayuwar da me ya yi kama? Kiyi hakuri Humaira, watakila laifina ne da na zo gidannan. Na saba ganin girmamawa daga mahaifinki, hatta da marigayiya Anti Fati ba ta taSa yimin koda kallon banza ba, amma yau ga Wiyarta nan ta sha?eni tana ?o?arin kai ni lahira. Aikuwa a yau zan bar maki gidanku."

Ta ?ara fashewa da kuka, Abba ya ji kamar ya ?ara rufe Humaira da duka, wannan banzan halin a ina ta Waukoshi? Tabbas ba halin mahaifiyarta ba ce.

"Nima yau zan bar gidanka Isuhu, tun zuwan yarinyarnan naga rashin kunya iri-iri da ban taSa gani a wajen yan uwanta ba. Na yi kokarin janta a jiki da nunamata kauna, sai dai ban sani ba ko tana ji a ranta ni ban kai ta girmamani ba saboda ina zaune ina cin arzikin gidan mahaifinta ba, tunda abin ya kai ga haka in sha Allahu zan tattara na koma can Agadez, kiyi hakuri Humaira, wallahi ni ba muguwa ba ce. Tsakanina da duk abin da ya fito daga jikin Isuhu babu komai sai girmamawa."

Dakyar Abba yake magana saboda Sacin rai ga nauyin Anna da ya dinga ji, wai yau diyar cikinsa ce ke ci wa tsohuwar mutunci ta hanyar dukan Wiyarta a gabanta.

"Ki yi hakuri don Allah Anna, wannan gidana ne ba na Humaira ba. Mallakina ne, kamar yanda uwata mahaifiya da ace tana raye take da iko kai karfi a kaina da gidannan, haka nake ganinki don haka ina ro?onki kiyi hakuri ki janye ?udurinki. In sha Allahu daga yau irin haka ko da wasa ba zai ?ara afkuwa ba. Ni zan Wau mataki kwakkwara a kanta."

Ya ?arashe yana duban Humaira da sai lokacin take sheshshe?ar kuka, itama shi take kallo, ta sunkuyar da kai.

"Don ubanki ba za ki buWi baki ki ba su hakuri ba?!"

Ya faWi a tsawace, hakan ya yiwa ran su Tasleem dadi, yau dai ga wacce suke ganin ta fi su a wurin Abba tana WanWanar kudarta. Abin ya zo musu a daidai. Ita kuwa mikewa ta yi dakyar ta durkusa sosai, hakuri ta shiga ba su har Jannat din. Dakyar suka ce ya wuce saboda ganin idanun Abba.

"Muje." Ba musu ta mike jikinta duk ya yi tsami ta bi bayan Abban zuwa falonsa yanda ya bu?ata.

***
Fadeel da murmushi ya Wagawa yayartasu hannu alamar jinjina. Yayar Ibb, Anti Ru?ayya wacce ke aure a Kano, sun saba sosai da Fadeel din tun kafin ma ta yi aure. Ibb ya dube shi.

"Wai ni ban gane ba, toh idan odar ta sauka wa zai karSa?"

Fadeel ya yi murmushi karo na biyu.

"Nan gidan Antinmu za'a kawo mana, ni kuma sai na zo na karSi rabona."

Hajiya Ru?ayya ta yi dariya.

"Amma dai wannan ina zaton ita ce zaSin ?anin nawa ko?"

Ya kasa magana sai shafar sumar kai, Ibb ya taSe baki.

"Ita ce dai yake yiwa son mutuwa ba ta san da zamansa ba."

Fadeel ya harareshi shi kam dauke kai ya yi ya cigaba da ba Ru?ayya labarin komai. Sosai ta ji ya ba ta tausayi.

"Allah Sarki, yanzu kai zaman jiranta za ka yi kuma?"

"Um." Shi ne kawai abin da yace yana hararar Ibb da ya kasa rufamasa asiri. Ibb shima ya rama sannan ya ce.

"Ai wai haka yake nufi, nidai ban san irin wannan abu ba, ace mutum ya kasa hakura da son wanda ba ka gabansa? Kinsan Allah, mutumin nan akwai mata da yawa da suke kawo mishi hari, na ce ya runtse ido ya zaSa ya darje amma ina. Wai ya hakura da auren har sai Humaira ta yi koda ba shi ta aura ba sannan zai yi nashi."

Rukayya ta yi salati.

"Fadeel kana cikin hayyacinka kuwa? Wannan wane irin so ne?"

Nan da nan fuskarsa ta sauya.

"Nawa son da haka ya zo. A sanya ni a addu'a kawai Anti."

Ta Wan yi jim tana kallonsa. Sai kuma ta numfasa.

"Shikenan, Allah ya zaSa abinda ya fi alheri. Zan so naga wannan yarinyar da ta sace zuciyarka har haka."

Ba musu ya fiddo waya ya buWe hotunan Humaira wanda hatta a saman screen dinsa ita ce ya mi?a mata. Ta kalla sosai ta ce.

"Babu ?arya Humaira kam ta haWu. Daga kuma yanayin fuskarta ka san za ta yi ha?uri."

Yabon da ta yi sai ya karawa Fadeel farin ciki, a duniya ya tsani wanda zai kushe abar sonsa. Ganin har Ru?ayya ta yaba sai hankalinsa ya kwanta. Sun jima suna hirar lamarin Humaira kafin a karshe su yi sallama bayan Fadeel ya ce mata zai dawo idan an kawo odar snacks ya karSa.

***
Jannat ce tsaye tana kallon hanyar waje, har lokacin zafafan hawaye take fitarwa na ba?in cikin abinda Humaira ta aikata gareta. Fuskarta ya yi jazur, ta juyo ta kalli Anna wacce ta yi shiru tana kallonta, a duniya Anna ba ta son damuwar yaranta.

"Anna, na yi al?awari sai na ga bayan Humaira da duk abin da take ta?ama da shi. Ta yimin cin fuskar da ban taSa tsammata ba, ni zan nunamata iyakarta koda kuwa zan yi yawo tsirara."
A firg??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ice Anna ke duban Wiyarta, ta san halin kayanta, muddin ta furta abu, komai nisan lokacin da za a Wauka sai ta aiwatar. Wani lokacin ma, sai ta tabbatar da shafewar abin a kwakwalwarka kwatsam sai dai ka ga sakamako a aikace. Don haka ta sani ko mene Jannat za ta aikata ba ?arami ba ne duba da yanda ta saki fuska lokaci guda har da dariya. A karshe ma hatta da abincin da Humairar ta kawo sai da ta Wiba ta yi zaman ci tana santi. Ita dai Annar ba ta ce mata komai ba, ta fi kowa sanin ba?ar zuciya irin na Wiyarta.
***
Kanta na ?asa, fiye da mintuna uku shi bai ce mata uffan ba kamar yanda ita Win ma ba ta buWi baki ta ce komai ba face kukan da take yi ?asa-?asa. Can dai Abba ya sauke ajiyar zuciya ya soma magana a kausashe.

"Kin bani kunya da mamaki Mamana, ban yi zaton hali na rashin kunya da Wa'a daga gareki ba. Me ya hau kanki har haka? Meke yawo a kwakwalwarki kika aikata abin da yau ace mahaifiyarki na raye za ta yi bakin ciki?"

Humaira ta ji ?arfin kukanta ya ?aru, kewar mahaifiyarta mai yawa ta ji, ta sani ta aikata ba daidai ba amma ba ta jin Mahaifiyarta za ta kasa fahimtarta koda kuwa ace ta nunamata kuskurenta. Ta danne abin da ke taso mata dakyar ta iya magana.

"Nayi laifi Abba, ka yi hakuri ka yafemin."

Ya kuramata idanu duk sai ta ba shi tausayi kuma, sai dai hakan ba zai sa ya fasa nunamata kuskurenta ba.

"Shikenan, amma ki tabbatar kin samu uwarki kin ba ta hakuri. Matar da take ?imanta ki, ai yau ko wani mugun bautar mahaifiyarta da ?ar uwarta ke nunamaki ai sa ci albarkacinta ballantana ma babu Waya. Amma ki rasa da me za ki sakamata sai da cin mutuncin yan uwanta? Wannan ba daidai ba ne Humaira, Maryama ta wuce nan a wajenki idan kina da tunani. Burinta duk a kanki ya ?are, kar ki so ki ji yadda koyaushe ba ta da magana sai naki, kullum cikin yabonki take da burin ki zama hamsha?iyar ?ar kasuwa mai siyar da abinci irin wanda ko Otel sai haka. Ba ina faWamaki ba ne don wani abu? a face sai na son ki fahimci irin girman da ta ba ki. Daidai da batun bikin yarannan idan aka Wauko, sai ta ce ita dai burinta ta ga auren ?an ukunta (Ummita, Raihana da Humaira), su ne ?a?anta. Toh kiyi takatsantsan, ki kuma kara martaba wannan girma da soyayyar da take nunamaki. Na san ke Win mai jin magana ce kuma ba na shakku akan tarbiyyar Dada, sai dai ina ro?onki kar ki sake na ?ara jin makamancin wannan daga gareki. Kin ji ko?"

A sannan kukanta ya tsaya, sai Mami dake yawo a kanta wadda Abban ya kara sa ta ji kaunarta ta cika zuciyarta ga wani irin nauyi da kunya da ta ji. Shakka babu ta kai ma?urar da har ta kasa danne a zuciyarta ta aikata abinda zai sosa ran Mamin da ma Raihana da ?asim wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login