Showing 162001 words to 165000 words out of 189325 words

Chapter 55 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

213

shi ta yi, doguwar riga ce mai hawa biyu kalar maroon. Gefenta wani gashi ne mai laushi. Ta shiga bandaki ta sauya shiga sannan ta fito ta nemi wuri ta kwanta bayan ta kashe fitila. Ba ta fi mintoci da kwanciyar ba ta ji shigowar Fadeel, kirjinta ya hau bugu tara-tara, wai yana nufin anan zai kwana? Shi ne tambayar da ta yiwa kanta, ta runtse idanunta tamau alokacin da ya hau gadon sosai, fitilar ya kunna haske ya karaWe Wakin, da kallo ya bi fuskarta, ya sani ba bacci take yi ba, runtse idanun na dole ne. Ba ta yi aune ba ta ji ya yaye gaba Waya bargon, da sauri ta dora hannuwa saman fuskarta. Ya yi murmushi ya kashe fitilar kafin ya maida bargon ya rufa musu. Janyo ta jikinsa ya yi sosai, ya fidda hannuwanta saman fuskarta, duk kuwa da cewar dakin da duhu ba ganin idanunta zai yi ba.

"Please faWamin koda sau Waya ne naji. Kinji?"

Ya na maganar tamkar mai raWa. Ta yi shiru sai bugun kirjinta da yake ji, yanayin maganarsa sai ya ba ta tausayi, ta tuna dukkan gwagwarmayar da ya sha a kanta. A hankali ta bude baki ta ce.

"Ina matu?ar so da ?aunarka Fadeel."

Ya yi Wif na lokaci ?alilan, ita kuwa ta samu wani irin kuzarin da sai da ta ?ara maimaitawa, kaunar tasa take ji yana fisgarta sosai. Ai ba ta yi aune ba ta ji sauran kalaman bakin nata sun ma?ale adalilin toshe nata bakin da ya yi da gurbin nasa.

Daren dai sun raya shi tamkar ba za su yi bacci ba. Washegari suka tashi zuciyoyinsu cike da walwala da soyayya mai tsafta. Humaira kuwa jikinta ya yi mugun sanyi don tuna ?ar uwarta Ummita. Wannan abun shi Wizzy ya kwatar mata da ?arfin tuwo. Wannan dai ?ancin da Fadeel ke ta cin alwashi da al?awarin kyautata mata saboda shi? Dakyar ta samu lamarin ya fice a ranta sakamakon kulawar da Fadeel ya dinga ba ta tamkar ya haWiye ta. Sun kira waya ta gaisa da Raihana ta kuma tabbatar da samun saukinta, hakanan da su Hajjo suka zo yi mata sallama sun ba ta tabbacin Ummita ta Wan saki ranta har Abba na fadin zai haWa ta da Anti Maijidda su wuce Bichi.

Hakan ya yiwa Humaira dadi kwarai domin ita kanta ba ta kaunar ganin Mami a wannan gaSar, zuciyarta ba ta amince da ita ba kamar a baya.

***
Kafin su Hajjo su kai ga dawowa gidan Mami, sai ga Jannat sun dawo gidan har da Futuha gaba Waya. Sun samu labarin komai dangane da zargin da ake yiwa Mami na satar su Ummita. Futuha da Tasleem waWanda suka san da zancen hankalinsu ya tashi ainun domin sun san komai ba kuma zargi ba ne. Jannat kuwa ashariya ta dinga zundumawa gami da yiwa Mamin Allah ya ?ara.

"Kin fifita su akan yaranki na cikinki ai ga sakamakon abin da kika yi nan kina gani."

Ita dai Mami ba ta ce uffan ba, Tasleem ko da tun a gidan Futuha take fama da lemun tsami a baka saboda tashin zuciya, wani amai ne ya taho mata da ya yi sanadin mi?ewarta a guje ta faWa banWakin Anna. Gaba Waya suka bi ta da kallo. Mami kirjinta ya yi wani irin duka da ?arfi.

"Wannan tashin zuciyar da kike ta yi dama tun a can ai nasan ba a banza ba. Sai ki tattara ki koma gidan Hamza tunda akwai sauran rabo tsakani."

Mami ta juyo a ruWe ta ?ara bin Anna da kallo mai maganar hankalinta kwance. Futuha da Jannat babu wanda ya dara don gaba Wayansu zuciyoyin ba dadi, ga Futuha, ba?a?en maganganun da ake yi mata da habaici a Tiktok ya fi ?arfin kanta. Ga kuma Yakubu da ya Wauki ?ar Snow zuwa Saudiya inda daga nan za su wuce Dubai sai ko London. KuWin da ya bar mata a wannan tafiyar shi ne rabin abin da yake ba ta kyauta a wata, gaba Waya ya rufe bakin aljihunsa sai dan abin da bai taka ya karya ba yake ba ta. Ta kuma fahimci azabar da yake son gana mata muddin ta yi sake za ta dame ta shanye irin kalar na uwargidansa. Jannat ma dai rigima ce ake ta yi da nata mijin, inda mahaifiyarsa da danginsa suka dage akan lallai sai ya rabu da ita ko kuma ya yi aure. Zafi biyu ya haWe mata ga tunanin inda za ta fara samu ta tattaro kan kudadenta da ta yi asararsu.

Mi?ewar Mami ce ya sa duk suka dube ta, kai tsaye banWaki ta je ga Tasleem, suka yi kiciSus sadda take fitowa tana share baki.

"Ke, yaushe rabonki da al'ada?"

Tasleem ta Wan yi shiru, ita dai ta san koda ta dawo daga gidan Hamza tana jego ne ba ta yi wanka ba,? tun da ta yi wankan kuma ba ta ?ara ganin jini ba.

"Ina magana kin mayar da ni sakara! Nace yaushe rabonki da al'ada?!"

A firgice Tasleem ta amsa.

"Tun farkon dawowata da na yi wankan bi?i. Amma Mami ai shayarwa nake yi, shi ne dalilin rashin ganin al'adata."

Mami ta Wan yi jim tana lissafawa, kai ba za ta taSa yarda ba, hankalinta ba zai kwanta ba idan har ba bincikawar ta yi don kanta ba. Wa????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
nnan yasa ta yi kiran ?assim a waya ba shiri ya zo. Su Jannat dai sun yiwa Mami caa wai akan me take zarginta ita dai shiru kawai ta yi. Har ?assim ya shigo ta ba shi kudi ya amso mata Pt-strip ba ta ko sauraron zantukan su, Anna har da su zaginta wai tana zargin Wiyarta da bin maza alhalin tana idda? Ita dai ba ta tanka ba, Tasleem kuwa shiru ta yi ba ta ce uffan ba. Suna nan hira na gudana tsakanin Anna, Jannat da Futuha har ?assim ya kawo aiken. Mami ta karSa ta ce ya fice, da kanta ta titsa ?eyar Tasleem har bandaki. Tasleem a dole ta bi umarnin Mamin don itama tana son tabbatarwa, ana yi kuwa sai ga ran?walelan shaidar positive ya nuna a jiki. Mami ta kusan sakin ihu a bandaki, ciki dai ciki?? Toh uban waye ya yiwa Tasleem din ciki?

A haukace ta ?ara tambayarta cikin fita hayyaci.

"Don ubanki wani abu ya shiga tsakaninki da Babandi ne?"

Ta kasa magana, jikin Tasleem ya hau rawa, dama ta soma zargin cikin ne ashe ko ya tabbata. Wannan ruWewar ta Mami ya sa tsoronta ya daWu. Ita kam ta shiga uku idan ciki ne ya shiga jikinta. Shirunta kuwa ya tabbatarwa Mami cewa eh, wani abu ya gifta tsakaninta da Babandi. Ai sai ta shiga duka Tasleem kamar an aiko ta, Tasleem har ta fito daga bandakin a guje Mamin na biye da ita har cikin Wakin. Tana dukan tana tsinewa Babandi. Sai da su Jannat suka ri?e ta gami da yi mata inkiya kar mutane su dawo su ji.

"Wai waye Babandi? Me kike magana a kai? Ciki kuma?"

Anna ta nemi ba'asi a ruWe. Nan Mami ta kora musu bayanin bokannata da yanda suka yi kaca-kaca akan aikin Humaira da Fadeel da ma yanda ta tura Tasleem wajensa har mai afkuwa ta afku.

"Maryama baki da hankali! Ke mahaukaciya ce ashe ina maki kallon mutum mai hankali? Ta ya ya za ki samu saSani da mutum ki yi mishi zagin uwaka ubaka kuma ki tura Wiyarki wajensa?! Shikenan! Yanzu dai ta tabbata Wan Bokanki ne a cikin ?iyarki."

Wannan kalma ta ?arshe na Anna ya mugun jijjiga zuciyar Mami. Ai sai ta fashe da wani irin kuka, Jannat masoyiya ga Tasleem itama kukan ta sanya gami da zuwa ta Wago Tasleem tana rantsuwar ita dai wallahi sai ta kai ta an zubar da cikin. Nan da nan Tasleem ta ture ta.

"Aa wallahi! Ba wanda ya isa ya zubarmin da ciki, Babandi ya ce idan na tabbatar ciki ne da ni toh yana son abinsa idan na haihu na kai masa!"

Tana maganar kamar ba Tasleem ba cike da faWa idanunta tsaye kai ka ce ba ita ta gama kuka yanzu ba. Gaba daya suka bi ta da kallon mamaki. Kiran da Dawud ke kwalawa Mami iyakar ?arfinsa ya yi sanadin da suka Wunguma cikin tashin hankali zuwa waje. A falo suka yi kiciSus da shi, lokacin su Hajjo sun dawo ba su kai ga shigewa masaukinsu ba. Wasu kuwa sun fice zuwa kasuwa ?arasa siyayya.

"Meyafaru Dawud?" Ta tambaya jikinta a mugun mace. Kan ya kai ga cewa komai sai ga Ridwan cikin kayan aikinsa da abokan aikinnasa su uku, biyu mata sai Waya namiji. Fuskarnan tamkar ba shi ne mai fara'a ranar bikin Fadeel ba. Ya Waure ta tamau, ya fito a jami'in aikin na gaske marar son wasa. Arrest warrant ya buWe ya nunawa Mami.

"Hajiya mun zo tafiya dake bisa zargin da ake yi maki na garkuwa da yaran maigidanki. Hukuma ta bamu damar shigar da ?ara kotu."

Wani razanannen ihu Futuha ta saki tana ?unduma uban ashar wai ?arya ne. Shi kuwa Dawud hawaye kawai yake fitarwa don dama labarin da ya zo kawo wa Mamin kenan. Su Hajjo suka yi cirko-cirko suna kallon ikon Allah har matan nan suka nufi Mami da zummar tisa ?eyarta a tafi.

"Me kuke nufi? Ina ku ke zaton za ku kai ni?! Yanzu a ganinku zan cutar da yaran da nake yiwa so fiye da yara a da na haifa?"

"Hajiya wannan duka shari'a ce za ta bayyana. Yanzu dai ki bamu haWin kai mu yi aikin da ke gabanmu."

Wannan ranar ta zo musu da tashin hankula iri-iri. Futuha ta Wauki waya ta yi kiran Abba, koda ta sanar masa ban da Allah ya kyauta gami da kashe wayar babu abin da ya ce. Nan Futuha ta hau fadin wai dama Abba ba sonsu yake ba, ya fi so ya ga sun watse sun bi duniya! Mami kadai ke son su tsawon shekarun nan komai da take yi don su take yi.

Ganin Futuha na kokarin yin suSul da baka ne ya sanya Mami dakamata wata tsawar.

"Ke! Ya isa hakanan! Nace ki bari haka! Ai ?arya fure take ba ta ?a?a. Idan ma an yi hakan don a Satawa uwarku suna ki kwantar da hankalinki babu inda ?arya za ta je. Duk inda za su kai ni zan fito."

Abin da Mamin ta ce kenan sannan ta yi gaba ma'aikatan suka mara mata baya. Ridwan sai da ya tsaya ya Wan waiga, rashin ganin Ummita a wurin sai ya ji hakan bai masa dadi ba. Kawai sai ya sa kai ya fice.

Nan fa yaran Mami kamar su yi hauka. Suka kira Mubarak suka labarta masa, hankalinsa ya tashi. Ya kira Abba, Abba ya kwantar da hankalinsa ya ce ya yi hakuri ya nutsu tunda satika ya rage ya kammala ya dawo, ya bari zai kula da komai.

***
Kamar da wasa sai ga Mami har tsawon sati a hannu hukuma, babu duka balle zagi, ta kafe akan ita ba ta san Wizzy ba kuma ba ta san ma a inda ya santa ba. Wizzy ma an tambaye shi yace shi bai taSa ganin wacce suke waya ba, amma ya ri?e muryar. Ya kuma sani matar uban su Humairar ce.

Sai da Mami ta cika sati aka shiga kotu, duka wannan Abba yana asibiti adalilin ciwonsa da ya tashi. Raihana ko ta dawo gida amma Abba ya bata umarnin tattarawa ta koma gidan Baba Amina don ta ?arasa jarrabawarta. Ummita kuwa tana Bichi amma sanadin shari'ar sai da ta dawo.

Ita da Humaira aka nemi su bada bayanin komai da ya faru da su, haka kowaccensu ta yi magana zuciyoyin cike da rauni babu kamar Ummita dake ?ara jin tsanar Sadik Wizzy? da su Baaba wadanda duk aka titso ?eyarsu ta hanyar Wizzy din, kowannensu ya amsa eh ya aikata laifin idan ka cire Mami da ta dage akan ita sharri da ?age akai mata. Lauyar da Hajiya Lubna ta Waukar mata ta tsaya tsayin daka wurin yi mata wannan ya?in. Aka yankewa su Wizzy hukunci daidai da laifukansu yayin da kotu ta wanke Mami daga zargi bisa duba da rashin hujja koda ?waya Waya da za'a kama ta dominsa.

***
Ta dawo gidanta hankali kwance, yaranta gaba daya su na cike da farin cikin kuSutar mahaifiyarsu da kuma wanke ta da kotu ta yi idan ka cire Raihana da ba ta gidan kuma ko labarin ma ba ta kaunar ta ji. Ummita da Humaira kuwa har abada ba su jin? za su ?ara aminta da Mami. Ballantana kuma Abba da yake ji a jikinsa lallai da saka hannunta. Ya kuma kara yarda da kalar zalunci na matar da yake aure.

Ta iske Abban a falonsa zaune yana kallon labarai, ga dukkan alamu hankalinsa ma ba ya kan talabijin din, ya zurfafa cikin tunani. Gaba daya ya rame kamar wanda ya yi cutar watanni. Ita kanta Mami ta rame saboda tashin hankulan da ta gani a wannan ?an watannin. Zama ta yi gefensa. Ya ji zuwannata amma bai ko kalle ta ba. Kafin ta kai ga magana ya riga ta cikin sha?a??iyar murya.

"Maryam, zaman me Jannat take yi a gidana?"

Ta yi turus, ta yi zaton zai ce wani abu a kanta amma sai ta ji ba ma ta itan yake ba. Cikin ?ar borin kunya ta ce.

"Ina za ta iya tafiya gidanta alhalin yar uwarta na gar?ame a wajen jami'an tsaro? Adalilina ne ya sanya ta ke zaune."

Ya mi?e zaune sosai daga kishingiWar da ya yi.

"Ta tattara ta bar min gidana, ba na bu?atar ganinta. Abin nufi, koda wasa kada ta ?ara gangancin takowa cikin gidannan! Gida dai nawa ne, ni ke da iko da shi! Toh daga yau ba na bu?atar ta ?ara zuwa."

Sulhu take nema, tana so ta shawo kansa don ta san meke tafe a ransa a kanta don haka sai ta yi saurin amsawa.

"An gama Abban yara. Zan sanar da ita ba za ta ?ara takowa ba."

Bai ce uffan ba ya na ta tufka da warwara har sai da ya ji ta kwantar da kai saman kafaWarsa.

"Abban yara kana kaunata, naji ance har kwanciya asibiti ka yi sadda aka tafi da ni. Nayi mamakin wannan ?azafin da wannan ba?in azzalumin ya so ya yimin, ya kusa raba ni da rigar mutuncina."

Abba ya yi wani murmushi mai ciwo.

"Kika ce rigar mutunci Maryama? Ina rigar mutuncin naki yake? Ai a yanzun ma da nake tare da ke, DARAJA ?AYA kawai kike ci. Ban da wannan kusan zan iya cewa babu komai da ya rage a tsakanina da ke."

Yana kai wa nan ya zame kanta daga kafaWarsa, ta yi wani irin zama tana kallonsa satoto.

"Bangane nufinka ba? Daraja Waya kamar ya? Igiyar auren fa?"

Ta yi tambayar zuciyarta na duka da karfi, kallonsa take yi kawai tana lissafo ire-iren tashin hankulan da ta jefa kanta ciki duk a sanadiyyarsa da yaranta. Toh me Yusuf ke shirin ce mata?
Abba ya yi Wan murmushin takaici.

"Aure? Ai ba ki Wauke ni miji ba. Nima rashin sani ne ya kai ni ga Waukar mace irinki a matsayin matar aure, uwa ga yarana. A iyakar zaman da nayi da ke, ki faWamin abu guda da na tauye maki na ha??o?inki dake rataye a wuyana Maryama. Abin da ban taSa zato ba, ashe wayona da hankalina bai min rana ba tunda har na rayu da mace irinki mai fuska biyu har na tsawon shekarunnan ba tare da na ankara ba. Kura da fatar akuya, kin cutar da ni kin cutar da ahalina. Na ri?e ki da zuciya daya, na kula da ke da kuma naki. Wannan wane kalar sakayya kika yimin? Ni dai Yusuf kika so a kashe? Kika gurSata rayuwar yarana? Da me na rage ki? Wace bu?atar ce da ta zame min wajibi ba na kokari wajen sauke shi?"

Mami sauraronsa take yi amma fa gaba Waya ya gama kashe mata dukkan wani kuzari. Kirjinta ya hau bugu fat! fat! Wato ta tabbata dai Abba da kansa ya sani ta yi yun?urin kashe shi da Humaira? Ashe dama kurum ya yi yake bin ta da kallon shashasha? Dama rigar mutuncinta ya jima da kecewa a idanunsa? Wani gumi ya shiga tsirfo mata, tana sauraronsa amma ba ta iya fadin ko harafin A ba har ya kammala ya mike ya fice zuwa Waki ya bar ta da nanata zantukan ?arshe da ya yi.

"Ki nesanta kanki daga zuwa Wakina Maryama. Ki zauna a naki Wakin har zuwa sadda mai yiwuwa ko zaman ya ?are ko wani abun daban saSanin tunaninmu ni da ke."

Mikewa tsaye ta yi gwuiwoyinta a sake, ashe dai har yanzu akwai sauran rina a kaba, a tunaninta ta gama rufe bakin tsanyar tunda har shari'a ta wanke ta ba tare da kawo hujja ko daya zai nuna akwai sa hannunta ba. Lallai kafin Abba ya ankare da abubuwan da ta shuka na baya, ya kamata ta san mafitarta. Da wannan ta mi?e ta koma Wakinta.

***
Kwanaki uku, abu dai kamar wasa ta ga dagaske ne, tsakaninta da Abba sai idan ta gaida shi ya amsa, babu sakin fuska balle har ta samu damar wata maganar. Zai shirya ya yi ficewarsa ko abincinta ba ya saurara. Jannat kuwa ta tattara nata ya nata ta bar gidan. Anna abin ya taSa ranta ta kuma rantse sai ta yiwa Abba magana akai. Mami dai ta hana ta amma ina! A rana ta huWu ne da tafiyar Jannat, ta tsaya a hanyar da ta san cewa dole ta nan din yake zuwa ya fice. Yana fitowa kuwa ya gan ta. ?an dur?usawa yanda ya saba ya gaishe ta a mutunce. Ta amsa tana cin magani gami da gyara tsayuwa sakamakon ?afa da ta matsa mata.

"Isuhu, na yi shiru ne saboda ban sani ba ko Maryama za ta iya kokarinta wajen ganin ta sa ka janye dokar da ka kafawa Auta na zuwa gidannan sai na ga hakan ya faskara. Wannan ne ya sanya ni zuwa da kaina domin na ji ba'asi. Haba Isuhu, duk wani abu da yarinyar nan ta aikata sharrin shaiWan ne, ta ba da ha?uri ta kuma nemi gafarar yarannan (acewar Annar kenan), toh na mene ne za ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login