Showing 51001 words to 54000 words out of 189325 words

Chapter 18 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

253

da ta sanya mishi."

"Um um Raihana, kada fa ta ji babu dadi."

Raihana ta Wan harareta.

"To ke za ki faWamata?"

TaSe baki Ummita ta yi gami da neman wuri ta zauna.

"Me ya yimin zafi? Ke ce dai abin ji tunda bakinki ba ya shiru."

Raihana dai ba ta ?ara tankawa ba, sai da ta tabbatar ta kwafi lambar Fadeel ta yi mishi sallama ta whatsapp gami da gabatar da kanta sannan ta mike ta maida wayar inda ta Waukota, baiwar Allah ba ta san ma meke faruwa a duniyar ba tsabar gajiya da baccin da ke kanta.

***
Mintuna kusan sha biyar da shigowarsu gidan daga masallaci, Fadeel wanda ya sha gayu da babbar riga fara ?al mai kwalliyar ba?i, ya shige sashinsa ya bar Alhaji anan falon saukar ba?i tare da makwafta an kai musu abinci iri-iri. A duniya idan akwai abin da ke damunsa to fa babbar riga, ya matsu ya cireta. Hakan yasa tun kan ya ?arasa Wakin ya cire hularsa ya ri?e a hannu, yana shiga kuwa ya fidda ya Wora saman kujera. Zama ya yi sannan ya fiddo waya ya hau kan whatsapp. Anan ya tadda missedcalls din ?anwarsa Hannatu, ya danna mata videocall kamar jira take ta Waga. Sun jima su na hira har ya gaisa da mijinta da kuma Wanta ?arami kafin daga bisani su yi sallama. Sauka ya ?ara yi ya kira wayar kakansa wanda ya haifi Mamansa, nan ma ya gaisa sosai da ?an Kamaru har da wasu cikin ?an uwansa. Bai ajiye wayar ba sai da ya kira Mahaifin Ibb da suke kira Daddy ya yi mishi barka da sallah ya ci sa'a su na tare da Maama, itama sun gaisa ya kuma jaddada musu zai shigo zuwa anjima ganin Maama na faWin ba ta karSar mi?e ya zo har gida.
? Koda ya ajiye wayar sai ya ji wata irin nutsuwa ta ziyarce shi, wato dai babu abin da ya kai zumunci daWi. Wayar ya ?ara janyowa, a hankali yake sarrafata har ya kai kan lambar da babu ranar da ba ya buWowa. Kewar muryarta ya ke sosai, kullum cikin sauraron phone record dinsu yake amma ba su ?osar da shi ba. So yake ya ji muryarta a zahiri, da kuma yana da dama ace ya ganta.

"Why all this?" Ya furta a sanyaye yana kallon lambarta kamar wanda yake jiran jin amsa daga garesu. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, damuwar da yake kwana da tashi cikinsa ita ce ta ke kokarin mamayeshi, idanunsa suka kaWa. Kalmar kora da halin da Ibb yake faWi ba ya so ya kasance gaskiya. Sai dai kuma ya sani, gaskiyar kenan, mai Waci. Amma ya zai yi? Ya kasa raba zuciyarsa da Humaira. Ya kuma kasa yi mata gangancin tura magabatansa kai tsaye wajen nata, ba ya son ta kalleshi a mugu mai son kai. Yana da ya?ini irin su Humaira idan suka faWa tarkon so su ne masu ri?on al?awari, zai wahala su Sata ran masoyi da gangan.

Idanunsa ya sauka saman alamar faWowar sa?onnin whatsapp da ke nuni ta saman screen din.

"Raihana ce ?anwar Humaira."

Wannan sa?on shi ya Wauki hankalinsa daga ba?uwar lamba. Cikin sauri ya buWo whatsapp din ya shiga. Aikuwa idanunsa suka yi kyakkyawan gani saman hotunan abar kaunarsa. Ya rasa me zai yi don farin ciki da kuma dadi, ya ja filo ya yi jifa da shi ya mike tsaye ya shafi sumar kansa yana bin hotunan da kallo yana murmushi. Wannan zinariyar kuma lu'u-lu'u a cikin mata ita Ibb ke cewa ya rabu da ita? Inaa! Ba mai yiwuwa ba ne, sai ko idan ?addararsa ce ta zo a haka. Ya kasa hakuri kawai ya dannawa Raihana kira.

***
A lokacin tana tare da su Futuha a Wakin Anna, ita kuwa Mami tana falo amsar gaisuwar ?an barka da sallah yaran makwafta sai wasu a cikin ?an uwan Abba da suka zo. Mikewa Raihana ta yi da sauri ganin sunan FH a saman screen Winta, ta san Fadeel ne. ?ar barandar dake a wajen ta nufa ta tsaya gami da yin sallama. Ya amsa mata suka kara gaisawa kafin ya Wora da fadin.

"Kin bani kyakkyawan goron sallah ?anwata, na kuma ji daWi sosai. Ki turon acc no dinki nima na ba ki naki goron."

Ta yi ?ar dariya.

"Aa Yaya Fadeel, ni wallahi don Allah na maka. Ba abinda ni da Ummita ba mu sani ba game da sharuWWan da Humaira ta gindaya maka. Ni kuma sai na ga wannan hanyar ce kawai zan yi na ragemaka damuwa."

Ya ji dadi kwarai, ya kuma tabbatar da cewa iyalan gidan abar sonsa su na da kirki kamar ita. Bai yi zaSen tumun dare ba.

"Nagode sosai ?anwata, ki gaidamin Ummita. And please ki turo idan kin bani matsayi Waya da Humaira."

Ta amsa da toh sannan ta yi godiya. Koda ta tura ta yi mamakin ganin dubu ashirin matsayin barka da sallah, ya aiko da text ya ce su sha sweet. Ta kuwa hau washe baki da murna har su Futuha da Anti Jannat na neman ba'asi, sai kawai ta mike ta bar su tana dariyar jin su na cewa wai alert ta ji daga saurayinta. A dakinsu ta iske Ummita, karasawa ta yi a hankali ta ja hannunta gudun kar su tashi Humaira, Mami ta ce a rabu da ita ta huta. Sai da suka fito Ummita ta tambayeta.

"Ke wai mene ne?"

Ta nuna mata kuWin da Fadeel ya turomata, Ummita ido waje don ba ta ma fahimci sunan ba ta dube ta.

"Wa ya aikomaki wadannan kudaden?"

Ta yi mata alama da yatsu cewa ta yi a hankali. Nan ta nunamata hotunan da ta aikawa Fadeel da kuma yanda suka yi a waya. Ummita duk sai ya ba ta tausayi.

"Allah Sarki Fadeel, nikam yana burgeni wallahi. Humaira ta tsinci dami a akala take wasa da shi."

Raihana ta yi ?wafa.

"Rabu da ita, in sha Allahu ba ta da miji sai shi. Itama ai tana sonsa gulma ce kawai."

Girgiza kai Ummita ta yi.

"Bari faWin haka, kar ki manta jinnu babu abinda ba su sanyawa, Ya Sayyadi ya ce har raba mata da miji su na yi saboda sanyawa Waya ?iyayya da kuma hana zaman lafiya."

"Allah ya karemu da sharrinsu. Itama Allah ya yi mata magani."

Ummita ta amsa da amin.

***
Hajiya Kubra wacce suke kira da Maama, mahaifiya ga Ibrahim (Ibb) ta dubi Fadeel tana mai faWaWa murmushinta har ana ganin ha?orin makkanta mai she?i.

"?an Alhajinsa, ganinka sai an yanki tikiti."

Fadeel ya shafi ?eyarsa yana murmushin jin nauyi, yau gaba Wayansa cikin nishaWi ya ke ji, babu hoton dake yawo a kansa sai hoton Humaira da ya gani tana murmushin da wushiyarta ta bayyana zahiri.

"Ina nan Maama, ai ko ba ku yanka ba ni fa Wanku ne."

Ta yi dariya aka ?ara gaisawa. Suka Wam taSa hira bayan an kawo mishi ruwa da lemu sai snacks ya ci. Ibb ba ya nan sun Wan fita da Daddy. Maama ta gyara zama sosai babu alamun wasa a fuskarta ta ce.

"?ana kamar yanda ka ce ni uwa ce gareka, ina son ba ka wata shawara kar kuma ka ce na maku katsalandan kai da abokinka."

Duk da cewa tuni ya Wago zancen, tunda ai tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ?o?i sai ya tattaro dukkan hankali gareta ya ajiye kofin dake hannunsa.

"Maama kin isa da mu Win ne, uwa kuma da ta isa, ai Wa ba ya taSa wuce faWa daga gareta ba ballantana kuma nasiha ko shawara."

Maama ta yi murmushi, hakika kalamansa sun burgeta. Ta jinjina kai.

"Wannan hakayake Fadeel, maganar ba wata mai tsawo ba ce sai ta buri da mafarkan iyayenku. Mun yi hakuri mun zuba idanu, daga kai har Wan uwanka kamar babu niyyar faranta mana. Kun fi kowa sanin bamu da burin sai na ganin kun fidda matar aure amma shiru kamar maye ya ci shirwa. Ba mata a garin ne?"

Ta ?arashe da ?ar dariya, shi ma murmushin ya yi mai dauke da damuwa.

"Akwai Maama, ku yi hakuri, in sha Allah zamu yi. A taya mu neman zaSin Allah. Mun fi kaunar farin cikinku sama da komai."

"Shikenan, Allah ya yi maku zaSi mafi alheri da albarka."

Ya amsa da amin. Yana shirin tafiya sai ga Ibb ya shigo tare da Daddy. Shi ma fararen kayan ya sanya irin na amininsa. Nan kuma hira ta dawo sabuwa, Daddy ya hada su ya kara yi musu zancen aure. Ya jima a gidan kafin ya fito tafiya. Sai da suka karasa har bakin motarsa sannan Ibb ya dube shi.
"Wai lafiya? Yau kamar wanda aka yi ma albishir da aljanna sai fara'a kake yi. Akwai labari ne?"

Fadeel ya ?ara fadada murmushinsa. Hotunan Humaira ya nunamasa, da mamaki Ibb ya dube shi murna fal ciki.

"Dagaske ne abin da nake gani? Ita da kanta ta turomaka? Ah lallai dole ka yi fara'a, ka ce tsayuwar darenka a azumi Allah ya karSa."

Fadeel ya Wan basar ta hanyar sosa kara hanci.

"No ba ita ce ta aikon ba, Raihana ce ?anwarta."

Nan fa Ibb murna ta koma ciki, ya ja guntun tsaki.

"Allah ya yayemaka wannan makahon son Fadeel. Ka ture batun wannan yarinyar ka nemi matar aure ta gaske please. Ni dai dab nake da kawowa su Daddy matar aure."

Fadeel ya bude mota yana murmushi yana kallom hanya har wasu ?anmatan da suka zo giftawa suka maida mishi martani don a zatonsu da su yake. Ya kauda kai.

"Shikenan, ka ga na huta sai ka yi auren ka samar mana yara da wuri, su Alhaji idan su na ganin jikokinsu hankalinsu zai kwanta ni kuma na cigaba da jiran abar ?aunata."

Ibb ya harareshi.

"?an iska, sai aka ce maka daga auren sai haihuwa ko?"

Fadeel dai dariya ya yi.

"Toh me ya yi saura idan har ba juya ba ne kai?"

Shima Ibb dariyar ya yi. Anan yake faWawa Fadeel wata ce Salma, likita ce kwararriya ta mata. Sun jima su na abotar da ta juye ta rikiWe zuwa soyayya a yanzun. Ya yi shiru ne don ya gani ko abin zai Waure.

"Masha Allah, Allah ya tabbatar mana da alheri." Cewar Fadeel.

"Ameen, kai ma Allah ya kawomaka mace tagari da za ta mantar da kai Humaira."

Ya yi murmushi ba tare da ya amsa ba ya shige mota abinsa. Ibb ya matsa shi kuma ya ja ya tafi. A ransa ya na auna addu'ar Ibb din, ba kuma ya jin mai tabbatuwa ce.

***
Murja ce zaune gaban Malam wanda tun a waya ta zayyane mishi komai, batun Fadeel da kuma Humaira wacce ta ke bu?atar a shiga tsakaninsu a raba su gaba daya, ya kasance son da yake yiwa Humaira kacokam ya dawo kanta. Malamin bayan ya kammala aikin da duk abin da ya kamata ya mata umarnin ta zo. Tun da ta zauna take cike da fargaba na tunanin me zai fito a bakinsa, malamin yayarsu ce tana yawan zuwa karSomata sa?o wurinsa, ba ta taSa zuwa don aikin kanta ba sai a yanzun da soyayyar Fadeel ke neman haukata ta.

"Akwai hatsari a kanki babba idan kika ce za ki raba waWannan mutanen."

Ji ta yi cikinta ya kaWa, ranta idan ya yi dubu ya Saci har wani duhu take gani ya mamaye idanunta.

"Akwai hatsari fa ka ce? Toh wallahi na shirya tunkararsa nidai, zan aikata ko mene ne duk tsananinsa don Fadeel ya zama mallakina."
Ya yi shiru yana dubanta gami da auna irin rashin hankalinta kafin ya jinjina kai.
"Aa Murjanatu, kar ki zo gaba kiyi kuka da ni, jimawar da muka yi da da yar uwarki da irin alherin da nake samu a wajenta, ba zan yi abin da zai cutar da ke ba. Ki je nan da kwanaki uku ki kara nazari, idan kin shirya fuskantar kowane ?alubale da zai biyo bayan aikin, sai ki dawo."

Murja ta yi jim, a yanda ta ke jin Fadeel gani take babu wani abu da ba za ta iya jurewa ba. Can ta nisa ta ce.

"Malam, idan har dai ba hauka ba ne ko wata nakasa naji na gani zan jure."

Ya yi wani murmushi.

"Kina da gaggawa Murjanatu, eh ba nakasa ba ne, amma rushe maganar wannan yarinya a zuciyar Fadeel ba zai amfaneki da komai ba sai halaka. Abin nufi, har abada kema ba lallai ki aureshi ba, idan kuwa aurenku ya tabbata toh fa har ki mutu ba zai kusanceki ba. Ke za ki kasance kare ma ya fiki daraja a rayuwarsa. Ki yi hakuri, ita gaskiya Waci gareta kuma kin fi kowa sanin ni Malam Tanimu ba na Soyewa mutum koda kuwa idan ya aikata abun zai haWu da mummunan bala'i sai na sanarmaka idan ka ji ka gani a tafi a haka, sai a tafi. Kin yarda kin amince?"

Ta ji zufa na karyomata, ita da take burin rayuwa mai kyau da inganci da shi? Take burin ta mallake shi su ji dadin tarayyar aure? Kai sam ba ta yi imani da faWar Malamin nan ba duk kuwa da sanin da ta yi mishi ba na yau ba don haka kawai sai ta ce ya ba ta lokacin shawara, daga haka ta mi?e ta bar wajensa da nufin sauya she?a. Wannan Malamin ba abokin tafiya ba ne, ba zai mata yanda take so ba.

***
Sun yi yawo sosai gidan ?an uwan Abba, wannan kam ita da Ummita ne sai ko Raihana da ta jera da su. Si Futuha kuwa daga gidajen ?awaye sai ko ?an makarantarsu na sakandire da suka haWa reunion aka ci aka sha. Sun je hawan sallah Humaira ta sha kallo, abin ya yi matukar burgeta. Ta dauki hotuna sosai a wayanta, ita kuwa Raihana babu kwalliyar Humairar da ba ta Waukarwa Fadeel ba, daidai da bidiyonta a wurin kallon hawa sadda take murmushi da haska bidiyon sarki ta Wauka ta tura wa Fadeel. Sosai sallar ta yi mata dadi, ta kuma yaba da kalar wasannin da aka yi.

***

Zaune take a falo tana ta kallon yanda a hankali ta soma samun mabiya a shafin Instagram, hakanan hatta a facebook da Raihana ta budemata ta sanya ta a shafukan tallace-tallace na sana'o'i nan ma ta samu abokantaka da mutane da dama, sai dai babu wanda suka taSa hira a akwatin sirri (inbox). Ita kaWai tana ta murmushi ganin yanda hotunan girke-girken da ta yi yake samun likes da kuma comment. Jannat ta shigo falon da rawar jikinta, dawowarta kenan daga gyaran gashi. Su Futuha sun fice shoprite sun kai yara, Ummita ta je albarkacin yaran Jannat da suka sa rigimar su sai an tafi da ita don ba karamin sha?uwa suka yi ba.
Humaira ta Wago tana dubanta don har ta tsorata ta, sam ba ta tunanin ta yi sallama. Su na cikin sati na uku ga sallah, a yanda ta ji daga Ummita, bai fi kwanaki uku ya rage Jannat ta bar gidan ba wannan yasa take ta shirye-shirye. Kallo Waya Jannat din ta yi mata ba ta ko amsa sannu da zuwan da take mata ba ta yi gaba, har ta Wan yi nisa ta dawo baya tana yatsine fuska.

"Ke, ki dafamin abu marar nauyi yanzu."

Humaira ta amsa da toh, daga haka ta watsa mata harara ta shige. TaSe baki Humaira ta yi, ko kaWan ta daina jin ciwon ?iyayyar da suke mata, ta lura ba ?asa suka kwasa ba. Jinin Anna ne dole su kwatanta halinta. Ban da ma rashin ta ido, ina uwar mace da zuwa gidan surukai ta tare ko tuna asalinta ba ta yi? Mami ce dai ta sha bamban da su.

Tana wannan sa?e-sa?en zucin wayarta ta Wauki ?ara. Ganin ba?uwar lamba ya sanya ta yin jim tana tunani, tana da tabbacin ba shi ba ne. Mutumin da gaba Waya ya sauya bai ko ?ara kiranta ba, ganin wayar na shirin katsewa ya sa ta Wauka. Muryar mace ce, ta amsa sallamarta suka gaisa.

"Ina magana da Humaira? Humaira Yusuf mai yin snacks?"

Ai sai ta mi?e tsaye ta hau washe ha?ora. Ta amsa cikin za?uwa.

"Eh, ita ce."

"Masha Allahu, ina bibiyarki a shafinki na instagram, na ga tallace-tallacenki. Ina son snacks ne, za'a iya samu nan da kwanaki hudu haka zuwa biyar?"

Humaira ta Wan yi tsallen murna sai ta Wan toshe baki gudun kar dariyar farin ciki ya suSuce mata, wannan kusan shi ne order din farko tun da suka soma talla. Nan ta tambayeta kalolin snacks din da take so, ta yi mata bayani, a karshe suka yi sallama da zummar Humaira ta lissafa adadin kuWinta sannan ta turo acc number. Ai don murna tuni ta mance da batun wata Jannat, gudu-gudu ta nufi falon Mami tana kwala mata kira. Amma ina! Ba ta nan tana bangaren Anna, tsabar rufewar idanu kawai sai ta sa kai har cikin dakin Anna tana kwala kiran Mami. Su na zaune su na hira sai ganinta suka yi. Mamin ta nemi ba'asi nan ta hau sanar da ita yanda suka yi da mai order. Itama sai murna da hamdala.

"Kai Alhamdulillah. Dole kiyi murna, maza muje ayi lissafin sai a turamata."

Da murmushinta mai bayyana kyawunta da tsantsar kamanninta da Abba ta amsa da toh. Har ta juya za ta fice ta ji tsawar Anna.

"Ke!"

A firgice ta juyo kuwa, har ga Allah sai a sannan idanunta suka buWe. Ta tuna inda ta faWo da kuma kuskuren da ta yi na rashin sallama ballantana gaisuwa. Kawai sai ta durkushe ta gaida Annar, Jannat ta karasa ta ja kunnenta har sai da ta saki ?ara.

"Don ubanki dayake kin raina mutane uwarmu sa'arki ce da har ki faWo Wakinta kamar na uwarki?! Ba aiki na sanyaki a kicin ba? Kema kuma Mami laifinki ne."

Daga nan ta juya harshe zuwa buzanci ta cigaba da sababin faWa, Anna itama tana taya ta. Daga yanda Mami ta yi shiru ta haWe girar sama da ta ?asa Humaira ta fahimci magana suke gasamata. Nan da nan jikinta ya yi sanyi, a gefe guda ga na gorin Wakin uwa da aka yi mata, ba don darajar Mami dake a idanunta ba sai ta faWamusu mai zafin da ba zasu ?ara mararin daWa kwana ko Waya a gidan ba idan har su na da sauran kunya.

"Humaira, tashi ki je, ki yi aikin da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login