Showing 87001 words to 90000 words out of 189325 words

Chapter 30 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

215

kamar kirjinsa zai fashe haka yake ji, nan take idanunsa suka kaWa jawur. Gaba Waya ta lalace ta yi rama tamkar wata halittar ce ba ita ba sai ko hancinta da ya ?ara fitowa. Har aka shige da su bai iya kauda kansa ba. Shi ya yi ?arfin halin biyan dukkan abin da aka kashe har da na kama Waki.

? Cikin ?an?anin lokaci labarin kuftowar su Humaira ya cika gari, mutane da waWanda suke dangi da ma yan uwa na gari suka dinga tururuwar zuwa yi wa su Abba barka, babu wanda aka bari shiga wajensu, hakanan labarin abin da ya afku gare su bai fita ba. Yan jarida kuwa suka dinga yaWa rahoto, hakanan social media ta dauka.? Futuha mutanen Dubai ta ?ara yin bidiyo mai nuni da damuwa da kuma farin ciki tana shaida wa jama'a cewa an ga ?annenta. Nan aka hau taya ta murna sosai.
Mutanen Bichi da labari ya iske su su ma baa bar su a baya ba. Anti Maijidda ta yi kuka kamar ranta zai fita jin labarin keta haddin da aka yi ga Ummita, matsayinta na babbar yaya ga uwarta ya sa Abba sanar da ita a sirrance.

? Sahabi kuwa baki har kunne, sun zo shi da abokansa yayinda mahaifinsa takanas ya zo ya taya Abba murna da addu'ar Allah ya kiyaye gaba.

? Kwanakin su Humaira biyu suka dawo hayyacinsu. Ummita ce ta soma farfaWowa, ranar Allah ya ta?aita Anti Maijidda na zaune tare da Baba Amina sun yi jugum su na dan hira jefi-jefi hannuwansu ri?e da casbaha. Wani gigitaccen ?ara Ummita ta saki da ya yi masifar tayar da hankulansu.

"Wayyo Allahna! Kar ka kashe ni! Ka rabu da ni! Na haWa ka da Allah ka rabu da ni!! Wayyo Allahna!!!"

Cikin kuka da tashin hankali suka yi kanta su na ri?ewa, aka bankaWo ?ofar aka shigo, su Abba ne da? ihun Ummita ya iske su. Raihana a guje ta nufi wurin Nurses dake tahowa, kafin ta kai ga magana suka ce sun ji. An tafi kiran likitan. Su na shiga sai ga Likita, aka fitar da kowa a Wakin.

Gaba Waya matan kuka sosai babu kamar Raihana da take jin kamar ta shiWe. A yadda take jin zuciyarta za ta iya fille kan wanda ya aikata wa yan uwarta wannan tozarcin.

Koda likitan ya ?arasa gareta flask din ruwan zafin dake ajiye a gefenta kawai ta Wauka ta jefa masa. Ba don Allah ya sa shi kaucewa ba da babu abin da zai hana a same shi.

Tana cikin wannan gigitar Humaira ta farka a matukar firgice, ta kira sunan Ummita da karfi sannan a guje ta diro ta zo ta rungumeta tana kallon jama'ar Wakin kamar wasu sabbin halittun da ba ta taSa gani ba.

"Su waye ku? Me za ku yi mana?! Ku fice ku bar nan! Wallahi ku ka yi ?o?arin zuwa kusa da mu zan ji maku ciwo."

Sai kuma ta juya a mugun firgice tana tattaSa jikin Ummita dake kuka kamar ranta zai fita.

"Ummita! Yi shiru, Abba zai zo. Naji suna cewa yana hanya. Yi shiru, sai mun kashe su."

"Kin.."

Likitan ya ?araso zai soma magana Humaira ta juya da azama tana nunashi da yatsa. A sannan su Abba gaba daya sun shigo sun kasa daurewa.

"Kar ka taSamin ?ar uwa! Zan kashe ka!!"

"Humaira, Ummita."

Humaira na ganin Abba ba ta ko damu da sauran jama'ar Abba ta karasa a guje ta rungume Abba tana kuka mai tsuma zuciya.

"Abba za su kashe mu! Abba ka cece mu! Ka Wauke mu mu bar nan!"

Irin ri?on da ta yiwa Abban ba na wasa ba ne har maSallan wuyar rigarsa sai da suka fita.

Cikin hawaye ya ce.

"Mamana babu abinda za su yi maku, likitoci ne. Kun kuSuta daga hannun azzalumai. Ki kalla dakyau, ga Maminki ga yar uwarki Raihana. Kin gane Kawunki?"

Ta tsaya cak kamar wata sokuwa tana kallonsu Waya bayan Waya, Ummita kuwa da nos ta lallaSa ta yi mata allura tuni bacci ya kwasheta. Kawai sai ta soma ruwan wasu sabbin hawayen ta ma kasa cewa uffan. Zuciyarta ta gas?ata eh sun kuSuta daga hannun azzaluman, amma kuma ta ji tana tantama tana gani ko mafarki ne. Wannan ya sa Raihana tahowa da sauri ta rungumeta ta kara sautin kukanta.
A hankali ta Waga hannunta ta Waga fuskar Raihana ta na kallo kamar wata ba?uwar halitta ce gabanta, sai kuma da rawar murya ta ce.

"Raihana ce?"

Raihana saboda ?arfin kukan ma ta kasa magana sai kawai ta Wagamata kai. Humaira ta rungumeta sosai suna kukan tare.

"Amm, don Allah a ragu a Wakinnan. Alhaji ina son magana da kai."

Fadin Likita, ganin haka duk aka fice banda Raihana wacce Humaira ta ri?e hannunta gam tamkar ita kaWai ta gani.

***
Likita ya dubi Abba cikin nutsuwa ya soma magana.

"Lamarin ita Ummita na bu?atar rarrashi da ja a jiki. Kaso casa'in na ire-irenta da hakan ke afkuwa a kansu sukan samu matsala ta rudani, firgici da kuma rashin yarda ga kowa. Wasu kuma yakan taSa musu kwakwalwa. Zamu yi mata gwajin kwakwalwa don a tabbatar da komai na ta lafiya kalau yake."

Abba ya share fuskarsa.

"Toh Likita, nidai babban burina lafiyarsu. Allah ya sa komai lafiya."

"Ameen." Ya ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?amsa cikin tausayawa yana mai lallaSar Abba.

***
Cikin iko na Ubangiji an yiwa Ummita gwajin kwakwalwa kuma an tabbatar da komai lafiya. Wannan ya kwantar da hankulansu. Humaira dai ba ta dogon magana tun farkawarta, kowa ta gani sai dai ta ambaci sunansa, idan an rungumeta an sa kuka itama ta soma. Da daddare ba bacci sai razana, ga Ummita haka. Wannan yasa aka raba musu Waki. Fadeel na zuwa, kuma abin mamaki Humaira na ganinsa ta kira sunansa, abin sosai ya ji dadinsa ya kuma tsaya a ransa.

Sai da suka kwashe sati biyu a asibiti kafin su tattara su dawo gida. Babu laifi sosai zuwa lokacin sun samu nutsuwa ba kamar farko ba. Sai dai daga Ummitan har Humaira duk sadda tunanin cin zarafin da aka yi musu da kuma keta haddin da aka yiwa Ummitan sai su yi ta kuka. Har zuwa lokacin babu wanda ya san da mummunan labarin sai ko Anti Maijidda da Mami wadanda Abban ya faWawa.

Anti Maijidda nan fa ta dage akan lallai sai a ba ta Ummita su tafi Bichi, Abba ya ?i amincewa. A dole ta ha?ura ta tafi tana ?unar rai da jin tsanar Mami har cikin ?o?on ranta.
Jannat ko a fuska sai ka rantse nan jimamin duniya take yi akan lamarin don ba ta nuna komai wanda zai sa wanda bai sani ba ya fahimci takun sa?arta da su. Hakanan Anna wacce ta daurewa zuciyarta ta taka har Wakinsu ta duba lafiyarsu bayan ta je asibitin a baya har sau uku. Wannan ya wanke ta daga zargin mutane da rashin nuna kauna ga su Humaira a baya.
***
Sai da su Humaira suka samu sati hudu cif kafin su Wan maido da jikinsu, da kuma walwala kaWan. Sukan zauna cikin jama'a, a taSa hira da su idan ka cire Ummita da har lokacin ta tuno aika-aikar da aka yi mata sai kawai ta fashe da kuka wanda hakan ke tayarwa Humaira hankali itama ta sa nata kukan sai su haWu su yi ta yi. Kawun Humaira ya so su koma can Nijar da ita amma nan ma Abba ya nuna sam bai amince ba dole haka ya tattara matarsa suka koma gida.

? Su na zaune a Waki, Ummita ri?e da Al?ur'ani tana karantawa zuciyarta na yin sanyi yayinda Humaira ke kwance saman katifa ta yi shiru gami da zubamata idanu kusan ma hankalinta ba a kanta yake ba, ta lula wata duniya ta daban na tunani. Raihana ta shigo ta iske su haka, dawowarta kenan daga makarantar boko wanda har lokacin Ummita ta ?i amincewa ta koma ganin haka babu wanda ya takura mata shi ma mai makarantarsu da ya zo har gida ya jajanta ya ce a kyale ta zuwa wani lokacin.

"Wash! Wallahi na gaji! Ke kuma kina da ba?o a falon Abba."

Ta faWi da murmushi tana duban Humaira duk a ?okarinta na son ta ga komai ya dawo daidai a mu'amalarsu. Humaira ta Wan dube ta gami da Wan haWe gira kaWan.

"Wa kenan?"

"Fadeel."

Ta yi shiru, ita ba ta ce uffan ba balle ta yi wani yun?urin kawai sai ta maida kai ta kwanta ta yi shiru. A karan kanta ba za ta ce ga abin da take ji game da Fadeel din ba, lamarin dai ba yabo balle kuma fallasa. Ummita na ji ba ta iya cewa?komai ba, Raihanar ma ba ta sake magana ba sai ta mi?e ta rage kayan jikinta ta shiga wanka, ba ta son duk abin da zai takurawa rayuwar ?an uwannata da ta ?ara sanin girman ?auna da sha?uwar da ke tsakaninta da su bayan sun yi mata nisan da ta zaci har abada ba za ta ?ara sanya su cikin kwayar idanunta ba.
? Ummita tana kai wa ?arshen surar da take karantawa ta juya ta dubi Humaira.

?? "Ki je ku gaisa mana."

Humaira ta yi mamakin jin wannan furucin naga bakin Ummita, tun bayan dawowarsu ba ta wani magana kwakkwara, ko hirar Raihana ke jansu da shi, sai dai ta basar ta yi shiru. Wannan murmushin da ba ya barin fuskar Ummita, babu shi babu labarinsa tun dawowarsu. Ita Winma ?arfin hali take yi don faranta ran Mami da su Raihana ga kuma ?asim waWanda gaba Waya suke nuna musu kulawa da ?o?arin ganin sun saki jikinsu.

"Kin ji?"

Maganar Ummitan ya ?ara katse mata? tunani. Tana so ta ja musu amma a yanzun duk duniya babu abin da ta ke so irin ta ga ?ar uwarta ta dawo tamkar yadda ta ke rayuwa a baya. Abu na? biyu kuma ta sani ba ta jin za ta iya Waukar waya ta kira shi da zummar godiya bisa hidimar da ya yi akan fitowarsu, don ko cikon da suka bayar na kuSutar da su a hannun ?an fansa ?in karSa suka yi da Abban ya maida musu, ta sani wannan ita ce damar ta amma hakanan ba ta son Fadeel din ya cigaba da shigemata shiyasa.

Abban har gidansu ya je ya ?ara godiya sosai shi da Mami wacce a sannan ne ta ga gidan da ya kere na Aminiyarta Hajiya Lubna.

Ganin Ummitan ta zubamata idanu ya sanya ta mi?ewa.

"Toh, na ji Ummita."

Ta faWi kamar ta fashe da kuka sai ta mi?e ta Wora hijabi akan doguwar rigar atamfar da ke jikinta.

Suka ci karo da Mami a falon wannan ya sanya ta tsayawa.
Gidan yanzu duk an watse sai su kadai, Jannat ta tattara ta koma bayan dogon kiran da mijin ya dinga danno mata har abin ya kusan zame musu rikici sannan ta tafi ba don ta so ba. Tasleem kuwa tun fitowarsu da kwana biyu Hamza ya zo suka koma gida.
?
? Cikin sakin fuska Mami ta dubi Humaira.

"Ina zuwa haka?"

Ta sunkuyar da kai sannan ta ce.

"Wai Fadeel ne ya zo za mu gaisa."

Nan da nan fara'ar dake saman fuskar Mamin ya ragu.

"Zuwan me yake ta yi haka ne alhalin jinyar ta ?are? Ina ce na muku iyaka da shi tun a baya?"

Humaira ta jinjina kai.

"Hakane Mami, kiyi hakuri. Ai gaisawa kawai zamu yi. Ya yi abin da ko ma?iyina ne ya cancanci na ?ara yi mishi godiya."

Mami ba ?aramin mamakin furucin Humairar ta yi ba wanda daidai da fuskarta ta nuna. Sai kuma ta jinjina kai.

"Shikenan, ki je amma kar ki Wau lokaci."

Murmushi kaWan Humaira ta yi sannan ta amsa da toh ta cigaba da tafiya. Ban da abin Mami, ita ba ta tunanin ma za ta yi auren, wane namijin ne zai aure ta bayan ta gama wula?anta duk masu kaunarta domin Allahn? Ta rasa dalilin da a ?an kwanakin nan take jin sauyi a jiki da kuma kwakwalwarta. Wannan ne ya sa Fadeel samun rangwame daga wurinta.

?angaren Mami kuwa ji ta yi kirjinta ya yi wani irin bugu. Meke shirin faruwa haka? A duniya ba ta kaunar Fadeel ya raSi Humaira kamar yanda bai raSi Tasleem ba. Kai ba ma shi ba... Sai kuma tunaninta ya katse, ta haWiyi miyau da ta ji yana mata zafi. Sai kawai ta nufi Wakinta a gaggauce. Tabbas ta yi sake a kwanakin da suka shuWe ba ta bayar an Woramata sabon aiki ba.? Wayarta ta fiddo ta shiga zarya a tsakar Wakin tana jira a Wauka daga Waya Sangaren. Doguwar magana suka yi sai kuma ta hau murmushi hankali a kwance ta katse kiran ta shiga danna wayar karo na biyu inda ta tura kuWi ga wani akawun lamba. Daga nan kuma ta ji wata irin nutsuwa ya saukar mata.

***
? Ya kwashi mintoci? masu yawa a zaune anan, shigowar su Waleed ne ma ya Wauki hankalinsa suke hirar makaranta yana biyemusu. Ya gama fidda rai daga ganinta, gefe guda ga tsoron kada a koma ?ar gidan jiya, tunanin da ya sanya gumi tsastsafo masa a goshi duk kuwa da iskar dake kaWawa a falon har tana kaWa labule. Sai dai kuma ba zato ya tsinci sallamarta, cikin sauri ya kalli hanyar yana mai amsawa da rawar murya.
??
'Please Fadeel, Control.' Zuciyarsa ta ba shi shawara, ya sauke nannauyan ajiyar zuciya. Ya zubamata idanu, ta? fara dawowa ainahin Humairarsa, fuskar ta Wan ciko ba kamar farkon dawowarsu ba. Hakanan ta yi haske fayau dama can a bayan har da rashin samun wanka ga uban cizon sauron da tabonsa ya yi ja a jiki da fuskarta.

? Ita kuwa kanta a ?asa ta ?arasa ta zauna Wan nesa da shi, tana ji ya kaWa su Waleed ciki akan su je su cire uniform dinsu.

"Barka da rana."

Ya yi furucin yana dubanta tamkar ya haWiye ta. Sai a sannn ta Wan Waga kai ta dube shi. Ganin yanda ya zubamata idanunsa ya sanya ta maida kanta ?asa ta na jin wani yaam a jikin da ba ta saba ba a baya.

"Ina wuni, ya wajen su Baba?"

Fadeel da ke jin kamar an tsoma shi a aljanna ya faWaWa murmushin fuskarsa yana hamdala a ?asan ransa. Dama komai Wan hakuri ne, idan ka yi to fa zai wuce. Ya shanye wulakancin da zagin, yanzu ga shi nan ya soma cin galaba.

"Kowa lafiya kalau Alhamdulillah, Sisterna ma ta zo daga Adamawa. In sha Allah zuwa gobe za ta zo ku gaisa."

Sai ba ta watsa masa ?asa a ido ba ta amsa da toh. Shiru ya biyo baya, a Sangaren Fadeel ba ya so ya faWi abin da bai yi daidai da ra'ayinta ba ta sauya fuska ta mi?e ta bar shi anan, ita kuwa godiya take son yi mishi don su yi sallama ta koma ciki amma ta rasa ma ta inda za ta fara sai can da ta ga ba shi da niyyar ce mata uffan sai aikin kallon da ba za ta ce yana ba ta haushi ko kuma faranta mata ba a lokacin, ta daure ta soma magana.

"Mun gode bisa dukkan Wawainiyar da ku ka yi mana, Allah ya ?ara arziki."

"Ban yi abin da za ki godemin ba. Ke kika yi wanda zan godemaki. Nagode sosai and I..."

Sai kuma ya yi saurin haWiye zancensa, ya san komai na tarihin Humaira a sannan daga bakin Raihana, ya san ba ta jin turanci amma kuma dai kalmar I Love You ko yaro ?arami da bai je makaranta ba ya sani. Shirun da ya yi ganin zai yi taSargaza ne, gaba Waya ji yake da ace Humaira za ta ba shi dama, zancen aurensu kawai za a yi. Ya sani hatta da Abbanta ya bu?aci a ba shi lokaci kaWan yaransa su dawo cikin nutsuwa sai a haWa auren Ummita da na su, shi ne a karon kansa ya ro?i alfarma a kyale Humaira ta amince da batun aurensa da kanta. Yana kuma ji a jikinsa hakan ce za ta kasance daga yanayin sauyin da ya gani tattare da ita.

"Shikenan?"

Ta katse mishi tunani, ya Wan lumshe idanu sannan ya buWe su a cikin nata, ta kauda fuska ta yi shiru.

"Toh, zan koma bakin aiki, dama zuwa nayi na duba lafiyarku. Ki gaishemin da Ummita da mutan gidan. Allah ya ?ara lafiya."

Ta amsa da amin, cikin sanyin muryar ta ce.

"Zan fadamusu. Nima ka gaidamin ?ar uwarmu, sai ta zo goben in sha Allahu."

Ambaton ?anwarsa Hannatu da ?ar uwarmu da ta yi ya sanya shi jin tamkar yana tafiya a iska tsabar mamaki da farin ciki. Ya ji dadin wannan lamarin sosai.

"Nagode."

Hakan ya furta kawai sannan suka mi?e kusan lokaci guda, sai da ya ga shigewarta sannan shima ya juya yana murmushin da har ha?oransa suka bayyana, ga duk wanda ya ga fuskarsa ya san yana cikin farin ciki da annashuwa.

***
Washegari Mami ta tashi da aikin girki na tarbar Futuha wacce ta yi waya ta sanarmata dawowarsu a ranar. Daga Dubai sai da suka je Saudia suka yi Umarah kafin su juyo. Humaira ba ta yi ?asa a gwuiwa ba wajen shiga kicin Win din taimaka mata da aiki, zaman kaWaicin babu abin da yake jefa ta ciki sai kogin tunani. Ummita ma ta fito falo kasancewar akwai wuta ta kunna tashar Saudia tana kallo.
Gaba Waya samarin gidan sun dawo, Mubarak da ya kammala shima yana gida hakanan Yassar da Dawud wadanda sun fi sati da dawowa daga Camp suna nan tare da su. Anan Kano aka yi posting Winsu inda zasu yi service.
Daga Humairar har Ummita ba su ?ara samun matsala da su Yassar ba, musamman Humaira wacce a baya suke ?i sosai, ita hakan ma har mamaki yake ba ta. Tsakaninsu gaisuwar mutunci, wasu lokutan har su Wan tsoma ta a ciki idan suna ?ar hira. Har a lokacin ba ta saki jikinta da su ba don ba ta saba da hakan ba.

Suna girkin Ladidi na taya ta murnar yanda ta soma sakin jikinta tamkar a baya. Raihana ta shigo kicin din kamar an jefo ta har Mami na mata faWa.

"Ku yi hakuri. Humaira, Yaya Fadeel

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login