Showing 153001 words to 156000 words out of 189325 words

Chapter 52 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

204

kara shinshinarta sosai, Tasleem ji ta yi kamar ta saki fitsari a wando.

"Me ya yi maki?"

Ta tambaya cikin tsananin ruWani.? Girgiza kai Tasleem ta yi. Ta tuna gargaWin Babandi cewa muddin ta sake bakinta ya furta abin da ya faru ga kowa wane ne toh ta sa a ranta aikin ya lalace har abada kuma ba za ta samu koda rabin mutum? irin Fadeel ba balle a kai ga shi da kansa. Wannan ya sanya ta samarwa kanta nutsuwar dole ta fisge hannun Mami daga jikinta.

"Mami mene haka wai? Me kike tunanin ya yimin? Babu fa abinda ya yimin, kawai dai ya ban wasu turaruka na shafa ya ce na zauna ya dinga yimin wasu karatuka bayan ya kammala kuma ya ce naje na jira zan soma ganin sakamako. Gobe ma yace na koma zai ban wani garin magani da zan barbaWa a makwancin Humaira."

Ajiyar zuciya mai karfi Mami ta yi har da kama jikin madubi. Sai bayan tafiyar Tasleem ta dinga tunanin anya ba ta aikata kuskure da ta tura ta wajensa ba musamman da ta tuno yanda suka kwashe. Ta kira wayar Tasleem din ya fi a ?irga amma ba ta ko Waga ba hakanan na Babandi ma sai a ce mata a kashe. Tana niyyar zuwa da zummar kai mata yarinyarta dake faman kuka sai ga Tasleem din ta shigo gidan.

"Shikenan, ki wuce ki je kin bar yarinya tana ta kuka."

Itama ajiyar zuciyar ta sauke ganin Mamin ta yarda da zantukanta na bogi. Har ta kai ?ofa Mamin ta dakatar da ita hakan yasa ta waigo.

"Ki kula sosai da duk wani abu da Babandi zai sanya ki yi, idan har kanki ya ?ulle a kai ki sanar da ni kafin ki aikata."

Gyadamata kai kawai ta yi kafin ta juya ta nufi dakin Anna don gaba daya ma ta tattara kayanta daga ainahin dakinsu, ba za ta juri ganin wannan rawar ?afar da ake yi akan auren Humaira da Fadeel ba.

***
?angaren Humaira ba ta da ko Wigon damuwa game da komai. Idan ka ga yanda ta yi kyau za ka rantse ba ta taSa sanin wata aba wai wahalar rayuwa ba. Ummita ita kanta ta bar damuwa da yanayin kaddararta, gaba daya ma babu mai yi mata tuni a kai, yanda ?an uwan Humaira ke haba-haba da ita da nunawa Ahmad kauna sai ta ?ara sakewa da su. A yanzu babu abin da ke damunta dangane da abin da ya faru da ita na baya sai ko yanzun da Ridwan ke neman takurawa rayuwarta da kira da ?ara fallasa mata zahirin zuciyarsa. Ga kuma Mubarak a gefe wanda ya ce babu gudu ba ja da baya don ya samu labarin Ridwan daga bakin ?an uwansa. Ita kam gaba dayansu babu wanda ta ke jin ma kaunarsa a ranta sai tausayi da suke ba ta ganin su matasa su na neman daukarwa kansu abin da bai dace da rayukansu ba. A cewarta.

Safiyar ranar Juma'a su na zaune a daki, Humaira sai yatsine fuska take tana kallon kwanon da Baba Amina ta dire a gabanta na kazar da aka dafa da sinadaran gyaran mata.

"Ki kalla dakyau Humaira, hakanan za ki ci shi ko bakya so."

Fadin Baba Amina kenan, yanmatan dake dakin aka kwashe da dariya har Ummita da Raihana wacce ta saki ranta saboda murna da farin cikin ganin auren Fadeel da Humaira na niyyar tabbatuwa, abin da ta jima tana son gani.

"Nikam Baba idan ta ?i ci a mi?omin yanzun nan na tashi da shi."

Cewar Raihana tana ?ar dariya.

"Aa Raihana, wannan kam na matan aure ne. Ki jira zai zo kanki ke da Ummita nan ba da jimawa ba kuwa sai mu gani ko cika baki ne ko kuwa dagasken za ki iya ci."

Aka yi dariya, Ummita ko murmusawa ta yi, ita ba ta fiye son ana sanya ta a layin waWanda za'a aurar ba.

"Allah kuwa Baba cikina ya cika, dazunnan fa na gama shan wani..."

"Toh marar sirri, a gaban ?an uwan naki za ki tona abinda aka baki?"

Hajjo ta katse zancen Humaira, anan kuma sai Baba Amina duk ta sa aka fice a dakin aka bar Humairar sai ko Ummita da Hajjo.

"Kinga Humaira, wadannan abubuwan da nake sanyaki sha da ci, suna daga cikin abin da za su ?ara siyamaki daraja a wurin mijinki. Ba ki da wanda ya wuce mu da zamu tsaya don ganin rayuwar aurenki ta inganta da taimakon Allah. Abu kuma na gaba da nake son faWamaki, bai wuce akan Maminki ba. Kar ki ga don ta sauko kamar ta sauya fuska ta shiga cikin sha'anin bikinnan na jiya ki yi zaton babu sauran SurSushin hassada da bakin ciki a ?asan ranta. Ta riga ta fiddomaki da kuma mu da zahirin wace ce ita wannan kadai ya isa ki kula koda bayan aurenki ki yi kokari kada ki bada wata ?ofar da za'a ji kanki keda mijinki. Ki godewa Allah, samun miji irin Fadeel a zamanin nan sai a tona. Mutumin da tun kina gwada masa tsana da kyara yake bibiyarki da nuna maki kauna ta gaskiya, wallahi Humaira koda wasa kika cutar da shi a zamantakewarku sai Allah ya yi masa sakayya. Kar ki yi amfani da wannan dumbin kaunar da yake gwadamaki wanda hatta a dangin Mahaifinki akwai wadanda suke nuna adawarsu da shi ki yi tunanin cutar da rayuwarsa. Ki yiwa kanki karatun ta nutsu, ki yi hakurin zama da mijinki kar ki yaWa matsalar da za ki fuskanta da shi ga kowa ba ma fatan matsalar ake maki ba, amma ki kula ki san me kike yi."

Haka Baba Amina ta yi ta yi mata maganganu masu ratsa zuciya har sai da jikinta ya yi sanyi. A karshe ta soma cin kazar su na zolayarta. Hajjo ta mike ta fice zuwa wurin yan uwansu da suke Wakin ba?i. Itama Baba Amina ta fita wannan ya ba Raihana damar dawowa ta zauna gefen Humaira tana yamutsa fuska.

"Wai kun ji labarin an yiwa Sis Futuha kishiya kuwa?"

Dagaske ba su da wannan labarin, Humaira dai ta ganta tana kuka ranar da Fadeel ya zo amma ba ta samu damar cewa uffan ba saboda umarnin da Mami ta ba ta a lokacin.

"Kai Raihana, dagaske kike?" Fadin Ummita.

TaSe baki ta yi.

"Allah ko dagaske, ?ar Snow mijinta ya aura."

"?ar Snow fa kike ce?!"

Fadin Ummita idanunta waje. Humaira ko sai da ta Wan yi jim don ta na tunani kamar ta san sunan kamar kuma ba ta sani ba. Can ta tuna wace ce, wacce dai ta yiwa Futuhar mummunan ?azafin da ya yi sanadin aurenta da Yakubu ba Ibb da take mutuwar so ba.

"Ita dai, yau ma za ta tare kuma a gidan da Futuha ta fito. An mata gyara sosai. Hum, ta tashi hankalinta ita kuma, dazu har rotse ta yi mishi a goshi dakyar ya kwaci kansa ya bar gidanta. Abba ma ya je ya yi mata kaca-kaca da barazanar saSa mata muddin ta ?ara gangancin kashe rai. Ba don Abban da abokin Yakubun ba ai da tuni itama ta dawo gida zawarci."

Raihana ta karashe zuciyarta a karye har kwalla sai da ta cika idanunta. Rashin sa'ar ?an uwa mata da ma rashin sa'ar uwa ta gari yana mata zafi a ranta. Me suka Wauki duniya ne haka? Kowanne cikinsu dogon buri ya ke ci mata kai ka ce shi ke da alhakin ?ayyadewa kansa lokacin da zai mutu. Futuha a zahiri ta nuna kwadayin abin hannun Yakubu, yau gashinan ya nuna mata halin maza ire-irensa. Tasleem ko ba ta ma san a layin da za ta jera ta ba.

"Allah ya kyauta. Ya tsare. Amma ta bani tausayi gaskiya. Ai ko ni duk hakurin ba na jin zan iya zama da wacce ta yimin ?azafi ba a rayuwa."

Fadin Ummita kenan da ya katse tunanin Raihana.

"Amma a ganinki tun farko laifin waye? Laifinta ne da ta zaSi duniyar Tiktok akan zahirinta, Allah dai ya tsare."

Suka amsa da amin.

***
Misalin karfe biyar na yamma aka shirya Humaira cikin wani arnen leshi mai daukar idanu kalar yellow ochre, ta yi wani irin kyau da ta fito tamkar a matar wani hamsha?in. Ummita kanta ta ci ado sosai cikin wani leshi golden da suka yi ankonsa da Raihana. Su biyu kacal suka yi shi, Ahmad kuwa Hajjo ta karSe ta ce wajenta zai zauna ita ce mai rainonsa. Duk kuwa ta yi hakan ne don kar ya hana Ummita sakewa a wurin biki, tana fatan itama Allah ya fiddo mata da miji ta yi aure.

Gidan gaba daya aka fice har Mami wacce Hajiya Lubna ta yi ta yiwa famfon kar ta bari a kwace mata ragamar gida. Wato ta zuba idanu Baba Amina ta yi mulki a gidan mijinta alhalin ita ya dace komai ya Sulla ta hannunta. Anti Laila kuwa ?anwa ga Hajiya Lubna, wato matar da ta koyawa Humaira girke-girke. Takanas ta zo har da ?atuwar ledarta na taya murnar aure da ta tahowa da Humairar. Ita kam da zuciya Waya ta ke sonta. Ta kuma iso da ?aramin akwati mai dauke da agogo mai dankaren kyau daga Kabir dan Hajiya Lubna ya ce a ba Humaira. Humaira duka ta amsa ta dam?awa Raihana. Ita ko ta je ga Baba Amina dake zaune ta nunamata. Mami na kallon wannan diramar, haushin Raihana tamkar ya kashe ta, wato ba ta ma dauketa komai ba don tun zuwansu wurin yinin komai aka bada na Humairar wajen Baba Amina take kai shi. Ko inda Mamin take ba ta kalla, Mamin dai ta haWe itama cikin wata shaddarta sabuwa da ta sa aka yi aikinta daga can Mali amma ba ta taSa sanya ta ba sai a yau ta yi mata rana.

"Hajiya Maryam wallahi sai mun tashi tsaye, nikam ina tsoron kar wannan abu ya tabbata. Kiga yarinya duk ta fi yaranki more aure? Duba kiga yan uwan mijinta babu na raini a cikinsu. Suturarsu masu tsada ne na ?arshe ina faWamaki."

Hajiya Lubna ke wannan bayanin tana karewa su Anti Amarya da su Hannatu ?anwar Fadeel kallo. Mami ta cika ta yi fam, ta ji kwallar ba?in ciki sun cika idanunta.

"Bar ni haka Hajiya Lubna, wallahi kuka nake son fashewa da shi. Wannan ranar ba?a ce a gareni kuma ba don kin matsa akan zuwan ba da babu inda zan tako don ban ga wani abu cikinsa bayan ba?in ciki ba. Yarana su na can cike da tashin hankali, amma wadannan hotihon banzan ba su kishin yan uwansu sam, ji yanda ita waccan ke zirga-zirga ke kya ce bikin kanin ubanta ake yi, ji don Allah yanda wancan soloSiyon ya wage baki yana zubawa Humaira kudi."

Ta karashe tana duban Yassar da ya ke ti?ar rawa yana yi wa Humaira karin kudi da take tsaye a fili.

"Sai hakuri, farin cikinnan zamu san yanda zamu yi daga baya ya koma ba?in ciki."

Kallo bai tashi komawa sama ba, sai da aka yi kiran uwar Amarya ta fito, Mami da Baba Amina suka fita a lokaci guda. Wannan abu ya yiwa Mamin ciwo amma hakanan ta danne ta dinga zuba murmushin da bai je zuci ba. Humaira kuwa har hawaye ne suka zubomata, babu wanda ya fado a ranta sai Dada da mahaifiyarta. Baba Amina ta dan ja ta a jiki ta a goge mata fuskar da handkerchief sai hoto da li?in ya koma kansu wannan ne dalilin barin Mami hall din gaba daya don hatta da MC din idan ya ambaci sunanta sai ya ambaci na Baba Amina.

Raihana ta fito don kai wa wasu ?awayensu na makaranta kati dake waje, ta ji wayar Ummita dake jakarta na ?ara. Kafin ta ciro ya zama missedcall, ta ga ba ma kira daya ba ne, kira ne wurin goma sha wani abu daga Mubarak, Ridwan da kuma wata lambar da ta dauki hankalinta matu?a kuma ta girgizata. Tana nan tsaye bayan ta ba da katin sun shige ta rasa abin yi sai kakkarwar hannu da jiki, wayar ta ?ara ringing. Lambar ce dai dagaske, lambar da ta gani a wayar Mamin har ta tura wa Abba. Ta yi saurin Wagawa kirjinta na harbawa. Kafin ta yi magana ya riga ta.

"Blackbeauty, ina fatan kin dauki muryata? I am the Wizzy the father of Ahmad."

Ai ba ta san lokacin da ta dur?ushe a cikin fararen duwatsun dake wurin ba, Wizzy da ya yiwa Ummita fyaWe? Shi ne Wizzy da Mami ke waya da shi? Ta kara fiddo wayar a kunne ta duba dakyau, tabbas lambar ce ba ?arya ba ne. Ta katse kiran ta ciro wayarta tuni hawaye sun gama wanke fuskarta ga wayar har tana faWuwa a kan duwatsun ta buWe ta fiddo lambar Wizzy dake wayarta, ta ?ura idanu tabbas ita ce dai lambar.

Mami wacce ke tsaye tare da Hajiya Lubna su na jiran direban Hajiya Lubnan da aka nema aka rasa ya kaWa yawo, ta hango Raihana cikin halin ruWani. Ta dubi Hajiya Lubna.

"Raihana kuma? Meyafaru da ita?"
Hajiya Lubna ita dinma sai lokacin ta ankara da ita, cikin sauri suka hau tafiya zuwa inda take.
Kafin Raihana ta kai ga daukar kowane mataki, wayar Ummita dake hannunta ya ?ara ringing, Mami daidai lokacin suka karaso ita kuma ta Waga wayar tana fadin.

"Waye Wizzy? Mene dalilinka na kiran Ummita?"

Kirjin Mami ya bada dam, suka dubi juna da Hajiya Lubna cikin tsananin kiWima. Wizzy kuma? Kiran Ummita? Ai sai kafafun Mami suka hau rawa, dakyar ta karasa ta zagaya gaban Raihana, ita kuwa Raihana ganin Mami ya sanya ta ?ara nanata tambayar da ta yiwa Wizzy don ta ga yanayin da za ta shiga. Ai kuwa zaro idanu ta yi waje, hannu ta kai ta fisgi wayar.

"Bani mu ji waye?"

Haka kawai ta fadi ta sa wayar a kunne ta dan yi gaba acewarta wai ?arar sautin da aka sanya a cikin hall ya sa ba ta jin abin da yake fadi. Hajiya Lubna cike da dabara ta ri?e hannun Raihana.

"Ki kwantar da hankalinki, ko waye za mu sani. Me ya ce maki ne naga duk kin shiga ruWani har da su kuka?"

Raihana ta bi matar da kallon munafuka mai ?ara tunzura uwarta. Ai dama sai hali ya zo Waya ake ?awance. Ta sani sarai don kada ta bi bayan Mamin ne ya sa ta ke siyasance ta. Sai ta kauda kai ba tare da ta ce mata uffan ba. Hankalinta na kan Mamin da ta ba su baya ta kuma yi can nesa da su.

Mami kuwa ta saurari kalaman dake fitowa a bakin Wizzy.

"Ke wace ce? Ki ba wayar ga mai wayar uwa ga yarona ita nake son magana da ita kar ki bari na wulakanta rayuwarki kema."

"Wizzy." Ya ji muryar Mamin cikin kunnuwansa, sai kuma ya kyakyace da dariya.

"Oh, ki ce wayar fasin fasin ake da ita, daga hannun wannan sai na waccan, Hajjaju kenan. Kin yi mamakin jin na kira lambar Uwar yarona ko? Ki. Yi zaton zan zuba idanu na biyewa shirme da shiriritarki? Kin kasa cika umarnina ma fiddo Nusy har jami'ai sun fara farauta ta saboda ta ba da kwatancen inda nake, ta ci amanata. Yanzu haka na yi nesa da Kano da ma duk inda aka san za a gan ni na koma ainahin ?auyenmu. Toh ki sani, a duk radda na tashi dawowa zan yi zuwan a mutu ko a rayu, ba Ahmad kadai ba har uwar Ahmad zan dauke ke kuma haWuwarmu dama na faWamaki ai ba za ta yi kyau ba. Ki shirya tonan asirikanki."

Gumi ya shiga tsirfowa Mami, ta dan juya ta dubi? su Raihana, ta kuwa kuramata idanu babu ko kiftawa. Ta kauda kai ta ce.

"Shikenan, ka yiwa Allah kar ka kara kiran wayar Ummita. Zan maka yanda kake so kafin a kammala bikin auren nan."

Ta dinga magiya har sai da ya ce ya ji. Da haka suka yi sallama ta goge lambar bayan ta yi blocking dinta. Kasancewar wayar Ummita babu wani lock da ta sanya hakan ne ya ba ta damar yin yanda ta so kafin kuma ta koma ta ba Raihana wayar. Har lokacin kallonta kawai take yi hawaye na zuba a saman kuncinta. Wai wannan matar da Allah bai raga da komai na kyawun fuska ba sai ko munanan Wabi'unta ita din mahaifiya ce gareta babu yanda kuma za ta yi ta sauyawa tuwo suna.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Raihana kin ji masifar dake shirin tunkaro mu? Wai uban Ahmad ne yake son karSar Wansa? Lallai ki kiyaye furta wannan zancen ga Ummita, mun samu ta dawo cikin nutsuwarta yanzu, idan wannan magana ta fito bamu san halin da za ta shiga ba kuma."

Mami duk ke wannan zantukan har da fidda hawaye itama ta a share su. Hajiya Lubna? ko sai ?ara jinjinawa irin salon kisisinar Mami take. Gaba Waya ta rikiWe zuwa ta Allah, wanda bai santa ba ma zai ce har zuciyarta dagaske ta ke. Raihana ta kauda kai tayi murmushi mai ciwo lokaci guda tana sa yatsunta ta share fuskarta. Allah ya taimaka ba ta yi kwalliyar hodar foundation ba, babu kuma irin nacin da Ummita ba ta yi mata akan ta yi din ba ta ce ba ta ra'ayi hakan ya ba su mamaki kwarai game da ita don ta fi su ma son kwalliyar sosai.

"Shikenan, ba zan fadamata ba. Ni bari na koma ciki kar a neme ni."

Daga haka ta juya ta bar su a tsaye, suka bita da ido.

"Hajiya Maryam, jikina yana bani akwai wani abu da diyarki ke Soyewa."

Cewar Hajiya Lubna. Mami ta girgiza kai tana wani murmushi.

"Ko kusa Lubna, ban gan shi ba. Na san Raihana sarai, da ace akwai abu a ranta ba za ta iya yin shiru ba. Haka take, ba ta Soyon abin da ke ranta."

Hajiya Lubna dai ta ji ta amma ba ta yi na'am ba. Daga nan suka rankaya zuwa wurin motar inda direban tuni ya dawo yana jiransu. Hakuri ya dinga bayarwa da Hajiya Lubna ke mishi fada kafin su shiga ta ba shi umarnin ya jira a waje sai ta mishi iznin shiga motar. Dole haka ya bi umarninta ya samu can gefe ya tsaya yana kallon masu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login