Showing 156001 words to 159000 words out of 189325 words

Chapter 53 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

224

shige da fice ?an biki. Sai lokacin Mami ta labarta mata yanda suka yi da Wizzy, ta kara da fadin.

"Na riga na yanke zan sa Bala (wanda ya haWa ta da Wizzy tun farko) ya yi amfani da damarsa wayar yaron nan ta shiga hannunsa ya kai wurin masana kwamfuta a yi resetting ta dawo kamar sabuwa. Wannan damar zai sa ya rasa komai da muka yi tsakaninmu. Kinga koda asirinshi ya tonu wanda nake ji a jikina zai tonun tunda dai an kama budurwarsa an kuma fara harinsa, babu wata shaidar da zai nuna gaban kotu da za'a ce har da ni a ciki. Abin godiyar ma, bai taSa yin ido hudu da ni ba ballantana ya ce ya san ni. Nima a bangarena zan fidda komai nasa daga wayata."

Murmushi sosai Hajiya Lubna ke yi.

"Tabbas wannan babbar dabara ce. Nima dai akan ta wa matsalar na auren da Honarabul ke shirin Waukowa na waccan shuwa arab din dole na je na ga Babandi. A baya ya yi aikin kamar za a fasa amma kinga ashe magana tana nan kuma yan banzan danginsa sun nuna goyon bayansu. Kinsan duk yanda ka kai ga kyautatawa dangin miji tsinannu sai sun ga aibunka. Koda dai bana tsinana musu hatta uwarsa bai isa ya yi mata ba sai da iznina. Watakila wannan ?arfin da ya bani na iko a gidansa da kuma kaunar da ya nunamin ce ta yi sanadiyyar da suke nunamin hassada da bakin cikinsu."

Fuska Mami ta yamutse.

"Hum, ba ki ga waccan balbelar ba?"

"Wa kenan?"

"Wace ban da yar iskar bazawarar can Maijidda? Nifa ko zan yi yawo tsirara ba zan aminta da aurenta da mijina ba."

Dariya Hajiya Lubna ta yi.

"Kai kai kai Maryam, yanzu ke da bakinki kin ce Babandi bai tabbatar maki da aure tsakaninsu ba. Toh na meye za ki yi wannan irin yanke hukuncin da gaggawa haka?"

Girgiza kai Mami ta yi.

"Uhm uhm Hajiya Lubna. Babandi shegen kansa ne. Ni jikina yana bani zai wahala idan ba dangantaka ta auren yake nufi ba. Sai yanzu ma nake ganin wautarmu na tsayawa kan mutum daya don yi mana aiki. Yanzu gashinan abubuwa ba sa tafiya yanda muke so, ya kamata dai ki lalubo mana wani gwarzo kuma babban malamin da ya shahara da zai iya yi mana aiki."

"Nima nayi wannan tunanin Hajiya Maryam, lallai mu tsaya mu nemi wata mafitar, akwai masu taimakon jibgi guda suna nan. Shi kuma Bala ki yi maza ki kirashi yanzu, ai da zafi akan bugi karfe, gwara ki ba shi wannan aikin da alkawarin manyan kudade idan ya aiwatar kada lokaci ya kure."

Bisa wannan shawarar Mami ta fiddo waya ta kira Bala, ta ci sa'a ba ta sha wuyar samunsa ba. Suka yi magana ya kuma ji daWin kudaden da aka yi mishi al?awari ya ce zai yi yanda ta ce. Da haka suka yi sallama.

Sai da suka gama ?ulla-?ullarsu kafin Hajiya Lubna ta kira direbanta ya zo ya ja suka bar farfajiyar wajen taron.

***
Tasleem kuwa tun da aka sa ?afa aka tafi wajen biki, ta zari mayafinta jikinta har rawa yake ta wuce gidan Babandi. Ta rasa meke janta zuwa gareshi. Kiranta kawai ya yi ya sanar da ita ta zo yana jiranta ta ji nan duniya idan ba ta je ba akwai matsala, ko makaranta ta kasa mayar da hankali kan jarrabawar karshe da take yi. Haka Babandi ya more ta sannan ya ba ta wani ?ullin magani akan ta yi yanda za ta yi ta sanya a abin ci ko shan Humaira, sai ko wani t????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
urare da za ta shafe a kayan da ta tabbatar shi Humairar za ta sanya ranar daurin aure. Da wannan murnar ta dawo gidan. Koda Mami ta tambayeta daliin jimawarta, cewa ta yi layi ta tarar.

***
Washegari ya kama ranar Waurin aure da kuma yinin cikin gida sai ko kai Amarya duka. Tun safe jikin Humaira a sanyaye yake, kewar yan uwanta da tunanin sabuwar rayuwar da za ta shiga na aure sun tsaya a ?o?on ranta. Tana gani ana ta shige da fice ana shiri, masu wanka nayi masu karyawa suna yi, ita ko ta kasa sa komai a bakinta balle ta samu ta ji faWan Hajjo ta mi?e ta shiga wanka. Da ta kalli Ummita sai ta ji hawaye na ?ara zuba kamar famfo a fuskarta. Ummitan ma daurewa kawai ta ke yi, ita ko Raihana ma gaba daya ta dunkuke cikin bargo tana kuka. So take ta je ga Abba ta fayyace masa komai amma kuma ba ta son raba masa hankali gida biyu. Ta san yana ta hada-hadar fita zuwa daurin aure. Wannan dalili ne ya sanya ta bar komai a cikinta.

?angaren Anna kuwa, murna har da su rawa saboda kudaden da aka turo mata ya yi daidai da wadanda aka suka rage ta cika wajen fiddo autarta. Ta yiwa Mami magana, suka dunguma har Futuha da ta shigo gidan da safe? zuwa inda Jannat din take. Tasleem ko ba ta bi su ba sai tunanin ta inda za ta shiga dakin ta shafa turare a kayan Humaira alhalin babu ko tsinkenta a dakin. Ga mutane an cika a ciki, gaba daya kanta ya ?ulle. Ta fito falon goye da Wiyarta a baya wacce ko wanka ba ta yi mata ba ga famfas ya cika sai tashin zarni take yi. ?azanta na Waya daga cikin halayyarta. ?azamar gaske ce har ma fiye da Futuha kai ka ce ba Nos ba.

"Ladidi don Allah yi da jiki ki mi?awa Amarya wannan shayin yarinyar ta ?i cin komai, ni bari naje na ga ko masu kai kayan can gidanta sun tafi."

Baba Amina ke maganar ba ta ko lura da Tasleem ba, ta fice da sauri Ladidi na amsa mata da toh. Wani irin sauke ajiyar zuciya ta yi tana jin wani sanyi a ranta. Ta yi sauri ta fada kicin din. Suka gaisa da Ladidi. Ta dubi tire din mai dauke da filas da kuma kofi sai kayan shayi da plate wanda aka soya kwai aka rufe.

"Ladidi don Allah dubamin akwai ragowar fulawa."

Ta amsa da toh sannan ta shige store din dake jingine da kicin din tana fadin ba za a rasa ba bari ta duba. Tasleem a gaggauce ta fiddo ?ullin maganinta cikin zanin goyon, ta kunce ta bude kwan ta barbaWa kadan a sama, ta rufe ta kara bude murfin filas din shayin ta zuba ciki kadan ta rufe ta jijjiga ta ajiye, ganin Ladidi na shirin fitowa ta yi saurin tura maganin cikin zani ta saita tsayuwarta.

Ladidi ta fito rike da karamin buhun fulawa ta ce.

"An ci sa'a kin samu ba yawa, haka mutumin naki kike son ci?" Tana nufin danwake. Tasleem ta dan yi dariya ranta fari sol ganin a saukake ta aiwatar da guda daya saura Waya.

"Kamar kin sani, don Allah taimaka ki yimin idan kin mi?a sa?on Humairar."

"Ya akai kika san an Humaira ne?"

Tambayar da Ladidi ta jefomata kenan, ta dan ji faduwar gaba kadan, ashe fa ba ta riga da ta shigo kicin din ba sai kuma ta basar.

"Ah, na ji Baba Amina na baki sa?o tana fita."

Sai a sannan Ladidi ta saki fuska.

"Auho, toh bari na kai sai na zo na Woramaki."

Daga haka ta dauka ta fice zuwa dakin su Humaira. Ajiyar zuciya mai karfi Tasleem ta saki, murmushin jin dadi ta yi har da Wan buga tsalle. Lallai idan Humaira ta ci a yanda Babandi ya ce za ta ji nan duniya ba ta son auren Fadeel. Shi kuwa turaren da za ta fesa a kayan da Humairar za ta sa, zai yi sanadin da za ta haukace ta bi duniya.

Da wannan farin cikin ta fice a kicin din. Sai dai me? Bayan awa guda ta shiga dakin don ta ga irin sauyuwar fuskar da Humaira za ta yi da borin ba ta son auren Fadeel, amma ta tarar ma waya take yi da Fadeel din tana doka murmushi yanmatan dakin na tsokanarta. Wani zafi da jiri ta ji a kirjinta da kuma jikinta. Jiri har yana so ya kayar da ita. Tana da tabbacin Humaira ce ta ci ta sha shayi da kwai, don har? shigowa ta yi da zummar neman wani mayafinta a sif din Raihana ta tarar Humairar ta a yagar kwai tana loma a baki amma ya akai bai yi tasiri a jikinta ba?

"Ke Tasleem lafiyarki kuwa?"

Ta dubi mai tambayar, Sauda ce diyar Baba Amina dake aure a Zaria.

"Babu komai, kaina ke ciwo tun safe da shi na kwana."

"Ayya, ai sai ki nemi magani. Sannu."

Ta amsa da yauwa tana murmushin yake da kallon Humaira. Ta sa kai ta fice za ta nufi dakin Anna. Sai ta hangi kaya a hannun Raihana za ta shiga falon Abba da su wanda ba ya nan ya fice zuwa wajen daurin aure.

"Kayan waye wannan?"

Tasleem ta tambaya da dan sauri. Raihana ba ta ko kalleta ba don haushinsu take ji su duka ta amsa.

"Na Mrs Fadeel in sha Allah."

Wannan Mrs Fadeel din ya ba?anta ranta sosai, ta ja tsaki, Raihana ta fice tana wa?ar.? "Ko an?i ko an so, aure zai Wauru.." Ta sani da ita take, ba ma haka wa?ar take ba amma don ta ?o a ranta ya sanya ta juya shi, wallahi ban da da wayonta aka haifi Raihana za ta rantse ba jininsu ba ce yanda ta fifita Humaira sama da su.

Wata ?wafa ta yi, tana gani Raihana ta shige bangaren Abba ta ajiye kayan ta fito bayan ta jawo kofar, key kawai ta murWa amma ba ta zare shi ba ta wuce dakinsu da zummar taso Humaira da ta yi wanka ta je ta shirya a can saboda mutane sun yawaita a dakinnasu. Cikin sa'a kuwa ta yi sauri ta afka ciki ta daga kayan ta fiddo kwalbar turaren ta fesa a jikinsu sosai ta mayar yanda ta gansu ta ajiye. Ta bude kofar ta fita ta rufe ta fada sashin Anna tana dariya.

"Ai idan kinsan wata ba ki san wata ba. Babandi ya cemin sai kin haukace kin bi duniya, wannan ranar nake jira. Maza jeki Mrs Fadeel ki sanya kayanki. Uniform dinki na asibitin dawanau."

Tana kaiwa nan ta feshe da dariya. Sai a lokacin ne ta samu nutsuwar shiga wanka, yarinyarta can ta jefa ta wajen Ladidi don a yi mata wanka. Zuciyarta fari ?al za ta zama matar Fadeel.

***
Gama wayarsa da Humaira ya shiga wanka, bayan ya fito ya kammala shirinsa tsaf cikin shadda ruwan goro da ta sha aiki, kyau iyaka kyau ya yi. Dogo mijin doguwa, ga cikar zati ga kyau da haiba. Fadeel kenan. Ya fito falonsa inda Ibb da su Idris abokansu ke jiransa. Nan suka sanya mishi ihu da zuzuta haduwar da ya yi a yau.

"Ka ga angon Humaira."

Ya yi wani murmushinsa haWadWe.

"Ku tashi muje dama shi muke jira, yana so amma yana Satawa mutane lokaci."

Ibb ya fadi yana harararsa don tun dazu suke zaman jiransa sai da ya shiga kawai ya ganshi ya yi daiWai a kan gado yana waya da Humaira.
Fadeel ya yi dariyar da fararen hakoransa da dimple suka fito.

"Sorry, muje toh."

Daga nan suka fito gaba daya, ba su ko shiga bangaren Anti Amarya ba saboda cunkoson jama'a suka bari akan sai sun dawo.

A kan idanunta ya shiga mota suka fice daga gidan, ta ji saukar hawaye a kuncinta. Ta saki labulen dakin Antinn nata ta juya zuwa ciki. Zama ta yi ta shiga kuka kamar ranta zai fita. Wato Fadeel ya rantse ba zai aure ta ba, Humaira ya zaSa sama da ita?

A wannan halin Rabi yayarsu ta iske ta.

"Haba Murja, wai sai yaushe za ki sa wa zuciyarki dangana?"

Ta dago fuskar tana dubanta, gaba daya tayi wata iriyar rama da ba?i, dama rabin farin na mayuka ne, har wani ja take yi kamar na soyayyen ?osai.

"Anti wallahi ina son Fadeel."

Rabi ta zauna a gefenta.

"Amma shi kuma ba ya sonki. Wannan bai isa sanya ki hakuri da shi ki rungumi mai sonki ba? Anas ?anin mijina sai binki yake kina wula?antashi."

"Anti shaye-shaye yake fa."

"Sai me? Kar ki manta ya fi mijina kudi sosai. Kedai ba burinki ki yi auren kudi ki hutawa ranki ba? Mu din ma ai fatan da muke yi maki kenan. Ki rungumi kaddara ki aminta kawai a daura maku aure. Kina haifar namiji shikenan mu burinmu zai cika kin zama matar gida. Wallahi a yanda halittar fatarki ta kara munana Fadeel ba zai taSa kallonki ya ji sonki na aure ba balle sha'awa. Ki yi hakuri ki lallaba rayuwarki da auren Anas kar ki yi saki na dafe. Watakila ma sai kiga sanadin soyayyar da yake yi maki Allah ya shirya shi. Sai kiga ya sauya daga yanda kika san shi. Mu dai ki zama Matar Gida, ki haifar masa Wa namiji dukiyarsa ta zama ikonki."

Rabi ta dinga yi mata famfo, har a karshe ta ji ta saduda ta amince da hakan. Da wannan murnar da farin ciki ta kira Anas ta yi mishi albishir cewa ai Murja ta aminta da batun aurensa. Shima ya yi farin ciki sosai ya kuma ce a ba shi Murjar ya ji ta bakinta. Nan ta sanar da shi eh hakane ta yi na'am har feeto ya yi mata a kunne ta cikin wayar tsabar farin ciki. Ita dai ta yamutsa fuska. Ai gwara ma ta yi kudin ta nunawa Fadeel ba shi kadai ke da arziki ba.

***
Ta shirya tsaf cikin leshin da Raihana ta tanadar mata. Raihana na kokarin mi?a mata sar?a ta ga Humaira ta yi wani dumm, lokaci guda kuma idanunta suka kaWa. Ta rike kanta ta shiga tari.

"Lafiya Humaira?" Ta tambaya hankali tashe.
"Masha Allah, ga nan Ango da tawagarsa nan shigowa."

FaWin wata mata, nan aka hau gyara hanya, suka shigo da sallama dauke a bakunansu kowannensu cikin gayu. Matasa masu jini a jika ga ruwan arzi?i.

Ummita ta kauda kai daga kan Ridwan tun ganin da ya yi mata ya zubamata mayatattun idanunsa kamar ya haWiyeta.

"Wancan guy din fa ke yake ta kallo, ke kuwa kin ?i ba shi dama."

Raihana ta faWi ?asa-?asa, tuni ta gyara fuskarta ta fito, ba?in cikin halayyar yan uwanta ba zai sa ta kasa nunawa Humaira murnarta da samun miji Waya tamkar da dubu ba.

Harararta kadan Ummita ta yi.

Humaira ko tun da wata abokiyar tso?anarta ta sanya hannunta cikin na Fadeel ta yi Wif ta kasa magana, duk iyakar kokarinta na ganin ta zare amma gogan sai ya tamke su tam a cikin nasa. Nan fa aka shiga hotuna bayan kammala gaishe-gaishe. Fadeel ya matsu ko kallonsa ne Humaira ta yi amma ina, kunya ba ta bar ta ba. Zuciyoyinsu sai wani zillo yake yi na farin ciki.

Wizzy na tsaye daga baya yana ?arewa gidan kallo da mutanen dake ciki, bai san Mami ba a fuska hakanan ita din ma balle ya yi tunanin za ta gan shi ko kuma shi din ya gan ta. Yana kuma da tabbacin zai wahala wani cikin su Humaira da Ummita su iya gane shi, a ganinsa abu har an shekara zai wahala su gane shi.

"Ke Ummita, yaron nan dai Wuminki yake son ji." FaWin Hajjo tana mai mi?o mata shi bayan ta je sun kammala hotuna da su Fadeel an gaisa. Hankalin Wizzy gaba daya ya yi kansu, Ummitan ta ci wani irin kwalliya da blue lace ta yi kyau tsaf. Ahmad din ma shigar ?ananun kaya aka yi masa, ya yi SulSul abinsa. Yana kallonsu cike da wani irin kauna da bai san daga sadda ta faro ba. Ya bi Ummita da kallon sama har ?asa, ta ?ara zama wata yarinya sharr da ita.
Daidai sadda wani ya karasa kafin Humaira ta kai ga sa hannu ta karSi Ahmed, ya ce Hajjo ta mi?a masa shi. Wani ?ululun bakin ciki ya tokare a wuyan Wizzy, wannan wane Wan iskan ne haka? Dama ya kula da irin shishshigin da yake yiwa Ummitan, toh kuwa bai isa shiga tsakaninsa da Wansa ba. A yau zai raba su da wannan farin ciki ya Wauke jininsa idan ya so daga baya ko Ummitan ya dawo ya sace. Shi ya ji ma zai iya aurenta su rayu tare.

Ummita ta dubi Ridwan. Ya kashe ta da wani sassanyan murmushi, ta yi ?asa da kanta. Ganin haka Hajjo da murmushi ta juya ta bar musu wurin tana mai fatan alheri a can ?asan ranta. Ta tabbatar idan har wannan aure ya tabbata toh shakka babu Ummita ma tana cikin layin masu dace a rayuwa. Tana da labarinsa a bakin su Raihana da Humaira a sadda suke koWa shi duk don su nemi kafa shi a zuciyarta.

"Ni ake ta yiwa yanga? ?an nawa ma rowar ganinsa ake yimin?"

Duk sadda ya kira Ahmed da Wansa wani daWi take ji amma ta ke kannewa. Yanzun ma ba ta ce komai ba sai kauda kai gefe.

Ya taka zuwa inda ta mayar da fuskarta. Idanunsa ya kai ga Wizzy, ganin haka Wizzy ya kauda kai da sauri yana kallon wani Sangaren, shima sai ya Wan share amma tun sadda aka shigo yake lura da shi, gaba Waya zuciyarsa ba ta yarda da shi ba.

"Mama tana tambayar yaushe za ki je ta ganki? Kinsan fa na ce mata sa ranar kawai ya yi saura. Kin amince."

Ya karashe da Wan Waga gira, ta zaro ido gami da Wan dafe kirjinta.

"Ni da bakina na ce maka na amince?"

Ya Wan bi bakin da kallo yana murmusawa kafin ya maida idanunsa kanta. Ta kauda kai, ta rasa dalilin da idanunsa ke mata wani irin kwarjini.

"Ko ba ki furta ba ai idanunki sun fallasa sirrin dake cikin zuciyarki."

Ta kasa cewa komai sai giftashi da ta yi ta wuce murmushi dauke a fuskarta. Shi dinma bin bayanta da kallo ya yi cikin murmushin har sai da Idris ya Wan buga kafaWarsa. Ya basar gami ga mi?a Ahmed ga ?ar yarinya kuma jika ga Baba Amina dake ta faman mi?a hannu wai ya ba ta shi. Ta karSe shi kuwa ta yi gaba tana masa? wasa. Dukkan wannan abu akan idanun Wizzy suka faru. Ya gama sha?ar ba?in cikin wannan soyayyar da Ummita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login