Showing 18001 words to 21000 words out of 189325 words

Chapter 7 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

194

ya ba Alhajin nan mamaki, ba ta jira komai ba ta sauko daga adaidaita sahun ta Waya Sangaren mutane na mata sannu. Matashin da ya tattara mata kayan ta yiwa godiya ta karSi jakarta, ba ta so dubawa ba amma da yake ya matsa sai kawai ta duba, komai nata yana nan cif ba abin da ya Sata. Dakyar take tafiya dalilin gefen cikin da har sannan ke mata Wan zugi.

"Sannu baiwar Allah, kiyi hakuri ba da gayya hakan ta faru ba. Direbana ne ya Wauki waya bisa umarnina ba kuma mu ankara ba hakan ta kasance. Akwai inda ke maki ciwo sai a karasa asibiti."

Ya karashe yana kai idanunsa kan gefen cikinta da take ta faman dafewa. Ganin haka sai ta saki cikin don ba ta kaunar taimakonsa saboda irin kallon da yake jifanta da shi, kwatankwacin irin kallon Kabeer. Fuskarta a daure tamau ta amsa.

"Na ce maku babu abin da ke damuna, lafiyata kalau. Nagode da taimakon."
Daga haka ta karasa tana cije lebba ta yiwa Wan sahun sannu kafin ta kai hannunta dake rawa don har lokacin ba ta dawo daidai daga razanin da ta shiga na hatsarin ba ta fiddo kudi za ta ba Wan sahun na hakkinsa dake wurinta amma ta kara tsintar muryar Alhajin nan wannan karon muryarsa har ?ar rawa take yi, kirjinsa kuwa bugu yake da karfi tsabar son da ya shiga zuciyarsa farat Waya na yarinyar.

"Ki bar shi zan biya. A wane unguwa kike sai mu sauke ki?"

Jama'ar duk idanunsu a kansu, wadanda suka lura da yanayin mutumin ba su ga laifinsa ba don Humaira ta haWu iyakar haWuwa, sai dai a ganin wasunsu, girma ne zai fadi muddin ya bari ta gasa mishi magana. Aikuwa masu wannan tunanin ba su kai ga furtawa ba suka tsinkayi muryarya cike da tsiwa tana magana tana kara zaro manyan idanunta masha Allah.

"Baba ina mutunta furfurarka hakan yasa nake gargadinka akan ka fita a hanyata wallahi tun ban gasamaka wacce za ta hanaka bacci ba. Haba! Wannan ai shiga sharo ba shanu ne, ka kusan kaimu lahira na maka uzuri yanzu kuma me ya shafeka da kudin da zan bayar? Da kai ke biyamin kudin motar? Ina ruwanka da ni?" Daga haka ta ja dogon tsaki ta mi?awa Wan sahun dubun gaba daya na motarta zuwa da komawa ba tare da ta jira chanji ba, daga haka ta juya daidai sadda wannan matashin ya kara mi?o mata ledar da shaf ta mance da batunsa, sa?on Mami zuwa ga Anti Laila. Sai lokacin ta ga ashe ma leshi ne sai atamfa. Godiya ta yiwa matashin a fusace ta bar wurin tana huci, ga cikinta inda ta Wan bugu bai bar raWaWi ba. Kunya da tarin bakin ciki suka lulluSe Alhajin, bai taSa zaton yarinyar ba ta da kunya ba da tuni ya Soye zalamarsa a kanta.

"Sai hakuri Alhaji, yaran yanzu ba su da kunya."

Ya basar da zancen yana maida duba ga ?an sahun nan da ba da umarnin ya tashi su karasa asibiti ko kuwa dai ya sallame shi yanzun a nan, Wan sahun ya aminta da hakan, nan take ya ba shi kuWaWe masu Wan kauri gami da ?ara ba shi hakuri. Daga haka ya juya zuwa motarsa har lokacin bai daina jin kunya da Sacin rai ba su sake shi ba. Ya kuma ?udurta a ransa idan har haka yaran zamani su ke, to ya yi Allah wadai da ire irenta, ba kuma ya jin zai kara kallonta da sunan wata da ya taSa gani har ya ji kaunarta cikin ransa.

***
A Sangaren Humaira dakyar ta karasa gidan Anti Laila, ita sai da suka yi nisa ma ta tuno ba ta da chanjin da za ta sallami mai adaidaitan don haka ta ce ya jira ta kawo mishi. Wajen Anti Laila ta karSa bayan ta mata bayanin hatsarin da suka yi, nan kowa ya hau ta da sannu. Anti Laila da kanta ta kira Mami ta shaida mata, hankali tashe ko mintuna talatin ba a yi ba sai ga Mamin da direban Abba. Daukarta ta yi suka nufi asibiti, koda likita ya duba ta ya tabbatar kawai buguwa ce. Magunguna ya ba ta sannan suka wuce gida. Maganin ta sha bayan ta ci abinci ta kwanta.

Abba har Wakinsu ya shigo ya duba ta, ganin da sa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????uki bacci ma take ya sanya shi fita.

Sai da ta yi kwanaki uku ba ta le?a ko farfajiyar gidan ba a rana ta hudu ta koma zuwa koyon girke-girke abin ta.

***
Rayuwar ta ci gaba da tafiya yau dadi gobe babu, rashin dadin a wajen Humaira bai wuce na yadda su Tasleem ke kara nuna mata kiyayya a fili ba. Har ta kai da an wayi gari watarana sun yi mata sharrin sata, domin an tashi Mami tana neman kudin har dubi ashirin da ta ajiye ?asan filo, gaba daya ran Mami a Sace yake, sannan ma ita Humaira ba ta nan kuma ita ce ta gyara Wakin kafin ta fice gidan Laila. Ganin an duba ko'ina sai Futuha da su Yassar suka ba da shawarar a duba Wakunansu. Mami a farko ta ?i, sai da Ladidi ta ce ya kamata a duba ko'ina tunda dai nema ake kuma abin da yasa Ladidin faWin haka ganin su na neman Worawa yarinyar kirki Humaira ita kuwa tana da ya?inin idan har Humaira ce ba za a sami ko sisi na wani a kayanta ba. Tasleem da ta dage tunda Humaira ce ta yi gyaran Wakin a soma duba kayanta ya sa Ummita cike da kwarin gwuiwar sanin wace ce Humaira ta shiga fiddo kayan Humairar daga sif dinta. Sai dai tun kan ta yi nisa Futuha ta zura hannu ta jawo wata doguwar riga.

"Kambu! Dama yarinyar nan ita ta Waukarmin wannan rigar? Tasleem ku dubi rigar da nake tunanin ta Sata a wajen wanki?"

Mami ta kalle su, ta yi shiru da mamaki. Can kuma sai ga Wan kunne da sar?a sun faWo. Raihana ta zaro ido tana Wauka.

"Innalillahi, ku ga sar?ata da nake nema kwanaki? Ashe ita ta Wauka?"

Kai kamar wasa jikin Ummita na sanyi da wannan sharrin, ba ta yi aune ba ta kai hannu kan takardun kuWi, tsabar razanar da ta yi ya sa ta fiddowa da sauri. Ladidi ce ta karSa tana salati ta ?irga, aikuwa dubu ashirin cif ne wanda Mami ke cigiya, Ummita kawai sai ta fashe da kuka tana faWin.

"Wallahi Mami wannan sharri ne, Humaira ba Sarauniya ba ce. Ko kwandalar mutum ta gani idan tana aiki ajiyesu take a wurin da ta gan su."

Mami dai ba ta iya magana ba domin kanta ya ?ulle, a sanyaye ta sa hannu ta karSi kuWin ta fice a Wakin tana ji su Yassar na yiwa Ummita masifa wai sai ta faWi wa ke mata sharrin amma ba ta ko iya tankawa ba. Ita kanta ta sani sata ba ya daga halayyar Humaira don ta sha ajiye kuWin da suka fi waWannan kauri ba ta taSa su ba, amma ta sani mutum ka iya sauyawa. Bare ma a irin gidan nan na Alhaji Isuhu da ba a facaka da kuWi.

Humaira ba ta dawo gidan ba sai yammaci bayan la'asar, da murnarta ta tura kyauren gate ta shigo bayan ta gaida Baba dattijo dake zaune a benci yana siyan rogo a wurin ?ar tallah. Farin cikin bai wuce na yadda suka yi snacks har biyu a yau ba, samosa da springroll kuma cikin ikon Allah ta yi ya yi kyau a ido ya kuma yi daWi a baki har a foilpaper ta nannaWe ta kawo don Mami ta ci ta ji. Muryar ?asim ta tsinta a kanta.

"?arauniya ta dawo."

Kallonsa ta yi gabanta ya faWi, a duk irin wulakanci da jefa-jefan mugayen sunaye da suke mata, babu wani cinikinsu a ya taSa kiranta da Sarauniya wannan ya sa ta ji wani irin sanyi har ta kasa mayar masa da martani yadda ta saba idan ya jefe ta da marar dadi. Ya Wan Waga gira.

"Oh, bakin ta kanwa ya yi la'asar kenan saboda kin sani kin sata shiyasa. Dama ustazancin ashe na ?arya ne, toh yau asirinki ya tonu. ?an adam butulu."

Ta dafa kirji idanunta da suka cicciko da kwalla tun soma maganarsa ta kafa mishi.

"Yaya ?asim sata fa ka ce? Ni na yi satar?"

Ya harareta ya wuce kawai ba tare da ya ce komai ba. Ta bishi da kallo har ya shige gidan, itama a hankali ta soma taka ?afafuwanta da suka yi mata nauyi saboda mutuwar da jikinta ya yi ta yi cikin gidan kirjinta na harbawa.
***
Tasleem, Dawud, Yassar da Futuha ne zaune cikin falon sai dai ba ta sha mamakin ?in amsa sallamarta da suka yi ba, dama ya lafiyar giwa ballantana kuma an jefe ta da kashi? Su na ganinta Tasleem ta mi?e ta yi kerere gabanta hannuwa a ?ugu ta ce.

"?arauniyar banza da wofi, kin dawo kina wani sum-sum kamar munafuka. Koda dai dama munafukar ce, Mamin da ta daukake ki tana maki kallon kamar wata waliyya ai gashinan kin watsa mata ?asa a ido. Ke ni ba wannan ba ma, earpiece dina da na jima ina nema idan kinsan ke ce Sarauniyarsa wallahi tun wuri ki fiddomin abina. Atoh, bari ma Abba ya shigo gidan, ko Mami ba ta faWamasa ba sai mun faWa."

Humaira wacce ta kasa tsaida hawayenta, kallon Tasleem din kawai take har ta kai aya, lebbanta na rawa amma ko harafi guda ta kasa fitarwa tsabar ba?in ciki. Wannan wace irin ba?ar rana ce a wajenta haka da za a wayi gari da yi mata ?azafin sata? Ta kasa motsawa, haka Futuha ma ta taso da nata kalar rashin mutuncin, su Yassar na taya ta. Ba ta iya cewa uffan ba sai kukan da ta ke rusawa kamar ranta zai fice. Tsawar da ta ji an daka musu ya sa ta kallon hanya, ruwan hawaye ya sa ganinta komawa dishi-dishi, sai a hankali bayan ta Wan runtse idanu sun Wan zuba ne sannan ta lura ashe Mami ce. ?arasowa ta yi fuskarta a Waure, sai ta koma mata Mamin da ta fara cin karo da ita a ranar farko na zuwanta gidan. Kirjin Humaira ya hau dukan tara-tara, ta runtse idanu saboda ta gama hasaso abin da zai afku, wato mari za ta sha a wajen Mami, sai dai ga mamakinta ta ji akalar faWan sam ba a kanta yake ba, su Tasleem ta shiga yiwa tamkar za ta ari baki.

"Ashe rashin mutuncin naku ya kai har haka? Raini ne wannan ku ka yimin ko mene? Ban hana Wayanku yiwa Humaira maganar abin da ya faru ba? Ina ce har Waki ke Futuha kin biyo ni akan sai an Wauki mataki na ba ki sa?o ga ?an uwanki cewar na kashe maganar kada wanda ya tayar? Oh saboda ku nunamin ni banza ce wurinku, hukuncina ma na banza ne shi ne dalilinku na yin watsi da zancena a kwandon shara ko?! Toh wallahi ku fita idona tun wuri, kuma daga rana irin ta yau ku ka ?ara tada wannan batu sai na saSamaku kamanni."

Tana kai wa nan ta ja hannun Humaira zuwa Wakinta. Ta bar yarannata a tsaye tamkar su haWiyi zuciya su mutu don haushi, Yassar ne ya soma jan wani dogon tsaki kafin ya sa kai ya bar falon, Dawud ya mara mishi baya. Tasleem kuwa ?wafa ta yi.

"Innalillahi, ke Futuha na soma tsoro, na yarda dagaske ne da ake cewa ?an ?asarsu na da asirai, anya wannan shu'umar yarinyar da Kawunta hakanan suka? bar mana uwa? Anya ba sai da suka shuka tsiyarsu sannan ta dawo wajenmu ba?"

Futuha da ta kasa magana kawai sai ta ja tsakin itama ta Wauki wayarta ta wuce sashen Anna idanunta cike da kwallar ba?in ciki.

***
A gefen Mami kuwa, su na shiga Wakinta ta rungume hannuwanta a kirji ta daure fuska tamau har sai da Humaira ta sha jinin jikinta.

"Zauna." Ba musu ta zauna a saman kafet, ita kuwa ta hakimce a gefen gado.

"Na tsawatarwa yarannan saboda na riga da nasan takun sa?ar da ke tsakaninku, ba na son a samu fuskar da za su ?ara Wora maki karan tsana a matsayinki na yar uwarsu ta jini. Wannan Win ma da suke gwada maki fatana su daina na kashe shi gaba Waya. Amma meyasa haka Humaira? Har yanzun ina kokwanto akan kin aikata wannan laifin na Waukar kudi a Wakina, amma idan? na tuna ganin da na yiwa kuWin a cikin kayanki sai zuciyata ta tsinke. Ki faWamin iyakar gaskiyarki, kamar yanda idan na ci karo da Waya cikin su Tasleem sun aikatamin laifi zan hukunta su, kema matu?ar da zuciya Waya nake zaune da ke ya zama wajibi na dauki mataki idan kin yi ba daidai ba."

Humaira ta ja majina tana kallon Mami. Girgiza kai ta soma cikin muryar kuka ta ke magana.

"Wallahi Mami, Allah Waya, ba zan yi wasa da Ubangijina wurin yi maki ?arya ba, ban taSa Waukar ko abin sakacen ha?ori a Wakinki ba tare da izninki ba ballantana kuma kudin da ba nawa ba. Mene ne bakya kokarin yimin a gidannan da zan yi maki sakayya da hakan? Kina yimin kyautatawar da ko na rayu da mahaifiyata abin da za ta yimin kenan. Toh a wane dalili zan zama butulu har na Wauka daga asusunki? Mami wallahi ban Wauka ba, ba ni kuma da masaniyar yanda aka yi kudin suka je cikin kayana, nidai na san na maki gyaran Waki, na kuma adana su a inda na gansu, na fita zuwa gidan Anti Laila."

Mami ta yi shiru tana nazarinta, duk kushen mai kushe ba zai taSa zama da Humaira ya ji ta masa karya ko sau Waya ba. Toh wannan dabi'a ce ta mahaifiyarta, ta sani sarai mahaifiyar Humaira haka take da faWar gaskiya. Ta san kuma ko a gaban Abban maganar ba za ta chanja zani ba. Sai ta yi nufin kasheta a yanzu ta hanyar numfasawa ta dafa kan Humairar cikin taushin murya ta ce.

"Ya isa hakanan, bari kukan kar ya ja maki ciwon kai. Na yarda dake ai dama, sai dai kin san kudi ba zai kai kansa cikin kayanki ba ko? Koda ace ba ke kika kai ba akwai yadda aka haihu a ragaya, kin ga kuwa dole na bincika matsayina na matar gida ko?"

Humaira ta gyaWa kai har sannan tana sauke hardadden numfashi irin na wanda ya ci kuka ya ?oshi. Mami ta dora da fadin.

"Toh don haka kar ki fahimce ni baibai don na tuhumeki, ya zama dole na aikata hakan ne ko don sauke hakki, yanzu kuma da ya kasance ba ke ba ce, zan bincika a sannu gaskiya za ta yi halinta. Tashi ki je ki ci abinci ki huta."

Humaira ta gyada kai kawai ta mike ta fita. Har sannan jikinta bai bar Sari ba, sharri ya fi komai Waga mata hankali, ta tsani sharri, ta kuma ci alwashin ita kanta za ta dage da addu'a har sai gaskiya ta yi halinta don a yanzu kam ba ta da amsar ba su Tasleem sai lokacin da komai zai bayyana muraran.

A can Waki ma Ummita ta tarar tana nata hawayen, sai ya zamana ita ce mamai rarrashin Ummitan da nuna mata ai Mami ta fahimce ta. Ummita ta labarta mata yadda komai ya faru. Ta kara da fadin.

"Ba ni da tabbaci akan ko su Tasleem ne da aikata hakan, amma shakka babu ina zarginsu."

Murmushi Humaira ta yi.

"Kar ki damu yar uwa, idan ma su ne ina mai tabbatar maki wataran gaskiya za ta bayyana."

Daga haka suka bar zancen, koda Abba ya zo, babu wanda ya tunkareshi da zancen don ba karamin gargadi da jan kunne Mami ta yi musu ba, koda Anna ta hau faWa, sai Mami ta sanyayar mata da jiki da faWin abin da ta fi tunanin akan sharrin da aka yiwa Humairar. Dole itama Anna ta lallaSa su akan zanceya mutu. Daga ranar kuwa ba a kara tayarwa ba kuma basu fasa kiran Humaira da wannan sabon suna na Sarauniya da suka la?aba mata ba. Wanda hakan ya fi komai yi mata zafi, duk kuwa da Mami ta tsawatar amma a fakaice a bayan idon Mamin ba sa fasa faWi.

***
WATA BIYU BAYAN HAKA...

Ranar ta kasance yammacin Asabar, gaba Waya ahalin gidan su na nan idan ka cire Abba wanda ya fita zuwa kasuwa tare da Dawud. Fuskar Mami a kallo daya za ka shaida tana cikin farin ciki. Su Tasleem dai murnarsu ba yabo ba fallasa. Humaira kuwa da Ummita aiki suke tare da Mami ba kama hannun yaro, Raihana na can Sangaren yayannasu tana aikin gyara bisa dole don ba yadda za ta kaucewa umarnin Mami, sai dai rabin aikin tana yi ne amma hankalinta na ga chatting din da take yi da sabon saurayinta wanda ya kasance abokin yayan ?awarta.
Humaira ta zage damtse wurin yin kayan snacks yayinda Mami da Ladidi su ke aikin girka masa dambun shinkafa da kuma kunun aya, kamar dai yanda ya bu?ata. Sun kammala da wuri suka jera komai a saman tebur, Humaira a gajiye ta nufi hanyar Wakinsu da zummar watsawa jikinta ruwa adalilin zafin da ke tasomata, Mami ta dakatar da ita ta hanyar kiranta. Juyowa ta yi gami da amsawa.

"Maza je dakin Yayanki ki dubamin waccan mashiriciyar ko ta kammala gyaran nan, idan ta kammala ki dawo ga charcoal ki kunna a sanya turaren wuta."

Ta amsa da toh sannan ta juya cikin bin umarnin Mamin. Tana zuwa daidai kofar dakin Yaya Mubarak ta ji muryar namiji kamar ta waya ya na fadin.

"Um um sweetheart, ban gaji da ganin su ba, ni da ace za ki Wan buWemin ko saman ne kaWai na kalla zai taimakamin ya magancemin wani abin. Please taimakamin kin ji? Gaba Waya ta mi?e wallahi."

Humaira ta zaro ido, sam ba ta fahimci komai ba, ta na shirin faWawa Wakin don ta ga meke gudana ta tsinkayi muryar Raihana na amsawa da wata murya tamkar ba nata ba tana wata iriyar shagwaSa.

"Um um Baby, ba zan iya buWemaka ba ina jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login