Showing 105001 words to 108000 words out of 189325 words

Chapter 36 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

211

ya ninka nawa kenan? Ban yi ?asa a gwuiwa ba, ban kuma damu da cewar tsohon ciki gareni ba, na bi shawarar Lubna na ni?i ?afa na koma wurin Babandi. Nan na nemi a yimin aikin da zai sa a raba Fatima da abinda ke cikinta da duniyar ma baki daya. Ya nunamin yanzu haka da muke magana Fatima na?uda take yi, ya tabbatarmin zaa turamata ba?a?en aljanun da za su yi sanadin rayuwarta. Na yi murna kwarai, amma abin ba?in ciki ya cemin abin da za ta haifa dole zai rayu a doron ?asa, nidai ban wani damu sosai ba. Koda ya gama dubansa ya ce aikin zai yiwu haka na tattara na tafi da farin cikin Fatima za ta bar duniyar baki Waya. Za ta bar mijina. Sati uku da haihuwar Fatima, labari ya zo mana na rasuwarta. Zo ki ga kuka a wurina kamar zan shiWe. Na nuna zan je gaisuwa, amma Yusuf ya hana ni saboda cikina ya shiga watan haihuwa, da wannan hujjar ya tafi har ina ce masa ?afarsa ?afar jaririyar Fatima ya kawomin ita zan ri?e. Wannan ya sa Yusuf ya ji dadi sosai ya dinga yimin godiya bisa kaunarsa da nake. Har a zuciyata addua nake kada a ba shi Humaira ya kawomin. Aikuwa haka ya dawo babu ita ya cemin wai Dadar ta daukarwa Fatima al?awarin kula da Humaira, ya yi hakuri. Daga nan fa rayuwa ta dawomin sabuwa fil a gidan mijina. Daga ni sai yarana, na haifi Raihana bayan Jamila ta haihu da kusan watanni shida, Humaira na da watanni hudu itama lokacin. Shekaru suka tafi har aka shekara biyar, zuwa lokacin rayuwar kunci da talaucin ya ishe ni, samun Yusuf ya ja baya sosai. Gaba daya ya zamana hatta kudin makarantar yara daga aljihun Muntari yake fita, wannan ya kara sanyamin ?iyayya mai tsanani na Muntari da Jamila. Ban samu sukuni ba har sai da na biya wasu yara suka haWa gobarar da ba a fitar da komai a gidan Muntari ba sai Ummita."

Idanu waje Futuha take duban Maminta wannan karon.

"Ma..ma.." Ta ma kasa magana taabar firgicin da ta shiga da tsananin ruWani. Tana kara tabbatar da nisan da mahaifiyarta ta yi a fannin da suke ganin sun fi ta. Mamin ta yi yar dariyar mugunta.

"Yes, ni na sanya aka ?ona iyayenta, aka kashe jaririyar da Jamila ta haifa da Jamilar ma. Ban san ya aka yi shegiyar yarinyar ta tsira ba. Haka labarin gobarar ta zo mana, hankalin kowa ya tashi ciki har da ni da na nuna ban san komai ba. Shegiya Maijidda tun a sannan ta nuna ita wallahi ba ta amince gobarar gaske ce ta kashe Jamila ba. Ta ce a bincika amma kowa ya yi burus da ita ga tunaninsu kawai zafin mutuwar Jamila ne saboda irin sha?uwar da suka yi da juna. Da nayi wani tunani akan dukiyar Muntari sai na shawarci? Yusuf akan ya Wau ri?on Ummita kar a raba ta da dangin mahaifinta. Nan fa ya amince, ya kuwa dage akan lallai shi sai an ba shi Ummita. Sun so yin fada da Maijidda wacce ta dage lallai ita za ta dauketa, a karshe dai da Kawunnansu suka sanya baki dole ta hakura ta kuma kalleni ta bini da Allah ya isa. Na fashe da kuka ina nunawa jama'a Maijidda ta tsane ni, nan aka hau rarrashina har yan uwan Jamila ana ganin ba?in Maijidda. Yusuf har kusan faWa ya yi da Maijidda a kaina dakyar dai komai ya lafa. Wannan shi ne silar dawowar Ummita hannuna, daga baya kuma Humaira ta zo wannan kin sani."

Futuha ta ja dogon numfashi.

"Tab! Mami kina da abubuwan mamaki sosai. Wallahi ba don ke da bakinki kike fadamin ba, da ace a wani wurin na ji dukkan wadannan zan ?aryata ko waye ya faWi."

Murmushi Mami ta yi.

"Ku ne ba ku san rayuwa ba, yanzu da ace wani mugun halin na nuna a zahiri, kuna zaton Abbanku zamu kai yanzu da shi ba tare da mun rabu ba? Ko kuwa kuna tsammanin a baya ida? kishi ya kwashe ni na kashe Fatima da hannuna yanzun zan cigaba da rayuwa a duniya? Ai hakan ba zai taSa afkuwa ba, komai Wan hakuri ne da bi sannu-sannu. Ka yi siyasa a komai, ka shanye komai ka danne sai ka ci riba. Ina dab da cin ribar kwace dukiyar Yusuf saboda na faranta maku, na ba yarana maza jari su huta daga ma?on da Yusuf ke yi musu, na kuma nunawa Anna ba Firdausi Jannat ce kaWai Wiya ba, nima na san yanda zan iya kwatar kaina a wurin miji, wannan ne dalilin daya sa na sanya aka sace yarannan, sai dai kuma kuWaWen su na dab da samuwa, komai ya rushe saboda zuwan ?an sanda. Amma ban saduda ba, ban kuma karaya ba, har gobe ba zan fasa yun?urin ?watarwa yarana ha??i ba tunda ubansa marowaci ne mai shegen ma?o."

Fuska a sake Futuha ta rungume Mami kafin ta saketa ta ce.

"Wai Mami ashe daman kina kaunarmu?"

Harararta ta yi.

"Wa ye ba ya kaunar nasa? Na fadamaki ai duk duniya wanda za ki ga ya nuna ba ya son nasa ya fi kaunar wasu toh ?arya yake yi, munafuki ne."

Jinjina kai Futuha ta yi tana washe baki.

"Hakane, Mami na kara sonki wallahi. Kin wanke tunanin dake zuciyata na ganin bakya kaunarmu. Ni fa lallaSa Humaira nake yi so nake ta zo gidana ta koyawa yar aikina girke-girke. Shiyasa kika ga ina ta janta a jiki da kissa."

Mamin ma dariya ta ce.

"Sai ki bada himma."

Sai kuma ta daure fuska sosai.

"Ina kara jaddada maki, koda wasa kika yi yunkurin sanar da wani ko wata labarinnan wallahi zan iya kashe ki."

Sosai furucin ya tsoratar da Futuha, ta yi saurin rike hannunta.

"Aa Mami, wallahi na rantsemaki babu wanda zai ji. Ai ina sonki, ba zan so hukuncin shari'a ko yaya ya hau kanki ba."

Sai anan ta saki fuska ta shafa kan Futuha. Daga haka suka bar zancen suka koma falo inda Tasleem suke zaune da su Mubarak ana cin abinci. Ko kallon Futuha ba ta yi ba, tsanarta take ji a zuciya, wato saboda tana da kudi shiyasa har wani shiga daki suke su rufe su na kwasar hira ita da Mami. A duniyarta ko a mafarki aka ce Futuha za ta samu miji wanda ya fi nata za ta ?aryata. Ga Hamza yanzu ya sauya mata, zamansu gaba daya babu dadi hatta a bangarenta da uwar mijinta da ma yan uwansa. Albarkacin cikin jikinta kawai take ci ta san da wannan. Don ma dai Anti Jannat ta ce ta kwantar da hankalinta har ta haihu sannan su san yanda za su Sullowa lamuran. Wannan ne kadai ya sa ake ganinta cikin nutsuwa, kuma ita dinma ba ta ragawa Hamzan.

***
? Da yammacin ranar daidai lokacin da su Futuha suka fito da zummar tafiya gida har da Tasleem wacce za ta sauke nata gidan sanadiyyar Hamza da ba? zai samu zuwa daukarta ba, sai ko Humaira wacce a dole ba don ranta ya so ba bisa umarnin Mami za ta bi Futuha gidanta ta yi zaman sati biyu kawai don ta koyawa yar aikinta girke-girke, su Raihana sun yo musu rakiya farfajiyar gidan. Humaira tana tuno Fadeel wanda ya ce yana hanya, tana son ta dakata ta jira shi amma wata zuciyar na kwaSarta da nuna mata babu amfanin sauraronsa tunda ba aurensa za ta yi ba. Suna nan tsaye, tana sanye da yadi mai taushi maroon colour wanda ya fiddo tsantsar kyawunta da hasken fatarta, ta Wora karamin mayafi a kanta golden colour. Babu kwalliya ko na Wigo a fuskarta amma kuma sosai kalar ta karSe ta, zama wuri Waya babu fita ya sanya har wani she?i fatarta ke yi. Daidai sadda Futuha ta bude ?ofa tana shirin shiga, daidai lokacin maigadi ya wangalewa Fadeel ?ofa ya turo da hancin motarsa ciki. Bisa umarnin Abba, Fadeel ya zama Wan gida, duk sadda ya zo yana da damar da zai yi parking a farfajiyar gidan. Ya kuma shiga idan an mishi izni su gaisa da mutane. Shi din ne dai ya zaSi rashin zuwan akai-akai saboda gudun kada ya ba?antawa Humaira ta ga kamar yana neman shigarmata hanci da ?udundune alhalin gidansu ne.
"Wannan motar kuma fa?"
Fadin Futuha tana karewa motar kallo, lexus Ls blue black sai she?i take yi, daga gani ba a moreta sosai ba don ba ta nuna alamun tsufa ba.
"Wannan motar Fadeel ne. Na gane, ya taSa zuwa da ita sau Waya wurin Abba."
"Fadeel?" Tasleem da Futuha suka nanata sunan a zahiri. Aikuwa kafin su rufe bakunansu haWaWWen matashin nan mai sa numfashin yan mata tsayuwa na wucin gadi ya fito daga cikinsa. Sanye yake cikin maroon tshirt da ba?in wandon jeans kamar da hadin baki shi da masoyiyartasa. Ya rufe idanunsa da ba?in gilashi yana wani murmushi mai ruWar da zu?ata. Duhun kayan da ma motar da yake jingine a jikinta sai suka kara fiddo da tsantsar farinsa na usulin bafalutani Wan asalin garin Yola.?
Gaba daya Tasleem ta yi wani shock, suka yi mutuwar tsaye. Idanunta har wani ruwa-ruwa yake yi saboda tsabar kallonsa da ta?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? shagala yi ga wani irin so da kauna dake fisgarta har ta mance da wasu igiyoyi masu ?arfi da suke nannaWe da ita suka yi mata shamaki da dukkan wani Wa namiji da ba muharraminta ba. Shi kuwa Fadeel idanunsa a saman na Humaira har dai su Yassar suka karaso aka yi musabaha.
Humaira kuwa ta yi wani irin dauke kai daga kallo daya ba ta ?ara ba.
"Wajenki ya zo ne?" Futuha ta wurga mata tambayar tana Wan murmushin ya?e, a ranta kuwa jinjinawa Mami ta yi, tabbas ba karamin kokari tayi wurin danne abin da ke ?asan ranta ba, akwai masifar wahala. Sosai itama ta ji kishin ace Humaira ce ta samu wannan kyakkyawan matashin kuma mai rufin asiri.
"Ban sani ba." Amsar da Humaira ta bayar kenan tana ?ara tamke fuska. Tasleem kamar ta sha?e ta, yarinyar ta samu dama amma tana nuna girman kai. Ita da ace itace da wannan damar ai sai inda ?arfinta ya ?are.
"Assalamu alaikum."
Sallamarsa ta katse musu tunani, Raihana ta jingina jikin Humaira dab da kunnenta ta ce.
"Ki ri?e wannan bawan Allahn sosai idan kuwa ba haka ba ni zan maye gurbinki."
Ba ta san ya aka yi ba sai tsintar idanwanta ta yi da wurgawa Raihana wata muguwar harara mai nuni da tsantsar kishi, Raihana ta sa dariya tana ri?e kunnuwa gami da Wan jujjuya kai alamun ta tuba. Tana kuma kara gas?atawa Humaira na son Fadeel, ba kuma ta san abin da ya danne wannan soyayyar ba.
Tasleem ta amsa sallamarsa ciki ciki yayinda Futuha ta saki fuska sosai aka gaisa sannan ya dubi Humaira da shanyayyun idanunsa bayan ya cire gilashin.
"Boddo, barka da yamma."
Ya fadi yana mai Wan dun?ule hannu da Wan ran?wafar da kai kaWan tamkar wani basarake. Nan fa gaba Waya idanun ya koma kansu ana ganin ikon Allah.
*LITTAFIN NAN NA KU?I NE. SIYA AKAN NAIRA ? 400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645



Ba ta ce uffan ba sai idanuwanta da ta sauke a cikin nasa. Ya ji kallon har a ?asan ransa.

"Sauri fa muke yi." Tasleem ta furta cikin Waure fuska, gaba Waya wani irin mugun kishi ke cin zuciyarta. Fadeel bai ko kalle ta ba ya dubi Futuha.

"My sis, ko za ki ban aron ?anwartaki for just 5mins?"

Murmushin da bai kai zuci ba Futuha ta yi.

"Ba ka da damuwa. Humaira jeki."

Humaira da ke jin kamar ta sha?o wuyan Fadeel amma sai ta kasa yi mishi musu ta bi bayansa sadda ya yi gaba zuwa inda ya ajiye motarsa. A jikin motar suka tsaya su na hangen su Futuha da ke hira sai ko Tasleem da ta zubamusu idanu tamkar makauniyar da ta samu ido.

"Ka kirani kuma sauri muke za mu tafi."

Ya ji babu dadi daga yanayin muryar da ta yi mishi magana, ya dai daure ya haWiye kamar koyaushe.

"Humaira kina addu'a sosai kuwa? Kina nafilfiloli da sallar dare? Kina mayar da hankali wajen yawan karatun Alkur'ani?"

Ta yi shiru kamar ruwa ya cinye ta, ta sani tana sallolinta biyar akan lokaci, tana kuma addu'a daidai gwargwadon yinta, amma yawan karatun Alkur'ani da kuma sallolin dare da ma nafila ba za ta iya buWe baki ta ce mishi aa a kansu ba, kawai sai ta ji hakan ya yi mata nauyi a saman harshenta.

Ya tsinci amsoshin tambayarsa daga shirunta, don haka ya cigaba da magana a nutse ba tare da ya dauke idanu daga saman fuskarta ba.

"Salollin farillah wajibi ne Humaira, amma su Nafiloli neman ?arin lada ne da kusanci ga Ubangiji. Za su buWemaki ?ofofin rahma wadanda ba ki taSa zato ba. Hakanan shi kansa karatun Alkur'ani, yawan tilawarsa da yin azkar safe da yamma zai ba ki kariya daga shaiWanu da ma jinnu. Babu wani ko wata ko kuma wani abun da zai cutar da ke. Ina ro?onki ki yawaita addu'a, ina kuma ba ki shawarar yawan hailala, istigfari da salatin Annabinmu s.a.w. Ki Wauka tamkar wani Wan uwa ne gareki na jini yake ba ki wannan shawarar. Kin yarda kin amince za ki amfani da ita?"

Ba ta taSa jin wani irin sanyi da nutsuwa tattare da kasancewarta da Fadeel ba sai a yau kuma a yanzun da yake kwararo mata waWannan shawarwarin. Sai gaba daya ya tuno mata da Kawunta da ma Dada, ta tuna da kalar rayuwarta a Nijar, koda wasa idan ta idar da sallah, Dada ba ta barinta ta bar saman darduma sai ta yi nafila ta kuma tsaya ta ga ba ta yi wasa da addu'a ba, hakanan tilawar Alkur'ani, duk juma'a Kawunsu na tattara su har yaransa su yi tilawa, kowacce ta biya inda ta iya. ShaiWan kwarai ya yi tasiri a zuciyarta da har ya sanya ta yi watsi da dukkan wannan, ta zama daga ta idar da sallar asuba sai bacci ba kamar a farkon zuwanta Kano ba da ma rayuwarta a Nijar inda koda wasa ba ta isa ta koma shimfaWarta ba har sai rana ta fito bisa koyarwar Dada. A farko tana yi daga baya duk ta watsar. Ummita duk ta fi wannan kokarin. Ita kuwa kasala ya mata yawa.

"Kinji? Please."

Ya kara nanatawa. Ta dube shi sai ta yi murmushin da rabon da ya gan shi saman fuskarta har ya mance. Ta gyada mishi kai.

"Naji, nagode sosai da tunatarwa kuma zan kiyaye in sha Allah."

Ai sai ya ji tamkar an jefa shi wata duniyar ta nishadi da farin ciki, sai kawai ya rasa me zai ce ban da leSe da ya Wan lasa yana maida mata martanin murmushin. ?arar hon da aka danna da ?arfi ya sanya suka dubi wajen, har ga Allah shi Fadeel ya ma mance adadin mintocin da aka yi mishi alfarmarsa, balle kuma Humaira da ta lula tunanin sakancin da take yi da addu'a tun zuwanta garin. Tasleem ce da wannan aikin ranta a mugun Sace.

"Nagode, kije suna jiranki. Sai mun yi waya ko?"

Ta ji tamkar ta ce eh, sai kuma ta fasa ta juya kawai ta kama tafiya, ya bita da kallo sai kuma ya buWe motarsa ya shiga, ya sani Abba ba ya nan balle ya shiga su gaisa. Don haka ya yi ribas aka buWe gate ya fice. Itama tana shiga gaban motar kusa da direba, direban ya ja suna Wagawa juna hannu ita da Raihana.

Tasleem da Futuha a bayan motar zaune sai yare suke yi. Ita kuwa duk ta tsargu amma ta haWiye Sacin ranta.

Tasleem ke mitar dole ne ma Humaira ta rabu da Fadeel tunda har ita ba ta same shi ba to kowa ma ya rasa. Yayinda Futuha ta ce ta kwantar da hankalinta soyayyar babu inda za ta kai. Haka suka yi ta gulmar Humaira ba tare da ta tsinci ko harafi ba. Ba ta da haWi da buzaye balle ta fahimci akan abin da suke tattaunawarsu.

Har aka sauke Tasleem, ba ta da walwala, ganin haka itama Humaira ta ja jikinta ko ki gaida gida ba ta ce mata ba.

A gidan Futuha, Wakin dai da ta taSa sauka wannan karon ma shi ne ya kasance masaukinta. Ta ajiye jakar kayanta ta faWa ta Wauro alwala ganin ana dab da kiran sallar magriba, sai a lokacin ta jawo waya ta kira yar uwarta Ummita. Suka Wan taSa hira don ta ?ara kwantar mata da hankali, cikin ikon Allah ma sai ta ga ko a muryarta babu wata damuwa. Koda ta ajiye ta kara tsunduma da tunanin Fadeel, wai me ya yi mata ne ma da har ta tsaneshi hakan? Oho, ta ba kanta amsa, sai kuma ta ja tsaki cikin jin zafin rai, to meye nata ma na tsayawa tunaninsa? Don haka sai ta mi?e ta shimfiWa darduma jin an soma kiraye-kirayen sallah. Koda ta idar sai da ta yi nafila sannan ta yi salati da istigfari. A karshe ta yi addu'a sosai. Sai kuma ta tsinci zuciyarta da yin wani sanyi tamkar an yayemata wata damuwar. Sabuwar wayarta ?irar Huawei da Abba ya dam?a musu bayan fitowarsu daga hannun ?an ta'adda ta yi ?ara sauti mai dadi shaidar shigowar sa?o. Ta Wauka ta duba.

*_Babu wata damuwa ko ba?in ciki da Allah ba zai iya magancewa Wan adam ita ba. Ki mi?a dukkan lamuranki gareshi, ki kusanceshi, zai kusanceki. Allah yana son masu ambatonsa safe, rana da kuma dare. Ina miki fatan alheri koyaushe._*

Ta karanta fiye da sau uku, ya yi mata dadi sosai, ta kuma kasa barin murmushi. Fadeel ne, koda babu suna a lambar tana da haddarta saboda kira na yau da gobe da yake yi kuma duk da ita ne. Ta sauke ajiyar zuciya, kwankwasa ?ofar da Futuha ta yi da shigowarta da sallama ya sanya ta ajiye wayar ta dube ta. Murmushi Futuha ta yi mata.

"Yauwa Humaira idan kin huta ki fito ki Webi abinci a kicin. Daga gobe za ki soma gwadawa Hafsatu yanda kike tsara abinci da komai, yau kinga sai ki huta ko? Ni zan shiga ciki ba lallai kuma mu haWu ba sai da safe."

Ita dai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login