Showing 120001 words to 123000 words out of 189325 words

Chapter 41 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

203

ki ka fita wajen Fadeel?!"
Kamar an Winke mata baki sai ta kasa cewa uffan yayinda Raihana ta yi caraf ta amsa.

"Mami na fadamaki fa kuma Abba yace Yaya Fadeel ya zama Wan gida tunda zai auri ?ar gida. Kiyi hakuri please ki daina jin haushinsa yanzu tunda har Sis Tasleem ma ta yi aurenta ta manta da shi."

Wani kallon banza Mamin ta watsamata, Anna da Jannat dai idaunsu kawai suka zuba ga Mamin saboda sun kasa yarda ita ce, a zu?atansu basu taSa jin sanyi cikinsa ba kamar yanzun musamman Anna da take ganin fuskar tsohuwar Mamin da ta sani a Agadez a na wannan. Mami kuwa kamar ta yi shiru sai ta yi tunanin watakila shirun nata ya tona ainahin abin da ke ranta musamman ma ga su Jannat ga Mubarak da suka zubamata idanu cikin hankalta. Don haka ta sauke ajiyar zuciya.

"Shikenan wuce ki shiga ciki ki sauya kaya. Anjima zamu yi magana."

Humaira wacce idanunta suka cicciko da hawaye ta gyaWa kai gami da mi?ewa ta bar falon tana ji kamar an muzanta ta. Haka ta koma Wakinsu cikin mutuwar jiki.

"Ke da Mami ko?"

Ummita ta wurga mata tambayar da ya sanya ta dubanta, tana daga zaune saman darduma bayan ta idar da salatin Annabi s.a.w. Kaf abin da ya faru tana ji daga inda take. ?an murmushin ya?e ta yi mata.

"Ban san kuskuren dake cikin nagartar Fadeel ba, watakila kuma sai yanzu da idanuna suka soma ganinsa da ?ima wata silar za ta raba mu ta nisanta mu da juna idan har hakan zai faranta ran Mami."

Girgiza kai Ummita ta yi.

"Ban ce ki bijirewa dukkan wani umarni na Mami ba, amma ki sani, ba Mami ce kaWai me iko a kanmu ba. Abba shi ne mafi ?arfin ikon zartarwa. Idan har Allah ya ?addara aure tsakaninku babu wani mahalu?i da zai iya dakatar da faruwar hakan. Mami hujjarta ba karSaSSiya ba ce, akan wane dalili don bai auri wata ba wacce dama tun farkon fari ba dominta ya ?ulla zumunta da gidannan ba, ace za a haramtawa wacce ba ta ji ba kuma ba ta gani ba abin da Allah bai haranta ma ta ba? Anan dai na raba fahimta da Mami."

Humaira ta sauke nannauyan ajiyar zuciya har a lokacin ba ta dauke idanu cikin na Ummita ba ta ce.

"Bana son sa?e-sa?en da zuciyata ta soma yimin akan Mami, iyakar ?arfina nake ?o?arin ?aryata tunanina Ummita sai dai hakan na nema ya faskara."

?an murmushi mai ciwo Ummita ta yi mata.

"Na fahimceki, ba kuma na son saka Mami a jerin masu son zuciya idan nayi haka kamar ban mata adalci ba duba da yanayin ri?on da ta yi mana na nuna fifiko akan yaranta na ciki. Sai dai a wannan gaSar bana goyon bayan hakan, ki toshe kunnuwanki Humaira. Fadeel mutumin kirki ne, a duniya ban da soyayyar iyayenki, zan iya rantse maki Fadeel ne masoyinki na gaske bayansu don ko mu ba lallai mu nuna mishi sonki ba. Ya sadaukar da lokacinsa duk a kanki, shekara da kusan watanni ya jure dukkan wulakanci da ba?a?en maganganun da sauran mazan da suke sonki da aure suka kasa jura suka kama hanyar gabansu, Fadeel ya cancanci ki aureshi. Ba fata nake maki ba amma muddin kika zama mai juya baya a gareshi da ?in yarda da shi, wallahi Humaira ha??insa ba zai bar ki ba."

Daidai wannan gaSar hawaye suka wanke fuskar Humaira, ta sani gaskiya Waya ita ce Ummita ta faWamata. Har haushin kanta take ji idan ta tuna yanda ya dinga ya bibiyarta a bainar jama'a tana yan?wana shi. Ya jure dukkan wannan ya kuma sadaukar da lokacinsa don kawai ya ga ta sauko don kanta ta aminta da shi, ita kuwa me zai sa ta butulce masa?

Daga haka Ummita ba ta ?ara ce mata uffan ba, ai ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali, don haka ta bar ta da tunani iri-iri a ?asan ranta.

***
A falon kuwa da fitar Humaira sai Jannat ta kwashe da dariya.

"Mamin yara kenan, yau kuma marainiyar Allahn ?ar gaban goshinki da ba ta laifi ita kike yiwa wannan Wibar albarkar?"

Mami ba ta ce uffan ba don har lokacin zuciyarta a zafafe take musamman da Jannat ta ala?anta Humaira da sunan ?ar gaban goshinta. Wannan ko a mafarki ba ta hangen haka.

"Mami, don Allah ki bar Humaira da Fadeel haka, idan har yanda Raihana ta ce sanadiyyar Tasleem ne. Yanzu Tasleem igiyoyi uku ne a kanta har da ?aruwar Baby da ta samu. Ni ban san dalilinki na hana ta kula matashi mai kirkinsa ba."

WaWannan zantukan su na fitowa kai tsaye daga bakin Mubarak, kafin ta tattaro amsar da za ta ba shi sai ga Futuha ta bankaWo labulen falon ta shigo a haukace tana wani irin kuka da sheshshe?a, ta ci uban ado an shafe fuska da Foundation amma sanadin kukan da ta sha duk sai ta koma kamar wata aljana. Ganin Mubarak a zaune bai sa ta bar ihu da kukan da ta fasa ba, gaba daya suka mi?e ita kuwa kai tsaye jikin Antinta Jannat ta faWa gami da ?ara sautin kuka da ihu. Wannan ya yi sanadin shigowar Abba falon don tun Wazun yake tsinkayar muryoyi a sama amma na yanzu ya fi duk na baya shiga kunnuwansa don haka ya shigo falon a hargitse. Ganinsa sai Anna ta Wan ja jiki ta koma ladabin ?arya kamar yanda ta saba yi a gabansa. Tsawa ya dakawa Futuha ba shiri ta kame bakinta ta yi shiru, Mami sam ba ta so zuwan Abban ba don zai iya lalata shirinta ya sa Futuha komawa dakin mijinta a yau. Ya kuwa jefowa Mamin tambayar abin da ke faruwa idanunsa ma ko kan Anna bai kai ba saboda tsoro da fargabar da ihun Futuha ya haifar masa. Mami ta Wan gyara murya ta ce.

"Ke Futuha sai kiyi masa bayani, wa?a a bakin mai ita ta fi dadi ai."

Futuha ta dubi Mami sannan ta maida kai ga Abba amma ta kasa cewa komai tsabar fargaba. Jannat ta yi kundunbala ta soma magana muryarta dauke da salon makirci, nan ta labartawa Abban ?arya da gaskiya akan ginin da Yakubu ya yiwa Futibar ya maida ta. Abba ya tamke fuska tamau, Jannat ba ta taSa ganin ya dube ta da tsantsar Sacin rai da rashin walwala ba sai a ranar.

"Shi ne me?"

Tambayar ta sa Jannat kasa cewa uffan, sai Mubarak ne ya yi caraf ya amsawa Abban.

"Shi ne ita kuma ta dawo gida ta ce ba za ta rayu a cikinsa ba."

Abba ya nuna Futuha da yatsa.

"Ke, ki saurare ni dakyau, ni dai ubanki Isuhu ina raye a kan idanuna ba za ki maida ni mutumin banza ba da bai san me yake yi ba. Kai Mubarak ka dauki mota ka maida ta ka kuma tabbatar ta shiga gidan aurenta kafin ka dawo gida. Ba zan Wauki wannan sakarcin wofin ba."

Anna tana so ta yi magana amma tana gudun zubewar girmanta a idanun Abba, girman da ta Soye ainahin zuciyarta ta danne komai ta shekara da shekaru wajen gina shi a idanun Abban don haka ta ja bakinta ta yi shiru, Jannat kuwa ta ?ulu iyakar ?uluwa. Balle kuma Mami da take jira Abban ya koma Sangarensa ta je su buga wacce za su buga don bai isa ba sai ya ?watarwa diyarta ?anci. Hakanan Futuha tana kuka ta bi bayan Mubarak suka tafi, a mota ganin ta cika shi da ihu ya dakamata tsawar da ta hargitsa ta, ya koma Mubarak Winsa sak da suke shakka, dole ta haWiye sauran kukan ta koma yinsa a ciki ciki yanda ba zai ji ba.

***
Ya kammala shirin baccinsa tsaf zuciyarsa duk a Sace saboda takaicin Futuha, haka Mami ta shigo tana Waure masa fuska, ya dube ta kadan kuma ya ba kansa cewa damuwar ce itama ke cinta wannan ya sa bai ce mata uffan ba. Sai da ta mula don kanta sannan ta magantu.

"Abban yara wane irin hukunci ne ka zartar akan al'amarin da ba ka ganewa idanunka zahiri ba?"

Da Wan mamaki ya juyo daga barin chajin da yake ?okarin sanyawa a wayar ya dube ta.

"Kika ce me?"

Ta kauda kai har lokacin fuskarta a daure ta amsa.

"Ai ka ji abin da nace. Fisabilillahi ta yaya yarinya za ta tashi cikin gida babba kamar haka, miji ya yaudareta ya soma kai ta wuri mai kyau daga baya kuma ya sauya mata muhalli zuwa ?as?antaccan wuri sannan ta dawo da kokenta ta sanar da mu amma mu kasa magance mata mu ?watar mata ha??inta? Wannan yanzu daidai ne a wurinka?"

Abba ya dan yi jim yana duban Mami, ya lura tun lokacin da suka tattauna a Wazun dangane da batun tsaida ranar auren Humaira da Fadeel take tattare da rashin walwala ya kuma fi kyautata zaton rashin sanar da ita kan lokaci ne ya jawo hakan amma kuma sabon zancen da ta yi a yanzun shi ya sa shi tunanin damuwarta kala biyu ne. Wato har da lamarin Futuha. Uzuri ya yi mata ganin bai taSa samun matsalar ja in ja da ita ba har kuwa a shekarun baya da ya je mata da batun ?arin aure. Can dai ya nisa ya ce
"Idan dai muhallin da diyarki take ciki shi ya zama dalilin Sacin ranki shikenan, gobe zan je naga gidan bisa adalcin da kika nema."

Duk da haka ba walwala ta dora ?orafinta na gaba.

"Sai na biyu, idan har ni Maryam kana yimin kallo na matsayin Uwa a wajen Humaira ba mari?iyarta ba, ka janye batun auren Fadeel da ita saboda ina da wanda na zaSa mata ya kasance abokin rayuwarta."

Maganar ta shiga kunnuwan Abba a bazata, sai da ya yi Wan shiru na lokaci kaWan yana jin muryar Mamin na masa amsa kuwwa cikin dodon kunne.

"Maryama, kinsan abin da kike faWi kuwa?"

Ta dube shi tsakar idanu, ta koma Maryam dinta ta Agadez sak wacce ba ta ragawa kowa balle kuma ganin kowa da ?ima ta ba shi amsa kanta tsaye.

"Yes Isuhu, ni Maryam na faWi na yiwa Humaira mijin aure. Idan kuma kana son nunamin ni ban isa da ita ba saboda ba ni ce uwarta ba toh bismillah."

*_Aikinki akan yarinyar ya Saci gaba Waya kuma ba komai ya jaza hakan ba face samun tsayayyen matashin da yake tsananin sonta kuma ya jajirce wajen yi mata addu'a da ma koyamata yanda za ta ?arfafa ibadunta.*_ *_Ina mai tabbatar maki Hajiya Maryam matukar kika bari auren Fadeel da Humaira ya afku toh ki tabbata rushewar dukkan tubalin ginin da kika dauki tsawon lokaci kina ginawa zai afku._*

WaWannan maganganun na Babandi su ne suka ?ara assasa wutar ?iyayyar Fadeel a zuciyarta, har shi din waye? Me ya taka da zai iya Sata mata Soyayyen shirinta? Yau dai gashinan a sanadiyyar ba?in nacinsa ya soma maida mata hannun agogo baya, ta soma fiddowa Abba ainahin kalar Maryam din da bai taSa sani ba. Daga sama ta ji muryar Abba.

"Ki faWi ?wakkwarar hujjarki koda kuwa guda Waya ne tak, ni kuma idan na duba ?arfinta na maki al?awarin zan yi yanda kika ce koda kuwa zan ji kunyar mutanen da bani da tamkarsu a yanzu wato iyayensa."

Kai tsaye ta ce.

"Saboda na yi mata miji, sannan ita kanta Humaira ba ta sonsa."

Cikin Wan haWe gira Abba ya ce.

"Wannan biyun da kika lissafo ba su da matsuguni Maryam, eh tabbas ke kike ri?e da Humaira kuma kin yi abin a jinjina maki kuma a ?ara sonki dominsa kamar yanda wannan ya ?ara siya maki daraja da ?ima da ma kauna a zuciyata, amma fa ki sani, ni ke da ha??in yiwa yarana zaSin miji kaf dinsu, soyayya kuma ina da tabbacin soyayyar da yaron ke yi gareta zai isa su rayu cikin aminci da kyautatawa. Ina kuma da tabbacin in sha Allahu koda a baya ta furta ba ta sonsa, a yanzun ko don irin halaccin da yake kan nuna mana shi da iyayensa, ta sauko daga dokin..."

"Ka ga Yusuf ya ishe ni hakanan! Na rantse maka muddin ba ka janye kudurin aurawa Fadeel Humaira ba ni Maryam ba zan ?ara kallonta da idanun rahama ba saboda ka nunamin ba ni na haife ta ba kuma ban isa na zartar da hukunci a kanta ba."

Ran Abba ya Saci, yau duniyar gaba daya ta yi masa ?unci. Wannan wane irin tashin hankali ne haka kuma daga wajen wacce bai taSa zato ba, wacce koyaushe sai dai ta kwantar masa da hankali idan ya shiga irin wannan yanayin. Meke faruwa ne haka?

"Wace irin ?iyayya kike yiwa Fadeel haka Maryama da har kika kasa tankwara zuciyarki ki san da wanda kike magana?"

Mami ta kasa tankawa saboda Wacin zuciya, ji take yi kamar ta sha?o wuyansa ta kashe shi ko ta huta da wannan zazzafar ?iyayyar da ta kwashi shekaru tana dannewa a ruhinta har sai da tura ta kai bango. Amma sai ta zaSi ta mi?e kawai ta fice ta bar masa dakin. Ranar dai haka suka kwana kowannensu a Sangarensa rai a Sace. Ga Abba mamaki da al'ajabi ne suka lulluSe shi, to ma waye mijin da take ikrarin ta yiwa Humairar? Shi Sacin rai ma bai sa ya tambaya ba saboda bai ga amfanin tambayar da amsarta ba lallai ya aiwatar ba. Ga Mami kuwa haka ta yi ta zarya a daki ga dare ya tsala babu damar kiran Hajiya Lubna don kai mata kokenta balle kuma Babandi da take shakkar kira kar ya ?ara sanar da ita wani abin shiga ruWanin da fargaba. Don haka sai ta ci alwashin sauyawa Humaira ko a fuska, a ganinta ko don kaunar da ta nuna mata a baya zai sa zuciyar yarinyar ta russuna ta hakura da Fadeel ita kuma za ta yi tunanin wanda ya dace ya yi daidai da Humairar su haWa kafaWa a wurin aure amma ba tsara ko fiye ma da mazajen da yaranta ke aure ba.

***
Abba kuwa ya cika alkawari domin duk da irin bacin ran da Mami ta ?unsa mishi a daren jiya sai da washegari ya wanki ?afa bayan sanar da Yakubu mijin Futuha (wanda ya cilla Abuja saboda yasan za a rina) ya yiwa gidan diyartasa tsinke tare da Mubarak da ya yi masa jagoranci. Ya tarar da mata kusan su biyar cikin shiga ta alfarma sai baza ?amshi suke su na ta bugu amma ko gezau kamar babu rai a gidan. Ganin dattijon mutum bai sa sun damu da gaida shi ba, gogaggun ?an duniya ne daga kallo daya sai faman yatsina fuska suke ana taunar cingam har Waya na fadin kodai ba nan ne gidan Futuhar Tiktok ba? Sunan da Abba ya ji sun fadi ya yi matu?ar ba shi mamaki, wato dai Futuha har yanzu tana sharafinta a sosha midiya kenan duk da ya hana? Mubarak kuwa da yake tun sadda zai yi jarrabawar karshe ya raba kansa da soshal midiya ya sa ko bayan dawowarsa bai damu da leka Tiktok ba kamar yanda bude buden status ba Wabi'arsa ba ce hakan ya ?ara dalilin da bai san me Futuhar ke shukawa ba.

Kai tsaye Abba ya kira ta a waya, ta amsa da murya ciki-ciki don sosai Abban ke ba ta haushi. Ya ba ta umarnin lallai ta zo ta bude masa ?ofa yana tsaye a bakin kyaurenta. Jin haka hankalinta ya tashi, ga kuma matan Tiktok da suka yi cirko-cirko a gaban gidanta su na jira ta bude, ta rasa uban wa ya ba su adireshin gidanta kuma cikinsu har da ?ar Snow don ta dauki muryarta ta kuma ji an ambaci sunanta. Babu yanda ta iya hakanan ta bude kyauren cikin rawar jiki.

"Don ubanki shi ne kika shanya mu muna ta buga maki ?yauren gida? Lallai ai dole ki kasa buWe mana ?yauren saboda kin gama cika shegen baki kin yi mana kurin gida. Toh bari mu shiga mu ga uwar dake cikin gidan mu yiwa jama'a bidiyo."

Duk wannan zantukan na fitowa daga bakin ?ar Snow kuma kishiyarta mai zuwa, da kissa da kisisina ta samu Yakubu ya ba ta kwatancen gidan da zummar za ta je taya ta murna.

Abba ya yi shiru ya kasa magana kamsa har wani sarawa yake yi, wannan tashin hankalin har ina? ?arka ta jawo an zageka a gaban idanunka? Mubarak kuwa da ya zo wuya ya daka musu tsawa da ba su umarnin barin wajen tun suna shaida juna. Kasancewarsu tsageru suka hau duramasa ashariya yayinda ?ar Snow ta bude motarta ta shiga tana masa zagi na uwa da uba, Abba ne ya dakatar da shi daga tankawa har suka ja motarsu suka bar wajen. Futuha kuwa kuka sosai take yi, duk rashin kirki da mutuncinta ba za ta so a zagi iyayenta ba. Yau gashinan sanadiyyarta an zage Abbanta tas a kan idanunsa. Abba ya dago ya dubeta da idanunsa da suka kaWa, sai kuma ya kada kai ya juya ya nufi mota bayan ya ba Mubarak umarnin ya zo su wuce kar yace mata komai saboda makwafta da kuma masu wucewa duk sun fito gulma har da matan aure. Tun a hanya kirjin Abba ya yi wani irin nauyi da zafi, nan da nan kuwa idanunsa suka soma kakkafewa hakan ya yi mugun tashin hankalin Mubarak kai tsaye ya nufi asibiti da shi. Sai da aka shawo kansa ya dawo hayyacinsa kafin ya kira gida ya sanar da Mami. Hankalinta ya tashi, ko babu komai duk da irin guma mata da ya yi tana son abinta, dalilinsa ne ta aikata duk abin da ta aikata a rayuwa hankali tashe ta sanar da mutan gidan ta yi shirin tafiya.

"Mami ina iya binku?"

Wani banzan kallo Humaira ta samu daga Mamin wanda ya kara sanyata shan jinin jikinta amma tana ji a ranta duk runtsi duk wuya ba za ta iya rayuwa babu Fadeel ba. Ta kara jinsa a rai musamman da ta yi istihara a kan lamarinsa bisa shawarar shi kansa Fadeel din da ya kirata a daren ta kara jin ta samu nutsuwa da lamarinsa. Wannan ya sa ta nufi dakinsu ta a hawayen ciwon Abba da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login