Showing 48001 words to 51000 words out of 189325 words

Chapter 17 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

240

ja tsaki ya fi a ?irga a hanya har ta ?arasa Wakinta.

***
Azumi yana ta tafiya har a yau sun kai goma sha shida, lamarin su Tasleem da Abba ya ?ara tsauri musamman da ya fahimci ba su bi zancensa ba na shiga kicin. Futuhar da ta soma shiga, tun bayan faWan da Abban ya yi ya goyi bayan Humaira sai ba ta ?ara le?awa ba. Cikin ikon Allah wataran kwatsam sai ga shi a kicin din abin da Humaira za ta ce tun zuwanta gidan banda ranar da ya ji fitar gas ya cika gidan ya shigo, ba ta taSa ganinsa a ciki ba. Ganin daga ita sai Ladidi da Ummita a kicin din ya shiga bambamin faWa, a sannan Raihana na fama da Malaria mai zafi har allurai ta sha. Aikuwa har Wakin ya shiga ya titsa ?eyar Tasleem da Futuha zuwa kicin din yana gargadin Humaira akan lallai duk sadda ba su shiga ba ta sanar mishi. Tun daga wannan ranar ba su ?ara fashin shiga ba. Sai dai shigar da rashinsa ba amfani don kusan zama suke yi kawai ba sa komai.
Abba ya yi siyayyar kayan sallah, kamar kowace shekara wannan ma da kansa ya yiwa kowa zaSi idan ka cire samarin da ya ba kowannensu kudi su siya shadda. Yanmatan kuwa atamfa ce iri Waya sai dai bambancin kala, sai dubu uku da ya ba kowace budurwa a siya takalmin sallah. Shikenan bai ?ara daga haka ba, su Futuha aka dinga kauWi ganin Alhajinta ya kawo mata shadda da atamfa har da leshi masu tsada sai kuwa dubu ashirin na mayafi da jaka da kuma Wan kunne. Tasleem kuwa dayake ta soma sha?a sai ta budewa Hamza wuta akan ko kyautar biyar bai taSa ratsawa tsakaninsu ba. Ranar shi kansa ya yi mamaki da ta iya karya bille ta tambaye shi kuWi, aikuwa ya ce ta turo acc no, take ya yi mata transfer dubu goma sha biyar. Tsabar rainin da ta yiwa kyautar ko faWawa su Mami ba ta yi ba sai dai sun mata amfani ta siya abin da take so. Su Humaira kuwa Mami da kanta ta kara musu dinki, leshi mai kyau na Wankwarai ta siya musu su uku kala Waya. Ana saura kwana biyar sallah sai ga Anti Jannat a gidan. Zuwanta ya yiwa su Futuha daWi ko ba komai mace ce mai sakin bakin aljihu ga fankama. Burinta ta buWa ko don ta nunawa Mami ita fa mijinta mai bayarwa ne, yana da kyauta sosai. Daidai da Anna ta fi ji da ita, abinda ya hana ta zama wajen Jannat din bai wuce na ganin surukanta sun nuna ba su kaunar hakan ba. A farko ta gwada amma aka so samun matsala, dole ta tattara ta dawo gidan da ta raina, gidan Abba.
Suna zaune a Waki bayan sun kammala gwada dinkunansu na sallah, ya yi musu cif da cif, washegari kuma sai tafiya kitso da ?unshi. Sai faman tsokanar Ummita suke yi ganin saurayinta ya kira tana kashe murya a waya, koda ta ajiye Raihana ta dube ta.

"Wai ni yaushe za ki ba Ya Sayyadi damar zuwa gidannan?"

Kasancewar zuwa lokacin sun sani ba kowa Ummitan ke soyayya da shi ba face Ya Sayyadinsu na makaranta hakan yasa suka samu abin tsokanarta. Ashe wai dama yawan tashinta da yake yi ta biya musu karatu mai dalili ne. Ummita ta Wan harareta.

"Ke me ya hana ki ba Jafar daman zuwa gida? Ni ai mun kashe magana da shi, na ce ya bari sai nan da shekaru biyu ko ma ince Waya da rabi idan mun yi candy, tunda yanzu muna SS2."

"Kai Ummita, shekara Waya da rabi fa? Gaskiya sun yi yawa ina laifin ma shekara Waya?" FaWin Humaira dake tsaye tana maida kayanta sif. Raihana ta tari numfashinta da sauri ta ce.

"Wai ke ce mai yiwa wata faWan shekaru sun yi yawa? Allah ya ba Fadeel hakuri. Wallahi idan na tuna abinda kika yi masa sai na ji kamar na yi maki dukan tsiya."

Ummita ma kwafa ta yi cikin kunar rai ta ce.

"Bar ta kawai Raihana, nima ba ki ji raina ba. Kuma babu kunya ba tsoron Allah har faWamana take yi ya hakura sai nan da shekara. Shi marar zuciyar ina ne da zai biyemaki ya yi zaman jiranki? Ai tana sane, kora da hali ne kawai ta yi mishi. Ba fata nake maki ba, amma wallahi kafin ki samu kamar Fadeel a maza sai dai tsananin rabo."

Humaira ta taSe baki gami da jan guntun tsaki.

"Kanku ake ji, ni na faWamaku ina so nayi auren ne? Auren ku yake burgewa ba ni ba. Sai me? Idan ba auren zan fasa rayuwata yanda ya kamata ne? Ya yi ma gangancin zaman jirana ya gani idan ha?ansa zai cimma ruwa. Ya ?are rayuwarsa a tuzuru."

"Allah ya kiyaye wallahi, bakinki ya sari Wanyen kashi. Fadeel ya wuce nan, kuma ina masa fatan alheri, ya samu haWaWWiyar da ta fi ki komai ?ar kwalisa in sha Allahu." Cewar Raihana.

Haka kawai sai ta ji zafi a ranta, ta ji tana son yin kukan da ta rasa dalili, kawai sai ta fashe da kukan ba tare da ta yi shawara da zuciyarta ba. Raihana ta dubi Ummita kafin su dube ta jiki a sanyaye. Tun tana kukan su na ganin kamar wasa su na rarrashinta, har dai suka ga kamar kukan ba na lafiya ba ne suka fita da sauri suka yiwa Mami magana. Kai abin tsoro Humaira duk iyakar rarrashin Mami ba ta yi shiru ba, hakanan harafi Waya ya kasa fita a bakinta. Mami ta juya garesu.

"Meyafaru ta soma kukan?" Nan suka ba ta labarin komai, ta ja hannun Humaira kawai suka fice a Wakin. Su Raihana za su biyo bayansu ta dakatar da su, can falo suka tsaya yayinda Mamin ta shige Waki da ita. Sun yi jugum kuma sai ga Mamin ta fito ta dube su ranta a Sace.

"Don me za ku dinga yi mata batun saurayin da ba ta so?! Ina gargadinku daga rana irin ta yau koda wasa kada wanda ya kara kuskuren ko ambaton sunansa balle ya yi mata zancensa. Fadeel ko? Daga yau sunan nan ya fice a bakinku." Suka ce toh, su ma abin ya tsorata su, sun kuma kara gaskata zancensu, Humaira na da aljanu musamman da suka ji Mami ta mike tana fadin wai ta samu bacci idan ta tashi komai zai wuce a ranta. Tabbas zarginsu ya tabbata gaskiya, aikuwa ga mamaki Humaira sumul ta tashi tamkar babu abin da ya faru. Yanda ba ta yi zancen ba hakanan su ma ba su kara tada shi ba. Ba ma kamar Raihana mai shegen tsoron aljanu, Ummita sai dariya take mata ciki-ciki ganin ko zama kusa da Humairar ta Wan rage yi a ranar. A gefe guda kuma ta yi al?awarin muddin ta je Bichi za ta yiwa mijin yar uwar mahaifiyarta magana akan lamarin Humaira, yana ba da hayaki da maganin jinnu, in sha Allahu za ta karSo mata.
***
*LITTAFIN NAN NA KU?I NE. SIYA AKAN NAIRA ? 400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645




Ibb ya mike tsaye yana safa da marwa kafin ya naushi bango a zuciye ya juya ya nuna Fadeel da yatsa.

"Wai kai wace irin soyayya ce wannan da ba ta da mafaWi? Wace irin soyayya ce mai neman kai ka ga halaka?"

Murja wacce ke shirin kwankwasa ?ofar Wakin don ta mi?a musu fruitsalad da ta haWa ta tsaya cak jin abin da ke fitowa daga bakin Ibb, kirjinta har wani lugude ya ke yi.

Fadeel kuwa jin an danganta soyayyarsa da sunan halaka ya Wan Wago idanu dakyar ya dubi Ibb sanadiyyar ciwon kai da ya wuni da shi ga azumi a baki. Ibb ya kara jaddada masa furucinsa.

"Yes halaka mana, mutumin da ya amince da zaman jiran gawon shanu alhalin yana da damarmaki da yawa da ma ?anmata masu ilimi da aji da ke rububin ya amince ya aure su ai kuwa ya jefa kansa a halaka tunda wacce ya ke zaman jiran kora da hali ta yi mishi. Fadeel wake up, ka runtse idanunka da kyau ka fahimci yarinyar nan kora da hali ta ke maka, ba soyayya ba ce. Ba ta sonka, a wautarta lokacin da ta Wibarmaka zai sa ka ?osa har ka gaji ka sauya she?a amma ba ta san yanda ka mace a kanta ba, ka shirya aikata komai! Toh ni abin ya ishe ni, zan je na sanar da Alhaji komai a je a nema maka aurenta."

Fadeel dai ya yi shiru kawai yana cigaba da kurSar ruwan shayi don? ba su jima da shan ruwa ba. Jin maganar tunkarar Alhaji ya sanya shi Wago kai ya daure fuska.

"Ban saka ba Malam, kar ka sake ka aikata wannan gangancin. Ba za ka taSa fahimtar ya nake jin Humaira ba, ni dai na yarda ita Win mahaWi ce ga rayuwata. Kai duk fa son da za ku yimin ba zai kai yanda ni nake son kaina ba, tun farkon ganina da ita nake addu'ar neman zaSin Allah amma daidai da sakan guda ban ji ta sauya a raina ba. Ni dai na sani, ina mata so ba iyaka wanda nake da tabbacin ko ba ta sona, nawa son ya yi ?arfi da isar da zai wadace mu gudanar da kyakkyawar rayuwar aure, na koyar da ita yanda za ta fara sona. Ballantana kuma ina ji a jikina tana kaunata."

Tsaki Ibb ya ja ya koma ya zauna, tabbas ya ji daWin dawowar Wan uwansa wajensu, amma ya yi danasanin haWuwar da suka yi da Humaira. A can ?asan ransa tausayinsa ne lulluSe, son maso wani akwai wahala. Don haka sai kawai ya ja bakinsa bai kara cewa uffan ba ya tsiyayi ruwa mai sanyi a kofi ya soma kurSa.

Daga can bakin ?ofa kuwa, Murja tuni tsayuwar ta gagareta, don haka ta ja ?afafunta da suka yi mata nauyi ta bar wajen cikin sauri ba tare da ta mi?a musu abin da ta kawo ba. Dama na gulma ne ta kirkiri aikinsa don kanta kawai domin ta burge Fadeel, daga abin da ta ji yanzu ta fahimci babu abin da za ta yi ta burge shi tunda ya makance har haka a san wata banza wacce take da ya?inin ba lallai ta fi ta kyawun zubin jiki ba. Kafin ta karasa falon Anti Amarya idanunta sun yi jage-jage da ruwan hawaye, ta gifta yaran ta shige Wakin da kusan yanzun ya zama mallakinta bayan ta ajiye kwanon fruitsalad a falo gami da ba su umarnin shanyewa idan su na so. Kuka sosai ta fashe da shi, babu kalamin da yake mata ba?i kamar na jin da ta yi Fadeel na ambaton wata Wiya mace da sunan so har yana ikrarin wai yana mata son da ya ishe su rayuwar aure koda ita ba ta sonsa. Ta nanata sunan a ?asan zuciya, wato Humaira. Sai ta yi ?wafa gami da tsaida kukanta, a fili ta ce.

"Fadeel muddin ina numfashi sai na mallake ka a rayuwa koda ace hakan na nufin na Satar da Humaira a doron ?asa."

Wannan shi ne al?awarin da ta Waukarwa kanta.

***
A daren da aka yi shelar ganin wata kowa ya tashi da farin ciki da walwala. Humaira tuni sun sha kitso da ?unshi abinsu, a wannan daren wuni ta yi a kicin tare da Ummita su na aiki ita kuwa Raihana tana can falo tana taimakawa Tasleem jera stones a atamfarta da tela bai samu damar yi ba. Shirin waina, sinasir da miyar taushe ake yi, tun safe suke aiki inda Humaira ta yi snacks har kala hudu, samosa, springrolls sai meatpie da cincin. Ko kusa ba ta huta ba, wata iriyar gajiya ce tattare da ita dukkan gaSSanta ciwo suke, kusan ita kadai da Ladidi ne karfin aikin don Ummita ba ta zauna ba, tana kula da yaran Anti Jannat, ko mintuna biyar ba ta yi a kicin din take kiranta ta sanya ta aiki. Dahuwar indomie, haWa cornflakes, wankin kashi da sauransu.
Ita kuwa Futuha ta tare can sashin Anna wajen Anti Jannat suna hira kamar ba gobe. Mami sai dai ta le?o ta bita da sannu ta kuma ga yanayin tafiyar aikin sannan ta koma. A wannan daren ba ita ta bar kicin ba sai wuraren karfe Waya da mintoci. Da asuba dakyar ta tashi ta yi sallah ta faWa kicin aikin suyan waina. Kasancewar Ladidi a gidan ta kwana bisa umarnin Mami ya sa ta kama mata. Sai dai duk da gajiyar dake tattare da ita, ranta fari sol, kowa ya san irin murna da farin ciki da bayi ke tsintar kansu ciki idan aka ce yau sallah. Wannan murnar ne ya Wan ?ara mata kuzari, kafin dai zuwa karfe takwas sun yi sun kammala. A gaggauce ta sanya zuba komai kamar yanda Mami ta umarce ta, ta dauki na Abba za ta kai sai ga Ummita wacce ta tsaya shirya yaran Anti Jannat ta shigo tana mata sannu. Ta karSa ta ?arasa da shi. Ya yi daidai da fitowar Mami wacce ta ci adonta cikin doguwar rigar atamfa dinkin three-quarter da zani, peach colour ya sha adon stones. Ta yi kyau sosai abinka da farar fata. Humaira ta gaishe ta, fuska a sake Mamin ta amsa tana mata sannu da aiki.

"Kin yi kyau sosai Mami."

Ta yi ?ar dariya.

"Nagode. Muje na ga aikin naki sai ki je ki shirya."

Ta amsa da toh, suka koma kicin ta bubbuWa tana jinjina kai. Cike da farin ciki ta dube ta.

"Girki ya yi kyau Humaira, na kuma sani a baki ma zai fi haka. Sann???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?u da aiki. Ladidi kun sha aiki, Allah ya bada lada."

Ladidi dake tsaye tana Wan tattara kwanuka ta amsa fuska a sake. Daga haka Mami ta juya itama ta bi bayanta. Dakinsu ta nufa, tun kafin ta karasa ta ji ?amshi iri-iri na turare yana busowa. Hakan sam bai burgeta ba don ta sani Futuha ce da wannan aikin, yarinyar babu ruwanta da haramcin fesa turare mai ?arfi ita kusan ma turaren maza ya fi burgeta akan masu sanyin ?amshi marasa ?arfi. Futuha ce kuwa tana tsaye an ci ado cikin atamfarta super mai kyau sky blue da ratsin fari da ruwan toka mara turuwa cikin wanda Alhaji ya kawomata, ta yafa blue mayafi mai kauri da girma kasancewar sallah za ta je yi sai takalminta mai shegen tsini shi kuma ba?i. Ko mahassadi ya sani ta yi kyau sosai, sai hotuna take Wauka tana cuno baki. Ita kuwa Tasleem bata kai ga zuwa kayan ba tana tsaye gaban madubi tana gyara fuskarta, Allah ya taimaka an kwana da wutar nepa kuma an wayi gari da shi. A gajiye take likis, ta zauna gefen gado zaman jiran fitowar Raihana daga wanka, babu wanda ya ce mata ci kanki kamar yanda ita Win ma ba ta kula su ba. Tun tsawatarwar Abba ta samu suka sakarmata mara kaWan, duk da a wasu lokutan ana bin ta da ba?ar magana ko kuma kallon banza amma ko kallo ba su ishe ta ba. Su din ma ba kasafai yanzun suke shiga harkarta ba, sun fi maida hankali a hirar bikinsu. Kusan kullum sai an shiga instagram an ga tsarin bikin ?an ?arya ana cewa irinsa za a yi, ko kuma kayan amaryar sun yi kyau shi za su yi.
? ?? Har ta soma buga hamma bacci na son kwasarta sai ga Raihana ta fito, ta mike Raihana na mata sannu da aiki ta amsa ta Wau zanin wankanta ta shige. Tana fitowa ta hau shiri, itama Ummita tuni ta yi wanka kafin ta ta je shirya yaran Anti Jannat don haka tana shigowa shirin ta hau yi. Atamfarsu na wurin Abba suka sanya. Sun yi kyau abinsu tsaf kowacce da jilbab wanda ya hau da kayanta. Humaira kalar maroon ne nata, ya fito da farar fatarta sosai ta yi kyau sai rama da fuskarta ta yi ba ma ita kadai ba, dukkansu babu wanda bai rame ba a watan azumi. Itama Ummita ta yi kyau tsaf cikin jan hijabinta mai haske, sai kuwa Raihana da nata brown. Sun yi kyau gaba Wayansu. Fararen ?a?an Mami kamar wasu larabawa. Haka suka jera har su Muhsin da Waleed da suka sha adon babban riga farare tas zuwa farfajiyar gidan. Nan ma su Yassar ne ke faman Waukar hoto hannun kowannensu sa?ale da darduma. Yaran Jannat ma har da su, mota uku suka yi har da motar Jannat wanda mijinta ya siyamata tun kafin kamawar watan azumi kafin su iso gari saboda zirga-zirga da yaransa. Kasancewar ta iya tu?i ita ta shiga su Futuha abokan hirarta suka shige motarta sai kuwa yaranta. Ummita da Humaira su na tare da Mami sai motar Abba da matasan yaransa ke ciki. Haka suka jera zuwa masallacin idi kasancewar akwai tazara da gidansu. A mota Jannat suka yiwa Raihana caa akan yanda take shigewa harkar Humaira da Ummita, ita dai ta hademusu rai kawai ta ?i cewa uffan. Bayan sun yi parking suka karasa da ?afa.
?? Koda suka isa gida nan kuma aka tsaya yin hotuna a farfajiyar gidan, anan ne Raihana ta dinga yiwa Humaira hotuna kala-kala, ita kaWai ta san me take niyyar yi. Ta kuma ranta sai ta aiwatar. Suna kammala cin abinci ana santin girkin Humaira, Abban da bai fiye kyauta ba shi ne har da ba Humaira dubu uku barka da sallah sakamakon girkin da ya yi mishi dadi sosai. Mami ta zuba na makwafta aka mi?a. Humaira ta ji dadi kwarai na yanda kowa ya ci sai ya yaba, hakanan abokanan su Yassar har da neman ?ari. Ita dai tana kammala ci ta yi daki ta sauya kaya zuwa doguwar riga marar nauyi ta shimfiWe a gado ta hau ramuwar bacci. A sannan ne Raihana ta shigo ta dauki wayarta dake a gefenta ta fice zuwa falon.
Ummita da ta kammala tattara falon ta dube ta.

"Ke kuma me kike shirin yi da wayarta?"

Ta yi murmushi ba tare da ta kalleta ba ta amsa.

"Lambar masoyinta zan Wauka na turamasa hotunanta. Ko ba komai zai rage zafin takunkumin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login