Showing 96001 words to 99000 words out of 189325 words

Chapter 33 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

207

fashewa da kuka mai tsuma zuciya.

"Dama na sani Yusuf, watarana sai ka ga gazawata akan yarannan duk kuwa da..."

"Haba Maryama, don Allah don Annabi s.a.w ki yi hakuri. Wallahi zafin bacin rai da damuwa da tashin hankali ne ya sanya ni wannan maganganun marasa kyawun ji. Ko daidai da kiftawar ido ban taSa kawowa za ki cutar da wani a cikin yaran da kika haifa a cikinki ba ma balle a kai ga Ummita. Yarinyar da kika daukaka ta kika kuma ri?e ta hannu bibbiyu tamkar ke kika haife ta a cikinki. Wane irin butulu ne ni da zan yi maki haka? Ki yafemin domin Allah. Na tuba kiyi min uzurin halin rudani da tashin hankalin da na tsinci kaina ciki."

Mami ta mike ta ja guntun tsaki ya yi saurin tarar gabanta.

"Haba Maryama, da wanne kike so na ji ne? Da tashin hankalin nan na Ummita ko kuwa da Sacin ranki? FaWamin, me kike so nayi ki huce?"

Jin haka sai kuma ta yi shiru tana goge fuska.

"Kar ka ?ara irin wadannan kalaman naka na rashin tawakkali."

Ya yi murmushin karfin hali ya rungumeta.

"Idan har wannan ne ba zan kara ba. Na ma yi istigfari tun sadda kika ankarar da ni kurena. Mu ji da damuwa daya yanzu."

Ta gyada kai, bandaki ta shiga ta Wora alwala ta sanya hijabi ta hau saman darduma. Sosai yake jin so da kaunarta a zuciyarsa. Shima sai ya fasa neman wuri ya kwanta kamar yanda ya so duk kuwa da irin sakensa a ibada lokuta da dama. Kusan wannan shi ne kadan daga inda ya kuskuro, rashin tsayawa kai da fata wurin ibada sosai sai idan ya fada matsala babba.

***
Washegari tashin hankalin da suka riski kansu ciki sai ya mantar da su wani batun zuwa kai Humaira asibiti.
Gidan ya zama tamkar gidan makoki. Suna zaune jigum suna jira Mami da Ummita su fita daga bandaki don sanin matsayar Ummita, akwai cikin ko babu. Abba ya kasa fita kasuwa si safa da marwa yake a falon balle kuma Raihana wacce tun jin abinda ke faruwa ta kasa motsawa ballantana ta wuce makaranta. Sai Humaira da ta dau carbi tana jin tamkar an yi mata mutuwa. Mubarak kuwa wanda shi ya fita ya siyo abin awon cikin, sai ya jingina jikin bangon falon ya yi shiru cikin bugun zuciya.
A wannan yanayin Mami ta fito a gigice kuma a guje, gaba daya suka yi kanta har suna rige-rige.
"Meke faruwa?" FaWin Abba yana jin kamar ya kife tsabar jiri.

Mami ta fashe da kuka.

"Mun shiga uku! Shikenan Abban yara asirinmu zai tonu. Ciki ne da Ummita."

Abba ya ja baya da sauri ya zauna saman kujera mafi kusa da inda yake, yayinda Humaira ta yi mutuwar tsaye. Ita kuwa Raihana kwasa ta yi a guje zuwa bandakin don ganin halin da Ummitan ke ciki. Aikuwa ta iske ta a kife tamkar babu numfashi. Ta kuwa ?walla ihun kiran sunan Abba. Kusan da rige-rige suka shiga banWakin. Mubarak ne ya yi ta maza ya cicciSe ta bayan ya tabbatar da bugun zuciyarta ya fiddo ta falon ya shimfiWe saman kujera sai dai duk wani kokari na watsa ruwa da ma sauransu anyi amma babu alamun Ummita ta san ana yi. Ana shirin fita asibiti Mami ta dakatar ta ce gwara a kira makwafciyarsu wata likita gudun fashewar zancen a duniya. Abba ya yi na'am, Mubarak ne ya fita da rawar jiki har gidan Dakta Inteesar an ci saa kuwa ta fito cikin shirin tafiya asibiti. Ganin Mubarak aboki ga babban Wan ta Najeeb ya sanya ta dakatawa. Ro?on da ya hau yi mata ya sa ba ta iya yi mishi musu ba sai ta shiga motarta suka kama hanyar gidan don akwai ?ar tazara kaWan ita daga bayansu take. Cikin ikon Allah ta ba Ummita taimakon gaggawa ta farfado sai kuma ta dube su.

"Ya dace a yi mata gwaji sosai din tabbatar da abin da ke damunta."

Ta furta hakan ta yi shiru don jin me za su ce, a matsayinta na likita ta gama tabbatarwa Ummita na da juna biyu. Shiru ta yi musu don ta fi son ji daga bakinsu sun amince da gwajin. Tana sane da labarin abinda ya afku ga Ummita. Su kansu mutanen gida ba su da masaniyar cewa duk yadda suka so da Soye labarin fyaWen Ummitan sai da ya fita ba. A duniyar yanzun ai mutum ake kiwo ba dabba ba, kana abu kana ganin tamkar duniya ba ta sani ba amma zirr ake kallonka.

Abba ya yi ya?e.

"Babu damuwa Dakta, zamu kai ta asibiti."

Ta lura ba su son zancen ya fasu, ita kanta ta tausaya musu babu kamar Ummita wacce tunda ta farfado uffan ba ta ce ba, kukan ma ta ?i yinsa sai sauke ajiyar zuciya akai-akai. Haka Dakta Inteesar ta yi musu sallama bayan ta rubuta magungunan da ya dace wanda take da tabbacin zai taimaki Ummita bisa yanayinta na mai juna biyu. Mubarak wanda ke tsaye ya ?urawa Ummita idanu yana jin abu mai nauyi na taso mishi wanda ya fi kama da tsabar tausayinta da kuma kauna ta ?an uwantaka.? Kamar dai yanda yake tunani. Shi ne ya karSi takardar magungunan ya fice.

***
Kwance yake idanunsa a lumshe, babu komai a ransa sai Humaira. Yana ji a jikinsa an soma zuwa gaSar da yake da tsananin bu?atar kasancewarsu tare a inuwar aure. Shi din fa ba dutse ba ne, namiji ne kuma lafiyye da yake bu?atar aure. Soyayya mai ?arfin da yake yiwa Humaira shi ne silar da ya danne wannan bu?atuwar ya Wora shi kacokam a kanta yana jiran lokacin da mafarkinsa zai tabbata. Sai dai kuma yaushe ne?

Wannan damuwar ce ta hana shi fita ko'ina, hatta da mai gyara mishi dakuna bai san yana nan ba, shi dai Nura yana falo yana aiki kafin ya shiga Wakin. Hatta shi bai dan cewa Fadeel na gidan ba sakamakon motarsa da ba ta nan tun daren jiya. ?aci ta yi a hanya ya bar ta can? makanikinsa ya je ya Wauka.

Daidai lokacin Murja ta faWo Wakin da ?unshin kayan gugan Fadeel din a hannunta wanda ta karSa a hannun Sadi mai gugansu, dama? ta jima a yar barandar da zau sada ta da Wakin Fadeel tana tunanin dabarar da za ta yi wa Lawal ta shiga. Sai ko ga Sadi ya zo wucewa nan da nan ta karSa ta ce za ta karasa da shi.

Suka gaisa da Lawal a falo, ta nuna zai karSa ya shigar da su ta ce masa ya bar shi za ta karasa ladanta. Bai ce komai ba, dama a farko gargadin da Fadeel din ya yi mishi ne ya sanya shi dakatar da ita, ya hana kowa ya shigo masa sashinsa idan ba ya nan matukar dai ba Fu'ad ko Alhaji da Ibb bane. Amma ganin kayan wankin ne kawai za ta ajiye ta fito ya sanya shi ba ta wuri shi kuma ya ci gaba da kakkaSe kakkaben kujeru da kayan kallo.

A lokacin da ta shiga dakin, Fadeel ya zagaya bandaki, yana dab da fitowa ya ji motsin mutum a dakinnasa, bai kawo kowa ba sai Lawal. Ya san ba shi da masaniyar yana gida bai fita ba. Don haka ya fito daga shi sai singilet da dogon wandon sport.

Daidai lokacin da ta ajiye kayan a gefe ta yi wurgi da filo ta Waga katifar gaba Waya da zummar sanya layar. Kasancewar idanunta ya rufe ko kadan ba ta ga wayoyin Fadeel din dake gefe ba a ajiye. Tana zuci-zucin ta yi ta ?are kafin shigowar Lawal ya isketa.

Fadeel ya bude kofar ya fito, hakan ba? karamin razanata ya yi ba ta saki layun dake a hannunta suka zube a ?asan darduma. Mamaki mai tsanani ya kama shi har ya bude baki ya kasa magana. Ya karasa sosai ya kara kallo, tabbas layu ne. Nan da nan ya tamke fuska tamkar bai taSa wani abu wai shi dariya ba.

"Zamanki a gidannan ya ?are. Wallahi kin ji na rantse maki ko yau Anti Amarya ce ta haifeki dole ki bar gidannan. Ni Fadeel na fi ?arfinki, na kuma fi karfin duk wani da zai sanyaki aikata mugun abu don ki ci galaba a kaina."

Jin haka sai kawai ta hau tsuma da borin kunya.

"Ni..nifa ba.."

"Shut up!"

Tsawar da ya yi ya sanya Lawal faWowa Wakin. Nan da nan hankalinsa ya tashi, shima idanunsa suka sauka kan layar dake ajiye a tsakar dakin. Fadeel ya hau shi da faWan don me ya bari ta shigo masa daki alhalin ya gargaWeshi.

"Ka yi hakuri YallaSai, wallahi na yi nayi da ita ta bani kayan gugar na kawo ta nunan ita za ta kai. Shi ne.."

"Shi ne me?!"

Fadeel a zafafe ya tari numfashinsa jikinsa har Sari yake yi ga tsikar jikinsa da ya tashi gaba daya. Abin da ya faru shekarun baya kawai ya fadomasa a rai, sadda ya kama? Mamar Fu'ad tsamo tsamo a Wakin Mahaifiyarsa tana barbaWa magani. Daga ranar ya tsane ta, rashin wayo da wauta kuma ya sanya bai yi tunanin sharewa ba. Tun daga kuma sadda mahaifiyarsa ta taka wannan magani ba ta ?ara zaman lafiya ba da Alhajinsu, har dai a karshe Alhaji ya yi mata sakin wulakanci. Shi kuma ya sha ba?ar wahala a hannun Mamar Fu'ad. Ya ji ya ?ara tsanar Murja ninkin ba ninkin. Kuma yanda ya rantse ba zai yi kaffara ba sai Murja ta bar masa gida ubansa idan ko Alhaji ya ?i to fa shi zai bar gidan gaba Waya.

Murja cike da kunyar kamen da aka yi mata ga uwa uba Lawal dake tsaye ya ?i fita yana kallon ikon Allah, ta durkusa ta kwashi layun ta fice tana dakawa Lawal wata uwar harara kamar idanunta zasu zazzago.

Fadeel ya dafe kai yana mai runtse idanu zuciyarsa na tafarfasa tamkar an kunna ruwan heater.?

"Ka yi hakuri in sha Allahu zan kara kiyayewa."

Gyada masa kai kawai ya yi gami da yi mishi alama da hannu akan ya fita, Lawal ya juya ya fice mamakin wannan hali na Murja da bai taSa zato ba. Lallai mutum ba abin yarda bane.

Shi kuwa Fadeel sai da ya samu nutsuwa sannan ya fada wanka, ba shi da niyyar fita daga gidan amman daga faruwar al'amarin ya ji gaba daya gidan ya fita a kansa. Kai tsaye wurin Ibb ya tafi, dama tun jiyan yake faman kiransa akan zancen bikinsa da ya taso yana ?in zuwa yana ba shi uzurirrika saboda damuwar Humaira da batun auren Ibb ke taso masa da shi.

Murja kuwa tana zuwa ta shiga haWa kayanta, ta gwammace ta bar gidan da ace Fadeel ya fasa zancen nan har Alhaji ya tsane ta ya kuma ?i jinin haWa zuri'ar Wansa da ita. Anti Amarya kadai ta fadawa, nan da nan hankalinta ya yi mugun tashi, ta hau ta da faWa tamkar ta ari baki. Babban ba?in cikinta ma ba ta yi shawara da ita ba ta yi raWin kanta.

"Ba ki da wayo ko kaWan Murja! Wa ya fadamaki samun Fadeel a hannu abu ne mai sauki? Ke kinsan irin karfin ibadar wannan yaron? Toh wallahi ko wani Malamin ba zai nuna masa tashin dare da nafilfilu ba ko an fadamaki ba?in tabon sallar dake goshinsa da goge dutse a goshin ta same shi? Kai Murja! Toh kuwa? ya zama dole ki bar gidannan! Ni zan samu shi Fadeel din nasan siyasar da zan mishi don kar magana ta je kunnen Babansa."

Murja ta kara jin wani malolon abu ya tsaya a ?ahon zuciyarta. Dama ta sani Anti Amarya ba za ta taSa goyamata baya ba. Ta kuma soma? yarda da yayarsu Rabi da ta ce Anti Amaryar kanta kawai ta sani, ba wani so take yi ta tallafe ta ba shiyasa ta ce? ta sauya dabi'u ta nuna ita wata salihar ce. Ban da haka ai ta san wannan ba abu ne mai sauki ba da kuma zai yiwu kawai a yi duka Waya lokaci daya a wuce wajen.

Ta shareta ta cigaba da hada akwatin kayanta. Kafin wani lokaci ta kammala ta fice abinta, Anti Amarya ba ta kara cewa uffan ba, ba karamin Sata ranta ta yi ba, ita yanzu babban tashin hankalinta yanda za ta rufe maganar kar ta je kunnuwan Alhaji. Ta tsinewa Murja ya fi a ?irga. Wannan ya sa ko kallonta ba ta yi ba da ta fice. Allah ya ta?aita Hannatu ba ta gidan ta je wurin dangin Alhajinsu.

***
Gidan su Humaira tamkar gidan makoki, babu walwala a fuskar kowanne, Abba kasuwar ma kasa fita ya yi. Mami kuwa ta ?ulle a Waka ba wanda ya san me take yi. Ummita kuwa tana kwance shiru kawai har baccin dole ya dauketa sanadin magunguna da ta sha kuma a daren jiya ko kadan fargaba da damuwa sun hana ta runtsa.
Karatun alkur'ani Humaira ta kunna a waya ya karaWe Wakin don su samu nutsuwar zuciya. Tana sauraro tana bi a hankali ta hanyar motsa lebSanta duk cikinsu sun kasa yiwa Ummita kwakkwarar magana don ba su san ta inda za su fara ba. Raihana kuwa kanta ta cusa karkashin pillow tana kuka a hankali tana kuma bin karatun. Ji take yi inama komai dake faruwa a mafarki ne. Amma ina, wannan zahiri ne, shi ne kuma gaskiya mai mugun Wacin da ke addabarsu.

Hatta da Mubarak ya shiga wani irin hali, komai yake yi Ummita ce a ransa, bisa umarnin Abban ya bi su Yassar shago amma yana zaune cikin mugun Sacin rai. Ya rasa dalilin da ya sa ta tsaya mishi a ?ahon zuci watakila kuma tsananin tausayi ne da duba da irin kirkin Ummitan yarinya mai kirki da sanin ya kamata. Bai taSa ganinta ba face da murmushi saman fuskarta, tana da hakuri sosai da sanyi. Dabi'unta abin so ne ga kowane namiji.

***
Mami a hargitse take ta faman danna kiran layin wayar amma abu Waya kwamfutar ke nanata mata, a kashe wayar take. Koda ta gaji ta yi wurgi da ita tana mai jan tsaki. Goshi ta dafe cikin tsananin ruWu. Can kuma ta ji wayarta ta Wauki ?ara. Ta yi azamar karasawa saman gadon ta Wauka. Lambar dai da take ta kiciniyar kira ita ce aka kirata da ita. Ta Waga cikin sauri.

"Kai Bala! Ina ka shiga ne?"

"Kiyi hakuri Hajiya, chaji na bayar sadda kika kira ba'a Waga ba sai mai chajin kawai ya kasheta gudun a yi ta kira. Ina fatan lafiya?"

Ta girgiza kai idanu a runtse tamkar yana ganinta.

"Ba lafiya ba Bala, aiki ya Saci! Duk inda mutanen nan suke ina bu?atar ganinsu. Wannan karon ni da su zamu tattauna. Sun min ba daidai ba, na fadamusu dama idan har sakamako bai yi kyau ba to sai sun maidomin hatta rabin kudin da na ba su. Ba za su ci komai daga dukiyata ba tunda har kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba."

"Hajiya ban fahimci me kike son cewa ba? Ke ce fa kika ba su umarnin barin wajen koda kuwa kudaden ba su shiga hannunsu ba? Ta ya ya kuma za ki Wora musu laifi kacokam?"

"Bala sun yiwa yarinya fyaWe, yarinyar da ban so hakan ta kasance da ita ba. Da ace waccan mayyar aka yiwa ba zai dameni ba. Yanzu dai mugun abun da suka yi ya bayar da mummunan sakamako, ciki ya shiga."

Bala ya doka salati mai karfi. Can kuma cikin rage murya ya ce.

"Ciki kuma Hajiya? Toh me ake jira da ba za'a zubar ba?"

Mami ta sauke huci.

"Zubarwa ai wajibi ne. Dole na zubarmata da shi ko don gudun tonuwar asirina. Amma yanzu ni ka nemo min su mutanen ko kuma ka aikon lambar shi Babban nasu sai muyi magana."

"An gama Hajiya, zan kira na sanar da shi sai na hadaku a waya don dama ina shirin ce maki ba ya garin ya dan yi bulaguro zuwa Kaduna."

"Shikenan, sai ka turo."

Tana kaiwa nan ta katse wayar tana ji kamar ta zabga ihu, babu abin da idan ta tuna take takaici kamar rashin cin nasarar mallakar dukiyar Abba da ta kwallafa a rai. Ga kuma shirin tonuwar asirinta da ke son afkuwa, matukar cikin Ummita bai fita ba lallai babu shakka watarana abin Soye zai fito fili.

***
Mami ta tabbatarwa Abba lalali sai dai a zubar da cikin Ummita gudun zubewar mutuncinsu a idanun duniya. Tun Abba ya na nuna bai amince ba har dai ta ci nasara a kansa ya yarda.

Ranar da zasu je a daren Mami ta shiga wurin Anna don amsa kiranta. Anna ta dube ta a yamutse.

"Sai wani rawar ?afa kike yi a cire cikin yarinyar nan, idan an cire wa kike tunanin zai aure ta? Shi Sahabin ko kuwa dai shi mijin naki ya ba babban Wansa aurenta? Ba kya wannan hangen?"

Mami ta ji kirjinta ya buga da ?arfi. Wannan zance na Anna ko kusa bai mata dadi ba amma sai ta zaSi ta Soye saboda dalilin da ita kadai ta bar wa kanta sani.

"Idan har asirinmu zai rufu mene ne ciki Anna?"

Da?uwa Anna ta wurga mata.

"Ungo nan nace! Ni dai da ace a asibiti nayi na?udarki zan iya rantsewa sauyamin ke aka yi ba ke ce jinina ba. Yanzu ke koda wasa idan mijinki ya ce zai hada auren wannan gantalalliyar da Wansa abin yarda ne a wurinki? Babban Wanki wanda bai taSa kusantar zina ba a duniya shi ne za ki yarda a hada shi da ita?"

Kafin Mami ta kai ga cewa komai Anna ta ji an bata amsa.

"Anna, kar ki kara danganta yan uwana da zina, kowa shaida ne ba zina suka aikata ba, kaddara ce da za ta iya faWawa kan kowa. Sannan idan auren ne ma sai me? Ni ina sonta kuma na rantsemaki a yau Sahabi ya janye da batun aurensa da Ummita to fa ki rubuta ki ajiye ba ta da miji sai ni nan Mubarak!"

Ba Anna kadai ba, hatta da Mami wanda ganin inuwar mutum a farko yasa ta Soye abinda ke ranta sai da maganar ta yi mata wani irin duka a kirji. Ta dago tana kallon Mubarak din, sanin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login