Showing 141001 words to 144000 words out of 189325 words

Chapter 48 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

214

harshen fillanci ta ce.

"Komai da ya faru ya riga ya faru sai dai a kiyaye gaba. Yanzu tunda har ka gano bakin zaren sai a yiwa abin tufka ta hanyar cigaba da kula da yarinyar da dora ta bisa turbar addu'a da kuma nema mata abubuwa tsarin jiki duk da cewa babu tsarin da ya fi addu'ar."

Kawu ya numfasa cike da jimami da taraddadi.

"Mamaki da tsoron halayyar DAN ADAM ya ?ara shiga ta Hafsatu, yanzu ke kya ce wannan baiwar Allahr za ta iya cutar da ko mage ne balle kuma mutum?"

Murmushi Hajjo ta Wan yi.

"Meye abin mamaki anan? An fa yi wanda ya fi haka. Kuma kar k manta zargi ne.."

"Ko kusa bana kokwanto ko zargi a kan haka, wannan gaskiya ce da na jima da ji kuma na ?i yarda sai yanzu da komai ya bayyana a zahirance. Ba zai yiwu ace haya?in da Maryama ta ba Fatima shekarun baya ba irinsa take haya?awa Humaira kuma yanayin da Fatima ke shiga dalilin haya?e-haya?en ace iri guda ne da na Wiyarta. Wannan ai ko akwai ban mamaki, ban da kuma toshewar basira irin tamu a lokacin, mun kasa tunanin akwai cutarwa a ciki ba? Kowannenmu ya shaida da irin kaunar da Fatima da Isuhu ke yiwa junansu ba amma rana Waya ta yi masa tsana wadda da bakinta ta furta mana ba ta san dalilinsa ba? Kai Hafsatu, nikam ba zargi nake yi ba, na riga da na tabbatar da sa hannu wannan makirar."

Hajjo ta jinjina kai yayinda kwalla suka cicciko mata na tuna yanda Adda Fatima (kasancewar yaya take a wurinta koda babu aure tsakaninta Kawu, don yar uwarsu ce ta fannin Baffansu) ta sha fama kafin rasuwarta.

"Amma idan har hakan ne toh wallahi matarnan ta jira sakayyar Ubangiji don ta dauki alhakin wacce ba ta ji ba kuma ba ta gani ba. Matar da ta yarda da ita tsakani da Allah mu ma haka. Ni babu abin da ya ban tsoro sai wannan bori da tada jijiyoyin wuyan da Humaira ta ce tana yi akan ba ta kaunar aurenta da Fadeel. Toh a zatonta yarinyar za ta yi ta zama babu aure? Ai ni tun da naji cewar wai Humaira ba a sanyata a makarantar boko ba sai da na yi maka magana idan ba ka manta ba, nace maka ko ?ar gidan Iyagana da ta girmi Humaira da suka koma can Katsina da zama an maida ta boko kuma yanzu gashinan har ta kusa kammala kwalejinsu. Ka hau ni da faWan ai wannan ma gata ne za ta yi mata. Eh gatan ne, amma yanzu wa aka cutar? Za ta shiga rayuwar miji Wan boko fisabilillahi daga shi har danginsa na san sun ci sun tada kai da biro da takarda yarinya babu faransancin babu turanci."

"Hafsatu don Allah abar maganar tunda dai mai afkuwa ya riga da ya afku. Ki yafemin faWan da nayi maki a lokacin, amma ki sani ko Humaira ba ta yi wata aba boko ba, mu godewa Allah tunda ta tsira a hanyar tsirar, wato na islama da ba a hanata ba. Sannan karki manta duk fa yanda Allah ya tsarawa bawa a rayuwa hakan ne zai tabbata. Yanzun ba gashinan ba nan da ta yi mana girki kamar kunnuwanmu za su tsinke don dadi? Ai DUKAN RUWA BA ZAI HANA GWARJE AMO BA! Mu je zuwa muna nan dake wataran yarinyar nan sai ta zama tamkar farin wata mai haska darare a cikin yan uwanta. Babu abin da zai hana zakaran da Allah ya so ya yi cara."

Ta ji karfin gwuiwa bisa maganganunsa har sai da ta murmusa.

"Allahu ya nunamana wannan ranar."
Kawu ya amsa da amin yana jawo ?waryar furarsa.
***
Mami sosai ta cika da mamakin ganin Abba bai ce uffan ba game da dawowar Tasleem gidansa matsayin bazawara. Koda ta kalallameshi banda Allah ya kyauta babu abin da ya ce. Tunanin shirye-shiryen bikin da ya sa a gaba shi ya dauke hankalinsa ne ya sanya ba ta kawo komai ba amma a kaifin basira irin nata ta sani akwai dai abinda ya sauya Abban, ko fara'arsa ta daina gani.

?angaren jannat kuwa ranar da ta kama na dawowar Humaira, a ranar ne aka gurfanar da ita gaban al?ali, a ?an kwanakin da ta yi gaba daya ta fita hayyacinta duk kuwa da cewar babu duka balle zagi amma fa wahalar zama a inda ba ta sama ba ya sauya ta. Tasleem koda ta ganta fashewa tayi da kuka, sai kuma a lokacin ne suka san Fadeel ne ya ?arfafa binciken har mai afkuwa ta afku. Wannan ya ?arawa Mamin tsanar Fadeel, itama Tasleem sai da ya yi mugun Sata ranta.

Mami tana ganin an shige ciki domin shari'ar ta koma da baya ta fidda waya ta kira Wizzy. Tuni ta shiryamasa cewar ya aika mace gidan ta daukar masa Ahmad tunda babu kowa sai Anna da Ummita.

"Ka gaggauta wanzar da shirin don bana son a samu wata matsala, ka kuma tabbatar da komai ya tafi daidai."

Daga haka ta katse kiran ta shiga dakin shari'ar.

A gabansu al?ali ya yankewa Jannat hukuncin biyan tara na Sata sunan da ta yiwa su Ummita, miliyan biyar ga kowaccensu. Sai kuma ?aryata kanta a gidan jaridu da ma rediyo da kuma soshal midiya kan cewar ita ce ta sa aka yi wannan mummunan aikin da kuma ba da hakuri. Hakanan shi ma Joshua. Tun daga lokacin ya hau kuja da ro?on gafara don ya sani ba shi da ma?udan kuWaWen da zai biya don wake kansa a gaban al?ali. Ya shiga tsinuwa ga Jannat wacce ita ce ummul-aba'isin na shigarsa wannan hali. Shi da ya yi aikin akan kuWaWe ?alilan sai ga shi ya jawowa kansa, ga mahaifinsa da ya ce babu shi babu hannunsa a ciki.

Daga haka aka ?ara titsa ?eyarta aka tafi da ita har sai lokacin da aka biya tara sannan.

Haka suka fito bakin kotun su Tasleem da Mami na kuka, ga Anna can a gida ta baza idanu tana jiran ta gansu tare da ita.

Mami kuwa zuciyarta cike take da zullumin ko Wizzy ya aiwatar ko kuwa an samu akasi. Ta duba ta ga dukkan yaranta idan ka cire Mubarak da ke can Sokoto a camp babu wani da ba ya tare da su. A iyakar saninta babu wata matsala da za a samu da shigar mace cikin gidan tunda dai babu kowa.

***
A daidai wannan lokacin motar su Humaira ta tsaya a tasha, suka fito ita da Hajjo a take aka samar musu abin hawa da zai kai su har gida sakamakon lodin kayan da suka taho da su. Suna hanya zuciyarta cike taf da farin ciki, ba ta kira kowa ba da zummar sai dai kawai su ganta.

***
Wizzy ya bude motar gami da duban matarnan, matashiyar budurwarsa da yake ji da ita a lokacin, sai da suka kai ruwa rana kafin ta aminta da bu?atarsa har sai da ya yi nata al?awarin da ta jima tana son ji, wai aure. Ta sha zabgegen hijabi da ni?af.

"Nusy, kar ki bari a samu wata matsala. Ki bi komai daki-daki yanda muka tsara."

Ta yi mishi farr da idanu bayan ta Wage nikaf din.

"Wannan ba damuwa ba ne Guy, komai zan yi dominka."

Ya jawo fuskarta ya sumbaci goshin sannan ta sauke nikaf din ta dauki jakarta ta fita. Yana daga can tsallaken ya ga shigarta gidan ba tare da dogon zance da maigadin ba. Sai ya sauke ajiyar zuciyar, ribas ya yi da motar ya koma daga can bayan gidan ya tsaya gudun kada a gan shi duk kuwa da cewa motar tinted ce amma ita ce dai motar da ya kai wa su Abba hari.

***
Ummita dake zaune a falo ga Ahmad a gefenta yana bacci cikin net dinsa. Hankalinta gaba daya ya yi zurfi a tunanin yanda aka kaya a wurin shari'ar amma ta kasa kiran koda Raihana ce don ta ji meke faruwa. Sallamar budurwar ta katse tunaninta, ta dubi ?ofa gami da amsawa. Ganin mace da nikaf ba ka ganin komai sai idanunta ta dan yi jim, ba don ba ta saba ganin mai irin shigar ba sai don kasancewar abu ne mai wahala su yi ba?uwa da irin shigarnan. Kamar Nusy ta san zargin da take yi, sai ta Wage nikaf din, kyakkyawar fuskarta ta bayyana da murmushi mai bayyana ha?orinta na makkah.

"Sannu, nan ne gidan su Futuha Yusuf?"

Ganinta har da ha?orin makkah da kuma yanayi na kamala sai ta Wan saki jiki, itama cikin Wan murmushin ta amsa.

"Yauwa, eh nan ne. ?araso ciki mana."

Nusy cikin tabbacin samun nasara ta ?arasa ta zauna idanunta ya sauka kan wanda ta zo dominsa, wato Ahmad. Yaron tubarakAllah, da alama goyo mai kyau yake samu don yana da kumari sosai fatarsa kuma ta ?ara gogewa.

"Ba ki sanni ba ko? Ni makwafciyarta ce ta Kuntau ana cemin Maman Suhail, mun yi da ita dama zan yi mata rakiya wata unguwa shi ne ta yimin kwatancen gidan nan ta ce na zo mu hadu anan mu tafi."

Ba wani sanin gidan na su Futuha na yanzu ta yi ba balle ta fahimci gaskiyar lamarin, ta ba da gaskiya sosai akan zancen Nusy.

"Allah Sarki, eh sun dan fita ne amma na tabbatar sun kusa dawowa yanzu. Bari na kawomaki ruwa."

Tana fadin haka ta mi?e, an zo daidai wajen da Nusy take so, tana ganin shigar Ummita kicin ta yi saurin mi?ewa ta bude net din Ahmad ta daukeshi. Ta Wago suka yi ido hudu da Waleed da ya shigo daga bangaren Anna rike da ball a hannunsa. Ya gaida ta don bai mance sadda Ummita ta yi ba?uwa ba ya ?i gaishe ta Antinsa Humaira ta yi mishi tsawa. Ta amsa tana dan wayancewa da jijjiga Ahmad kai kace kuka ne yake yi. Waleed kuwa dama ruwa ya fito sha sai kawai a guje ya yi kicin yana wasanninsa na yara. Ta sauke ajiyar zuciya da sauri ta Waga zumSulelan hijabinta ta sanya Ahmad a ciki ta rufe, ta kama hanya ta fice bayan ta sauke nikaf din ya rufe fuskarta.

Har ta fice daga farfajiyar gidan, Allah ya taimaka Maigadi ya Wan mike wannan ya sa ta ?ara Waga kafafunta ta fice a gate din.

Daidai lokacin motar su Humaira ta tsaya suka fito, idanunta akan matar dake ta baza sauri ga kukan jariri na tashi cikin hijabinta. Kafin ta yi wani tunanin sai ga Ummita a haukace ta banko kyauren gate din ta fito.

"Ahmad! Wayyo jama'a ku taimakamin Wana!!"

Jin haka ai sai wasu samari da ma ita kanta Humaira dake tsaye suka nufi matar a guje, daidai sadda Wizzy ya yo gaba da zummar kawai ta bude motar ta shiga daga ta iso, sai dai ina, wata irin raruma da wani ya kai mata sai ga ta nan yiff a ?asa, yaro kuwa ya ji buguwa ya fasa ihun da ya fi kukan da yake yi a baya. Da rawar jiki kuma a haukace Ummita ta hau Wage hijabinta sai ga Ahmad, Wizzy kuwa tuni ya yi wata muguwar ribas ya bar wurin a miliyan, duk iyaka kokarinsu na ganin sun dam?eshi abin ya ci tura. Nusy dai ta zo hannu tana kuma ji da gani wanda ta aikata dominsa ya juya ya bar wurin.

Nan da nan Ummita ta dam?e Ahmad tana kuka har lokacin jikinta na kakkarwa. Samarin nan kuwa suka shiga kokarin bugun Nusy wani dattijo ya hana ya bada umarnin a dam?a ta a hannun ?an sanda.

Ana nan ba a kai ga tafiya da ita ba sai ga motar su Abba ta sanyo kai. Mami tun daga nesa ta hangi cincirindo ai sai da ta ji wani mugun jiri daga zaune yana son kwantar da ita.

"Meke faruwa haka kuma? Waccan ba Mamana ba ce?"

Fadin Abba yana Wan ?ara ?urawa wurin idanunsa. Mami dai ta kasa ce masa uffan sai Raihana daga baya ta amsa da su ne har da Ummita. Sai kawai ya ja burki ya tsaya ya fito, Mami dai ta kasa motsi balle ta fito daga motar. Suna fita wayarta ta hau ?ara. Ganin sunan Wizzy sai da ta ji wani guntun fitsari ya kufce mata ya zubo, ta Waga ba tare da cewa uffan ba.

"Ke tsohuwar kilaki! Ki saurare ni dakyau! Na rantse maki tunda har aka kama min farin cikin rayuwata sai na salwantar da rayuwarki! Sai na kasheki da hannuna muddin asiri ya tonu! Kuma yanzu na gaji da bibiyar Wana ta hanyarki! Zan tunkari ita banzar gyatumarsa ta ba ni Wana ko ta halin ?a?a ne! Ke kuma ki saurari abin da zai biyo baya! Ba ki san waye ni ba! Labarina kawai kike ji!"

Yana kai wa nan ya datse kiran, wasu hawaye masu Wumi na bakin ciki ya zubo saman fuskar Mami, ta yi saurin kauda su ta bude murfin mitar ta fito. Duk wannn abu da take yi akan idanun Hajjo wacce tun fitowar su Abba ta lura da Mamin da kuma yanayinta, tana ganin wayar da ta amsa. Mamin na fitowa itama idanunta ya sauka cikin na Hajjon, ta gane fuskarta sarai, matar Kawun Humaira sai ta kauda fuska ta daure ta tamau.

Abba ya dubi Ummita da neman ba'asin yanda lamarin ya faru. Cikin kuka ta labartamasa komai, Futuha tunda ta ji an ambace ta da ma sunan unguwar da take sai ta zaro manyan idanunta waje gami da dafe kirji a mugun firgice. Kafin ma Ummita ta kai aya ta hau rantse rantse.

"Na rantse da Allah karya take yi, ke a ina kika san ni? Wallahi Abba karya ne ni tunda naje wannan unguwar ma ban taba shiga kowane gida ba don ba class dina ba ne su. Wallahi sharri take yimin."

Nusy kuwa dai ba ta tanka ba sai jin ciwon gudun da masoyinta ya yi ya kyale ta a nan, idan wani ya ce mata zai aikata hakan gareta za ta ?aryata. Mami kuwa tana gefe ta yi gum ba ta ce uffan ba.
Hajjo dai ba ta bar kallonta ba har sai da Abba ya ba su umarnin duk su shige ciki shi zai juya a mi?a Nusy hannun hukuma. Da wannan gaba daya suka yi cikin gidan, Raihana ta rungume Humaira ta fashe da kukan da Humairar ta ba kanta ko don abinda ya kusan faruwa ne. Tun tana rarrashinta har dai kukan ya soma karyar da nata zuciyar. Dama ta lura da irin muguwar ramar da Raihana ta yi. Tasleem ta tsallake su gami da jan tsaki ta shige ciki don yanzu ta koma ainahin dakinsu kuma tsohon gadonta. Futuha kuwa Sangaren Anna ta yi don ta kwantar mata da hankali bisa hukuncin da aka yiwa Jannat.
***
Ta fakaici idanun jama'ar dake falon ta shige Wakinta ta sanya mu?ulli. Waya ta fitar ta dannawa Hajiya Lubna kira. ?ara uku ana hudu ta Waga.

"Lubna ki taimakamin, komai ya lalace."

Tana maganar ne cike da tashin hankali.

"Kwantar da hankali ki sanar da ni a nutse. Meke faruwa ne?"

Nan da nan ta zayyane mata komai ta ?ara da fadin.

"Muddin waccan yarinyar ta buWe baki ta yi wata maganar toh ki sani akwai babbar matsala. Nikam ban san kuma me zan yi ba."

"Wannan ba damuwa ba ce Maryam, yanzu dai abin da nake so ki yi kokarin sanin station din da aka mi?a ta ni kuma zan nemi Alhaji don ya yi magana su sake ta. Ai harka ce ta kuWi kwantar da hankalinki komai zai tafi daidai."

Ta dan ji sassauci kaWan.

"Shikenan, bari Abban yaran ya shigo. Amma lallai muddin wannan yarinya ta fito zan dauki mummunan mataki akan Wan iskan yaron nan."

"Ko kefa, ki kwantar da hankalinki komai zai tafi yanda muke so. Ai ko ba ko faWa ba dole Wizzy ya ci ubansa. Ya batun can kuma na baya, kin gano wanda ya sanar da ?an sanda? Na fadamaki Maryam koda yaranki kar ki sake ki aminta da su."

Wannan ya tunasar da Mami tashin hankalin da ke gabanta.

"Uhm, bari kawai Lubna. Ai yanzu an yanka ta tashi domin babu wani abu cikin sirrina da ?ar banzar nan Tasleem ba ta ji daga bakin Futuha ba wai har ni ta ke yiwa barazana akan maganar? Wancan batu kuwa har gobe na kasa fahimtar komai, karshe na zargi Abbansu ko shi ya sanar toh idan haka ne kuma meyasa har yanzu bai dau mataki ba? Nidai na ga y sauyamin, babu hira da ni balle a sakarmin fuska."

"Toh kuwa lallai ki zauna ku yi magana da shi sosai ki fashe da kukan kissa ki nuna sauyin nan da ya yi maki sam bai maki dadi koda dai duka wadannan ba sai na koyamaki ba ke dinma Malamata ce a wannan fannin. Yaranki ko zan yi waya da Babandi mu sanya a ?ulle musu baki ta yanda babu inda maganar za ta ?ara fita."

Sanin da Mami tayi Anna ba matsala ba ce ya sanya ba ta ma kawo ta a rai ba, ita idan ta sani ba wani abun bane. Tun kuma safiyar yau din sai yanzu ta yi wani murmushin da har zuciyarta ta ji daWin wannan zantuka na aminiyarta.

"Ina yinki sosai Aminiya, Allah ya kara doraki kan Alhaji da ma?iyanki."

Suka yi dariya, nan kuma suka koma batun Jannat wanda tuni ya baza gari, Hajiya Lubna ta jajanta mata da tambayar yanda za su yi da batun kudaden. Ta taSe baki.

"Motarta dai ta ce a siyar sai sar?o?inta da mijinta zai taho da su. Ya ce dai babu hannunsa a ciki don haka ko sisin kwabo nasa ba zai yi kuka ba."

"Shegen sama, shiyasani, ko me ake ciki dai sai ta fito. Sai kuma ta kiyayi gaba tunda yanzu idanun duniya duk a kanta suke."

Mami ta numfasa.

"Atoh, kinga bari naje ga waccan kafaffan mijin nawa ko zan iya tankwara zuciyarsa na gano dalilin sauyamin da ya yi."

Suka yi dariya ransu ?al kafin su yi sallama.

***
Hajjo ta yi wanka ta fito ta dubi Ummita baki buWe.

"Wai har yanzu ba ki bar wannan kukan ba? To maganin me zai maki?"

"Kema dai kya faWa Tanti, ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login