Showing 18001 words to 21000 words out of 186041 words

Chapter 7 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53931

shima Junaid yana ɗakinsa a kwance idonsa a rufe kamar mai yin bacci amma kuma ba baccin yake yi ba, ƙarar message yaji ya shugo wayarsa ta whatsApp, hannu yakai saman drower yana lalumen wayar! ɗauka yayi sannan ya buɗe secuirity wayar yahau whatsApp, baƙuwar number ya gani an turo video, yana lumshe ido kamar mai jin bacci ya buɗe saƙon ya shiga kan videon abunda ya ganine yasa ya buɗe idonsa sosai a zabure ya tashi zaune zuciyarsa tana ɗarɗar, da ƙarfi ya furta "whatttt?..." wani irin bugu zuciyarsa tayi, "Yushert kuma? with bad boy? kuma acikin gidan nan hakan ma akan gadonta?..."
zuciyarsa ce take tafarfasa ya sauƙa daga kan gadonsa a fusace yabar ɗakinsa, da sauri sauri ya sauƙa down stairs bai bi takan su Mommy ba haka yaje gaban Ayush yasa hannu ya fincikota ya wurgar da ita ƙasin carpet yana huci yace "daman ashe ke ba mutumiyar kirki bace? ke ƴar iska ce karuwa?.."

Su mommy ne suka miƙe tsaye da sauri suna faɗin "lafiya kuwa?.."
ɗaga musu hannu yayi yace "please mom karki dakatar dani" ya nuna Angel da yatsa yana faɗin "ke kuma karki kuskura ki saka mun baki..."

ya kalli gurin da Ayush take a zaune a ƙasin carpet yace "Allah ya rufa mun asiri da ba'ayi baikon nan ba, wallahi da kin cuce ni saboda ni ba abunda nafi tsana arayuwata irin a munafurce ni, tirr da halinki, bazan taɓa Auran karuwa ba irin ki kuma munafuka..."
Mommy ganin abun yayi tsanani ta dakawa Junaid tsawa tana faɗin "ya isa haka Junaid wani irin abune haka, kazo kana faɗan munanan kalamai akan yarinyar da bata san komai ba, yarinya mai haƙuri da juriya..."
mommy bata ƙarisa maganar ba Junaid ya katseta da cewa "Mom duk abunda kike tunani ba haka bane, wannan yarinyar shaiɗaniya ce ƙazama karuwa...." bai gama iddasa maganar ba Mommy ta zabga masa mari har sau biyu tana kuka tace "nace ka dakata haka ko, shin ka sanar mun meyake faruwa ne? kodai ka haukace ne?..."
cikin ɓacin rai yace "mom ba hauka nake ba amma zan nuna miki a zahiri..." ya miƙa mata wayarsa tareda faɗin "gashi nan ki kalla"
hannun mommy na kakkarwa ta karɓi wayar ta danna kan video, ta soma kalla da hawaye caɓa caɓa a fuska, itama Angel ido ta kai kan video ta zaro ido sosai,
Ayush tana daga zaune ta tashi da sauri taje itama tana kallon video, hannu tasa ta rufe bakinta tana kuka,
Mommy da Angel gaba ɗaya juyowa sukayi suna kallon Ayush sun kasa cewa komai,
murya na rawa Ayush tace "wallahi tallahi bansan da wannan videon ba.."
Junaid wani irin kallo ya watsa mata yace "daman taya zaki san da wannan videon bayan asirinki ya tonu..."

"wallahi Yaya Junaid bani bacee..." kafin ta rufe baki ya kai mata wani irin gigitaccen mari har saida ta faɗi ta kifu akan glass table dake tsakiyan ɗakin, nan take lips ɗinta ya fashe jini ne yake zuba sosai, juyowa tayi still bakinta bai rufu ba tana faɗin "wallahi ko zaka kashe ni bani bace, wallahi mai kama dani ne..."
nan ma wani irin harbi yakai mata da ƙafarsa saida ta yi rigingine, yasa hannu ya zaro belt ɗin wandonsa zai kai mata duka, mommy tayi saurin riƙe shi tana faɗin "kana da hankali kuwa Junaid? ciwo zaka ji mata ne, ka tsaya kayi bincike akai tukun ka yanke hukunci...."
fizgar hannunsa yayi da ƙarfi yana faɗin "mom wani irin bincike zanyi, bayan itace kuma da saninta tinda har magana take tana shashshafa shi balle kice ko tana bacci ne ko suma, kema kinsan wannan videon ba ƙarya bane, saboda taga babu kowa agidan shine zata kawo gardi cikin gidan nan?..."

agigice Ayush ta tashi da gudu zata haura upstairs, yayi sauri yasa ƙafarsa ya girbe mata sawayenta saida tayi sama tukun ta faɗo akan stairs goshinta ne ya bugu har saida ya fashe,

Angel ce ta taho tasha gabansa tana faɗin "wai meye hakane Junaid..." ɗauketa yayi da wani gigitaccen mari itama ta faɗa saman kujera,
Mommy tsabar takaici ganin ciwonta zai iya tashi tayi saurin wuce wa ɗakinta ta danna sakata,

Ayush kuwa kafin Junaid ya waiwayo kanta har ta miƙe da gudun gaske tayi hanyar waje tabar falon, gudu bana wasa ba haka ta nufi hanyar gate,
shima Junaid ɗin bin bayanta yayi ya nufi hanyar gate yana magana da maigadi cikin ɗaga murya yace "Baba tsoho idan ka kuskura ka buɗe mata gate ayau zaka bar gidan nan..."
maigadi jin abunda Junaid ya faɗa yasa kwaɗo ya kulle gate ɗin kafin Ayush ta iso,
itama Angel fitowa tayi tana faɗin "Ayush karki tsaya ki gudu, ki wabci key ɗin a hannun maigadin ki buɗe kije ki ɓoye..."

Junaid tsaya wa yayi har saida Angel ta zo zata wuce shi ta nufi gurin Ayush ya yi mata wani irin riƙo ya zazzabga mata mari sannan ya girbe mata sawu ta doku a ƙasi yana faɗin "ta gudu ko?.."
tace "dan Allah kayi haƙuri Ogah Junaid...." kafin ta rufe bakin suka jiyo Baba maigadi ya ƙwalla ƙiran "yallaɓai Junaiddd..."

waiwaya wa yayi yaga Ayush ce ta kama kunnensa ta garzaya masa cizo! da sauri ya miƙa mata key ɗin...

ta tusa key ɗin a jikin ƙwaɗon cikin sa'a kuwa kwaɗon ya buɗu dasauri tasa hannu zata buɗe ta fice har ya iso yanda take ya cabki hannunta ya fara janta zasu koma ciki, tana ihu tana neman agaji ta kafa haƙwaranta akan damtsensa shima ta garsaya masa cizo, tsayawa yayi yana mata wani irin kallo ko motsawa bayayi, ita kuwa sai cizonsa take amma kamar mai cizon bishiya,
kai wa hannu yayi ya zabga mata mari ta bayan hannunsa, agigice ta faɗi ƙasi tana ihu, tana shirin tashi ta gudu ya cabki wuyanta ta baya, tsabar a ruɗe take haka ta juyo takai bakinta saitin penus ɗinsa ta gasa masa cizo!
ƙara yayi kaɗan ya durƙusa tareda riƙe gurin, ƙansa a ƙasin floor ya yi sujjada, shi kaɗai yasan raɗaɗin da yake ji a gurin, ya juma kansa a ƙasi bai ɗago ba, lokacin kuwa Ayush harta koma falo ta haura upstairs tana shiga ɗakinta ta danna sakata...

itama Angel ganin yanda Junaid yayi tasan idan ya ɗago bazaiyi da wasa ba, haka ta tashi itama da gudu ta koma falo ɗakinta ta nufa tareda saka sakata itama...

Maigadi ne ya yo kan Junaid yana faɗin "yallaɓai Junaid! yallaɓai Junaid!!! lafiya kuwa, kaima cizonka tayi ko?..."

kafin ya iso dab da shi Junaid yayi saurin ɗaga masa hannu yana masa nuni akan ya tafi, still kansa a ƙasi bai ɗago ba...

haka maigadi ya juya ya koma gurin aikinsa yana faɗin "yarinya saikace mayya, bansani ba kota gutsire mun kunne..." ya ƙarasa maganar yana shafa kunnensa....


☆☆☆☆☆

Ɓangaren Sarki Ramoud!
misalin ƙarfe 12 nadare Sarki Ramoud da Uma Bara'at suna kwance sunata faman shan baccinsu, kamar a mafarki Sarki Ramud yake jin kukan mujiyoyi da yawansu acikin masarautarsa, sai kuma yake jin wani irin dariya mai rikitarwa na ban tsoro, a gigice ya tashi yana waige-waige tareda jero addu'o'i a tunaninsa mafarki yake ashe duk ba haka bane, kallon yanda Bara'at take a kwance yayi yaga sai fama shan baccinta take, a hankali ya sauƙo daga kan gadon ya buɗe ɗakin ya fita, kai tsaye babban falon masarauta ya nufa, yana zuwa yaga wani irin haske mai kashe ido, hannu yasa yana tare idonsa da ganin wannan hasken, murya a disashe yace "waye anan? mekuma ya kawo ka cikin masarauta ta? meke tafe dakai?...."
sassauta ƙarfin hasken akayi, hakan ya bawa Sarki Ramud daman ganin ko waye ne,
ganin mutumin dake kan kujerar mulki yasa sarki zabura, zuciyarsa ne ya fara bugu da ƙarfi a hankali ya furta
"MUNAFURR..."

tintsirewa da dariya yayi jin sarki ya ambaci sunansa yace "na dawoo, daman ai nace zan dawo ko, to na dawo karɓar mulkin california a hannuna, kuma na dawo tareda ƙarfin ikona sama da wanda nake dashi a baya, babu mai iya dakatar dani ko waye ne..."
Sarki Ramoud yace "meyasa kake son karɓar mulkin nan bayan bakada alaƙa da masarautar?..."
Munafurr ƙara tintsirewa yayi da dariya tareda faɗin "yarjejeniyar da mukayi da kai har ka manta? to idan ka manta zan ƙara tunatar dakai, a shekarun baya kace na temaka maka waran mallakar manya-manyan aljanu domin su baka kariya, na kuma yi sanadiyar haɗaka da shuwagabannin aljanun ruwa da duk wasu aljanu suka amince maka da sharaɗin bazasu ga hawayenka ba har abada,
ni kuma kayi mun alƙawarin indai aljanun nan suka ga hawayenka toh daga ranar zaka mallaka mun masarautarka shin ka tuno?..."

Sarki Ramoud durƙusawa yayi da gwiwowinsa yana tsiyayar da hawaye a cikin ƙwayar idanuwansa sai a yanzu yake ƙarayin nadama akan kuskuren daya aikata a baya,

ba tareda ya furta komai ba yaji anyi magana kamar daga sama,
ana cewa "BABU WANDA YA ISA YA MALLAKI MASARAUTAR NAN INDAI BA WANDA YAKE DA ALAƘA DA ITA BA..."

murmushin farin ciki Sarki Ramoud yayi ganin NARASIMHA ya bayyano,
Munafurr shima miƙewa yayi tsaye yana faɗin "masarautar nan ya zamo nawaaa, babu wanda ya isa ya dakatar dani akan abunda nasa a gaba na..." cikin tsawa yake maganar tareda zaro takobinsa mai farfatsin wuta duk jikinsa yayi jawur,
Narasimha kallon yanda Sarki Ramoud yake yayi tareda faɗin "wancan takobin da ka baiwa ɗiyarka shine makaryin tsafin wannan mummunan mutumin da zarar ya sareshi ko ɗan kaɗan ne, ka ɗauka ka baiwa Mayushert meye amfanin hakan? ga lokacin amfani da ita yazo..."
Sarki Ramud ne yace "ka temaka Narasimha an ɗauko takobin nan.."
Narasimha yana shirin ɓacewa zai je gurinsu Ayush domin ɗaukowa wannan takobin, Munafurr ya saita shi da takobinsa na tsafi saiga wani jar wuta kamar walƙiya ya fita daga jikin takobin ya shige ƙirjin Narasimha, lokaci guda Narasimha ya nemi hasken tsafinsa dazai ɓace ya rasa, an riga da an karya wannan tsafin Narasimha domin haske da wuta basa taɓa haɗuwa...

inda ace Narasimha yayi saurin wurga masa hasken tsafinsa to da sihirin Munafurr ne zai karye amma Munafurr ya rigada ya aika nashi saƙon zuwa ƙirjin Narasimha,
Narasimha ganin yanzu bashida wani sihiri hakan yasa ya amar da wani zobe daga cikin bakinsa ya wurga wa Sarki Ramoud yana faɗin "Raamoud ga wannan zoben kayi saurin sanya shi a yatsarka saika murza ka ɓace kaje ka ɗauko wannan takobin a ɗakin sirrin Junaidu, zoben zai kaika har yanda takobin yake kayi saurin kawowa ko kai da kanka zaka iya fitar masa da jini da wannan takobin shikenam shima nashi yazo ƙarshe...
kamar yanda Narasimha ya sanar masa haka kuwa yayi yana shirin ɓacewa Munafurr zaiyo kansa da gudu, Narasimha yayo tsalle ya doku akan Munafurr duk suka baje a ƙasi,
sarki Ramud kuwa har ya ɓace,

Macizen da suke jikin Munafurr ne suke kai wa Narasimha sara, ga dafi ne dasu kamar bala'i,
Munafur ne ya ɗago sannan ya buɗe bakinsa saiga macizai da yawansu suna fito wa, masu jajayen kamannu, sunada kayuwa bibbiyu, haka suka shishshige cikin gashin jikin Narasimha, shi kuwa miƙewa yayi yanata faman wurgar dasu, duk da saran da suka masa amma yaƙi kwanciya, haka idanuwansa suka canza launin jaa sosai, gashin jikinsa sunyi birtsi-birtsi sun tashi tsaye,
Macizai kuwa sunfi ɗari biyar a jikinsa manya da ƙananu duk suna mammanne a jikinsa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login