Showing 123001 words to 126000 words out of 186041 words

Chapter 42 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53941

WANDA BAI LURA BA, SHIMA ARTAFF BAMAI GANINSA YACE ƊAN NIGERIA NE, HABA BIRI YAYI KAMA DA MUTUM*



*MÁAHMUD ZAIDULLAH HUSSEIN*
*RAAMUD ZAIDULLAH HUSSEIN*
*ARTAFF ZAIDULLAH HUSSEIN*

*And their kids*

*JUNAID_KHAN MÁAHMUD ZAID*

*MAYUSHERT RAAMUD ZAID*

*with two kids from Artaff*

*Zaid Artaff Zaid*
*Maryam Artaff Zaid*
*Sumaiyah Artaff Zaid*

Sumaiya mahaifiyar su Sarki Raamud kenam yayi mata mai suna da mahaifiyarsa da kuma mahaifinsa.....

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 61 to 65



Bayan fitar Junaid da minti talatin sai gashi ya shugo hannunsa riƙe da tray na Apple har guda goma, kowanne saida yaje gabansa tukun ya bashi Apple, kowa acikinsu yaci amma banda Ayush wacce ta ɓare baki tana kuka kuma taƙi karɓan Apple cikin dabara Junaid ya ɗauki gudan Apple ya cusa mata a cikin bakinta yana mata alamar tayi shuru da yatsansa, itama shuru tayi tana ajiyar zuciya tareda gutsiran Apple,
A wannan lokacin dai babu wanda yayi wa kowa magana da haka aka sallame su suka koma gida,
Gidan da Junaid yake anan suka sauƙa saidai kowa an ware masa part ɗinsa,
Mommy da ɓangaren ta daban, shima Sarki Raamud da nasa ɓangaren, sai part ɗin su Junaid da Ayush dake can saman Upstairs....

Bayan an gabatar da Ayush a kotu tareda wanke duk laifukan da ake zarginta da aikatawa a lokacin akayi nasarar fitar da Hafiza daga prison, Amma Mommy ba ƙaramin ɓatar da kuɗi tayi ba a wannan case na yarinyar nan,
Iyayenta sunyi matuƙar farin ciki sosai da kuma yin nadamar Aurar da ɗiyarsu a gurin da ba'a ƙaunarta, haka Hafiza ta cigaba da zama agurin su Mommy bayan iyayenta sun koma garin Kano,
Ogah Junaid shi da kansa yasa Hafzat a makarantar sacondary, Hafzat ba ƙaramin farin ciki tayi ba kasancewarta dasu Mommy ga suna bata kulawa yanda ya kamata duk abunda ta nema bata rasa shi duk da tana da filako sosai dake bafulatana ce,

Yau Saturday ranar weekend Hafzat tana zaune a babban falo ta ƙurawa plasman ido ana showing indian film mai kyan gaske, ita kaɗai sai murmushi take ganin an nuno masoya biyu sunata shan love, har Ayush ta sauƙo falo Hafzat bata sani ba, Ayush tayi sallama shuru har ta komo tana gyaran murya amma ko motsi Hafzat bata yi ba, saida Ayush ta ɗauki remote ta chanza Film ɗin tukun ta waiwayo da sauri tana son ganin wanda ya canza mata,
ganin Ayush a tsaye tasha doguwar riga da gyalen kayan tayi kyau sosai tasau murmushi tana faɗin "laaa Aunty Ayusher kece?..."
Ayush girgiza kai tayi tana cewa "uhmm uhmm bani bace ke ce..." Hafzat ɗan turo baki tayi sannan tace "wallahi Aunty Ayusher bansan kin shugo ba, yanzun ina zakije na ganki da shirinki har haka?.."

"ina zaki san na shugo kina kallon yanda ake romance, mommy tana part ɗinta ne?.."
Hafzat tace "a'ah bata dawo daga hospital ba...".
"Okay Abbana pah?.." Ayush tayi maganar tana nuna part ɗinshi da yatsa..
"wallahi bansani ba ko yana nan, amma naga shiɗin baya fita ko ina ai.." a cewar Hafzat..
Ayush tace "Hmmm! Abbana kuwa ina ya sani a Nigeria, bari naje na dubo shi, daga nan zan wuce hospital ne zanyo scan, ita kuwa Mommy nasan zamu haɗu acan..."
Hafzat tace "toh Aunty a dawo lafiya"
Kai tsaye part ɗin sarki Raamud ta nufa wanda yake da tazara sosai da falon, tacan cikin falonsa akwai hanyar fita waje, tana shiga falon ta tarar baya nan, daga nan ta wuce bed room ɗinsa a bakin ƙofa ta tsaya tana knocking a hankali, daga ciki akayi magana tareda cewa "waye?"
Cikin sassanyar murya tace "Ni ce Abba..."
"Ok shugo mana" daga ciki ya bada permission..
tura ƙofar tayi tareda sallama ta shige ciki da murmushi a fuskarta ganinsa akan sallaya da Alkur'ani mai girma a gabansa, zuwa tayi ta zauna a kusa dashi tace "ina kwana Abbana.."
shima da murmushi a fuskarsa ya amsa mata cike da zolaya yace "Ɓingel Maman twins.."
zaro ido tayi tareda toshe bakinta da hannayenta biyu ciki² take faɗin "haba dai Abba twins kuma, a'a ni da guda ɗaya ɗaya zan haifa saboda samun sauƙi na..."
Dariya yayi tareda girgiza kansa idonsa akan Kur'ani yana shirin rufe shi yace "Ɓingel kenam har yanzu dai bakiyi wayo ba, yanzun sai ina?..."
ɗan turo baki tayi cikin shagwaɓa tace "hospital zanje.."
yace "a'a toh tashi kije kar lokaci ya ƙure miki, nima yanzu wanka nake son shiga.."
tashi tayi tareda cewa "toh Abbana saina dawo"


★★★★★★

Ata ɓangaren Lailah kuwa ta samu sauƙi sosai domin yanzu tana cikin hayyacinta amma saidai bata iya gane kowa,
yanzu waɗanda ta sani sun dawo mata tamkar sababbin fuskoki, amma zata zauna tayi hira da mutum, a yanzu dai iya Doctor Mansur kawai ta sani domin a koda yaushe shine a jikinta, koda wasa bai taɓa gajiyawa da ɗawainiya da ita ba, kuma wani ƙakƙarfar alaƙa ne ya shiga tsakaninsu wanda idan Lailah bata ga Doctor Mansur ba hankalinta tashi yake, shi kuwa baya ƙaunar tashin hankalinta shiyasa baya barin yanda take saidai idan tana bacci,
Doctor Mansur yana iya ƙoƙarinsa akan Lailah tasan tana da ƴan uwa musamman Doctor Hasheem da yake prison, koda yaushe yakan bata labarinsa har tasa a ranta cewa tana da Yayanta a prison kuma ana yawan nuna mata photonsa hakan yasa take muradin ganinsa,
yau ma kamar kullum tana zaune a saman gado shi kuma Doctor Mansur yana kusa da ita a zaune a bakin gado yana ɓare mata wasu maganinnuwa da bottle na ruwa akan table,
ta ƙura masa ido sai kallonsa take ko ƙibtawa bata yi tana motsa baki a hankali cikin sassanyar murya tace "JAAN..."
ɗagowa yayi da kyawawan idanuwansa yana kallon cikin taurarin eyes ɗinta da murmushi a fuskarsa ya amsa mata da "Na'am Baby..."
cikin kasalalliyar murya tace "kai kyakkyawa ne.." suna cikin kallon juna ya ƙibta mata ido ɗaya tareda kai hannunsa saitin bakinta yace "HAAAA buɗe bakin ki kisha magani.."
a hankali ta buɗe ya saka mata su tareda kafa mata bakin gorar ruwa, haka take shan ruwan tana lumshe ido,
shi kuwa hakan ba ƙaramin burgeshi take yi ba, shima haka ya ƙura mata ido da kyawawan sex eyes ɗinsa,
a cikin zuciyarsa kuwa cewa yake "Masha Allah! tabarakallah Godiya ta tabbata ga sarkin halittun duniya wanda ya halitta mun wannan kyakkyawar ɗawisu, Yaa Allah ka mallaka mun wannan halittar ka a mazannin matata ta Aure..."
duk Abunda yake so a game da mace gaba ɗaya Lailah ta tara su,
Lailah she is a black beauty, amma saidai baƙinta na haske ne domin babu mai cemata baƙar fata, chaculate colour sannan ta haɗa da ido da kuma ƙaramin baki sai dogon hanci,
itama tanada sumar gashi babu laifi bugu da ƙari kuma tanada ƙyakykyawar surar jiki, domin a dire take Lailah tafi Ayush da Maimoon dirin jiki,
Lailah ganin kallon da Doctor Mansur yake mata babu ƙarshensa yasa ta matso daf dashi takai bakinta saitin fuskarsa tana hura masa iskar bakinta, a ruɗe yayi firgit ya dawo hayyacinsa yana sauƙe numfashi da smile a fuskarsa, ita kuwa komawa tayi ta zauna a yanda take tana binsa da kallo,
wani irin yanayi yaji ya shiga lokaci guda daman hakane indai ya zauna a kusa da Lailah ya ɗan juma to saiya shiga cikin wani hali na feeling, ba shiri ya miƙe tsaye tareda faɗin "Baby zanje na ƙarasa Ayyukana amma zan dawo ba jumawa..."
yana kaiwa nan ya nufi hanyar fita har ya buɗe ƙofa zai fita ta katse shi da cewa "JAAN..."
juyowa yayi yana kallonta haɗe da sau mata ƙayataccen murmushi yace "My Baby..."
turo ƙaramin bakinta tayi a shagwaɓe tace "yau ɗin ba chaculaty ne?..". Dariya yayi har saida fararen haƙwaransa suka fito yace "waya gaya miki ana fashin kawo wa Baby chaculate ne? na yau ma yafi na kullum..."
sumbatar tafin hannunta tayi sannan ta hura masa iskar, yayi saurin dunƙule hannunsa kamar ya karɓi saƙon sannan ya ɗora hannun akan saitin zuciyarsa yana shafar wajen,
Lailah cikin jin kunya takai hannayenta biyu ta rufe fuskarta tana dariya,
shima da dariya yabar cikin ɗakin tareda rufe mata ƙofa....
Bayan fitarsa da awa ɗaya saiga Mommy ta turo ƙofar ɗakin Lailah da sallama a bakinta, lokacin Lailah har tayi nisa a baccin ta, zuwa tayi dab da gadonta ta zauna akan kujerar da yake fuskantar Lailah! zuba mata ido tayi tana tausaya mata a halin da take ciki, ga ta rasa tunaninta ga kuma Babban Yayanta a prison ga babu iyaye, tana cikin wannan tunanin taji ana faɗin "wacece ke? mezaki mu? kada ki cutar dani dan Allah, wayyo Doctor! Doctorr!! JAAN kazo ka temake niiii...." ta ƙarisa maganar tareda fashewa da kuka,
ita kuwa Mommy kaɗa mata hannu take tareda cewa "A'ah Lailah ki saurare ni, nasan kin manta ni amma Ni ba cutar dake zanyi ba, ki kwantar da hankalinki..."
Lailah girgiza mata kai take alamar bata gamsu da jawabanta ba, suna cikin wannan halin saiga Doctor ya shugo yana riƙe da baƙar leda, ya ƙarisa shugowa da sauri ganin yanda Lailah take ta kururuwa, zama yayi a bakin gadon ya kamo hannunta yana matsa mata a hankali, yace "colm down Baby, ki daina jin tsoron mutane domin sun zo duba lafiyarki ne bawai cutar dake ba, idan kikayi musu haka baki musu adalci ba, a yanzu kin mance komai but kina buƙatar ƙwanciyar hankali yanda zaki sake sabunta rayuwarki, waɗanda kika mance a baya yakamata ki dawo dasu cikin rayuwarki kinji koh Baby..."
Lailah fashewa tayi da matsanancin kuka tana faɗin "kenam wannan mah inada alaƙa da ita? wacece ita a gurina ina buƙatar sani domin na karɓeta da hannu bibbiyu..."
Doctor ya kalli mommy sannan yace "Hajia saidai kiyi mata bayani da kanki tinda har zata saurareki.."
Mommy hawaye ne ya kuɓuto mata tasa hannu tana gogewa tareda matso da kujerar ta kusa da ita tace "Lailah ki ƙwantar da hankalinki wannan ƙaddarar daya afku dake Allah Ubangiji yasa shine mafi Alkhairi agareki, Allah yasa canjin rayuwarki shine silar shiryuwarki akan komai duk da bana shedar ki akan aikata laifi amma na sanki da yawan faɗa da masifa...". Mommy ta ƙarasa maganar cikin zolaya tareda ja mata hanci, itama Lailah saida ta murmusa jin yanda mommy taso da nishaɗartar da ita,
Mommy ta cigaba da cewa "Ni Abokiyar mahaifiyarki ce wacce ta rigamu gidan gaskiya, ni nake yawan kula da al'amuranku ke da ƴan uwanki tin kuna yara da iyayenku suka rasu, kuna ƙirana da suna Mommy kasancewar kunbi bakin ɗana wato Junaid domin shi kawai na haifa..."

Lailah ƙura mata ido tayi har saida ta kammala sannan tace "na fahimce ki Mommy, kenam iyayena tin ina ƙarama suka mutu suka barni? niɗin marainiya ce daman? Allah Sarki mommy mun gode miki da ƙoƙarin da kikayi akan mu,
toh Amma su nawa ne ƴan uwana?.."
Mommy tace "ku huɗu ne Lailah, Babban Yayanki shine Doctor Hasheem wanda yanzu haka yana prison, sai kuma wanda ya biyo shi shikuma yana ƙasar Egypt karatu, sai kuma haidar wanda yanzu yana can Katsina gurin kakarku, kece kawai mace acikinsu kuma Auta..."
Lailah cikin yanayin tausayi tace "toh amma meyasa su ƴan uwan nawan basu zo sun dubani ba?.."
Mommy tace "saboda gudun tashin hankalinsu hakan yasa ba'a sanar musu rashin lafiyarki ba kuma hatta shi babban Yayan nakun basu san yana prison ba, amma da yardar Allah Yayanki ya kusan fitowa..."
Lailah tace "gwara ma da ba'a gaya musu ba saboda kar hankalinsu ya tashi, amma keɗin mommy ya sunan ɗan nakin?.."
Mommy tayi ajiyar zuciya tana mai jinjina wannan al'amarin daya faru da Lailah, gashi wanda take mutuwar so mah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login