Showing 24001 words to 27000 words out of 186041 words

Chapter 9 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53927

ne yayi maganar yace "yes come in"
turo ƙofar akayi a hankali,
da mamaki a fuskar su suke kallon Aditi wacce take a silent jikinta duk ya mutu ga hawaye caɓa-caɓa a fuskarta,
da sauri Junaid ya miƙe ya nufi gurin da ta tsaya yana faɗin "Aditi what is wrong with you? why are you crying?.."
hannu tasa ta rungume shi tana kuka, shima rungumarta yayi yana rarrashinta,
daga baya ya ɗago da fuskarta suna fuskartar juna yace "took to me mana Aditi.."

tana kuka tace "nima an ƙirani agurin aikin mu wai na koma china a yau akwai yaƙi a gaban mu,
kuma nasan a yaƙin nan babu wanda zai dawo da ransa..."

ajiyar zuciya ya sauƙe tareda cewa "ki kwantar da hankalinki Adity, insha Allahu zamu ci nasara akan yaƙin nan, babu wanda zai mutu kinji ko.."
ɗaga masa kai tayi sannan tace "to ni yanzu zan wuce airp inason jirgin da zai tashi da wuri, akwati na yana falo already nayi sallama da mommy itama tana jirana a falo.."
hannu yasa yana goge mata hawayen fuskarta yace "muje mu to na kaiki filin jirgin..."
juyawa sukayi suka fice daga cikin room ɗin a tare,
sai iya Angel kawai suka bari a zaune a bakin gado,
Aditi kuwa ko lura da ita batayi ba tsabar idonta a rufe suke damuwar ta shine yaƙin da zasu fita...

bayan sun sauƙa downstair Aditi ƙara rungumar mommy tayi suka sake yin sallama,
Junaid yace "mom zan rakata....."
mommy tayi saurin ɗaga masa hannu tareda cewa "kar ka mun magana Junaid..."
yace "toh..."
ya riƙe hannun Aditi suka fita yana jan akwatin kayan ta..

☆☆☆☆☆

ata ɓangaren su Doctor Hasheem kuma yana zaune a falo ne shi da Lailah suna kallon plasman,
Lailah har yanzu haushin Aditi take yi dukan da tayi mata, amma ta wani ɓangaren ta sauƙo zuciyar ta wasarr take tura video da tayi wa Junaid, ita kaɗai sai murmushi take tayi tana tunanin awani hali Ayush take ciki ne domin tasan halin ogah Junaid saiya ɗauki ƙwaƙƙwaran hukunci akanta...

tana cikin wannan tunanin taji Doctor Hasheem yana cewa "ni Lailah kin kaiwa Maimoon abinci kuwa?.."
a zabure ta miƙe tana faɗin "wallahi na manta bros bari nakai mata..." ta nufi kitchen ta ɗauko flask ɗin abinci da flask ɗin ruwan shayi ta miƙi hanyar da zai kaita ɗakin da maimoon take..

Maimoon tana zaune akan katifa taji motsin mutum yana tafowa da sauri ta miƙe tsaye ta laɓe a bakin ƙofa,
daman ta ƙudurta a ranta cewa yau kam zata bar gidan nan, zata koma gida tinda yanzu ta samu sauƙi tafiyarta ya koma normal,
ɗaukar ƙwalba tayi acikin ranta tace "wallahi ko waye rausa masa zanyi akai domin ba mai dakatar dani akan hanyar tafiyata.."

Lailah ce tasa key ta buɗe ƙofar da kayan abinci a hannunta ta shugo, tana shugowa kuwa Maimoon ta ɗaga ƙwalbar nan ta kwaɗa mata a goshi,
wani irin ƙara Lailah tayi, tasau kayan abincin a ƙasi ta dafe goshin nan ta faɗi a ƙasi sumammiya,
haka Maimoon ta tsallake ta da gudu tayi hanyar fita adaiden lokacin saiga Doctor Hasheem ya tafo jin ihun Lailah,
ƙoƙarin tare Maimoon yake yana faɗin "ina zakije kuma?.."
ƙure mata gudu yayi ya riƙo kunkumin ta ya ɗagata saman kafaɗarsa, ihu take tana kururuwa ganin yana shirin komar da ita cikin ɗakin yasa ta kafa bakinta a saitin wuyansa ta gasa masa cizo, ai kuwa ba shiri ya sauƙe ta ƙasi, yana sauƙeta ta zage tayi masa wani ƙwaƙƙwaran bugu a saitin penus ɗinsa da gwiwowinta, durƙusawa yayi yana ihu..
a lokacin ta samu damar fece wa har saida ta isa bakin gate ta buɗe tana fita kuwa saiga mai keke napep tayi saurin hawa suka miƙi bakin hanya....

☆☆☆☆☆

Ɓangaren Sarki Raamud..

yana zaune yana jimamin mutuwar Narasimha ga kuma nakasa shi da akayi, shi sai a wannan lokacin ya fahimci matarsa bata gani sannan bata ji, azabure ya riƙo ta yana girgiza ta tareda ambatar sunanta "BB! BB!! BB!!! meya faru dake dan Allah kiyi mun magana mana.."
ita kuwa babu bakin magana sai hawaye,

Munafurr yana zaune akan kujerar sarauta yaji sarki Raamud duk ya rikirkice yana ta ƙiran sunan matarsa,
tintsirewa yayi da dariya tareda faɗin "taurin kan ka ne ya jawo nayi muku hukunci daidai daku,
kai na raba ƙafafunka biyu, ita kuma matarka na makantar da ita sannan na kurmantar da ita, shi kuma wanda kuka ɗauke shi a matsayin abun kariya na gama da rayuwarsa, na raba kansa da gangar jikinsa...." ya sake tintsirewa da dariyaa...


Sarki Raamud ne ya ɗaga hannayensa biyu ya haɗe su guri guda yana hawaye yace "Munafurr da roƙeka ka tausaya mun ka sassauta hukuncin ka akan matata domin ita bata san komai ba, ni na yadda kamun komai amma ka ƙyale matata..."

Munafurr kallonsa yayi da jajayen idanuwansa sannan yace "ni banida niyar cutar dakai, amma ka nuna mun taurin kai ne, ka saɓa alƙawarin da muka ɗaukar..."

Sarki Raamud yace "kayi haƙuri indai mulki ne na bar maka, na bar maka masarautar nan, amma ka warkar mun da matata.."

ƙara tintsirewa da wani irin mahaukaciyar dariya Munafurr yayi sannan yace "yanzu naji magana Raamud, bama iya matarka zan warkar ba hatta kaima zan warkar da ƙafafuwanka amma bazaku fita daga cikin masarautar nan ba saboda kana fita kwananka ya ƙare domin mutanen garin jira suke ka fita su ɗau ranka,
zaka zauna da matarka a cikin ɗakinku ban yarda ku leƙo nan falon masarautar ba, zan kafa nawa tarihin acikin wannan masarautar, zan kafa nawa manya-manyan Aljanu acikin wannan masarautar, zan ninka ka ƙarfin ikon da kake dashi a bayaa..."

yana gama maganganunsa kuwa ya busar da hayaƙin bakinsa kan Bara'at, nan danan idanuwanta suka buɗu, bakinta ya buɗu,
shima sarki Raamud ɗin an warkar da ƙafafunsa sun koma normal,
Bara'at kallon sarki Raamud tayi tana kuka ta rungume shi sosai, shima rungumarta yayi yana rarrashinta...

Munafurr ne ya darara musu tsawa tareda faɗin "ku tashi ku koma cikin ɗakin ku, matarka tanada ciki har ta haihu kar naga kowa acikin ku ya fito falon nan, domin zan zuba manya-manyan aljanu ne suyi mun gadi....

da sauri Sarki Raamud ya ɗauki BB suka nufi upstairs mai hawa uku nan ne ɗakinsu ...


☆☆☆☆☆

Mommy tana zaune a falo kan sofa saiga Angel ta sauƙo down sai faman kalle-kallen saman falon take kamar mai duba abu,
Mommy tace "ke kuma fah Angel mai kike nema?.."
tace "mom ina duba cameran falon nan ta ina yake.."
mommy ta ɗaga yatsanta tace "gashi can.."
Angel da sauri ta kalli gurin tana faɗin "yes good! good, yanzu komai zai zomun a daidai, zan duba shige da ficen mutanen da suka shugo, zanga wannan mummunan mutumin shi da wa suka shugo ɗakin nan..."

Mommy tace "bangane mai kike nufi ba?.."
Angel tace "mom akan matsalar video da akayi wa Ayush ne, inaso na kawo ƙarshen matsalar..."

Mommy tace "kina tunanin ba ita bace?.."
Angel tace "gaskiya ita ce amma bana tunanin a cikin hayyacin ta akayi mata haka, amma ko ma waye yasa akayi mata haka sai na gano shi kuma zan sa a kamo shi dumu=dumu..."

Mommy tace "gaskiya nima abun ya ɗaure mun kai, har yanzu ban yadda cewa Ayushert zata iya aikata haka ba, to ma yarinyar da ba fita ko ina take ba balle tasan mutane aina zata samo mutumin nan? kuma ba wayane a hannunta ba, da iya Junaid kawai ta shaƙu, bata san kowa ba inba Junaid ba,
ni ko cewa akayi tayi ciki wallahi zanyi tunanin Junaid ne yayi mata, amma abun yayi matuƙar ban mamaki.."

dogon numfashi Angel taja sannan tace "Allah sarki tana zaune zuciyarta ɗaya amma tanada maƙiya a gefe,
yanzu dai mom aina computer camerorin gidan nan yake? inaso zanje na duba..."

Mommy tace "tab ai duk wasu abubuwan tsaro suna ɗakin Junaid, ɗakin ma can secret room kuma bazaki san da ɗaki a gurin ba, ki bari ya dawo saiki lallaɓashi kije ki duba duk da baya barin kowa ya shiga amma wata ƙil ke ya iya barinki tinda ga wayarsa ma a hannunki..."

dariya Angel tayi sannan tace "haba dai nifa ƴar hannun damarsa ce pah, ƴar gaban goshinsa kuma ƴar amanarsa ai dole ma ya barni na shiga wannan ɗakin domin aiwatar da bincike na, tinda shi baya duba camerar tsaro bai san abunda ke wakana acikin gidan ba,
shi wato yafi bada himma akan Sarki Raamud..."

tana daga tsaye ta kama kunkumi ta ɗan turo bakinta sannan ta kuma cewa "naga Aditi uwar bala'i har da kukan ta ita a dole tana tsoron karta mutu, ashe duk bala'in ta tana tsoro? nipa Mom wallahi yaƙin nan da za'a fita ko a jikina domin bana jinsa a raina, kwata-kwata ban damu ba..."

Mommy tsaya kallonta tayi tace "Hmmm! toh ke kuma uwar surutu kafin ki gama surutain nakin kije kitchen ki girka mana Indomie, domin yunwa nake ji, ga Ayush itama yanzu bata samu taci...."
Angel wuce wa kitchen tayi tana cewa "kafin na kammala ai Oga Junaid zai dawo, sai yaje ya buɗe mun secret room ɗin...."

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 15 ➡️ 16

Ayush tana kwance abun duniya duk yabi ya isheta, kwatsam sai abu ya faɗo mata arai! a razane ta tashi tana faɗin "littafin tarihin mahaifina, yana ina? na shiga uku aina na ajiye shi, kar wani ya ɗauka, asiri na zai tonu wayyo.."

dasauri ta tashi ta buɗe ɗakinta ta nufi ɗakin Junaid, cikin sa'a kuwa ta samu ɗakin a buɗe ta shige, bincike ta soma yi a ɗakin tana ɗarɗar kar yazo ya sameta, gaba ɗaya drowers ta bubbuɗe da wardrobe amma bata ga alamar littafin da takobin ba, zama tayi a bakin gadonsa tayi tagumi tana tunanin aina zata samu takobi da kuma littafin, hankalinta ne ya dawo jikinta ta ɗago tareda kai eyes ɗinta waran secret room, a ranta tace "wancan ɗakin na meye neh? me ake ajiye wa a gurin? tabbas indai Yaya Junaid yaga waɗannan abubuwan to bazasu wuce can ɗakin ba..."
tashi tayi a hankali take tafiya har ta iso saitin ɗakin tasa hannu ta tura ko zai buɗu cikin rashin sa'a taji ɗakin a rufe ansa masa key, yarfe hannayenta biyu tayi cikin nuna damuwa tace "kashhh..."
a ruɗe ta juyo ta nufi drowers tana checking key ɗin ɗakin, duk ta duba bata gani ba, har ta haƙura ta juya zata fice a ɗakin tayi tunanin ɗaga pillow bed ɗinsa, tana dubawa kuwa saiga key, a hanzarce ta ɗauka taje ta buɗe ɗakin, abunda ta fara gani shine ƙaton photon mahaifinta, shi ya ja hankalinta taje gaban photunan dake a mammanne a jikin bango ta tsaya, ganin photon mahaifiyarta kuma yasa ƙirjinta bugawa da ƙarfin gaske, kafin kace wani abu hawaye duk ya wanke mata fuska, tana kallonsu tana zubda hawaye ita har ta manta abunda tazo dubawa, tana cikin wannan halin taji motsin mutum ta wajen ɗakin wato bedroom, gabanta ne ya yanke tana faɗin "innalillahi wa inna'ilahi raju'un, nashiga uku ya dawo..."


Bayan shugowar Junaid cikin ɗakinsa zama yayi a bakin gado ya dafe kayinsa da hannayensa biyu yana kallon ƙasi kamar mai tunanin wani abu, yana cikin wannan halin yaji an turo ƙofa an shugo, ɗaga kansa yayi ya kalli Angel ya maida kansa a yanda yake tareda faɗin "jarababbiya kin dawo kenan.."
Zama tayi daf dashi tace "my man daman kai nake jira ka dawo, akwai wata alfarmar da nake so kayi mun.."

Ɗagowa yayi yana kallonta yace "ina jinki..."
tace "daman! daman!! daman so nake na duba cameran tsaro na gidan.."
yamutsa fuska yayi yace "mezaki duba?..."
cikin shagwaɓa take magana tace "inason duba fice da shige na mutane a ranar shagalinka.."
Ba tareda ya kalleta ba yace "akwai abunda ya faru ne agidan?.."

Kamar zata yi kuka tana yarfe hannu tace "kaiii Ogah Junaid I can't answering your questions is too much.."
juyowa yayi yana kallonta cikin yanayin jin bacci yace "ok leave my room if not.."

tana turo baki tace "toh daman akan case ɗin Ayush ce..."
girgiza kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login