Showing 36001 words to 39000 words out of 186041 words

Chapter 13 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53908

cin abincin,
yace "wacece ke?.."

wani irin tambaya yayi mata wanda ita kanta saida ta ɗan razana, still kallonsa take ta kasa buɗar bakinta,
yace "Yushert abunda banaso kenam idan nayi wa mutum magana ɗaya inaso ya amsa mun ne akan lokacin, ki kwantar da hankalinki magana nake so nayi dake ta fahimtar juna, ki faɗa mun gaskiya bana son ƙarya da salon yaudara..."

Ayush hawaye ta fara zubar wa domin tasan maganar bazai wuce akan video nan ba,
tana cikin wannan tunanin taji yace "wacece wannan matar mai niƙab wacce tazo a ranar shagali na??"

Gaban Ayush ne yayi matuƙar bugawa da ƙarfin gaske sai wani daram-daramm kake ji, sauran kaɗan ya hana zuciyarta bugawa, ta zaro ido waje ta kafe shi da kallo..

Shima kallonta yake yi yace "ina jinki..."
Girgiza masa kai kawai tayi babu bakin magana,
ya kuma cewa "Yushert wacece matar nan da kike ƙiranta da Uma?..."
nan ma shuru tayi mishi girgiza masa kai kawai take,

Jinjina kai yayi ya kawar da kansa gefe cike da takaici domin ya tsani yayi wa mutum magana ya tsaya yana kallonsa, still juyowa yayi idonsa akan nata ya kuma cewa " Yushert wacece matar da ta ɓace bayan ta fito daga ɗakin ki?.."
wannan lokacin kam Ayush har da sakin fitsari tana zaune bata ma san tanayi ba,
sai ƙarar zubar fitsarin kake ji yana sauƙa akan tiles tsuuuuuu🤣🤣🤣

Ogah Junaid kam jin sauƙar fitsarin ne yasa ya leƙa ƙasan kujerar da take zaune yaga fitsari yana zuba, shi yayi tunanin kofin ruwane ya zuba daga saman table, ɗagowa yayi yana kallonta cike da mamaki yace "Yushert bakida gaskiya kenam? meye manufarki na zama tareda mu? kinyi ƙaryar cewa bakida kowa ashe ke ba mutum bace, ashe ke ahalin Aljanu ce?, toh meyake tafe dake? inaso in sani yanzun nan.."

lokaci guda hawaye duk ya wanke mata fuska, idonta yayi jawur tana lumshe su a hankali domin ita kaɗai tasan irin tashin hankalin da take ciki...
ya kuma cewa "Yushert magana fah nake miki.."
Ayush ko ƙwakkwaran motsi ta kasa yi..
Ran Junaid ne yayi matuƙar ɓaci ganin tinda ya fara magana ko amsa ɗaya bata bashi ba,

Cikin zafin nama Junaid ya ɗaga hannayensa biyu da ƙarfin gaske ya doka a tsakiyar glass table na cin abinci
Glass dinning ne yayi wani irin ƙara ya dagargaje,
tsabar firgici da tashin hankali da kuma tsoro haka kujerar Ayush ya faɗi ta baya ta doku a ƙasi nan take ta fara wani irin shaƙuwa tana fitar da jini daga bakinta, ta zazzaro ido waje tana kallon sama tana shaƙuwa da ƙarfin gaske ga yanda taketa ambaliyar aman jini...

Mommy tana zaune a kujerar da Angel take a kwance duk saida suka razana da jin ƙarar fashewar glass table, a gigice Angel ta miƙe tsaye alokacin ma taji babu ciwon cikin,
zuciyar Mommy ne yake bugawa da ƙarfin gaske tsabar tsoritar da tayi duk suka nufi gurin da gudu!
Mommy tana faɗin "nashiga uku meya faru kuma du Junaiddd..."
Angel ganin yanda Ayush take kwance ido a ƙafe ga shaƙuwarta yanda yake dukan dodon kunnuwansu,. da sauri ta durƙusa tasa hannu ta tallafo kayinta tana ƙiran sunanta "Ayush! Ayush!! Ayushert!!! meya faru da ita haka..."

Mommy kam tsayawa tayi tana kallon yanda Ayush take tayi tama rasa yanda zatayi gaba ɗaya ta ruɗe, ta rasa mai zatayi ɗaya...

Shi kuwa Junaid yana zaune idonsa akan Ayush ya kasa motsawa shima jikinsa duk yayi weak, ga hannayensa duk sun faffashe sai jinin da yaketa zubarwa, ba ƙaramin ciwo yaji ba...

Angel ce tace "Mommy mu gaggauta kaita hospital dan Allah, zata iya mutuwa fah..."
agigice Mommy tasa hannu zasu ɗauki Ayush! Junaid ya katse su da cewa "kar ku yadda kuje hospital, ku kaimun ita room ɗina..."

Mommy tace "baza mu barta a gida ba, ciwo ba ƙaramin ciwo ba, idan baka sonta toh ni ina sonta, kar ka ƙara shiga shirgin Ayush daga yau! babu ruwanka da ita ko meye zatayi, ai ba kai ka kawota gidan ba kuma ba'ace wannan gidan naka bane gidan mahaifinka ne, idan kuma kana gadara da gidan mahaifinka ne toh zamu fita mubar maka gidan inyaso zanje na sayi gidan da zan zauna da Ayusher....."
Mommy tana kuka haka ta ƙarasa maganar tana riƙe da Ayush zasu huce Junaid ya miƙe a tsawace yake faɗin "ita ɗin ba mutum bace Aljanace, bamu san meye manufarta akan mu ba, ta ce batada iyaye ashe ƙarya take iyayenta Aljanu ne..."

Angel da jin wannan batun tayi saurin kwantar da Ayush taja da baya tana mammannewa ajikin bango,
Angel a rayuwarta bata son shiga harƙar Aljanu, tana mungun jin tsoron Aljanu, a duniyar nan ba abunda tafi jin tsoro kamar Aljanu, lokaci guda jikinta ya fara rawa tana kakkarwa! tinda tayi gamo da Aljani a asalin suffar su marasa daɗin gani daga nan take yawan mafarki mai ban tsoro na Aljanu kuma bata son taji an ambatu sunan Aljanu...

Mommy gaban Junaid taje ta tsaya tace "meye hujjarka na cewa Aljana ce? shin kofato ka gani a ƙafarta ne ko meye? toh bari na gaya maka ko ita mayyace mai cin naman mutane zan zauna da ita, saidai kabar gidan nan ko kuma ni nabar maka gidan amma Ayush ba yanda zataje a cikin gidan nan, ƙafarta ƙafata don haka karna sake jin wannan batun a bakinka,
Kuma last warning idan ka sake musguna wa rayuwar wannan yarinyar ko kuma ka sake dukanta toh wallahi wallahi saina tsine maka, kuma nabar maka gidan...."

Juyowa Mommy tayi ta kama Ayush zata ɗagata tace wa Angel "zo ki tayani mu ɗagata hospital za'a kaita.."
Angel tana manne da jikin bango tace "a'ah Mommy bazan iya ba..." muryar ta na kakkarwa kamar mai yin zazzaɓi,
Mommy tace "Angel kodai cikin nakin ne?.."
dasauri Angel tace "eeeeh ciki nane..."
Mommy tace "toh shikenam Allah ya yaye miki.." tayi ƙoƙarin ɗaga Ayush suna tafiya a hankali zasuyi waje...

Da gudu Angel ta wuce ɗakinta taje tasa sakata..
Mommy har sun doshi ƙofar fita daga falon taga an ɗaga Ayush sama dasauri ta waiwayo taga Junaid ne ya ɗorata akan kafaɗarsa yana kallon Mommy yace "am sorry Mom banaso akaita hospital kuma du ace mun ta ɓata, ki ƙira Doctor yazo har gida yayi mata magani..."
yana kaiwa haka ya juya ya nufi upstairs da ita, kai tsaye room ɗinsa ya shiga..

Mommy tsabar takaici kasa cewa komai tayi sai tsaya kallonsa da tayi har ya kule mata,
zama tayi akan kujera tayi tagumi...
Lokaci guda ta zabura ta miƙe da sauri taje ta ɗauki phone ɗinta ta ƙira number Doctor Samuel emergency...

Tana katse ƙiran tajiyo jiniyar motar sojoji, zama tayi akan kujera bata bi takansu bama,
Sojoji guda uku ne suka kawo Sauro bayan sunje an cire masa bullet a ƙafarsa,
shugo dashi sukayi kai tsaye part ɗin horo suka wuce dashi, suka zaunar dashi akan chair suka ɗaɗɗaureshi da igiya a jikin kujerar,
Sai nishi yake tayi tsabar azabar daya sha a hannun sojojin kafin su kawo shi,
suna gama aikinsu sukayi tafiyarsu, daman Ogah Junaid yace musu a gidansa zai hukunta shi...

Sojojin nan suna tafiya saiga motar Doctor Samuel ya tafo da kayan aiki,
Angel ce ta fito da gudu ta wuce Mommy a falo ta fice waje,
Mommy sake baki tayi tana kallonta tace "ohhhh mai ciwon ciki..."

Angel tana fita taci karo da Doctor Samuel bata tsaya bin ta kanshi bama tayi wucewar ta, shi kuwa kallonta ya tsaya yi har ta ƙule masa amma bai daina leƙenta ba har yaje ya gwara kansa ajikin bango bai saniba, saida ya bugu tukun ya dawo hayyacinsa ya shige falon..

Ita kuwa Angel gurin sauro taje tana zuwa ta cankeshi da ƙafa saida ya dungura, duk fuskarsa ya kumbura tsabar mazgar daya sha, ɗago kansa yayi ganin Angel ce kawai ya fara tintsirewa da dariya irin mai ƙona rai ɗin nan, Angel ta gama fusata haka ta ɗauki wani katako ta fara jibga masa amma bai daina dariyar ba, duk da yana jin zafin dukan amma bai nuna mata ba haka yaketa mata gwaliyo yana dariya,
yana mata hakane saboda ya ƙuntata mata...

******
Bayan Doctor Samuel da mommy sun shiga ɗakin Junaid! tarar dashi sukayi yanata danna ƙirjin Ayush, ya buɗe bakinta yana hura mata iskar bakinsa sakamakon rashin numfashi,
Ga yanda jini yake fita daga bakinta amma haka yake haɗe musu baki guri ɗaya yana hura mata iska,
Shima bakinsa yayi baje-baje da jinin bakin Ayushh
🤮🤮🤮🤮🤮🤮

Mommy da Doctor haka suka tsaya suna kallon ikon Allah,
shi Junaid bai ma san sun shugo ba, saida ya ɗago tukun yayi ido huɗu dasu
kana ganin shi kasan akwai damuwa a tattare dashi,
A fusace ya dakawa Doctor tsawa yana faɗin "toh tsayuwar mai kake yi, kazo ka dubata! banaso na rasata domin ita ɗin bugun zuciyata ce..."

Doctor dasauri yayo kan Ayush yana dubata ɗagowa yayi yace "batada jini pah.." yayi maganar ta harshen turanci,
Junaid miƙa masa hannu yayi yace "gashi kayi sauri ka ɗibi jinin..."
Doctor da saurinsa ya nemo allura da ledar saka jini ya soma jan jinin Junaid saida ya ɗebi leda guda na jini, tukun ya ɗaurawa Ayush!
Junaid ana gama ɗebe masa jini ya shige toilet ya wanke jinin bakinsa yayi brush tukun ya fito yayi ficewarsa acikin ɗakin...

______________ Angel kuma tana nan tana ta faman dukan mutuminta shi kuwa bai daina mata dariya ba,
dukansa take shi kuwa dariya yake mata duk ta faffasa masa jiki,
duk abunda yake yi kuwa Ogah Junaid yana tsaye a bakin ƙofa yana kallonsu, Angel har da kukanta tsabar takaici sai dariya yaketa mata,
Junaid ƙarasa shugowa yayi yazo gaban Sauro ya tsaya, alokacin ne Angel ta dakata da dukansa, shi kuwa Sauro ganin Junaid yasa yayi shuru da yin dariyar yana zazzaro da idanuwansa,
Junaid hannu yasa ya ɗago kujerar Sauro ya zaunar, shima kujera ya jawo ya zauna yace wa Angel ta miƙo masa jakar gefenta, acikin jakar kuwa tarukucen kayan horo ne har da su guduma ta miƙo masa ya ɗauko wani ƙaton almakashi na ƙarfe mai kaifin bala'i!

Sauro yana ganin ƙarfen da yake hannun Junaid ya fara zaro ido waje yana fitar da gumi,
Itama Angel tana tsaye tanason ganin shin wani irin hukunci Ogah Junaid zai aikata,
Fuskar Junaid ko Annuri babu haka ya kamo hannun Sauro ya saita ƴar ƙaramar yatsansa tin daga dungun da wannan ƙaton almakashin ya datsa yatsar,
Wani irin ihu Sauro ya ƙwallla su mommy suna can cikin ɗakin Junaid saida suka razana da wannan ihun,

Itama Angel rufe idonta tayi sosai bata son ganin wannan hukuncin,
Ɗan ƙaramin yatsar Sauro ne ya faɗo ƙasi, yatsunsa sun zama guda huɗu kenam,
Haka Sauro yake ihu kamar ransa zai fita, haka Junaid ya kamo ɗayan hannunsa yana ƙoƙarin yanke ƙaramin yatsar kuma du,
Haka Sauro yake magiya yana roƙonsa akan ya kyale shi haka, roƙonsa yake yana haɗashi da girman Allah yace "wallahi tallahi Lailah ce ta sakani amma ni bansan yarinyar bama sai a lokacin, Lailah ce ta bani dubu hamsin tayi mana video bayan ta bata ƙwayar maye da kuma tada sha'awa, amma banida laifi kayi mun rai Ogah Junaid...."
Itama Angel riƙe kafaɗar Junaid tayi tace "kayi haƙuri My man hukuncin yayi tsauri ka barshi haka, ka gundule masa yatsa ɗaya ka temaka karka yanke ɗayan..."

Junaid baice musu komai ba haka ya miƙe yana ƙoƙarin ficewa yace wa Angel "ki kunce shi yayi tafiyarsa idan zai iya, idan kuma bazai iya ba sai ki sa a nemo tifa a ɗauke shi...
Daga nan yayi ficewarsa.....



*DAN ALLAH KUYI MUN COMMENTS IRIN NA JIYA, ALLAH JIYA NAJI DAƊIN COMMENTS ƊINKU...*

*MASU FITA YAƘI KU AJIYE KAYAN YAƘI TUKUN DOMIN AN ƊAGA TAFIYAR SAI AN HUKUNTA LAILAH🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹*

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 21 ➡️ 22

Junaid fitarsa daga gida kai tsaye gidansu Lailah yayi,
yana zuwa ƙofar gidan ya sauƙo daga cikin motarsa ya fara knocking da ƙarfin gaske, maigadi ne ya buɗe yana masifar "wai waye wannan baƙon buga gate ne? haba jarababbu kawai.."
yana buɗewa yayi kucuɓus da Oga Junaiddd yanata huci, maigadi zaro eyes yayi waje jikinsa na ɓari yake furta "innahu min sulaimanu wa innahu Bismillahi rahmanu rahiiiim, ƙalu innalillahi wa inna ilaihi raju'unnnn...." bai ƙarasa addu'ar ba Junaid ya zabga masa wani irin gigitaccen mari har saida ya dungura, yayi wucewarsa ciki ba excuse..
yana zuwa ya tura ƙofar falo cikin sa'a kuwa yaci karo da Lailah tana kwance akan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login