Showing 183001 words to 186000 words out of 186041 words

Chapter 62 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53940

Shikam Areeph ƙin zuwa yayi yana tsaye sai faman haɗe rai yake tayi, shi daman baiyi murnar Auren ba, mommy ce ta fahimci Areeph yana cikin ɓacin rai tace "Angona lafiya kuwa meyasa bazaka je gurin Aunty ba?...".
ya kawar da kai gefe tareda faɗin. "Ni indai ba mommy nah bace bana sonta, kuma naji kunce mommyna ta mutu..."
Gaba ɗaya jikinsu ne yayi sanyi daga mommy har Ogah Junaid, duk suka kasa cewa komai, ga Khubayr a cinyar Daddynsa sai tsotsar babbar yatsarsa yake idonsa akan TV dake yaro ne bai san me ake tattaunawa akai ba, kuma shi baiyo wayon yayunsa ba, saboda shi har yanzu Khubayr bai iya magana ba, su kuma triplets tin suna yashi suka fara magana...

Suna cikin wannan halin saiga Amriish ta sauƙo down tana kuka Mommy tace "takwara meya faru ne?..."
Tana kuka tana faɗin "wannan Auntyn namun taƙi buɗe fuskarta mu ganta kuma taƙi zuwa muci abinci..."
Mommy tace "a'ah kuyi mata uzuri kunya take ji..."
Mommy ta kalli Junaid sannan tace "tashi muje na rakaka ɗakin Amaryarka inyaso saiku ci abinci gaba ɗaya acan..."
Junaid bai Musa ba haka ya tashi tareda ɗora Khubayr saman kafaɗarsa sannan ya riƙo hannun Areeph suka fara taka upstairs, itama mommy tana biye dasu a baya tana riƙe da flask ɗin ferfesun chicken duk suka haura, suna shiga ɗakin suka tarar da Angel a kusa da ita tanata kokarin leƙa fuskar Amarya ta cikin mayafinta, mommy tace "Amarya bakya laifi ƴaƴanki suna son ganin fuskar Auntynsu ki temaka su ganki mana..."
Amriish itama kusa da ita taje tana cewa "muna so ki zama Mommyn mu, kinga Mommyn mu ta guje mu, ta gudu ta barmu bata son mu...."
Itama Angel tace "bamu san laifin mai mukayi mata ba, har ciwon zuciyan Amrish yaita tashi sauran kaɗan ta mutu amma taƙi dawowa..."
Amriish fashewa tayi da kuka tana cewa "bata tausayin mu, ciwo na yaita tashi ina aman jini, ƙirjina yaita ciwo sosai...". Itama Angel kuka take ta riƙo hannun Amrish tana cewa "kiyi haƙuri Amrisha kar ciwonki ya ƙara tashi kinga mommy ba zuwa zatai ba, kawai muma mu manta da ita...."
Amriish tace "Ni daman babu ruwana da mommy, yanzu bana sonta tinda ga Auntyn mu kawai sai ta zama Mommyn mu koh?...". ta ƙarasa maganar tana gayawa Angel,

Ogah Junaid yana ɗauke da Khubayr lokaci guda ya tsinci kansa a wani irin yanayi, tinin hawaye suka wanke masa fuska, jin yanda yara suke ganin laifin mahaifiyarsu wacce ta daɗe da barin duniya...

Mommy itama jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba, haka hawaye yake gangaro mata ba ƙaramin tausayi yaran suka bata ba...
Itama Amarya ta kasa buɗe fuskarta acikin mayafi duk tana jin maganganun da yaran suke yi, sun bata tausayi sosai tana daga cikin mayafin amma kuka take yi sosai...

Areeph shima matsowa kusa dasu yayi yace "na gaya muku Mommyn mu mutuwa tayi..."
Amriish tayi saurin katse shi da cewa "a'ah ba mutuwa tayi ba guduwa tayi ta bar mu..."
Angel itama cewa tayi "meyasa ba'a sanar mana ta mutu ba, kuma banga mutane sun taru a gidan ba, ta haifi ƙanin mu ta aiko mana shi amma ita taƙi dawowa saboda bata son mu...."
Amriish fashewa tayi da matsanancin kuka tana faɗin "ku daina mun maganar Mommy ciwo na zai tashi, na fara jin ƙirjina ciwooo...."
Itama Angel fashewa tayi da kuka tana cewa "kiyi haƙuri Amrisha bana son ciwonki ya tashiii..."
Shima Areeph ɗin kuka ya soma yi ganin yanda ƴan uwansa suke kuka kuma sam baya son ganin ciwon Amriish ya tashi...

Ogah Junaid shima kukan yake yi yakasa dakatar da yaran da maganganun da suke yi akan mahaifiyarsu jin Amrish tana maganar ciwonta zai tashi ba ƙaramin tsorita yayi ba, haka zuciyarsa take bugun uku uku, nan danan ya miƙawa mommy Khubayr dake hannunsa yana ƙoƙarin nufan yanda suke kar Amrish ta faɗi...
Mommy abun mamaki yake bata ganin yaran tsawon shekara biyu amma sun kasa cire abu a ransu...

Junaid ganin Amarya tayi saurin durƙusa gwiwowinta a ƙasi duk ta rungumi yaran su uku a jikinta tareda fashewa da matsanancin kuka mai ratsa zukata, kuka take sosai still fuskarta na cikin mayafi tana rungume dasu,
Yaran ganin yanda ta rungumesu tana kuka yasa suka dakatar da yin kukan suna kallonta,

Abun yayi matuƙar ɗaure wa Junaid kai shin tausayinsu ne yasa take kuka haka ko kuma mai?
Kunnuwansa ne suke jiyo masa wani irin sauti wanda zaiyi wuya ya manta kalar sautin? wato kukan da yake jin Amaryarsa take yi, haka ya matso kusa dasu hannu na kakkarwa ya janye mayafin kan Amaryar,
Cikin firgici da tsoro haka Junaid yaja baya a razane da ƙarfi yake furta "Innalillahi wa inna ilaihi raju'un...". sauran kaɗan ya faɗi ƙasi yayi saurin dafe jikin gini ido a zazzare yana kallon Amaryar...

Ɗagowa tayi tana bin yaran da kallo cikin kuka har eyes ɗinta sunyi jaa tsabar kukan data sha,
Areeph da Angel da Amrish zaro ido sukayi waje cike da fargaba duk suka haɗa baki wajen cewa " *MOMMY*.."

tana kuka tareda faɗin "ku gafarce ni yarana, dan Allah ku yafe mun! Nasan banyi muku daidai ba amma inasonku har cikin zuciyata, ina ƙaunar ku..."
Angel cikin kuka tace "Mommy kin dawo gare mu?...". ta rungumeta tareda cewa "na dawo yarana kuna nan a cikin zuciyataa..."
Amriish itama kukan take tace "mommy kika sa ciwona yaita tashi sauran kaɗan na mutu...". Cikin yanayin kuka ta jawo Amriish jikinta ta rungumesu sosai kamar zata mayarsu cikinta,
Areeph shi kam babu bakin magana yana rungume da Mommynsa shima yana kuka yace "mommy akace kin mutu ashe ƙarya akeyi baki mutu ba..."
Tace "yarona ban mutu ba, gani na dawo gareku bazan taɓa yada ku ba har abada..."
duk suna rungume da juna sunata kuka babu mai rarrashin kowa daga uwar har ƴaƴan...

Ogah Junaid kam a tsaye ya ƙafe baki na kakkarwa cikin ƙinƙina yace "Yushertttt....."
wani irin sanyi taji a zuciyarta jin an ambaci sunan da ta juma ba'a ƙirata dashi ba...
Idonta a lumshe a hankali take buɗe su har eyes ɗinta suka sauƙa akan Junaid wanda shima idonsa akanta yake,
A hankali ta ɗago da yaran daga jikinta duk ta sumbace su akan goshi sannan ta tashi ta nufi gurin da Junaid yake tsaye, wani irin kuka ne ya kuɓuce mata tayi saurin shigewa jikinsa ta rungume shi sosai tana kuka,
A ruɗe ya soma yin magana yana cewa "shin mafarki nake yi ko kuwa abunda idona yake gane mun gaskiya ne? Dan Allah idan mafarki nakeyi kada ku tashe Ni har sai na kammala ganawa da Yushert ɗina..."
Muryar mommy yaji yo tana cewa "ba mafarki bane gaskiya ne, tabbas Yushert ɗinka kake gani a zahirance ba mutuwa tayi ba tana nan da ranta..."
Junaid ɗago da ita yayi suna fuskantar juna yace "tayaya hakan zata faru tsawon shekara biyu uwa tabar ƴaƴanta, mata tabar mijinta...".
Ayush kasa cewa komai tayi sai hawayen dake gangaro mata,
Mommy tace "Ba laifinta bane nasan bazata taɓa barin ƴaƴanta har tsawon wannan lokacin ba, sannan tana ji tana gani bazata iya haifar jariri ta barshi atafi mata dashi har tsawon wannan lokacin bata ƙara ganinsa ba,
Waɗannan tambayoyin da zakayi inaso ka adana su zuwa gobe da safe duk zakaji abunda ya faru, yanzu dai kabar uwa ta gana da ƴaƴanta kaima miji ka gana da matarka...."
Ta kalli Ayush tace "ganan jaririn ki har ya isoki girma..."
Ayush tana kuka tasa hannu ta karɓi yaronta a hannun mommy tana faɗin "Khubayr my son, nayi kewarka tin haihuwarka kullum tunanina akan wannan yaron da kuma sauran ƴaƴana da mijina duk nayi kewarsu...."

Khubayr har yayi bacci yatsa a baki sai tsotsa yake kamar wanda ya samu Nono, duk da yanzu ya wuce shan Nono two years now,
Mommy ficewa tayi daga ɗakin ta basu guri, around 11:30Pm yanzu...

A wannan daren Ayushert da Ogah Junaid kwana sukayi basu yi bacci ba a yayinda sauran ƴaƴan suka jeru duk sunyi bacci gasu akan gado gaba ɗayansu, sunyi kewar junansu sosai.....


Washe Gari kowa na gidan ya hallaru a babban fadar masarauta, ga sarki ga Mommy, uncle Artaff shi da iyalansa sai Ogah Junaid da Ayush ga yaranta duk sun mamaye ta...

Uncle Artaff ne ya kalli Junaid sannan yace "kayi haƙuri Junaid mun san munyi maka laifi, mun ɓoye maka abunda baka sani ba,
Ayshert ta shiga wani irin yanayi na ciwo wanda har anyi tsammanin ta mutu bayan ta haifi Jaririnta, har anyi mata wankan gawa an suturtata acikin likkafani za'a bisineta akaga ashe ba mutuwa tayi ba, saidai ta haɗu da ciwon hauka da kuma mantau hakan yasa muka tafo da iya Jaririnta, saboda babu halin shayar dashi domin bata san a yanda take Bama, sakamakon Jinn da suka raɓeta na cikin masarauta, sihirin dake jikinta na cewar babu wani Jinni dazai raɓeta ya karye hakan yasa tarin manyan Aljanu suka bibiyeta kuma niyarsu su rabata da Duniya saboda Aljanun da mahaifinta ya ƙoƙƙona su ta hanyar tsafi sune suka bibiyi Ayushert domin ɗaukar fansa, sun juyar mata da ƙwaƙwalwa, sun sa ta mance da ƴaƴanta, sun sa ta mance da mijinta, inda ace mun kawota nan yaranta bazasu samu nutsuwa ba sannan idon Aljanun zasu karkata zuwa kan yaran hakan yasa muka barta acan sannan muka sanar maka cewa ta mutu,
Malaman garin Makkah sun taya mu da addu'a sosai, da maganinnuwa na Musulunci saida aka dage da roƙon Allah tukun Allah ya bata sauƙi amma taci azaba bana wasa ba, kaima kanka Junaid bazakaso kaga Ayushert a wannan yanayin ba, domin ta koma tamkar Aljana, ason ransu in har basu kasheta ba toh kuwa zasu mayarta jinsinsu na Aljanu kuma zasu iya ɗauketa su mayar da ita duniyar su na Aljanu, a gaskiya ka godewa Allah sosai, Addu'a itace makamin mumini kuma itace ta ceci Ayusher daga hannun Azzaluman Aljiin, wannan tsawon shekara biyun duk ana fama ne dasu amma yanzu Alhamdulillah 🙏, yanzu babu wata matsala dazai ƙara afkuwa mana kumadu....

Sarki Raamud yana hawaye yace "haƙiƙa na ƙona ƴaƴan Aljanu ba adadi hakan yasa na nemawa Ɓingel sihiri wanda babu Aljanin dazai raɓeta sai gashi an wayi gari babu sihirin ashe kuma Aljanu sun ɗana mun tarko akan ɗiyata .......

Haka suka zauna sunata tattaunawa duk acikinsu babu wanda baiyi kuka ba,
Da haka har kowa ya koma part ɗinsa...

After one Month

Ayushert taje ɓangaren swimming pool yawon shakatawa tana sanye da doguwar riga baƙa mai botula har ƙasi ta gaban rigar,
tana tsaye a bakin ruwa ga sumar kanta a baje ya sauƙa har gadon bayanta, ita kaɗai sai murmushi take tayi kwatsam taji an dafa kafaɗarta a tsora ce ta waiwaya tana faɗin "innalillahi wa inna ilaihi raju'un....". daiden lokacin da ƙafarta ya zame tayi baya zata faɗa cikin ruwan a ruɗe shima yakai hannu zai riƙota tayi saurin cabko rigarsa suka faɗa cikin ruwan a tare,
Saida suka nitse cikin ruwan lokaci guda suka ɗago da kayuwansu suna maida numfashi, Ayush turo baki tayi tana kallonsa cikin yanayin shagwaɓa tace "ka tsoratar dani over...". ya rungumeta tareda cewa "toh Sarkin tsoro...".
Bugan ƙirjinsa tayi tana dariya nan suka fara wasa a cikin ruwan kowa yana watsawa kowa, suna cikin wannan yanayin shauƙin saiga triplets suma sunzo wajen har da Khubayr wanda yake binsu da gudu duk yanda suka je,
Areeph yace "Daddy mommy me kukeyi acikin ruwan?..."
Ogah Junaid yace "wanka muke yi mana..."
Haka duk suka haɗa baki wajen cewa "muma zamuyi wankannn...."
Yace "toh shikenam duk kuzo...". Duk suka cire kayan jikinsu daga su sai pant, shima Khubayr cire masa sukayi suna zuwa duk suka faffaɗa cikin ruwan, Khubayr kam Mommynsa ce ta ɗauke shi acikin ruwan saboda shi bai iya ruwa ba, ana ajiye shi zai nutse ciki, haka suka rinƙa wasa a cikin ruwan nan Iyaye da ƴaƴa duk ɗin su,
Saida suka kammala suna daga cikin ruwan Ogah Junaid ya ɗauki Areeph akan wuyansa, sannan ya ɗara Jarumarsa wato little Angel akan kafaɗarsa, itama Amrish ya ɗauketa ata ɗayan hannun,
Ayushert kuma tana ɗauke da Khubayr ta shige tsakiyar Ogah Junaid itama,

*NI KUMA ASMEETAH WACCE NA KASANCE MAI ƊAUKARSU A PHOTO NA SAITA KAN CAMERA TA NAYI SHUTTTTT NA ƊAUKE SU A PHOTO.....*




Alhamdulillah 🙏
Alhamdulillah 🙏
Alhamdulillah 🙏 ala kulli hali...

Allah ina mai ƙara gode maka daka bani damar fara rubuta littafina mai suna Matar Damisa yanzu kuma ka bani aron kwanaki na gama littafina cikin ƙoshin lafiya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login