Showing 27001 words to 30000 words out of 186041 words

Chapter 10 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53932

yayi sannan yace "daga ke har ita banida lokacin ku.."
Da sauri ta durƙusa ƙasi ta ɗora hannayenta biyu akan cinyarsa tace "Please My man I beg you ka temaka mun na gano gaskiyar lamarin, dan Allah ita fah Ayush ko baka ɗauketa a matsayin budurwa ba ya kamata ka riƙeta a matsayin ƙanwarka ita fah marainiya ce batada kowa in baku ba, nasan dai bazaka bar ƙanwarka ta shiga cikin wannan matsalar kuma ka shareta ba...."

Dogon numfashi yayi sannan yace "maganarki gaskiya ne but Yushert tayi hurting heart ɗina da yawa, koda yaushe matsala take kawo mun, idan har bazata iya faranta mun ba nima kuwa bazata ga abunda take so daga wajena ba, especially video da aka turo mun nayi danasanin haɗuwa da yarinyar nan, naji bana ƙaunarta a raina, wallahi na tsaneta bana sonta tinda har zata iya aikata wannan ƙazantar da ƙazamin mutum irin wannan ɗan shaye-shaye haba tirr, Angel idan zakiyi maganar Yushert kada ki sake sakoni acikin wannan al'amarin, na riga da na yanke alaƙata da ita, kije kiyi binciken ki amma babu ruwana..."

Angel kanta a sunkuye kamar ta rausa ihu tsabar takaicin jin kalaman Junaid daƙer take motsa baki tace "shikenam insha Allahu bazan sake yi maka maganar Ayush ba, yanzun ina key ɗin ɗakin?.."

Ayush tana daga cikin secret room tana jin duk tattaunawar da suke yi akanta, sam bata jin daɗin furucin Junaid ba haka take kuka a hankali mai cin rai, jin Angel ta tambayi ko key ɗin ɗakin da take ciki yasa ta zabura ta samu bayan kujerar ɗakin ta ɓuya a gurin!....


Idon Junaid ne yayi jawur tsabar baƙin cikin da yake ji idan ya tuno da video Ayush, kamar ya fashe da kuka haka yake ji, a hankali ya furta "ki duba ƙasi pillow zaki ga key..."

Da sauri Angel ta tashi ta nufin gurin ta ɗaɗɗaga pilolin bata ga key ba tace "My man nifa Banga key ba..."
Ɗago da kansa yayi da sauri yana kallon gurin, tunani ya shiga yi shifa a saninsa da hannunsa ya ajiye key ɗin nan, sai a lokacin ya fara bin ɗakin da kallo yana jinjina kai yace "da duk kan alamu an shugo mun ɗaki kuma anyi mun bincike.." ya kai idonsa gurin da ƙofar ɗakin secret room yake ya tashi yana takawa a hankali yaje gurin, hannu yasa ya turo ƙofar sai yaga ta buɗu,
zaro ido yayi waje da ƙarfi ya furta "whattt..."
ya juyo bayansa yana kallon Angel yace "kin shugo mun ɗakin nan before?.."
Girgiza kai tayi tace. "wallahi ban shugo ba, girki nayi wa mommy..." kafin ta ƙarisa maganar ya katseta da cewa "bana son ƙarya fa da kuma munafurci..."

murya na kakkarwa Angel tace "wallahi tallahi Ogah Junaid ka yadda dani ban taɓa yi maka ƙarya ba, ban shugo bedroom ɗin nan ba sai yanzu..."

Girgiza kai yayi sannan yace "good...."
ya shige cikin ɗakin yana kalle-kalle,
Ita kuwa Ayush tana bayan kujera tayi shuru ko motsi baka ji,. saida ya gama dudduba babu kowa yana tsaye idonsa suka sauƙa akan jan material ɗinta akwai ɗan zirin da bai gama ɓuya ba,
Junaid tsayawa yayi yana murmushin gefen baki irin na muguntan nan, ya ɗauki pillow kujera ya jefa mata shi,
a tsorace ta tashi tana kuka a zabure tayo kan Junaid tana faɗin "ganan kuliyar kwanaki tazo zata cutar dakai Yaya Junaid, ta rungumeshi sosai!

hannu yasa ya finciketa tareda wurgata saman kujera yana zazzaro ido yace "meya kawoki cikin room ɗin nan? me kika zo yi? sannan ki gaya mun taya kika san akwai ɗaki anan?..."

tasowa tayi tana faɗin "dan Allah Yaya Junaid kayi haƙuri, ka daina jin haushi na, wallahi ban aikata abunda kake zargin na aikata ba...."

Junaid zuciyarsa ce ta hauro sosai ga takaicin bata amsa masa tambayarsa ba, cikin zafin nama ya cabki wuyanta ya gwara da jikin bangon ɗakin, ƙara ɗaya tayi ta sume a gurin tsabar bugun da yayiwa kayinta, zata faɗi ƙasi yayi saurin riƙeta ya mannata a saman ƙirjinsa ya ƙanƙameta sosai shima fashewa yayi da kuka,
Hajijiya ne yake shirin ɗaukarsa yana rungume da Ayush ya zauna daƙer akan kujera, ita kuma ko motsi batayi ido a rufe sai goshinta da yaketa ambaliyar jini, shima duk ya ɓata jikinsa da jinin da Ayush take zubarwa,
ya kwantar da kansa akan sumar kayinta yana ta faman zubda ƙwallah....


Angel tana zaune a bedroom taji shurun yayi yawa har zuwa wannan lokacin Junaid bai fito daga cikin wannan ɗakin ba, miƙewa tayi ta nufi ɗakin don ganin meke faruwa domin duk ihun da za'ayi a cikin ɗakin nan ba jiyo mutum za'ayi ba sakamakon ta cikin ɗakin akwai glass door,
shige cikin ɗakin tayi taga ta ko ina haske ne tana juya ɓangaren damanta taga Ogah Junaid yana zaune ya kifa kansa a tsakiyar kayin Ayush, ga kuma jini duk ya ɓata masa kayan jikinsa daman kayan milk ne,
Da sauri ta ƙariso gabansa tana faɗin "My man lafiya kuwa meya faru da Ayush? taya ta shugo ɗakin nan?
amma kuma jini yana zuba mata fah sosai yakamata aje ayi saurin tsayar mata...."

Ɗagowa Junaid yayi ya zame mata ɗan ƙaramin gyalenta wanda ta ɗan ɗaure gashinta dashi, ya ruɓanya gyalen biyu sannan ya ɗaure mata goshinta, yana kammalawa yabi doguwar kujerar ya kwanta ya kwantar da Ayush a samansa yana kallon sama ita kuma fuskarta yana kife asaman ƙirjinsa har wannan lokacin tana nan a sume...

Angel tsayawa tayi tana kallon ikon Allah tace "Ogah Junaid...."

Kafin ta furta wani abu taji ya katseta da cewa "Please bana jin daɗin jikina ga can computer ki duba abunda kike son dubawa"
tace "toh shikenam"
ta nufi gurin tana maganar zuci "oh Junaid da Ayush ikon Allah, wato duk wanda yace zai shiga tsakaninku ma shi zaiji kunya, toh yanzun me yayi wa Ayush ne?
ita kuma Ayush metazo yi nan cikin ɗakin bayan tasan baya barin kowa ya shugo saida sanyewarsa..."
haka taketa tunanin nan har ta zauna akan chair tasa computer agaba tana ta faman daddannawa,
can kusan awa guda Angel tana duba lamarin nan kuma ta gano domin tana zargin da sa hannun mutane biyu..

A ruɗe ta juyo tana kallon yanda Junaid yake a kwance ido a lumshe ko motsi baya yi tace "Ogah Junaid na binciko komai wallahi wannan video da aka turo maka ba gaskiya bane,
domin bayan Ayush ta bar gurin taron baikon ku kai tsaye ɗakinta ta nufa, bayan wasu mintuna kuma saiga wannan matar mai liƙab wanda babu san ko ita wacece ba ta shiga ɗakin Ayush, daga baya kuma bayan wasu mintuna na shiga ɗakin Ayush amma saidai matar nan bata fito ba, amma kuma ban sameta a cikin ɗakin Ayush ba toh amma abun ya ɗaure mun kai kenam jin shugowata matar ta ɓuya kenam?
to ni bayan na fito matar bata fito ba har waran awa 3 lokacin kenam muna asibiti,
Laylah ta shiga ɗakin bata fito ba sai bayan wasu mintuna kuma sai ga wannan mutumin shima ya shiga ciki,
Ni abun yayi mungun ɗaure mun kai! mutane uku ne suke cikin ɗakin Ayush
toh idan hakane Ayush batada masaniya akan abunda ya faru da ita, mata biyu acikin ɗakin namiji ɗaya sunyi amfani da wannan namiji ne domin su ɓata mata suna, amma kuma daga baya namijin ne ya fara fitowa sai kuma Lailah ta fito itama,
gashi camerar kuma ta nuna da mangariba Ayush ta fito sanye da dogon hijab ɗinta ta fice a lokacin hospital ta nufa nasani domin a wannan lokacin taje asibiti, to kuma ina matar nan mai liƙab najira fitowarta amma shuru har yanzu har kuma yau duk shige da fice da ake yi bata fito ba, to kodai Aljana ce?...."

Bayan ta gama surutanta ta kuma cewa "Ogah Junaid kaji fah yanda ake ciki.."

taji shuru bai bata amsa ba still ta sake ƙiran sunansa "Ogah Junaid! Ogah Junaid!! My Man lafiya kuwa kodai bacci ne ya ɗauke ku..."

ta tashi taje gurin da suke a ƙwance tana bubbugar kafaɗarsa tareda ƙiran sunansa amma ko motsi babu itama Ayush ko motsi, tasa hannunta a saitin hancinsu basa numfashi a ruɗe Angel ta miƙe tsaye tana faɗin "innalillahi me kuma ya faru, nashiga uku mommy.." ta fice a ɗakin da gudu tana ƙwalla ƙiran mommy....

Ogah Junaid shima numfashin sa ne ya ɗage cak a sume yake...


*********

Maimoon ce take zaune a kan gadon Ammynta sai faman rera kuka take,
Mahaifiyarta ta sakata a gaba tanata mata tambayoyi acikin damuwa,
"Maimoon magana nake miki kin kasa bani amsa shin ina kika je tsawon kwanakin nan? baki taɓa tafiya wani waje ba tareda kin sanar mun ba, kuma baki taɓa yin wannan kwanaki a wani waje ba Maimoon so kike ki jawo mana abun magana?..."

Girgiza kai Maimoon kawai tayi ta kasa cewa komai,
suna cikin wannan halin saiga mahaifinta ya shugo shima yace wa Ammy "ta gaya miki yanda taje ta?..."

Ammy tace "a'ah tin jiya naketa binta akan ta sanar mun amma taƙi..."
Daddy yace "Okay.." ya fice a gigice, ba jumawa ya shugo hannunsa riƙe da wayar wuta yana zuwa ya fara zabga mata ajiki,
Maimoon ihu take tana kuka tanata sose-sosai har saida ya faffasa mata jiki abunka da farar mace, dakatawa yayi da dukanta yana zazzaro mata eyes yace "zaki faɗa mun yanda kika je ko kuma na cigaba da dukanki?..."

tana kuka tace "wallahi Daddy nima bansan yanda nake ba, wasu mutane ne suka kama ni suka ajiyeni awaransu, bana fita ko ina yanzun ma guduwa nayi basu sani ba..."

Daddynta yace "su waye ai dai kinsansu, kuma miye alaƙar ki dasu?.."
tana shessheƙar kuka tace "nima ban sansu ba, ina cikin tafiya taji an sakani a mota daga nan na nemi hankalina narasa..."

Daddy a fusace yace "ƙarya kike kice anyi kidnapped ɗinki domin da sun nemi kuɗi a waran mu..."

Ammy ta taso itama tana kuka tsabar tausayin ɗiyarta tazo gaban Daddy tace "Abul Bintu ka dubi wannan al'amarin Maimoon bata taɓa wannan dogon zango ba kuma ba tareda sanin mu ba, kaima dai kasan munada maƙiya zasuyi hakane domin su ƙuntata maka, fatan mu tinda Allah ya kuɓuto mana da ita mugode wa Allah kawai, amma ni na yadda da ɗiyata ɗari bisa ɗari..."

Dogon numfashi Daddy yaja idonsa akan Maimoon wacce kanta ke sunkuye yace "su nawa ne mutanen? kuma zaki iya gane fuskokinsu? sannan akwai abunda sukayi miki ne?..."

Maimoon ɗagowa tayi tana faɗin "gaskiya Daddy bazan iya ganesu ba saboda koda yaushe da baƙin hula a fuskokinsu, sun kai su goma amma babu abunda sukayi mun kawai dai acikin wani ɗan ɗaki suka kulle ni.."

Daddy ya kuma cewa "zaki iya gane gidan da suka kai ki?.."

Dasauri ta girgiza kai tace "a'a bansan lokacin da aka kaini gidan ba kuma lokacin dana fito ban tsaya dubawa ba saboda ina tsoron kar su fito su kamani..."

Daddy goya hannayensa yayi ta saman ƙirjinsa yace "inason shugo da hukuma cikin wannan al'amarin su binciko mun su waye ne waɗannan mutanen..."

Ammy tace "a'a Abul Bintu kar ka fara domin wannan maganar ba kowane ya sani ba, idan aka shugo da hukuma ai kowa zai san da maganar kuma akwai masu zargi da yawa, nidai a shawarce mu bar maganar nan a iya cikin gidan nan, ƴata da mutuncinta a idon jama'a kuma mahaddaciyar alƙur'ani, bazaiyu azo ana mata mummunar fassara ba..."

Daddy yace "toh shikenam tinda kince haka..."
yayi ficewarsa acikin ɗakin,
Da gudu Maimoon ta tashi ta rungumi Ammy tana kuka mai cin rai...

Duk tattaunawar da sukayi kuwa Laylah tazo ta laɓe musu taji duk maganganun da sukayi tin daga lokacin da aka fara dukan Maimoon,
jin fitowar Daddy ne yasa tayi gudu ta koma falo ta zauna,

Daddy yana fitowa Laylah ta durƙusa har ƙasi ta gaishe shi ya amsa mata tareda cewa "ki tashi kice gurinsu suna cikin ɗaki, kinzo ganin ƙawarki ko.." ya ƙarisa maganar yana murmushin yaƙe domin bayaso ta fahimci wani abu...

Itama tashi tayi tana dariya ta shige ciki, tana shiga kuwa ta samesu suna zaune asaman gado Maimoon ta ɗora kayinta akan cinyar Ammy.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login