Showing 48001 words to 51000 words out of 186041 words

Chapter 17 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53913

har yanzu ba'a gano ba har yabar duniya..."

Junaid tsayawa kallon mommy yayi bayan ta kammala bashi labarin abunda ta sani ya turo ɗan ƙaramin bakinsa yace "Hmmm matsalar ƴan Nigeria kenam shikenam daga temakon da yayi muku sai kawai ki Aure shi?..."

Mommy tashi tayi tana faɗin "your very stupid Junaid, bari naje kitchen domin nasan yunwa kake ji shiyasa ka kasa fahimta ta.."
Har zata fita ta sake juyowa da sauri tace "Junaid bakayi sallar mangarib ba gashi har ana ƙiran Isha'i, why Junaid?
please kaje masallaci banson sallarka a gida..."
tana kaiwa nan tayi ficewarta...

Shima tashi yayi ya nufi toilet zai ɗauro Alwala...

Kitchen mommy ta shiga ta haɗa mana haɗaɗɗen girki!
Abinci kala biyu ta girka kowa ta dafa masa abunda ransa yake so,
Shi Junaid indai a night lunch ne yafi son sakwara da miyan ugusi da kifi haka Angel ma ra'ayinsu yazo iri ɗaya,
Mommy kuma ita da Ayush sunfi son tuwon shinkafa da miyan ƙwai ko jar miya 😋😋😋😋😋

Junaid ne ya dawo daga masallaci zama yayi a falo yana kallon labarai, ta ko wani tasha labarin zuwa yaƙi ƙasar California ake, ana nuno photon Sarki Raamud a tv, sannan aka dawo nuno photunan sojojin da zasuje yaƙin! kowani ƙasa ana zaɓan sojojin da zasuje,
Aka zo kan sojojin Austaraliya Junaid yana ganin yanda aka nuno photon Rumana, murmushi kawai yayi tareda girgiza kai shi inda ason ransa ne da baza'ayi yaƙin nan da mata ba, domin a tunaninsa mata babu abunda zasu iya sai shirme da kuma suzo suyita ihu a mutane,
gani yayi anzo kan sojojin China, nan ma yaga an nuno photon Aditi dariya yayi a fili yace "gwara ke Sarkin faɗa..".
Bayan su sai aka nuno sojojin ƙasan da za'ayi yaƙin wato California Army aciki har da Angel ɗinsa lokaci guda kuma sai yaji tausayinta duk da Angel commander ce amma bayaso a tafi yaƙin nan da ita domin ita ɗin tanada rauni sosai ba kamar su Aditi ba,
Anan ana wuce ƙasashen sojojin da zasuje har aka zo kan ƴan Nigeria,
tsuka Junaid yayi yana faɗin "Nigeria Army kam ba abunda zasu iya, ni ban taɓa ganin ragwayen sojoji irin na nan Nigeria ba wallahi, sai gadarar aita jefar da bindigu suna guduwa..."
gani yayi an nuno photonsa ana sanar da cewa shine na ɗaya acikin jaruman sojojin Nigeria,
tsuka yayi ya tashi yana faɗin "banson shirme, kuna wani ƙirana da jarumi wato so kuke azo mun ta baya a hallaka ni kenam..."
yabar kallon ma ya nufi dinnig table sabo ƙar dashi saboda a yau ɗin nan aka kawo shi wancan table ɗin Junaid ya dagargaza shi...
Zama yayi yana ƙiran Mommy tareda cewa "Ni har yanzu ba'a kammala girkin bane.."

Mommy ce ta fito ɗauke da kulolin abinci ta jejjerasu,
ɗagowa tayi tana kallon agogon ɗakin, da sauri tace "na shiga uku ina yaran nan suka shiga ne?.."
Junaid yace "ina suka je ne?.."
tace "wallahi ban saniba, tinda rana suka fita gashi yanzu har ƙarfe 10..."
Junaid yana kallon kular abinci yace "Mom yunwa nake ji, ai ba ɓata zasuyi ba..."

Mommy tace "Dan Allah Junaid kafin ka fara cin abincin kaje ka nemo su mana..."
Junaid ya ɗago yana kallon Mommy tareda faɗin "whattt sorry I can't leave my food, ai su ba ƙananun yara bane da har sai an fita nemansu, idan sunada hankali ai da sukaga dare yayi sai su dawo gida..."

Mommy tace "toh ai su basuda hankali sai an nemo su.."
Junaid yace "toh su kwana acan indai ni zan nemo su.."

Mommy zatayi magana kenam ya katseta da cewa "Please Mom am hungry, wallahi idan nabar abincin nan toh na basshi kenam zan kwana da yunwa ne..."
Mommy tace "toh toh gashi ka fara cin abincin tukun saika je ka dubo mun su, idan ka gansu a hanya ka daka mun su..."

ta ƙarasa maganar tareda zuba masa abincinsa a plate, yace "toh shikenam kije ɗakina ki buɗe wardrobe zakiga dorina ki ɗauko mun, yau zasu raina kansu tinda yawo zasu koya..."
Mommy kallonsa take tace "toh bari na ɗauko.."
a cikin ranta kuwa cewa tayi "tab wannan ai kaine sarki zalimun ɗin..."
ta nufi upstairs tana takawa har ta iso ɗakinsa...

Gari kuwa hadari ne ya haɗu sosai lokaci guda kuwa aka fara ruwan sama da ƙarfin gaske don ko yayyafi ba'ayi ba, irin ruwan nan mai haɗe da iska ake yi,
Junaid yana cin abinci haka ya ƙara kallon agogo yanzu har 10:30 kuma ruwa ake sosai, ɗaukan wayansa yayi yana dialling call number Angel wayar ce take ringing har ta katse ba'a ɗauka ba,
tsuka yayi ya ajiye wayarsa a gefen table har ya kammala cin abinci ya zauna kamar mai yin tunani...

Mommy ce itama ta sauƙo down stairs hannunta riƙe da dorinar da Junaid yace ta ɗauko, tsayawa tayi ta jingina da jikin gini gaba ɗaya ta shiga damuwa,
kallon yanda Junaid yake a zaune tayi tace "gashi anata ruwan sama kaima ba halin fita, na ƙira wayar Angel shuru bata ɗauka ba Allah dai yasa lafiya.."
Junaid ne ya kalli Mommy yace "shine kika shiga damuwa haka?..."
Junaid yana rufe baki sai suka ji an turo ƙofa da ƙarfi, da gudu Angel da Ayush suka shugo cikin falon duk sunyi jirib sai haki sukeyi kamar waɗanda sukayi gudun tsere...

Mommy sake baki tayi tana kallonsu tama rasa bakin magana,
shima Junaid kallonsu kawai yake yi,
shine ma ya fara yin magana yace "daga ina kuke?.."

Angel tana fitar da numfashi daƙer tace "wallahi motar mu ne ta ɓaci mana a hanya, tin daga teepa garage muke tafe da ƙafa har muka iso gida, babu abun hawa ko ɗaya..."

Mommy tace "toh ina zakiga masu abun hawa acikin ruwan nan ga dare yayi yanzu sha ɗaya saura, na ƙira wayanki no picking kuma kafin ku fita saida na tambayeku ina zakuje baku gaya mun ba, wani irin hauka ne wannan..."

Angel tace "Sorry Mom, munje gidan Malam Lawan ne.."
Mommy tace "ai nayi waya da shi malam lawan bai ce mun kuna gidansa ba,"
Angel tace "wallahi Mom a gaban mu ai kukayi wayan naji kuna maganar ɗaurin Aure,
toh Amma Mom ni Auren wa za'ayi?.."

Mommy kawar da kanta gefe tayi tace "bansani ba kinyi laifi kuma kin saura da tambaya na abunda bai shafeki ba..."
a ranta kuwa cewa take "kaji mun ƴar banzar yarinya zata tona mun asiri nida nake ɓoye maganar auren..."

Ayush kuwa tin shugowarsu falon ta zauna a ƙasin carpet tana maida numfashi, domin ba ƙaramin gudu suka sha ba, gwara ita Angel ta saba da motsa jiki..

Junaid ne ya taso yana faɗin "Mom bani dorinan nan, jikinsu zai gaya musu ai..."
Mommy har zata miƙa masa Angel tayi saurin fizgewa tana cewa "tabɗin jan ai wallahi impossible, haba Mom keda kanki zaki goyi bayan a daka mu kamar wasu karnuka tab.."
Junaid ne yayo kanta yana faɗin "ki bani dorinar nace.."
Angel tana turo baki tace "haba dai soja ce fa niɗin, har zan bari ana dukana kamar wata non living thing, duka ai saina yaƙi idan munje mu.."

Junaid yana kallonta yace "Ni kike gayawa haka?..."
ƙara turo baki tayi, hannu yasa ya jawo lips ɗinta yana faɗin "zan yanke bakin fah"

Mommy kuwa nufo gurin Ayush tayi tana cewa "wannan ƙaton hijab ɗinki bazaki jiƙa mun carpet ba wallahi..."
haka tasa hannu ta cirewa Ayush hijabin jikinta, ta buɗe ƙofa taje ta shanya shi ta dawo...
Ayush kuwa da gudu ta tashi ta haura upstairs ta nufi ɗakinta saboda doguwar rigane a jikinta na bacci mai hannun breziya,
Junaid tsayawa kallonta yayi har ta ɓace daga ganinsa,

Mommy ce tace "wallahi Junaid kayi mata dukan tsiya indai bata faɗi abunda ya zaunar da su har wannan lokacin ba..."
Angel tana turo baki tace "haba Mommy abun farin cikine ya samu fah.."
Mommy tace "meye abun?.."
tana dariya tace "Mom na musulunta dai"

Junaid haɗe girarsa yayi cike da mamaki yake kallon Angel,
Ita kuwa Mommy zaro ido tayi waje tace "Angel musulunta kuma? Aina?..."
Angel tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya tace "to kodai bakuyi murna ba?..."
Mommy tace "bawai bamuyi murna ba, kawai dai unsuspecting..."
Angel tace "wallahi tallahi Mommy wutar jahannama indai ƙarya nake..."
Junaid jin kalar rantsuwar da Angel tayi yasa dariya ta kuɓuto masa, dariya ya shiga yi harda kama ciki, zaman yayi akan kujera yana dariya, daƙer ya iya dakatar da dariyar yana faɗin "wato yanzu kinsan wutar jahannama koh?.."
Angel tana kallonsa tace "eh mana yanzu nasan wutan jahannama..."

Mommy tace "toh banda abunki Angel ai saiki sanar mana koh, nima naso ace a gabana kika musulunta ai..."
Angel tace "ai mommy munyi video lokacin da nake musulunta, Ayush ce ma take mana video na sanyawa kaina suna Maryam..."
Mommy cike da farin ciki tace "kaiii amma naji daɗi wallahi, sannu maryamu..."
Angel tana dariya tace "ai abunda yasa muka daɗe saboda an koyamun karatun Alkur'ani irin short short ɗin nan wanda zan rinƙa karanta su a cikin sallah amma saika fara karanta fatiha tukunna.."
Mommy tayi hamdala cike da murna...

Junaid yana kallon Angel cikin damuwa yace "wani irin ƙalubale zaki fuskanta idan har iyayenki suka ji kin musulunta?
Kinsan mahaifinki tsohon soja ne hakan yasa ya ɗoraki akan aikinsa saboda iya ke kaɗai suka haifa, idan kuwa mahaifinki yaji toh acikin biyu ne za'ayi ɗaya! ko ya kashe kansa ko kuma ya kasheki domin babu abunda yafi tsana kamar musulunci ke kuma kinason mu'amala da musulmai gashi har takai kin musulunta, Angel mahaifiyarki zuciyarta zata iya bugawa saboda ita ɗin pastor ce a babban church ɗin ƙasar ku, toh mezai faru kenam?..."

Hawaye ne suka fara gangaro mata tana sharar hawaye haɗe da murmushi tace "bazan sanar musu yanzu ba sai mun kammala yaƙin da zamuje, da zarar mun dawo zan ɗora video musuluntar danayi a social media kowa ya gani, duk hukuncin da iyayena suka yanke mun shikenam, idan ma kasheni za'ayi naji zan amshi hukuncin, idan kuma sune suka mutu zan nema musu gafarar Ubangiji, idan korana sukayi ai nan ma gidan mu ne, idan inaso nayi hutuna zan rinƙa zuwa nan Nigeria ina hutawa na..."

Mommy tayi matuƙar tausaya mata itama saida ta zubda hawaye tace "Maryam kiyi haƙuri kinji koh babu wanda zai kashe ki, ni daman na ɗaukeki a matsayin ƴata wacce na haifeta a cikina, zaki zauna damu anan idan kuka kammala yaƙin ku domin ajiye aikin soja zakiyi saboda ki kare mutuncin kanki na ƴa mace, musulunci yanada ƙa'idoji da yawa, zan Aurar dake a duk wanda kike so...."
Mommy taja dogon numfashi sannan ta kuma cewa "ni yanzu ma na rigada na yanke hukuncin zan haɗaki Aure da Junaid da zarar kun dawo..."

jin haka saida ƙirjin Angel ta buga da ƙarfi, maganarta har yana harɗewa tace "Mom mom mommy Aure kuma da Ogah Junaid? to to Ayush fah?..."

Mommy tace "duk ba damuwa zai haɗaku ku biyun..."
Angel ta kalli Junaid yanata danna wayarsa shi ko alamar nuna damuwa baiyi ba
tace "toh Mommy shi Ogah Junaid ɗin yanada ra'ayin hakan ne? baki tambayeshi ba.."

Mommy ta kalli Junaid sannan tace "toh Ogah Junaid shin ka yadda zaka Auri Maryama?..."
Murmushi Junaid yayi yace "duk abunda kika yanke Mom..."

Angel dai har yanzu hankalinta bai kwanta ba saboda Ayush
tace "Mom toh Ayush fah? bazata yadda da hakan ba, kuma inajin tausayinta...."
kafin Angel ta rufe baki saiga Ayushert ta katseta da cewa "Aunty Angel ki daina sakani a lissafin ƴan matan Yaya Junaid, kedai idan zaki Aure shi ki Aureshi amma ni bana layin matan da yakeso, ni bazan taɓa Auransa ba, kuma bana ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login