Showing 39001 words to 42000 words out of 186041 words

Chapter 14 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53922

kujera tana chatting,
jin bugar ƙofa yasa ta tashi a razane tana bin Junaid da kallo, wani irin haɗiyar yawu tayi tana girgiza kai tareda faɗin "Ogah Junaid.."
wani irin tsawa ya daka mata yace "shut up! bana buƙatar jin kalmar ki ko ɗaya..."
yasa hannu ya finciko ta yana janta zaiyi waje da ita,
Ihu Lailah ta fara kurmawa cikin ƙarfin hali ta zame hannunta ta miƙe da gudu ta nufi ɗakinta, shima binta yayi yana cewa "yau ba abunda zai hana na hukunta ki Lailah, zan kaiki can gidan mu..."
turo ƙofar ɗakinta tayi zatasa key daiden lokacin ya ƙaraso da ƙarfin gaske ya tura ɗakin saida ta hautsina ƙasi tsabar bugar da ƙofar yayi mata, tana kuka tana magiyar "dan girman Allah Ogah Junaid ka kyaleni na tuba, wallahi bazan ƙara ba.."
ɗagota yayi daga ƙasin ɗakin ya wurgata saman gadonta sannan ya juya ya rufe ƙofar ɗakin yasa key tareda juyowa yaje bakin gadon yana daga tsaye ya ɗora ƙafarsa ɗaya akan gadon, ƙafa ɗaya kuma a ƙasi ya riƙo ƙafar Lailah ya jawota gabansa tareda zaunar da ita yayi mata alamar tayi shuru yatsarsa akan lips ɗinsa yace "shiisssh kimun shuru, idan kuwa ba haka ba zan ƙwaƙule miki eyes yanzun nan..."
Lailah da sauri tasa hannunta ta rufe bakinta tayi shuru gurin yayi tsitt kamar ba mutane a ɗakin, ga gumin da yaketa yarfo mata,
shi kuwa binta yake da kallo cikin ɓacin rai yace "meyasa kika aikata hakan? amsa ɗaya zaki bani..."

Ita kuma Lailah sanin halin Junaid yasa bata tsaya masa wani inda-inda ba tayi saurin cewa "wallahi saboda inasonka ne, ina bala'in kishinka...."
bata ƙarasa maganar ba ya daka mata tsawa tareda faɗin "you're an ingratitude fool Lailah, saboda kina sona shiyasa zakiyi haka? toh da kikayi hakan shi zai sa na soki kenam?..."
Girgiza kai tayi a tsorace,
hannu yasa a cikin aljihun wandonsa ya ciro wata ƴar ƙaramar wuƙa yana goge ta yace "ai saboda kinada idanuwa ne yasa kike aikata haka ko, toh yanzu zaki rabu da eyes ɗinki sai muga yanda zakiyi munafurci zuwa gaba..."

Lailah ganin Junaiddd yana saito mata wuƙa saitin idonta yasa tayi saurin sumewa a wajen ta faɗi a saman gadonta ta baya,
Sauƙe numfashi yayi yana kallonta,
miƙewa yayi ya ɗauko bottle na ruwa akan mirror yazo yana watsa mata ruwan a kan fuskarta a gigice ta farfaɗo tana sauƙe numfashi sama-sama, ganin fuskar Junaid yasa ta ƙara komawa sumar still ya ƙara watsa mata ruwa ta tashi zaune, kuma du ta juyar da idonta zata ƙara sumewa a tsawace yace "wallahi tallahi kika ƙara kwanciya mun saina faffasa miki ido da wuƙannan, a tsorace ta dakata jikinta na kakkarwa ta buɗe baki zatayi kuka ya ɗauketa da wani irin gigitaccen mari a gigice ta tashi da gudu ta nufi bakin ƙofa yayi saurin riƙe rigarta ta baya cikin rashin sa'a kuwa rigar ta ɓere gaba ɗaya tsabar riƙon da Junaid yayi mata,
fincikota yayi zai wullata saman gado shima ƙafarsa ta harɗe suka faɗi a tare kan gadon, yana saman kanta suna fuskantar juna, Lailah riga ya yage daga ita sai breziyya, rufe ido Lailah tayi sosai jin yanda Junaid ya faɗo mata a jiki! jin shurun yayi yawa ne yasa Lailah buɗe idonta a hankali, gani tayi Ogah Junaid ya kafa idonsa akan ƙirjinta ko motsi ya gagara yi, ita kuwa ganin haka yasa tasa hannu ta bayanta ta ɓalle rigar brezy ɗin ta saiga manya-manyan breast ɗinta sun wantsilo, ganin haka yasa Junaid ya ɗago yana kallonta cike da mamaki yace "Lailah are you stupid?..."
dogon tsuka yaja sannan ya ɗago daga kanta yana faɗin "bazanyi mamaki ba duk abunda akace kinyi, look bafa nayi miki hakane don saboda na rikice ba, nayi miki hakane saboda naga kalar taki tarbiya, yarinya ba kunya..."

tashi tayi a tsorace kamar zatayi kuka tana ƙoƙarin rufe jikinta da rigarta, tace "dan Allah Ogah Junaid kayi haƙuri..."
Murmushi yayi sannan yace "Hmmm! Lailah kenam..." yasa hannu yana ƙoƙarin cire belt ɗin kunkuminsa,
zaro ido Lailah tayi tace "dan Allah Ogah Junaid kar kayi mun fyaɗe..."

wani irin abu yaji ya daki zuciyarsa ya zaro ido waje cike da mamaki yace "whattt! raping? very stupid..."
fuska ba Annuri haka ya zaro belt ɗinsa ya fara dukanta cikin ɓacin rai, jin sauƙar dukan yasa ta tashi a gigice tana ihu tareda sosa jikinta, ga riga ya sulale ƙasi, breziya ya faɗi shima jikinta ba komai sai dogon wandon dake jikinta, haka yaketa dukanta kamar bazai barta da rai ba, duk saida ya faffasa mata jiki, acikin tana ihu har ta komo muryarta ya disashe kukan baya fitowa saida ya gama bata kashi a hannu tukun ya ɗauki rigarta ya ɓeɓɓera mata shi yayi igiya da rigar sannan ya ɗaure mata ƙafafu, yazo kan hannayenta suma ya haɗesu ya ɗaure guri ɗaya, ya janyo kujerar mirror ya taka ya tsaya sannan ya wurga igiya saman fankar ɗakin ya ɗaure sosai, ya sauƙo ya ɗauki Lailah a kafaɗarsa ya sake hawa saman kujerar ya kuma ɗaure mata ƙafa da igiyar panka ya sauƙo ya barta a sama tanata ihu, ƙafafunta sune a sama, kayinta kuma yana kallowa ƙasi sai lilo take tayi a sama,
Juyawa yayi har zai fita ya sake juyo wa ya ɗauki breziyar ta ya sake hawa kujerar ya rufe mata ƙirjinta sannan yasa gam ya manne mata bakinta,
ya sauƙa yana cewa "tinda ke bakida kunya toh ni yau zan nuna miki yanda ake asalin rashin kunya wawiya kawai..."
yana kaiwa nan yayi ficewarsa..


______________ Bayan Doctor Samuel ya gama treat ɗin Ayush tafiyarsa yayi,
Mommy kuma ɗakin horo taje ta dubowa meke faruwa duk da tasan aikin Junaid ne, shi inbaiyi mugunta ba baya jin daɗi...
tana tsaye a bakin ƙofar ɗakin tana kallon mutumin da Angel take since masa ɗaurin igiya,
Mommy ganin yanda jini yake malala a ƙasin tiles a ruɗe tace "Innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Angel meya faru dashi ne haka nake ganin jini kamar bazai rayu ba?..."

Angel tace "Hmmm Mommy kenam wannan babban mai laifi ne, ya cancanci wannan hukunci ne, abunda yasa zakiga zubar jinin yayi yawa na farko na harbe masa ƙafa da gun, na biyu kuma Ogah Junaid ya gundule masa ƴar yatsaa...". Angel ta ƙarasa maganar tana kwashewa da dariya..

Dogon tsuka Mommy taja tana faɗin "kenam abun dariya ne wannan? wai meyasa bakuda imani ne dake da Junaid? especially shi Junaid zuciyarsa kamar bana musulmai baa.."
Mommy shuru ta ɗanyi ganin yanda Angel ta haɗe rai tana fushi tace "kenam Mommy musulmai ne kawai masu imani?...."

Mommy tace "Ahh musulmai ne mana masu imani Angel, masu imani sai musulmai waɗanda sukayi imani da Allah da manzonninsa da mala'ikunsa da litattafansa da ranar tashin alƙiyama da kuma imani da ƙaddara mai kyau ko marar kyau..."

Angel fashewa tayi da matsanancin kuka ta miƙe tsaye tana faɗin "shikenam tinda ni banida Imani.." tayi ficewarta da gudu ta nufi falo...

Mommy sake baki tayi tana kallonta tace "Ohh kenam bazan faɗi gaskiya ba? saina mutu da a faɗi gaskiyar? toh dole na faɗi gaskiya tinda kin ƙi musulunta! na gaya miki Jesus ba Allah bane, mu awaran mu manzon Allah ne Annabi Isah...." haka Mommy ta rinƙa masifa, tazo kan Sauro tana faɗin "bawan Allah sannu ko! Allah Sarki saboda rashin tausayi a cirewa mutum ɓangare na jikinsa haba..."

Haka Mommy tasa hannu ta tallafawa Sauro ya tashi yana ɗingishi daƙer, haka mommy ta shigar dashi falo ta kaishi har ɗakin medicine zatayi masa magani ta tsayar masa da jinin...

Angel kai tsaye ɗakin Junaid taje ta tana kuka ta samu Ayush an ɗaura mata ledar jini,
bata bi ta kanta bama haka ta durƙusa a ƙasi ta kifa kanta tana ta sharar kuka haɗe da magana tana faɗin "ni duk sanda nazo ƙasan nan sai mommy tamun gorin musulunci, naga nima inada addini na, wai meyasa mommy take mun hakane, wallahi nima dole na musulunta a wannan lokacin kam! taya zan fara fuskantar musulunci..." duk wannan maganganun da Angel takeyi kaf a kunnen Ayush domin ta daɗe da farfaɗowa, a hankali Ayush ta buɗe idonta tana kallon yanda Angel take a kife a ƙasan carpet,
Ayush daƙer take motsa lips ɗinta ta furta "Aunty Angela..."
Angel dakatawa tayi da kukan jin an ƙira sunanta, ta ɗago tana kallon Ayush cikin mamaki tace. "daman kin farfaɗo ne Ayush?..."

Ayush tace "ehh Aunty Angela, duk naji abubuwan da kike faɗa! nima inaso ki musulunta, wallahi Aunty Angel musulunci akwai daɗi, ki musulunta mana, Mommy masoyiyarki ce shiyasa take miki akan ki musulunta..."

Angel jinjina kai tayi tace "shikenam Ayush zan musulunta da izinin Allah, amma saidai bansan yanda zanyi na musulunta ba..."
Ayush tace "karki damu duk wannan mai sauƙi ne indai har kinsa a ranki zaki musulunta da gaske saboda shi Allah mu yana aiki ne da zuciya...."

Murmushi Angel tayi sannan tace "har cikin zuciyata inaso na musulunta Ayush..."
Ayushert tace "karki damu Aunty Angel zan kaiki wajen wani babban malami zaki musulunta a hannunsa..."

Angel tace "please Ayush zamu iya zuwa gurin malamin a yau ko? saboda kinga gobe da asussuba zamu tafi headquarters, anan za'a turo mana jirgaye suzo su ɗauɗauke mu, gobe insha Allahu zamu kwana ne a ƙasar California, Ina tunanin idan muka kammala yaƙin mu zan iya dawowa na ƙara hutawa kafin nan ki koya mun abubuwan da musulunci yake ƙunshe dashi, sannan ki koya mun wannan karatun da kukeyi a sallah, ki koya mun sallah! idan na gama koya saina koma gurin aikin soja na..."

Murmushi Ayush tayi itama tace "indai kin musulunta kam za'a koya miki komai Aunty Angel, Amma inaso idan kun kammala yaƙinku ki ajiye aikin soja kema kiyi aurenki..."

Angel tunani ta shiga yi daga bisani kuma tace "bana tunanin aure araina Ayush, shima kanshi Junaid bawai son Aurensa nake yi ba no he is my Besty, Amma zanyi tunani akan maganar ki saidai kuma ina tsoron komawa ƙasarmu saboda iyayena bazasu yadda akan karɓar Musulunci danayi ba..."

Ayush ta tari yawunta tace "saiki dawo gurin mommy ki zauna, zakiga mijin Aure yazo miki..."

Angel murmushi kawai tayi ba tareda tace komai ba...

Ayush ce ta ɗan motsa tana ƙoƙarin tashi zaune taji an daka mata wani irin gigitaccen tsawa kamar daga sama, a firgice Ayush ta saki ƙara jikinta na ɓari tayi matuƙar tsorata sosai dajin tsawar,
Ba Ayush ba hatta Angel saida ta tsorata sosai da sauri ta waiwaya bayanta!

Junaid ne ya shugo yana nuna Ayush da ɗan yatsansa yana faɗin "kinada hankali kuwa Yushert? jini pah aka ɗaura miki amma kina ƙoƙarin tashi, kinsan irin matsalar da zaki samu kuwa idan jinin ya kauce hanya?..."

Angel tace "haba My man, wannan tsawar ai saika ƙara firgitar da ita yanzu ma ba lafiya ne da ita ba..."
Junaid juyowa yayi yana kallon Angel yace "meyasa lokacin da take ƙoƙarin tashi baki mata magana ba?..."
tace "toh ni ban lura da ita ba..."
yace "Okay toh tashi ki bani guri inason magana da ita.."

Angel tashi tayi tana ƙoƙarin tafiya!
Ayush tayi saurin dakatar da ita tana kuka tace "dan Allah Aunty Angel karki tafi ki barni wallahi kasheni zaiyi, banason kasancewa da shi, ki temaka mun..."
Angel kallon yanda Junaid yake zaune a bakin gado tayi tace "Ogah Junaid kaga irinta koh? ta fara fitar dakai daga cikin ranta, ko yaro ne yau da gobe ana masa tsawa dole zai gujeka balle ita data mallaki hankalin kanta, dole zatayi tunanin baka ƙaunar ta...."

rufe idonsa yayi yace "Please Angel leave my room, kar raina ya ɓaci..."
kamar zatayi kuka haka Angel tabar ɗakin, itama har cikin zuciyarta Junaid ya fara fita mata a rai saboda wannan tsawar da yake yi da kuma miskilanci irin nashi...

Ayush sunkuyar da kanta tayi ƙasi tana zubda hawaye tareda fargaban tambayoyin da zai ƙara yi mata,
Junaid yana kallon gabansa yace "ya jikin nakin?.."
shuru tayi bata bashi amsa ba, still kanta a sunkuye ko ɗagowa batayi ba.

Junaid yace "magana nake miki Yushert, kar kiyi tunanin zan barki ne akan wannan maganar da na fara miki tambayoyi akansa domin hankalina bazai taɓa kwanciya dake ba indai baki sanar mun ainihin ko ke wacece ba..."

Ayush still bata ɗago da kanta ta kalle shi bama balle ta bashi amsa, ita batama san mezata ce masa ba...

Ya kuma cewa "kaina a ɗaure yake kuma ke kaɗaice zaki iya warware mun, shin wacece wannan Uman nakin? a wace duniya take? shin mutum ce ko Aljana? sannan ke kanki mekika zo yi gidan nan?
Ina jiran amsar ki yanzun nan, duk waɗannan tambayoyin ba masu wahala bane indai kinada gaskiya..."

Ayush ɗagowa tayi tana kallonsa da idanuwanta waɗanda sukayi jajawur tsabar baƙin ciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login