Showing 111001 words to 114000 words out of 186041 words
my wife? meyasa zakuyi mata wannan hukunci? ku bari kotu ta yanke mata hukunci ba ku ba..." Marshal yayi saurin katseshi da cewa "kaii ka kama bakinka, kasan da wanda kake yiwa magana, General ne a gabanka..."
Junaid cikin fushi ya dakawa marshal tsawa da cewa "and so whattt? banda Allah babu wanda nake jin tsoro saidai nayi biyayya nabi dokar aiki." ya ƙarasa maganar tareda kallon yanda canal yake yace "tell me what's going on?..."
Canal nuna naseer yayi da yatsa yace "matarka ce ta yanke masa yatsu guda huɗu..." Junaid ya kalli Naseer yace "whatt? amma me yayi mata?.."
Canal yace "muma bamu saniba yaƙi yin magana kuma itama taƙi cewa komai" Junaid ɗago da Ayush yayi daga jikinsa yana kallonta yace "Yushert!.." ɗagowa tayi tana kallonsa itama ya kuma cewa "meya haɗaki dashi? kar kiji tsoron kowa ki buɗe baki kiyi magana babu abunda zai faru dake, ko waye bai isa yayi miki abunda Allah baiyi niyar miki ba..."
Ayush murmushi tayi ta ɗanyi nisa da Junaid kaɗan kafin ta ɗaga murya tana faɗin "Yaya Junaid ba wai tsoron su ne ya hanani yin magana ba, kawai dai inaso nayi magana ne a gabanka ka duba mun shin Abunda na aikata daidai ne ko kuskure...." ta kalli sojan ta nuna shi da yatsa tace "wannan mutumin idan shine zai riƙe ƙasa toh tabbas duniya bazata zauna lafiya ba, idan yasu ne zasu kare ƙasa toh kuwa saidai ayita mutuwa domin basu da wani daraja da kima, sannan basu san mutuncin mace ba, idan kuwa zasu iya lalata rayuwar mace to kuwa zasu iya yin lalata da mahaifiyarsu,
idan kuwa haka sojoji suke Allah ya wadaran su, idan haka soja yake bashida imanin da zai tausayawa mace ko yaro ko tsoho toh Allah ya tsine masa aikinsa bashida wani amfani, sai gadarar riƙe bindiga..."
Marshal ne ya katseta da cewa "kee ba'a ce kici mana mutunci ba don kina gaban mijinki to karki manta shima mijin nakin ai soja ne..".
Ayush tana fuskantar Marshal tace "ehh mijina soja ne amma ba irin lalatattun sojojin nan ba kamar waɗanda suka tsargu..."
Marshal ne zai nufo gurinta cikin zafin nama yana cewa "ke karfa kimun rashin kunya domin mijinki ma da kike gadara dashi a ƙasana yake yanzu kuwa an sallame shi gaba ɗaya bakuda bakin magana..."
General ne ya dafa kafaɗansa yana masa alamar sauƙowa..."
Junaid murmushi yayi yana kallon Ayush domin ba ƙaramin burgeshi tayi ba, yanzu babu wannan tsoron natan, zata iya tsayawa a gaban kowa tayi magana, yace "Yushert colm down kije kan maganarki kai tsaye..."
alamar voting tayi masa sannan ta cigaba da cewa "ina zaune yazo yana mun magana cikin rashin ɗa'a da daraja, a matsayina na mace kuma matar Aure shin ya kamata yayi mun maganar fasiƙanci? a'ah abun ya wuce fatar baki har hannu ya kawo yana shafa mun jiki da sunan saina biye masa yayi lalata dani, hakan yasa na yanke masa yatsun hannu saboda na koya masa darasin rayuwa...."
Junaid a zabure yace "whattt?..." zuwa yanda take yayi yasa hannu ya zabga mata mari ya riƙe mata kafaɗu da hannayensa biyu yana fuskantar ta rai a ɓace cikin ɗaga murya yace "hakan shine abun burgewa?..."
sauran sojojin da suke wajen abun ya ɗaure musu kai ganin yanda Junaid yake ganin laifinta, suna cikin wannan tunanin suka ji yace "amma kin cuceni Yushert, naso ace wuƙar da kika zara caka masa kikayi a maƙogaro, meyasa zaki tsaya a iya hannu? meyasa baki yanke masa wuya ba?..." kamar zaiyi kuka haka yake jijjiganta...
wanda aka yankewa yatsu ne ya soma magana cikin kakkarwar murya yace "wallahi ƙarya take...." kafin ya rufe baki Junaid yayo sufa kamar Damisa ya cabke masa wuya, da iya ƙarfinsa yake matse masa maƙogaro har saida yakai shi ƙasi, duk sojojin wajen ne suka rufu akan Junaid suka ƙoƙarin janye shi amma sun kasa, wani irin ƙarfin bala'i ne da Junaid, ko girgiza bayayi tsabar ƙarfinsa daya danna akan wuyan Naseer,
haka yake kakakin mutuwa ido sun fito waje, sai shure-shure yake numfashinsa a ɗage cakk, Junaid yana ƙoƙarin murɗe masa wuya akayi saurin kawo Alluran macewar jiki da sauri aka caka masa, daga nan ne akayi nasarar janye shi daga kansa, shi kuwa Naseer tinin ya suma kaɗan ne ya haka ya mutu domin inda anyi kuskuren jinkirin kawowa Alluran nan da Junaid ya karya masa wuya...
Junaid gaba ɗaya ya fita hayyacinsa sai cewa yake "ku barni na kashe shi, ku ƙyaleni nace, gaba ɗayanku zan kashe ku idan baku sakeni ba, zan kashe ku! zan kashe ku!! zan kashe kuuu!!!..." da haka shima ya sume a wajen sakamakon temporary da jikinsa ya ɗau ga kuma Allurar da aka masa,
sai a lokacin sojojin suka sake shi tareda ɗaukarsa suka nufi cikin ɗakunan quarters dashi...
Junaid wani irin zuciya ne dashi wanda lokaci guda hankalinsa zai bar jikinsa da zaran ransa ya ɓaci matuƙa, kuma ƙarfinsa ƙaruwa yake a lokacin,
dake Jinn sun shafeshi tin lokacin da sarki Raamud yake turo masa su, bayan hakan jinin tiger ya rigada ya gudana da jininsa dole da zaran ransa ya ɓaci abun zai ɗan motsa masa, amma ba kamar baya ba...
shiyasa General baya shiga sabgarsa sosai saboda gudun ɓacin ransa, iya marshal ne kawai yake fafatawa da Junaid dake shima yanada zafin rai amma bai kamo ƙafar Junaid ba...
Bayan shigar da Junaid cikin room marshal ne ya damƙi damtsen Ayush ya shigar da ita cikin mota shima ya zagaya ya shiga da gudu ya finciki motar suka tafi kai tsaye kotu suka nufa, sai kuma wasu motocin sojoji da suka biyo bayansu,
Naseer kuma hospital aka kai shi.
Bayan 10hours an gama Shari'a! malam Lawan ma ya halacci kotun, ba'a yanke hukunci ba amma an bada horo ɗaya, Ayush zata zauna a gidan gyaran hali har ta haihu, bayan ta haihu ne za'a sake zama a kotu anan za'a yanke hukunci,
Bayan an fito da Ayush za'a tafi da ita prisoner faɗuwa tayi ta fara burburwa a ƙasi tana juyi tareda zunduma ihu, wasu mata ne suka rirriƙeta suna shirin ɗagota amma sam taƙi shiga cikin mota, kamar wata mai Aljanu haka take ihu tana faɗin "wallahi bazanje prison ba! wallahi bazanje prison ba, wayyo Allah nah Yaya Junaid, nashiga uku ku temake ni wayyo Abbanaaa, Ummanaaa..."
kokuwa take dasu tana kai musu duka suma haka suke janta, ganin matan bazasu iya shigar da ita cikin motar ba yasa soja ɗaya yazo ya kimkimeta, shima haka take yakushinsa tana cizonsa tana kurma masa ihu da haka ya sakata a cikin motar aka rufe da ƙarfi, har aka tada motar suka tafi da ita tana wannan ihun, har muryarta yana shirin dishewa, fuskarta duk ya yi jawur tsabar kuka,
Malam Lawan yana tsaye a gurin saita yayi hawaye shima rai a jagwalgwale ya shiga motarsa ya tafi...
Acan ɓangaren Junaid kuma farfaɗowa yayi yana ambaton sunan Yusherttt gani yayi babu kowa a cikin ɗakin da aka ƙwantar dashi, tsararren ɗaki ne na hutawar manya-manyan sojoji ga sanyin A.C yanda yake ratsa shi ga kuma mashigar toilet ta gefe guda, da saurinsa ya tashi ya nufi bakin ƙofa zai buɗe ya fita, cike da mamaki yake bin ƙofar da kallo ganin an kulle ta waje, babu hanyar fita, da ƙarfi yasa hannu ya naushi ƙofar tareda yin ihu a fusace, ganin ƙofar bazai buɗu ba yaje ya samu guri a bakin gado ya zauna tareda dafe kayinsa da hannayensa biyu yana kallon ƙasi....
yana nan a haka har dare basu zo sun buɗe masa ba, kuma suna jin yanda yake ta buga ƙofar yana ƙiraye-ƙirayen sunayensu amma babu wanda yaje ya saurare shi domin bin umarnin Marshal,
shi ya sanar musu cewar kada su kuskura su buɗe masa ɗakin har washe gari, saboda yana tunanin zaije ya ɗauko Ayush ne da zaran an barshi...
*******
Ayush tana zaune acikin ɗakin da aka ajiyeta, ɗakin sun kai su goma aciki kowa da shimfiɗarsa kamar boading skull, ga an sauya mata kayan jikinta ya koma irin na sauran ƴan matan prison riga da wando iri ɗaya kowa da number a jikin rigarsa, kowa yana ƙwakkwance amma banda Ayush wacce take zaune a shimfiɗarta sai rera kuka take sakamakon yanzu dare ne misalin ƙarfe 12Am, duk ta cika musu kunne da kuka wata mata ce ta taso a zabure tayo kan Ayush tana masifar cewa "ke duk kin hanamu bacci, bama son sakalci fa kowa ma ba son zaman nan yake ba, dan haka ki rufe mana baki ko kisha mazga yanzun nan...."
Ayush ko sauraronta batayi ba saima ƙara volume ɗin kukan take, matar ce ta ɗagota tareda zabga mata mari har sau biyu tana faɗin "wallahi tallahi zan fitarki waje kika ƙara mana kuka .."
Ita kuwa Ayush tinin ta haɗiye kukan ta sai hawayen dake zubo mata ba ƙaƙƙautawa,
ɗaya ce daga cikin prisoner girl tace "haba Mimi ki ƙyaleta mana bakiga tanata juna biyu bane, kiyi mata uzuri dan Allah, kowa ma farkon zuwansa haka yayi..."
Mimi tace "bazan ƙyaleta ba Hafiza, idan kina mun shishshigi kema saina ci jatuminki, kina nam ƙarama dake sai iyeyin banza, ita kuma wannan idan na sake jin kukanta saina fasa mata baki wannan alƙawari nane babu ruwana na cikinta..."
tana kaiwa nan ta ƙwanta a wajenta tana surutan ta har bacci ya kwasheta,
Itama Ayush ƙwanciya tayi data ga ba wani sarki sai Allah duk da sauron dake ɗakin bai dameta ba saboda ta saba da zaman daji, batayi tsammanin zata zauna a prisoner ba.
Washe gari duk matan prisoner kowa ya fito da kwanonsa suna zuwa yin layin karɓan abinci, banda Ayush dake ƙwance a ɗaki ta kasa motsawa sai kuka, wata yarinya ce tazo kusa da ita takai hannu tana tattaɓata da sauri Ayush ta ɗago tana kallonta, yarinyar tace "kina ƙwance ki taso muje mu karɓi abun breakfast..."
daƙer Ayush take motsi da bakinta tace "bana buƙatar cin komai..."
yarinyar tace "idan bakije ba babu wanda zai saurareki balle ya kawo miki har yunwa tayi miki illa, ni idan naje da kwano biyu bazasu bani ba ki daure ki tashi muje kodan jaririn dake cikin ki..."
Ayush haka take bin yarinyar da kallo tana mamakin yanda akayi yarinya ƙarama tazo prison, gashi shekarunta bazata wuce 17 zuwa 18 ba, jinjina kai Ayush tayi tace "shikenam zanci ne saboda yarona..." haka ta tashi suka tafi tare da yarinyar har gurin karɓan abinci ga kayansu iri ɗaya mai launin sky blue..
Bayan sun karɓi abinci zama sukayi a wani waje su kaɗai yarinyar a hankali take feeding Ayush sakamakon yanayin abincin bazata iya ci ba saida dabara,
Bayan sun kammala breakfast yarinyar ce ta soma magana tana bawa Ayush labarinta tace "Ni sunana Hafiza asalin ƴar Kano ce, iyayena talakawa ne futuk sai nayi tallah muke samun abinda zamu ci, ƙwatsam wani saurayi ɗan gidan attajirai ya ganni yace yana sona, ni kuma a lokacin inada wanda nakeso shima talaka ne amma saidai yanada ƙwalin degree ɗinsa amma babu aikin yi, ni kuma a iya sacondary na tsaya, iyayena suka tilasta mun akan saina Auri ɗan masu kuɗi bana sonsa haka akayi mun Auren dole dashi, ƴan uwansa basa son mu ƙyamatar mu suke suna ƙiran mu da ƙazamai, da haka akayi auren aka kawoni nan garin Abuja, a daren farko na dashi ban yadda masa ba, haka nake gudunsa, a cikin daren nan na fito daga cikin ɗakin dake upstairs ne ina sauƙowa ƙasi shima yana biyoni a baya kwatsam tsautsayi ya rubta dashi ƙafarsa ta zame daga saman beni ya buga kansa da tiles, lokaci guda kayinsa ya fashe bama iya fashewa bama tsagewa kayin yayi daga lokacin bai ƙara motsi ba rai yayi halinsa...."
ta ƙarasa maganar tareda fashewa da kuka ta cigaba da cewa "shine ƴan uwansa sukai ta cewa ni na kashe shi wai, wallahi bani na kashe mijina ba, sun fimu arziƙi nesa ba kusa ba hakan yasa aka yanke mun hukuncin zaman gidan prison har tsawon ƙarshen rayuwata....". kuka ne yaci ranta sosai, Ayush itama kukan take domin ba ƙaramin tausaya mata tayi ba, gata ƙaramar yarinya, haka Ayush ta jawota jikinta tana rarrashinta, ita yanzu tama daina damuwa da kanta tinda a cikin prisoner har da ƙananun yara...
*BAYAN WATA 3*
Ayushert ta rigada ta sabarwa rayuwarta a cikin prisoner, yanzu ta daina damun kanta da yawan kuka, ga sun shaƙu sosai da Hafizat ta mayarta tamkar ƙanwarta ta jini komai tare suke yinsa, akwai abunda Hafiza bata barin Ayush tayi shine irin su wanki da ɗaukar abu