Showing 87001 words to 90000 words out of 186041 words
haka jikin maigadi yake rawa tsabar tsoro da firgici, yana tsaye sai haɗiyar yawu yake shi a tunaninsa har yanzu Junaid yana tiger ne, yana tsoro kar ya zama Damusa...
Ayush tana cikin raira masa waƙa taji jikinsa yana kakkarwa sosai, ga yaɗau zafi over, kuma jininsa ya zuba sosai yana buƙatar temakon gaggawa, ƙara fashewa tayi da matsanancin kuka still bata daina waƙar ba, suna cikin wannan halin sai suka ji horn ɗin motar, maigadi ne yayi saurin buɗewa ba tareda ya duba ba,
motar Malam Lawan ne ya shugo kai tsaye ko gama tsayar da motar baiyi ba ya fito da gudun gaske yayo kan Ayush yana faɗin "lafiya kuwa Ayshert meya faru da Junaid?..."
Ayush ko ɗagowa ta kalli Malam Lawan batayi ba still tana kan rera waƙarta, kayinta a kwance saman kafaɗar Junaid wanda shima kansa a ƙwance yake saman kafaɗarta, shi kuwa tinin har ya suma numfashinsa ya ɗage cakk..
Daƙer Malam Lawan ya ɓanɓari Junaid daga jikin Ayush domin ba ƙaramin riƙo yayi mata ba duk da yana sume,
Itama riƙe shi tayi sosai saida malam ya yageta a jikinsa tana kuka mai fitar hankali,
Shi kuwa murfin motarsa ya buɗe ya saka Junaid a ciki shima ya shiga suka bar gidan..
Bayan fitarsu Ayush ƙwanciya tayi a ƙasin floor ta cigaba da rera waƙarta tana kuma kuka, idon nan yayi jawur ga fuska shima yayi jawur abunka da farar fata,
Maigadi bayan ya rufe gate shima zama yayi akan kujerar robarsa yana fuskantar Ayush wacce take kwance a ƙasi kamar wacce take kan gadonta....
Malam Lawan kai tsaye hospital ya tafi da Junaid zuciyarsa cike da baƙin cikin abunda akayiwa Junaid...
Shima Doctor Hasheem hospital ya kai Lailah amma saidai ba asibitin Doctor Fateema yakai ta ba, wani asibiti daban yakaita....
*******
Maimoon tana durƙushe a gaban Daddynta a falo shi kuwa yana zaune akan kujera yana fuskarta ta ga wuƙa a hannunsa yace "Bintu zaki gaya mun wanda ya miki ciki ne ko saina yanka ki yanzun nan?..."
tana kuka tace "Daddy wallahi ban saniba, mutanen da suka sace ni ne suka mu kuma ban san su baa.."
Daddy cije leɓɓensa yayi cikin takaici yake faɗin "Bintu a baya na yarda dake sakamakon kinada hankali ga kuma biyayyar da kike mana, banida ko wace ƴa inba ke ba, ke kaɗai Allah ya mallaka mu! na ɗauki son duniya na ɗora miki, Allah ya baki ilimin boko da Arabic, a fannin boko kin gama degree ɗinki, a fannin Arabic ke malamar islamiyya ce kin haddace alƙur'ani mai girma, amma wai yau ani zaki bawa kunya a idon al'umma? haba Bintu! toh wallahi wallahi bazan taɓa yadda dake ba shin waya miki ciki?..."
Maimoon fashewa tayi da matsanancin kuka ga ciki ɗurumma agaba tace "Daddy gaskiya na faɗa maka..."
cikin takaici Daddy ya kamo hannun Maimoon ya yanka da wuƙa, nan danan saiga jini kamar ambaliya, haka take ihu kamar ranta zai fita...
Cikin tsawa yake faɗin "zaki gaya mun wanda ya miki ciki ko saina yanke hannun gaba ɗaya?
kar ki manta fahh an taɓa gaya mun cewa an ganku a hotel ke da Lailah shin me kuka je yi? gurin wa kuka je a hotel? an gaya miki ni sakaran uba ne wanda zan zuba miki ido kiyi abunda kike so?..."
Ammy tana can ɗakinta tana ƙwance in banda kuka ba abunda take, bazata iya juran ganin hukuncin da ake yiwa Maimoon ba...
Daddy haka ya kama hannun Maimoon ya rinƙa yankewa tin daga kan dantsenta har zuwa tafin hannunta haka yake sa mata wuƙa yana yankewa,
kamo ɗayan hannunta yayi shima ya rinƙa dasa mata wuƙa, nan danan jini kamar ambaliya duk ya wanke mata jiki da wajen da take zaune,
a cikin tana ihu har ta komo hankalinta ya soma fita daga jikinta, haka take lumshe ido kamar zata mutu,
Daddy magana yake mata amma ta kasa yin magana,
Haka ya tashi a fusace ya nufi ɗakinsa kafin ya dawo Maimoon har ta ƙwanta hankali yana shirin fita,
can saiga shi ya dawo hannunsa riƙe da Allura ganinta a ƙwance ya darara mata uban tsawa yana faɗin "waya baki izinin ƙwanciya dan ubanki, tinda har ni zaki tozarta toh zanyi maganinki, bazan taɓa jin tausayinki ba tinda har kema bakiji tausayin kanki ba, yau ko kinaso ko bakya so saikin gayi wanda ya miki ciki! bazan barki ba saidai idan mutuwa kika yi a yanzun nan..."
ya ƙarasa maganar yana caka mata allura a dantsenta,
wannan allurar bana komai bane sai fitar da mutum daga hayyaci yasa ya faɗi duk wata gaskiyar da aka tambaye shi...
Bayan wasu sakonni Maimoon tana ƙwance ta kasa tashi zaune ga yanda idonta yake juyawa, bakinta yana kakkarwa kamar mai jin sanyi, haka haƙwaranta suke dukan juna tsabar kakkarwar da suke yi..
Gyara zama Daddy yayi yana kallon Maimoon yasan a wannan lokacin Alluran ya gama bin jikinta yace "Bintu gaya mun waye ya miki ciki?..."
Maimoon baki na kakkarwa tace "D D Doc Doct Doctor Haa Haas Haashim neee, ya yaa yamuun f f fya fyaɗee...."
Daddy daƙer ya fahimci abunda Maimoon ta gaya,
Ƙirjinsa ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ya miƙe tsaye tareda faɗin "Whatttt! Doctor Hasheem?..."
*Toooh Matan Tigers kuna Ina neee*
*Nidai bakina da goro babu abunda zancen*
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 45 ➡️ 46
Lailah tana ƙwance saman gadon asibiti an saka mata na'urar auna ƙwaƙwalwa a kanta, sai tarin likitocin da suke dubata waran su uku,
Shi kuwa Doctor Hasheem yana zaune akan ɗaya daga cikin kujerun asibiti yana jiran fitowar likitocin, yayi tagumi yanata tunanin abubuwan da suka wakana, lokaci guda kuwa ya fara girgiza kansa yana faɗin "Please Ogah Junaid am so sorry, nayi regretted abunda na aikata maka, dan Allah ka yafe mun..." yana cikin wannan maganar zuci yaji an dafa kafaɗarsa ta baya da sauri ya waiwaya tareda miƙewa tsaye yana faɗin "Doctor ya jikin ƙanwata fatan dai tana lafiya, shin ta farfaɗo ne?.."
Girgiza kai Doctor yayi sannan yace "inason ganinka a office ɗina.." yana kaiwa nan Doctor yayi juyawarsa, gaban Doctor Hasheem ne yake yankewa duk jikinsa yayi sanyi da haka ya nufi office ɗin Doctor jiki ba ƙwari!..."
yana zuwa kuwa ya samu Dr a zaune a cikin office ɗinsa shima Dr Hasheem guri ya samu ya zauna yana fuskantar likitan,
gyaran murya Doctor yayi sannan yace "Ammm Dr Hasheem abunda zan gaya maka shine kayi haƙuri nasan zakaji ba daɗi amma inaso kayi la'akari da kaima Doctor ne kuma kuna samun irin waɗannan matsalolin a asibitinku, kamar yanda kuke cewa iyayen wasu suyi haƙuri toh nima yau zance maka kayi haƙuri ƙanwarka ta rasa tunaninta gaba ɗaya sakamakon buguwar da tayi akanta, ƙwaƙwalwarta ta juye bazata iya tuna duk abunda ya faru a baya ba, haka kuma bazata iya gane kowa a halin yanzu ba, ga sakamakon gwajin da mukayi mata..." Dr ya miƙawa Dr Hasheem wata doguwar takarda, jiki a sanyaye Dr Hasheem yakai hannunsa ya karɓi takardar hannu na kakkarwa, sannan ya buɗe yana karantawa lokaci guda saiga hawaye duk ya wanke masa fuska...
Dr ne yake ta faman bashi haƙuri...
Dr Hasheem yace "shin Dr babu wani maganin da za'ayi ta dawo hayyacinta?.."
Dr Mansur yayi murmushi sannan yake "Hmmm Dr Hasheem kenam inda ace bakayi karatun Biosciences ba sai inyi maka uzuri amma kai fah kasan kan tsarinnan yanda yake, idan Allah yasa ta farfaɗo za'a ɗorata ne akan maganin sakatiri, kuma dole sai an kaita babban asibitin masu juyayyun ƙwaƙwalwa..."
Dr Hasheem ne yace "shikenam Dr ni zan tafi, fatana Allah ya tashi kafaɗunta.."
Dr Mansur yace "no insha Allahu zata tashi ma"
ficewa yayi daga office yana sharar hawayen kan fuskarsa tareda duba agogon hannunsa misalin ƙarfe 10 ne na dare, shiga ɗakin da aka ƙwantar da Lailah yayi ya samu kujera ya zauna tareda kwantar da kansa a bakin gadon hannunsa riƙe dana Lailah sai faman zubda ƙwallah yake,
Ita kuwa Lailah gaba ɗaya ta zama abun tausayi har zuwa yanzu bata farfaɗo ba, anyi recovery bakinta da hancinta da Oxygen, ga gefe da gefen kayinta na'ura ne a jone yana aiki da computer, hannunta kuma yana ɗaure da drip na ruwa...
Can bayan wasu ɗan mintuna Dr Hasheem ya ɗago yana lalumen wayansa tunawa yayi ashe ya barta a gida daman bai fito da phone ba,
miƙewa yayi ya fita waje kai tsaye wajen ma'ajiyin telephone ya nufa wanda kowa da kowa zaiyi waya a duk lokacin da yaso, number maigadin gidansa ya ƙira bugu biyu aka ɗauki ƙiran daga ɓangaren maigadi sallama yayi tareda tambayar waye ne?
Dr Hasheem ne ya tambaye shi cewar "Ayushert tana gidan?..."
maigadin jin muryar Ogansa ne yasa shi amsawa da sauri yace "eh ƙwarai tana ciki yanzu kam hala tayi bacci..."
Dr yace "Okay duk wanda yazo karka buɗe saboda bazan samu damar dawowa gida ba, zan zauna agurin ƙanwata," daga nan ya katse ƙiran ya juya zai koma ɗakin da Lailah take....
*Ayushert*
tana cikin flawowin gidan tana laɓe da akwatinta ta wajen bakin gate, tana jin wayanda Maigadi yake yi da Dr Hasheem ita damuwarta maigadi ya tashi daga gurin ta samu ta fice a gidan, ga ta ko ina hasken nepa ne,
can tana tsaye sai taji maigadin yana faɗin "wayyo marata fitsari ya matseni da yawa, bari na ɗan zagaya nazo kuma na danna kwaɗo a gate nima na ɗan yi bacci na.." yana barin wajen kuwa Ayush tayi saurin buɗe gate ta fice tana jan akwatinta da sauri,
daƙer ta samu napep a wannan daren ta nufi hospital yanda Junaid yake,
suna isa asibitin kafin ta sauƙa daga cikin napep sai ga motar Malam Lawan ya fito daga cikin asibitin ya wuce cikin gari, fitowa tayi ta sallami mai napep sannan itama ta shige cikin hospital tana rurrufe fuska kamar wata marar gaskiya, ajiye jakarta tayi a guri guda tukun ta ƙarisa shige cikin compound ɗin hospital, lelleƙa ɗakuna ta shiga yi amma ta rasa a wani ɗaki aka ƙwantar da Junaid, wani ma'aikaci ne yayi mata magana ta bayanta yana cewa "Hajiya wa kike nema ne?.."
juyowa Ayush tayi duk ta rufe fuskarta da mayafinta tace "am amm room ɗin da aka ƙwantar da Oga Junaid nake nema..."
yace "Okay zo na nuna miki" yayi gaba itama tabi bayansa.
suna zuwa wajen tayi saurin buɗe ɗakin ta shiga ganinsa tayi a ƙwance yana lumshe da ido alamar bacci yake, ga yanda aka ɗaura masa ledar jini a hannu, da sauri ta ƙariso gurin tana kuka tareda sa lallausar hannunta tana shafa masa fuskarsa,
Junaid kamar a mafarki yake jiyo kukan Ayush, motsi ya fara yi a hankali yana ƙoƙarin buɗe idonsa, dasauri Ayush ta miƙe tareda shiga bayan labule ta ɓoye, buɗe eyes ɗinsa yayi ya juyo yanda yake jin kukan yaga ba kowa, ƙoƙarin tashi ya fara yi daiden lokacin da Malam Lawan ya shugo hannunsa riƙe da ledojin abun ciye-ciye, ganin Junaid yana shirin tashi ne yasa yayi saurin ƙarasowa yanda yake yana faɗin "lafiya kuwa Junaid? zaka gotar da alluran hannunka fah..."
Junaid hannu yasa ya dafe kansa dake bala'in masa ciwo, duk anbi an zazzagaye kayin da bandeji cikin sassanyar murya yace "malam ina Yushert?..."
girgiza kai malam Lawan yayi yana murmushi yace "Junaid kenam tin farkon farfaɗowarka kake ta tambayar Ayshert, yanzu ma kayi bacci ka tashi da sunan Ayshert a bakinka, shin meyasa bazakayi haƙuri ka danne zuciyarka ba..."
Junaid ɗagowa yayi yana kallon Malam kamar zaiyi kuka yace "bazan taɓa cire Yushert a raina ba, haka kuma bazan taɓa rabuwa da Yushert ba, domin ita ɗin matata ce kuma jinin jikina..."
Malam ne ya dafa kafaɗarsa tareda cewa "komai ɗan lokaci ne Junaid, idan kayi haƙuri Ayshert zata dawo gareka, a halin yanzu bazata fahimce ka ba, ka barni da ita Insha Allahu zata fahimce ka, inaso ka sani