Showing 171001 words to 174000 words out of 186041 words
fari kamar jini zai fita, tayi kyau matuƙa, duk abunda take buƙata kuwa dasauri ake mata, duk wani kulawa tana samu a wajen sarki Raamud, domin ba ƙaramin ƙaunarta yake yi ba, baya ƙaunar ganin ɓacin ranta.....
Yau ranar Monday Around 12AM na dare. Mommy tana ɓangaren ɗakinta ita kaɗai ta tashi tana salati tareda jero addu'o'i daƙer ta tashi akan bed ɗinta ta nufi hanyar fita, kai tsaye downstairs ta sauƙo falo, daga nan ta nufi wani ɗakinta na magungunuwa taje ta ɗauko boxes sannan ta haura saman ɗakinta, tana shiga bedroom ta shige toilet, saida tayi kusan awa guda acikin toilet kafin na fara jiyowa kukan jariri,
Ni Asmeetah ina daga bedroom abun ba ƙaramin bani mamaki yayi ba, ina tsaye sai kuma na ƙara jin kukan jariri kuma du, kafin kace mai sai muryoyin jarirai suka fara kuka a jere a jere, banyi gaggawar shiga cikin toilet ba, na cigaba da tsayuwa can sai naga ta buɗe ƙofar toilet, cike da mamaki da kuma son ganin abunda ke faruwa na zurawa ƙofar ido ƙwatsam sai naga mommy ta fito hannunta riƙe da jarirai biyu, tazo ta kwantar dasu saman gado daman ta rigada ta yanke musu cibiya ta wanke su tas, ta buɗe wardrobe ɗinta ta ciro kayan jarirai na sanyi farare masu kyau, duk ta sassanya musu ta feshe su da turare masu ƙamshin gaske wanda bazai cutar dasu ba, still ta kwantar dasu ta lulluɓe su, acikin wannan daren ta sake shigewa cikin toilet ta haɗa ruwan zafinta na gaske tayi wanka ta gyara cikin toilet ta feshe da turare yanda bazaiyi ƙarnin jini ba, ta wanke kayanta wanda ta ɓata, ta shirya kanta tsab itama ta gama feffeshe jikinta da turare da duk gaba ɗaya ɗakin, sannan ta tottofa wa jariran addu'o'i ta ƙwanta gefensu har zuwa sallar asuba...
Har gari ya waye sarki Raamud bai san mommy ta haihu ba, hatta suma ma'aikatan gidan mommy ta hanasu shiga cikin ɗakinta a yau, bata sanarwa kowa ba, kuma dake ɗakinta yana saman Upstairs ba kowa ne zai iya jiyowa kukan jariran ba,
Dalilin yin haka shine haihuwar nan ba ƙaramin kunyata mommy yayi ba, ita har cikin zuciyarta bata so ta haihu a halin nan ba, saboda a cewar ta bai dace ace yaranta suna haihuwa itama tanayi ba, taso ace tabar musu haihuwan ita kuma ta haƙuri amma saidai sarki Raamud ne ya tsayar mata akan cewa dole saita haifo masa wasu yaran, hakan yasa ta haƙura tabi umarninsa, shine dalilin da yasa yanzu ta haihu kuma ta gagara sanarwa kowa,
Saida wata daga cikin kuyangen tazo zata ƙonƙosa ƙafar ɗakin mommy taji kukan jariri, da gudu ta juya baya bata tsaya a ko ina ba sai a ɓangaren sarki Raamud, tana zuwa ta durƙusa a gabansa tana maida numfashi tace "mai martaba sarauniyarka ta haihu naji kukan jariri acikin ɗakinta..."
Sarki Raamud bai tsaya jin ƙarashen maganar ba ya miƙe tsaye da hanzarinsa ya nufi hanyar fita kai tsaye part ɗin mommy ya nufa, yana zuwa ya tura ɗakin yaji a rufe ta ciki, bugawa ya soma yi da ƙarfi yana ƙiran sunanta, daƙer tazo ta buɗe masa cikin jin kunya kanta a sunkuye, sarki Raamud kamar zai tashi sama tsabar farin ciki, cike da mamaki yake bin jariran da kallo sai kuma ya ɗago ya kalli mommy gaba ɗaya har shirin zaucewa yake tsabar farin ciki, dasauri yakai hannu ya rungumo mommy sosai kamar zai mayarta cikinsa,
tsawon shekara uku taƙi haihuwa sai a wannan lokacin, nan ma saboda ta farantawa sarki ne yasa ta haihu, yana cikin godewa Allah yaji tace "dan Allah ina neman alfurmanka mai martaba .."
juyowa yayi cike da farin ciki yace "ki faɗi duk abunda kike so zanyi miki Sarauniyata...."
Tace "dan Allah inaso ne kar a sanarwa su Junaid cewa na haihu, Ni kar a sanarwa kowa ma, dan Allah...."
Sarki Raamud yace "indai abunda kike so kenam shikenam nayi miki Alƙawari bazan sanarwa kowa ba saidai su zo su tarar dake da ƴaƴanki..."
Kallonsa tayi sannan tayi murmushi, yace "amma zaki ban mamaki, taya kika haihu ke kaɗai? Sannan ba wani jikkata ko rashin lafiya a tattare dake?"
tayi murmushi sannan tace "ikon Allah kenam, haka Allah yaso dani..."
Shima yayi murmushi yakai Idonsa kan yaran yace "Masha Allah duk mai aka samu?.."
Mommy tace "Namiji da kuma Mace..."
Sarki Raamud lokaci guda kuma sai yake jin hawaye yana shirin gangaro masa saboda ya tuno da Bara'at uwar Ayush, itama twins ne a cikinta akazo aka salwantar dasu tareda mamansu sai kuma gashi Allah ya maido masa su ata ɓangaren mommy,
Zama yayi ya ɗauki yaran ya tottofa musu addu'o'i sannan yace "na sanya wa yaron suna Artaff wato mai sunan Uncle Artaff (malam Lawan)...
Macen kuma na sanya mata suna Bara'at..."
Mommy taji daɗi sosai dajin sunan da ya sanya musu....
★★★★★
Ranar Bikin Hafzat da Judan kowa acikin danginsa sunzo ɗaurin Aure har shima kansa Judan, sarki Raamud shima yazo Nigeria amma banda mommy, ita mommy abunda ya hanata zuwa shine jariranta waɗanda suka ci sati guda a duniya, itama Hafzat ta koma Kano domin daga can za'a ɗaukota acikin ƴan uwanta...
Itama Lailah aranar aka ɗaura mata Aure ita da Doctor Mansur ɗinta, an kaita gidan mijinta cikin ƙoshin lafiya.
Itama Hafzat aranar aka sata a jirgi sai ƙasar Jidda ƙasar su judan kenam, anan zata zauna...
Ayush ba ƙaramin kewar Hafzat tayi ba, ga Ogah Junaid duk ya kori ƴan aikin gidan, saita jita shuru ba daɗi, ga yara na school shima idan ya fita yawonsa baya dawowa da wuri, gaba ɗaya zaman kaɗaici yayi mata yawa ga ayyukan gida sunyi mata yawa gaba ɗaya ta shiga damuwa sosai....
Akwana a tashi Uncle Artaff shima yana shirin barin Nigeria, zai koma can masarautar california da iyalansa, sunyi bankwana da kowa, anan ma Ayush ba ƙaramin shiga damuwa tayi ba ganin yanda kowa yaketa tafiya,
Bayan tafiyar Uncle Artaff da wata guda shima Junaid ya tada nashi tafiyan zai koma california shima tareda su Ayushert, a hutun da aka bashi ma har ya ƙara kwanaki, Ayush ba ƙaramin farin ciki tayi ba jin wannan Albishir daga bakin mijinta, ga murnar zata je ta tarar da mommy tayi missing ɗinta sosai, amma abun mamaki duk yaran babu mai son tafiyar, saboda basa so subar school ɗinsu, ga waɗanda suka shaƙu sosai especially matan sunfi ƙawaye amma shi Areeph daman bashida wanda zaiyi missing ɗinsa sai iya Rapeekh domin shine kawai abokinsa, shima Rapeekh bason tafiyar Areeph yake yi ba, harda kukansa cewar Areeph zai bar Nigeria, sunyi shirinsu tsab, akan washe gari da sassafe zasu tafi airport domin har sun yanki Viza,
Washe gari sun fito zasu shiga motar da zai kaisu airport kwatsam wani irin murɗa ya damƙi cikin Ayushert, bata san lokacin data fara jero addu'o'i ba, nan danan zazzaɓi mai zafin gaske ya rufe ta, ga hajijiya haka ta tafi luu zata faɗi Ogah Junaid yayi saurin tarota tareda faɗin "lafiya kuwa? meyake faruwa dake?..." kafin ta bashi amsa dasauri ta zame daga jikinsa ta nufi wajen fanfo anan ta tsuguna tana kwarara amai ba ƙaƙƙautawa, zuwa gabanta yayi ya tsaya yana kallonta yace "kodai mu fasa tafiyar nan yau naga bakida lafiya koh?..."
girgiza kai tayi tace "ba komai zamu iya tafiya..." matsowa dab da ita yayi ya soma taɓa jikinta ji yayi kamar garwashi tsabar zafin da jikinta ya ɗau, lokaci guda ta fita hayyacinta ido sunyi zuru-zuru, shima girgiza kai yayi yace "gaskiya mu haƙura da tafiyar nan, idan kin samu sauƙi inyaso sai mu tafi koh?...". Nan danan saiga hawaye kwance a fuskarta ita sam bataso a haƙura da tafiyar tasa ranta sosai a tafiyar, tace "ina zumuɗi naje naga mommy dan Allah My kar kace bazamu tafi ba a yau, wallahi bana jin ciwon jikina..."
yace "shikenam toh tinda kince haka, saiki wanke bakinki kizo mu tafi kar jirgin mu ya tashi .." a hanzarce ta wanke bakinta suka koma wajen mota, yaran kuma suna ciki sai wasan su suke ta sha yayin da shi kuma Areeph yake riƙe da wayarsa sai game yaketa yi,
Ogah Junaid ko kaɗan bai kawo komai a ransa ba na dalilin aman Ayush, ya ɗauka cewa rashin lafiya ne na halin rayuwa yau da kullum, baiyi tunanin akwai ciki a jikinta ba saboda a yanda ta sanar masa shine tace "bata son haihuwa yanzu saita huta, kuma wai taje tayi Allurar planning na tsawon shekara huɗu..." Kuma tayi lissafi ne da cewar a yanzu yaranta sunada shekara huɗu a duniya idan ta ƙara shekara huɗu kuma sunada shekara takwas alokacin ne zatayi ƙoƙarin yi musu ƙani ko ƙanwa, saidai kuma data je yin Allurar planning sai akayi mistake maimakon ayi na yanda takeso 4 years sai akayi rashin sa'a sukayi mata na Three months kuma tin kafin Ogah Junaid ya dawo taje akayi mata, saidai kuma shi ba'a son ransa tayi planning ba, kawai ya ƙyaleta ne a haka....
A yanzu ko ita kanta bata san tanada cikin ba, saboda yana yin planning saida ya ɗauke mata jini kwatata daga baya ta dawo tana gani, kumadu ya ƙara ɗage mata haka yake mata shiyasa bazata san tanada pregnant ba, gashi har na tsawon wata biyu.....
Haka suka shige mota sai airport anan suka shiga jirginsu,
Haka su Areeph da Angel da Amrish suka rinƙa tsalle suna murna cewar yau zasu shiga jirgi wai basu taɓa shiga ba,
Ogah Junaid sam baiji daɗin hakan ba, yaso ace yanda suke da kuɗin nan ace yaransa sun saba shiga jirgi, gashi yanzu yanda suketa tsalle kamar wasu baƙauyawa, son samu ace duk ƙarshen wata ana fita dasu yawon buɗe ido ƙasashe daban daban, amma laifin kansa yake gani da baiyi ƙoƙarin yin haka ba, ko ita Ayush ya kamata ace ta saba shiga jirgi amma itama yanzu ne karo na farko....
Bayan isar su ƙasar california a Babban Birnin Masarautar ƙasar suka sauƙa, Ayush gani tayi kamar ba masarautar ba duk an chancanza ko ina, suna daga cikin mota bayan sun sauƙa a airport daga cikin masarauta sarki Raamud ya tura driver akan yaje ya ɗauko su, gani sukayi an buɗe babban gate kai tsaye motar ta shige ciki, ga wasu manya-manyan Bodyguards a jere fuskokinsu kamar mutuwa ba alamar dariya, Areeph yana leƙensu ta window tareda cewa. "Daddy ina ganin waɗannan a Film, sune masu harbi da bindiga awajen yaƙi...."
Murmushi kawai Junaid yayi jin yanda yaran suketa mita akan Bodyguards, bayan sunyi gaba sosai suka ƙara tarar da wani gate kuma du, nan ma buɗe musu akayi kumadu wasu ɗirka-ɗirkan baƙaƙen Amurkawa aka ajiye a jere saboda tsaro ga wasu manya-manyan karnuka da suke yawo a compound ɗin gidan, daga nan ne sai babban ƙaton cikin fada yanda manya-manyan baƙi suke zama domin tattaunawa da mai martaba sarki Raamud wato fadar sarki kenam, anan kuma kujerarsa take na zinare, anan suka sauƙa part ɗin sarki Raamud kenam kafin su wuce part ɗinsu,
Karnukan nan har sun kewaye motar suna huci duk da sun san motar gidan ne amma so suke suga mutanen cikin, suna fitowa Ayush ta ƙanƙame Junaid da ƙarfi jikinta har kakkarwa yake ba ƙaramin tsoron kare take ba, ko a can Nigeria mah bata fitowa waje saboda karnuka har yaran suka saba, suma yaran fitowa sukayi duk da basa tsoron kare amma waɗannan karnukan sun razana su, saboda su kalarsu daban yake na turawa ga gashi tumuzu guda ajikinsu, suma karnukan ganin Ogah Junaid yasa duk suka kama gabansu saboda daman shine ya watsar dasu a cikin gidan, karnukansa ne,
Haka suka shiga cikin babban falon su Mommy, ƴan aiki kawai suka tarar sunata aikace-aikacen su, duk zama sukayi akan kujeru Ayush kam bazata iya zama ba haka tasa akayi mata kwatancen yanda ɗakin mommy yake, da gudu take taka matakala har ta isa part ɗin mommy tana zuwa tasa hannu ta buɗe ƙofar ɗakin da fara'a akan fuskarta, abunda ta tarar ne yasa tayi go slow awajen, ido a zazzare take kallon mommy tana bawa yaro nono ga kuma ɗaya a kwance saman gado,
Mommy kallon Ayush tayi tana dariya daman tasan dole abun zai bata mamaki, domin shima Uncle Artaff daya zo ya tarar da jarirai abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba,
Mommy tace. "shugo mana Ayusher...". cike da tambayoyi a bakinta ta ƙarasa shugowa tana faɗin mommy mezan gani haka daman kin haihu ne shine baki sanar mana ba haba Mommy ..."
Ayush tana ƙarasa maganar saiga Ogah Junaid shima ya shugo da sallama a bakinsa da Sarki Raamud yana riƙe da hannun Amrish da Angel, shima Junaid tsayawa yayi kamar wanda aka dakatar dashi, cikin rashin fahimta yace "Mom wadannan yaran waye? aina kika samo su, karfa ki cemun yaran wasu kika karɓa kina shayar dasu?..."
Mommy tace "toh idan ba yaran wasu ba shin yaran wa kakeso nace maka?..."
Gira a haɗe yace "yaran wasu mana, saboda ke dai nasan a yanzu bazaki haihu ba.."
Ayush tace "Yaya Junaid wallahi mommy haihuwa tayi gashi tana shayar dasu..."
Junaid hararar ta yayi sannan yace "kar ki gaya mun maganar shirme mana, nasan halin Mom yanzu haka ɗaukosu tayi a gidan marayu..."
Ayush ta kuma cewa "toh tayaya ruwan Nono zai zo mata alhalin ba haihuwa tayi ba..."
A ƙaiƙaice ya daka mata tsawa da cewa "yimun shuru, haihuwar lafiya..."
Mommy dai kai a sunkuye ta kasa cewa komai ga yaro yanda yaketa shan breast,
Sarki Raamud ne ya dafa kafaɗarsa yana cewa "Junaidd look at me, seriously Mom ɗinka ta haifi twins, kamata yayi kayi murna duk da nasan rashin sanar muku ne yasa ka shiga konkonto abun zaiyi matuƙar baka mamaki...."
Kafin sarki Raamud ya rufe baki Junaid ya katse shi da cewa "Da kuma bani haushi ba, haba tayaya zanyi murna tsofe-tsofe daku kuna haihuwa, ku dubi ƙananun jarirai fah wai ku kuka haifesu wallahi abun yaban kunya, ina laifin Ni na haifesu,