Showing 54001 words to 57000 words out of 186041 words

Chapter 19 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53915

tashin Ayush yin Sallah, kuma zataje ɗakinsa!
komawa yayi cikin toilet a ruɗe da zanin gadon daya ɓaci haka yasa a bucket ya zazzagi omo ya fara wanke zanin gadon, shi tinda yake ma bai taɓa yin wanki bama sai yau...

Ita kuwa Ayush jin yanda ruwan zafi yake ratsata ne yasa ta farfaɗo tana cikin baho ko kallon yanda Junaid yake batayi ba sai hawayen da yake gangaro mata, tayi shuru ko motsi batayi sai faman lumshe ido take...

Junaid da iya ƙarfinsa ya wanke bedsheet ɗin nan tas ya shanya shi acikin toilet ɗin dake akwai igiyar shanya a ciki,
yana gamawa da wannan ya nufi gurin Ayush, haka yasa hannu yana watsa mata ruwan ɗumi ajiki, itama saida ya wanketa tas ya ɗumama mata ƙasinta da hot water sannan ya ɗaura mata new towel daya ɗauko a cikin wardrobe ɗinta ya ɗauketa a saman kafaɗarsa suka fita bedroom,
Duk abubuwan da yakeyi tana jinsa bata ce masa komai ba, tsananin kunya ne ya isheta shiyasa ta kasa motsawa domin duk ya kalle mata tsaraicinta, gaba ɗaya taji Junaid ya wanke mata a rai...

Bugun ƙofa sukaji a yayin da Junaid ya zaunar da ita akan gadon daya gyara,
Zuciyarsa ne ta fara bugun uku-uku, jin yanda aketa buga ƙofar ɗakin,
muryar Mommy yaji tana ƙiran sunan Ayush akan tayi sallah ne ko kuwa,
Junaid da sauri ya buɗe wardrobe ya zaro mata doguwar riga marar nauyi mai gajeren hannu yazo ya sanya mata shi,
jin muryar Mommy ya kuma ji tana cewa "wai ni Ayush ƙalau kike ne? inata ƙiranki shuru kardai ace kin koma bacci ne,
shin kinyi sallah ne ko kuwa?..."
Junaid jin Mommy taƙi daina surutu kuma ga Ayush taƙi yin magana yasa shi yin muryar mata cikin sassanyar murya yace "ehhh nayiii....". yayi kalar muryar Ayush.
Mommy tace "ok ai sai kiyi magana tin ɗazu..."
tana kaiwa nan ta juya abunta,
tana barin bakin ƙofar Ayush kai tsaye ɗakin Junaid ta nufa,
Junaid yana jin yanda Mommy take bubbuga masa ƙofa tana ƙiran sunansa,
Junaid dafa goshinsa yayi yace "oohhh mom kin cika damuwa.."
Ayush kallonsa kawai takeyi babu alamun dariya a fuskarta,
sunkuyawa yayi a gabanta yana dafe da cinyarta yace "Yushert ba roƙonki zanyi akan ki yafe mun ba amma kuma ina neman alfurmanki dan Allah,
ki temakeni kar wanda yasan abunda ya shiga tsakanin mu, kar ki gaya wa mommy abunda na aikata miki Please ki temakeni Yushert..."

Ayush tana sharar hawaye tace "ka tashi ka bar mun ɗakina, bana buƙatar ganin fuskarka dan Allah, ka temakeni ka bar mun ɗakina idan kuma yin fyaɗen Bai isheka ba ga fili ga Mai doki..."

Junaid dafe goshinsa yayi yana faɗin "ohhhh my God! Yushert ki sani fah bawai fyaɗe nayi miki ba, wallahi bansan nayi miki haka ba, ba'a cikin hayyacina nake ba ki yadda dani manaa..."

Ayush a fusace ta miƙe tsaye tana faɗin "i said leave my room, please stay away from me..."
Junaid miƙewa yayi yana cewa "Okay okay it's okay, zan tafi yanzu ki kwantar da hankalinki..."
yana kaiwa nan ya nufi bakin ƙofa zai fice, ganin Mommy ta fito a ɗakinsa ne yasa ya laɓe,

Mommy kuwa a tunaninta Junaid har ya tafi masallaci ne,
sauƙa down tayi...
tana tafiya Junaid ya fito da sauri ya wuce ɗakinsa, zuwa yayi ya shiga toilet ya yi wanka da alwala ya fito yayi sallah ko masallaci baije ba a ɗakinsa ya yi sallar...


Angel itama tana cikin ɗakinta tayi sallah abunta tana zaune akan sallaya duk fuska yayi jawur, ido yayi lufu-lufu taji wayarta yana ringing, tashi tayi a kasalance ta ɗauki wayar a saman gadonta tayi picking tareda karawa a kunne tana faɗin "Hello gud morning sir..."

Sanar mata akayi cewa yau ne tafiyarsu ƙasar California tareda sojojin Nigeria domin yin shirye-shirye, gobe za'a fara gudanar da yaƙi,
haka ko wace ƙasa sojojinta zasu tafi California ne..."
Angel amsawa tayi da "Okay sir..."
daganan aka katse wayar
tana sauƙar da ajiyar zuciya saiga wani ƙiran ya sake shugowa ɗagawa tayi tana cewa "hello marshal sadeek well done.."

daga ɓangarensa kuwa cewa yayi "yauwa commander Angel the Army of California how is day?..."
amsa masa tayi cikin farin ciki,
sannan yace "na ƙira wayan Captain Junaid tin cikin dare bai ɗauka ba, lafiya kuwa?..."
Angel tace "ayya Ina tunanin bacci yake yi, amma ai maganar bazai wuce akan yau ne tafiya can ƙasar yaƙin ba koh?..."
yace "of course, zan tunatar dashi ne akan yanzu haka ma an tanadar mana da jirgayen da zasu ɗauke mu, duk sojojin da za'a tafi dasu duk sun hallara sauran 1hour mu tafi, kuyi sauri Please..."

Angel tace "innalillahi da wuri haka? toh yanzu ma zan sameshi muyi sauri mu shirya kam..."
yace "Ok...". daganan suka katse ƙiran...

Angel da gudu ta fice a ɗakinta kai tsaye upstairs ta haura tana zuwa ta shige ɗakin Junaid ta sameshi akan sallaya yana waya, ji tayi yana cewa "Okay Sir gamu nan fitowa.."
katse wayar yayi ya miƙe tsaye yana kallon Angel yace "lafiya kuwa?.."
tace. "daman nazo sanar maka..."
bata ƙarasa maganar ba ya katseta da cewa "kije kiyi wanka don ni yanzu kayana kawai zan haɗa na rigada nayi wanka nah..."
Juyawa tayi da gudu ta koma ɗakinta kai tsaye toilet ta shiga domin watsa ruwa...

Bayan awa ɗaya Mommy ta kammala haɗa kayan breakfast akan dinning table, tana zaune a falon tana jiran fitowar su suzo suyi kumallo...
tana zaune sai gani tayi Junaid ya sauƙo down yana jan akwatin kayansa yana sanye da kayan soja,

(wayyo Allah ni tinda nake ban taɓa ganin Junaid a cikin kayan sojoji ba sai yau, kunga yanda yayi matuƙar kyau kuwa...)

Mommy miƙewa tayi tsaye tana faɗin "lafiya kuwa naga ka fito da akwati Ina zakaje?..."
Murmushi yayi sannan yace "Mom anyi mana ƙiran bazata yau ne tashin jirgin mu, kuma yanzu haka ma jiran mu akeyi jirgi zai tashi..."

zuciyar Mommy ce ta fara bugawa da ƙarfin gaske tace "yau ne tafiyarku?..." lokaci guda kuwa ta fashe da kuka,
Junaid ne yazo gaban Mommy ya rungumeta yana rarrashinta tareda cewa "kar ki damu Mom insha Allahu zamu dawo lafiya, kedai ki taya mu da addu'a duk da nasan dole wasu daga cikin mu zasu rasa rayukansu..."
Mommy tana cikin kuka saiga Angel itama ta fito da akwatinta tana sanye da kayan sojoji na ƙasar California bana nan Nigeria ba,
Itama zuwa gurin Mommy tayi tana rarrashinta,
Mommy tace "toh amma zaku tsaya kuci abinci ai koh?..."
Junaid yace "indai haka shi zaisa kiyi farin ciki toh zamu ci duk da mun makara..."
Mommy tace "toh kuzo na baku abinci da hannuna kafin ku tafi..."
wajen dinnig suka nufa haka mommy take ta feeding ɗinsu da hannunta take ɗiban abinci tana basu a baki, idan ta bawa Junaid saita juya tana bawa Angel da haka har suka ƙoshi...
miƙewa sukayi kowa ya ɗauki akwatinsa suka nufi waje, mommy tana biye dasu tana ta musu addu'a da fatan cin nasara,
Bayan sun isa wajen da motocin gidan suke haka Junaid ya buɗe bayan mota ya ajiye musu akwatinansu sannan ya rufe,
ya juyo yana kallon Mommy yace "Mom zan aiko yarona ya kawo motar..."
Mommy tace "a'ah My son ni zan rakaku har wajen jirgin da motar..."
Junaid yace "toh mom ai headquarter zamuje daga nan acan zamu shiga jirgin.."
Mommy tace "hauka nake bazan ga tafiyarku ba? zan kaiku har headquarters ɗin..."
yace "toh Mom zomu tafi.."

Mommy tace "Amma kunyi sallama da Ayush kuwa?..."
bata rufe bakinta ba saiga Ayush ta fito tana ɗingishi haka ta ƙaraso wajen nasun...

Angel kallo ɗaya tayiwa Ayush tasan akwai matsala, dole akwai abunda ya faru a tsakanin Ayush da Junaid a daren jiya" haka Angel take wannan tunanin a ranta...

Mommy tace "lafiya kuwa Ayush yanaga kina ɗingishi?..."

zuciyar Junaid ne ya fara bugawa da ƙarfin gaske gaba ɗaya ya fita hayyacinsa tsabar tsananin tsoro, haka yake bin Ayush da kallo..."
Angel kallonsu take tana murmushi idan ta kalli Ayush saita juya ta kalli Junaid, cikin ƙanƙanin lokaci har ta karanci abunda yake cikin zuciyoyinsu...

Murmushi Ayush tayi tana kallon Mommy tace "wallahi Mom Ina sauri zan sauƙo daga stairs kawai na zamo na faɗo akan gwiwata, shiyasa ƙafar ta riƙe mun..."
Mommy tace "Ayya ki rinƙa tafiya a hankali mana, gashi kinji ciwo..."
sunkuyar da kai Ayush tayi hawaye yana shirin ƙwato mata tayi saurin goge ƙwallar ta ɗago tana murmushi,
Angel bata san lokacin da dariya ya kuɓuto mata ba jin rainin wayo irin na Ayush, taɓe baki tayi tana kallonta cike da mamaki...

Ayush kuwa gaban Junaid taje ta tsaya suna fuskantar juna, ba Annuri a fuskarta haka ta ɗago da wani jan ƙyalle ta naɗa shi ta ɗaura akan goshin Junaid, sai ƙyallen ya ƙara haskashi kyanshi ya ƙara fitowa,
Bakinta takai saitin fuskarsa ta sumbace shi a hankali ta furta cewa "inaso ka sani bazan taɓa sonka ba, i hate you! ka kula mun da kanka, Allah ya dawo daku lafiya kuma ka kula mun da wannan jan ƙyallen domin shine amanata, idan har ka ɓatar mun dashi to nasan babu amanar soyayya a tsakanin mu..."

Mommy da Angel tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah,
Ayush nufan gurin da Angel take tayi tana zuwa ta rungumeta tana faɗin "zanyi missing ɗinki Aunty Maryam, Allah ya dawo mana daku gida lafiya musha biki..."

Ayush tana kaiwa nan ta juya tana ƙoƙarin matse hawayen daya zubo mata,
Mommy tace "Ayush kizo mu rakasu mana.."
Ayush tace "a'ah bana jin daɗin jikina.."
haka ta shige falo tana ɗingishin...

Su Mommy kuwa mota suka shige, Junaid shine mai driving har suka bar harabar gidan still da wannan jan ƙyalle a goshinsa wanda Ayush ta ɗaura masa....

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 29 ➡️ 30



Da gudu ta nufi toilet tana kwarara amai acikin sink, ƙarar aman da takeyi ne yajawo hankalin Ammy zuwa ɗakin da take, kai tsaye toilet Ammy ta shige ta tarar da Maimoon a sunkuye sai faman shiɗewa takeyi,
Bayan ta kammala ne ta wanke bakinta sannan ta ɗago zata fice taga Ammy tana tsaye a bakin ƙofar toilet,
Ammy kallon Maimoon take sosai cike da mamaki tace "Maimoon wai meyake faruwa dake ne kam? duk abunda kika ci saikin amar idan bakida lafiya ai saiki sanar koh..."

Maimoon kanta a sunkuye tace "Ammy babu komai dai just tsutsar ciki ke damuna shiyasa duk abunda naci saina amar dashi..."

Ammy tace "toh kizo na kaiki hospital, inyaso sai likita ya ɗauraki akan magani,

Maimoon tace "a'ah Ammy ki barshi ba wani abu bane, tashin zuciya ne da zarar naci goro shikenam zai daina mun..."
Ammy tace "toh shikenam Maimoon gaba ɗaya naga kin canza ne bakya son shiga cikin mutane why? kinbi kin rarrame kin tuttuje daga kuka sai kuka idan akwai wani abu ki sanar mun mana.."

Girgiza kai Maimoon tayi tareda faɗin "don't worry your self my Ammy, komai lfy lau just yanayin ne yazo mun da haka, amma nasan abunda nake yi.."

Ammy tace "toh shikenam Allah yasa.." daga nan tayi ficewar ta.
Ita kuma Maimoon kwanciya tayi akan saman gadonta tana ta fatan sharar kuka...

Ita abunda yake bata tsoro shine yau wata biyu da dawowarta gida amma bataga period ɗinta ba,
kuma tin a gidan su Laylah ma ta daina ganin period ɗinta tsawon wata biyu agidan su Laylah, abun yana damunta saidai bata san ko meye matsalar ba..




******

Ayush bayan ta shiga ɗakinta kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login