Showing 165001 words to 168000 words out of 186041 words
kaine? Daman kana ƙasar?..."
yace "wallahi kuwa ina Nam tsawon shekaru bamu sake haɗuwa ba"
Zama tayi suka fara tattaunawa akan yanda rayuwa ta juya dasu, Doctor Hasheem ya kwashe labarin abunda ya faru dashi har zamansa a prison ya sanar mata, tayi matuƙar tausaya masa sosai, itama ta bashi labarin tafiyarta bayan tabar gidansa ta koma daji da zama har tayi zaman prison itama,
Zaro ido Doct Hasheem yayi yace "kema kinyi zaman prison ne?...". tace "ehh amma zaman wata uku nayi kai kuma gashi har tsawon shekara huɗu...".
Lailah tace "Aunty Ayusher..." Ayush ta kalli Lailah tace "Lailah ashe abunda ya faru dake kenam?..." ta amsa mata tace "toh Allah ya tsare gaba..." Duk suka amsa da Ameen...
Doctor Hasheem yace "amma Ayush meya kawo ku hospital..."
tace "wallahi satin mu guda a asibitin nan, na kawo Areeph bashida lafiya...". yace "Allah Sarki kinga kuma ina zuwa nima amma ban lura daku ba, nadai ga Ogah Junaid jiya shida Malam Lawan amma iya gaisuwa mukayi ban tambayesu abunda ya kawo su ba saboda naga suma sunada iko da asibitin ....". ya kuma cewa "toh amma meya same shi ne?..."
Tace "Babansa ne yayi masa dukan mutuwa don har saida ya suma..." ta buɗe ma Areeph riga duk ta nunnuna musu yanda ya faffasa masa jiki...
Girgiza kai Doctor Hasheem yayi sannan yace "innalillahi wa inna ilaihi raju'un irin wannan dukan ai yayi tsari a yaro ƙarami irin wannan, gaskiya Ogah Junaid bazai taɓa canzawa ba, har yanzu yana nan da wannan zafin ran nashin..."
Lailah wani irin ƙololuwar baƙin cikine ya ziyarci cikin zuciyarta ganin yanda Ogah Junaid yayi wa yaronsa, ko kaɗan bataso taga ana dukan yaro, sam ba ƙaramin haushin shi taji ba...
Kowa a wajen saida ya tofa albarkacin bakinsa....
Rapeekh yaron Doctor Hasheem yace "shiyasa bana ganinsa a makaranta yanzu, kuma a ajinmu an bamu result ɗin jarabawar mu na canjin aji, Ni nayo na ɗaya..."
Ayush tace "kai kayo na ɗaya? shima Areeph an karɓo result ɗinsa shima na ɗayan yayo kuma abin ku ɗaya?..."
Doctor Hasheem yace "ehh ajinsu ɗaya mana akwai wani malamin su yana gaya mun cewa dole sai an sake musu jarabawa a iya tsakaninsu domin kowannen su yanada ƙoƙari sosai sai anyi musu inter biyu..."
Areeph ya kalli Ayush yace "mommy aini bazan taɓa faɗuwa a exam ba..."
Shima Rapeekh yace "nima bazan taɓa faɗuwa ba..."
A haka sukayi wasa da dariyarsu suka fice a ɗakin,
A ranar aka sallami su Ayush suka koma gida,
Masha Allah Areeph duk ya rage abubuwanda yake yi a baya, kuma tsoron Daddynsa ya ziyarci cikin zuciyar shi, duk abunda aka ce masa yayi da hanzarinsa zaiyi, Amma saidai har yanzu akwai wannan zuciyar da kuma idan aka masa magana baya saurin bada amsa wannan ajininsa yake amma akwai ladabi da biyayya yanzu kam....
Ana falo kowa yana zazzaune an kafa eyes akan plasman ana kallo, Ogah Junaid yana zaune Angel da Amrish kuma suna gefe da gefensa, Ita kuma Ayush tana ƙasin carpet sai sheƙar ruwan tea take fuska ba Annuri, daman hakane indai tana wajen da Junaid yake toh bata dariya, shima Areeph yana gefen mommynsa a zaune, Junaid banda satar kallon Ayush ba abunda yake, gaba ɗaya a takure yake ganin fushinta yaƙi ƙarewa, kuma tin daga lokacin daya fara dukan Areeph ta ƙaurace masa, yanzu kowa a ɗakinsa yake kwana, yana so yayi mata magana amma saidai ya kasa sai kuma take masa ƙwarjini ga yanzu ta ƙara girma sosai, komai nata a cike pamm, ganin bazai iya yi mata magana kuma yanaso ya rarrasheta ta bashi haɗin kai waren ƙwanciya ya kalli Areeph dake gefensa yace "Daddyna zo mana..". Areeph tashi yayi yaje gabansa yace "gani...". ya shafa gefen fuskarsa yace "Daddy kana fushi dani ne?.." girgiza kai Areeph yayi alamar a'ah, Ogah yace "toh kayi haƙuri kaji koh! Insha Allahu bazan ƙara dukan ka ba amma kar ka ƙara yin laifi kaji koh?...". Areeph yace "Daddy bazan ƙara ba". Yace "kace a mommynka itama tayi haƙuri ta yafe mun..." Areeph yaje gaban Ayush yace "mommy kiyi haƙuri ki yafewa Daddy yace bazai ƙara dukana ba...". Shuru Ayush bata bashi amsa ba, sai shan shayinta take, bata ankara ba taji an karɓi cup ɗin hannunta, dasauri ta waiwaya tana kallon Ogah Junaid, shi kuwa ajiye cup ɗin yayi akan table ɗin falon sannan ya sauƙo ƙasin carpet shima suka jeru tareda riƙe haɓarta yace "my sweetheart har yanzu fushi kike dani? ko yanzu kin wahalar dani please my..."
Ayush kawar da kanta tayi gefe, ya kuma cewa Mommy ta aikoni gurinki akwai saƙonda zan gaya miki..."
daƙer take motsi da lips ɗinta tace "meyasa tinda kazo baka gaya mun ba.."
Yace "Noo na manta ne amma yanzu tashi muje bedroom saina gaya miki koh.."
tace "meyasa baza'a gaya mun anan ba" yace "bakiga da yara bane". turo baki tayi tareda miƙewa tsaye ta nufi upstairs, shima bin bayanta yayi dasauri,
Su kuwa yaran basu kawo komai aransu ba sai suka cigaba da kallonsu, bayan shigar su bedroom rufe ɗakin yayi tareda murɗa key, cike da mamaki tace "yada rufe ɗaki kuma ...". takowa yayi yazo gabanta yana ɗan rera waƙarsa ta soyayya yasa hannu ya jawota jikinsa yana shafeta, tace "wai meye hakane, Ni ka ƙyale Ni, hakan ne saƙo ko?...". yana lumshe ido yace "Ni mijinki ne bai kamata ki ƙaurace mun ba, don haka saƙon Baby zan ajiye miki anan..."
ya ƙarasa maganar yana shafa marar ta. Zaro ido tayi tace "meeee cab ɗin, ban shirya karɓan new Baby ba don haka kaban guri na wuce ...". Junaid ƙara rungumarta yayi yana kai mata kiss a ko ina na sassen jikinta...". Ita kuwa ƙoƙarin ture shi take tareda faɗin "kai da kayi shekara huɗu kana zaman kaɗaici shin mutuwa kayi ne?...". ta ƙarasa maganar daiden lokacin daya ƙwantar da ita akan gado, cikin dabara da ƙwarewa duk ya zamar mata da kayan jikinta shima ya cire nashi, ya jawo musu mayafi gaba ɗayansu.....
Sanadiyar wannan saƙon ne ya kawo musu sasanci da maslaha a tsakaninsu, komai ya wuce..
★★★
Washe gari za'ayi jarabawa a tsakanin Areeph da Rapeekh aciki za'a zaɓi gwarzo kenam wanda yayo na ɗaya da kuma na biyu acikinsu, kowa yazo school da niyar cinye exam acikin Babban hall na makarantar, kowa da wajen zamansa domin akwai rata sosai a tsakanin Areeph da Rapeekh, security ɗaya aka ajiye musu wanda zai rinƙa yawo akansu, only one hour kawai aka basu, tinda suka fara rubutu babu wanda ya ɗago da kansa,
Areeph burinsa shine yaga ya wuce Rapeekh a ilimi da komai, bayaso su rinƙa yin bracket...
Haka shima Rapeekh yafi son yazo na ɗaya a duk class ɗinsu in yaso Areeph yazo ana biyu, kowa yana kishi da kowa...
Hakan kuma ba ƙaramin burge malaman makarantar suke ba saboda kishi akan karatu abu ne mai kyau,
After 30 minute saiga Rapeekh ya tashi tareda miƙawa security takardarsa har ya gama nashi exam,
Ganin haka ba ƙaramin razanar da Areeph yayi ba, kawai tsayawa yayi yana kallon Rapeekh cike da mamakinsa har ya gama kuma duk questions iri ɗaya ne,
ƙirjin Areeph ne ya soma harbawa kamar zaiyi kuka shi har ya saddaƙar cewa ya faɗi a exam ɗin nan, duk da yasan amsoshin gaba ɗaya toh amma saurin fitar Rapeekh ne ya karyar masa da gwiwa, yana cikin tunani yaji security ya dafa kafaɗarsa yana cewa "too pass Areeph remain 15 minutes...."
Areeph miƙa masa takardar yayi yana shirin tashi security yace "ha'a ya baka ƙarisa ba?..." Hawaye ne suka fara gangarowa Areeph, security ya rarrashe shi tareda ƙarfafa masa gwiwa har ya ƙarisa exam ɗin shima ya fice jiki ba ƙwari, Areeph ba haka yaso ba, baiso ace Rapeekh ya riga shi zana exam ba....
tinda Areeph ya koma gida bai samu kwanciyar hankali ba, abinci ma kasa ci yayi gaba ɗaya Ayush ta shiga damuwa ganinsa tinda ya dawo yake ta kuka, kuma ya kasa gaya mata abunda ya same shi, haka akazo yin night lunch nan ma ya kasa cin komai sai a lokacin Daddynsa ya fahimci akwai matsala a game da yaron, ya jawo Areeph jikinsa yana tambayarsa abunda yake damunsa, nan Areeph ya fashe da kuka yana faɗin "Ni nasan Rapeekh ne zai cinye jarabawar..."
Junaid yace "meyasa? bakayi ƙoƙari bane? kodai ka manta wasu abubuwan ne?...". Areeph yace "ban manta komai ba duk na rubuta su, Rapeekh ɗin ya rigani gama exam ɗin..."
Dariya Junaid yayi sannan yace. "hakan ba shi yake nuna cewa baza kaci exam ba, ko mutum ya gama da wuri indai bai rubuta daidai ba toh bazai ci ba, don haka ka ƙwantar da hankalinka okay .."
Areeph ɗaga masa kai yayi sai yanzu hankalinsa ya kwanta,
Ayush tace "Ni wallahi har ka tayar mun da hankali, nayi tunanin wani abu ne...".
Junaid ya kalleta sannan yace "ehh ai dan ke baki shiga class bane shiyasa baki san muhimmancin karatun ba ...."
turo baki Ayush tayi tace "abun harda gori ne? Naji amma ai waɗanda sukayi bokon ma babu abunda zasu nuna mun tinda nasan kalmar baƙi da fari.."
taɓe baki Junaid yayi yana kallonta yace "toh ja da yellow fah?.."
turo baki tayi rai a ɓace ko kallonsa bata yi ba, ya kuma cewa "yarinyar nan babu yanda banyi dake ba akan ki shiga school amma kika ƙi ai da yanzu an nema miki aikin yi..."
ta juyo tana kallonsa tace "babu abunda ban iya ba..."
Yace "eh kin iya ƙwanciya kiyi bacci ba, girki ma ba wani iyawa kikayi sosai ba, ai duk zan sallami ƴan aikin nan domin a takure nake bana iya cin girkin su..."
Little Angel tace "Daddy daman mommy bata shiga school ba?..."
Amreesh tace "shiyasa ranar nace tayi mun Assignment ɗin Mathematics taƙi mun sai Aunty Hafzat ce tayi mun...."
Areeph yace "Ni daman nake yin Assignment ɗina da kaina, toh meyasa mommy bata je school ba? sai kace forest girl..."
Angel ta kuma cewa "wata ƙila forest school tayi..."
duk yaran suka kwashe da dariya harda shi kansa Junaid,
Ayush kuwa ta ƙulu har ta kusan fashewa tsabar kumburi,
Amreesh tace "daman fah forest habitat ce fah...". Areeph ya kalli Ayush yace. "La la la laaa daman mommy ke ƴar forest District ce?..." kuma du suka ƙara tintsirewa da dariya, dasauri Ayush ta ɗauki wayar wutar nepa ta nufo wajensu tana faɗin "ina dai Ni Abokiyar ku ce ko?..." duk su ukun suka rufu akan Ogah Junaid suka ihu tareda ambatar sunan "Daddy! Daddy!! Wayyo Daddy!!!..."
Junaid riƙo hannun Ayush yayi tareda jawota jikinsa yana faɗin "kiyi haƙuri mommy wasa suke miki dai ..". zamar da kanta tayi ta nufi upstairs tana gunaguni...
Da haka suka sha hirar su har kowa ya wuce ɗakinsa, yau kam Ogah da kansa ne ya gyarawa yara waran ƙwanciyarsu ya tottofa musu addu'a duk da suma sun iya haka suka shafa ya rufesu da mayafi sannan yasa key a ɗakin, shima Areeph haka akayi masa tukun Ogah ya wuce ɗakinsa da Ayush ɗinsa ....
Washe gari yau iyayen Judan daga ƙasar Jidda suka zo Nigeria neman Auren Hafzat, shi kuwa Judan ƙasar da yake aiki kuma ƙasar california ne, daga Abuja ne suka nufi garin Kano gurin iyayenta har da Junaid shima,
Masha Allah kuma an karɓesu hannu bibbiyu a lokaci ɗaya aka yanke ranar da za'ayi bikin,
Iyayenta abun ya basu mamaki daga zuwa neman Aure sai kuma a yanke ranar Aure? Amma dake sunga manya-manyan kuɗaɗe da hanzarinsu suka yanda, an yanke ranar sauran sati biyu ɗaurin Aure...
Ranar da za'ayi na Lailah da Doctor Mansur.....
A yau ne Ayush ta raka Areeph school ɗinsu domin karɓan result ɗinsa, tana ta addu'a Allah yasa kar Areeph ya faɗi a jarabawar,
Shima Rapeekh yazo karɓan tasa shida Abbansa, anan suka sake haɗuwa da Doctor Hasheem da Ayushert, amma wannan karan kam iya gaisuwa ne ya shiga tsakaninsu,
Kowa an bashi result ɗinsa a wannan karan ma Bracket suka sake yowa duk sun cinye...
Duk babu wanda yaji daɗin hakan a tsakanin Areeph da Rapeekh, amma saidai an sake basu wata dama kuma du na sake yin exam amma wannan karan exam zai kasance Verbal expression ne, wato magana ta Turanci har tsawon awa guda acikin bainar jama'ar malamai da kuma ɗaliban makantar da kuma iyayensu sauran nan da ƙwana uku za'ayi...
Duk wanda ya ƙafe toh ya faɗi, kowa an bashi takarda mai tsawon rubutu na English zasu je