Showing 99001 words to 102000 words out of 186041 words
yana faɗin "please Doctor Hasheem ka daina kukan nan kar ka hargutsa mata lissafi.."
Dr Hasheem ɗagowa yayi da rinanan idanuwansa yana riƙe da hannun Lailah yace "Doctor ba yanda za'ayi Lailah ta dawo hayyacinta?..."
Doctor Mansur ne ya dubi Dr Hasheem yace "kaima ai kana buƙatar dawowa hayyacinka, ka duba kaga yanda ka dawo Dr Hasheem? kamar ba kai ba, dubi fuskarka kamar dattijon biri, Ni tinda ka ajiye Lailah a asibiti tsawon ƙwanaki baka dawo ba na shiga ƙwanƙwanto sai daga baya aka cemun kana hannun sojoji ne..."
Doctor Hasheem ne ya fusata a tsawace yace "Please Doctor am asking you about my sister..."
Girgiza kai Doctor yayi sannan yace "kaga ka firgita ƙanwar takan ko.."
Lailah ƙanƙame rigar Doctor Mansur tayi tana kuka tareda surutai tana faɗin "ku temake ni!, ku temake ni!! ku temake ni!!!..."
Doctor Mansur ne yake faman rarrashinta yana cewa "kinga kinga Lailah kiyi shuru kiji wani zance..." ya kawo bakinsa saitin kunnenta yana mata busa haɗi da shuuuuuu...
lokaci guda tayi shuru tana sauraron Doctor,
Dr Mansur nuna Hasheem yayi yana faɗin "Lailah kin gane waye wannan?.." girgiza kai ta soma yi da sauri tana cewa "a'a! a'a!! a'a!!! ban sanshi ba, ni ban taɓa ganinsa ba, kar ku barshi ya tafi dani, banason ganin fuskarsa irin na gwaigwai..." ta ƙarasa maganar tana kifa kanta akan lap ɗin Dr Mansur,
ɗagota Dr yayi yace "okay kiyi haƙuri zan koreshi yanzu, ɗago kika shin kinsan wancan?.."
ya nuna Oga Junaid wanda ya tsaya yaci bomm hannayensa a goye kan ƙirjinsa idonsa a kanta,
Lailah ɗagowa tayi takai idonta kan Junaid, da sauri ta kanne idanuwanta da ƙarfi tana ihu tana faɗin "ku fita mun da wancan dodo, banason ganinsa, Lailah batason ganinsu gaba ɗaya, Lailah zatayi kuka idan ba'a fitar mun dasu baaa, wayyo Allah nahh dodonni...."
Dr Mansur ne ya ƙwantar da ita yana rarrashinta ya taso yana ce musu "dan Allah kuyi haƙuri Oga Junaid mu fita mu bata wuri ko zata samu nutsuwa..." haka Dr yasa hannu ya ɗago Dr Hasheem suka yi waje yana kuka yana ƙiran sunan Lailah..
Lailah bayan sun fita shuru tayi da yin kukan tana ƙwance tana fuskantar ceilling idonta a ƙafe ko ƙiftasu bata yi, duk fuska ya kokkoɗe ido sun tuttuje babu alaman ƙwalli, ga sumar kanta a baje duk ta fiffige shi, a halin yanzu Lailah bata san kowa ba sai Dr Mansur shima don koda yaushe yana tareda ita ne shiyasa, tana yawan ganinsa amma bayan shi ko wasu likitocin ne suka yo kanta ta rinƙa yi musu ihu kenam har sai sun fita mata a ɗaki...
Haka Dr Mansur yaja su Junaid zuwa office ɗinsa a lokacin ya basu kujeru suka zazzauna shima ya zauna yana fuskantarsu daga baya ya soma yin magana yana cewa "a gaskiya bazan ɓoye muku ba Lailah tana buƙatar temako, ta shiga wani irin halin da itama kanta bata san tana ciki ba, kuma wannan halin da take ciki ba haka kawai ta shige shi ba dole akwai abunda ya faru da ita, kodai an buga mata wani ƙarfe akanta ko kuma an gwara mata kai a jikin wani abu..."
ya ƙarasa maganar yana kallon Dr Hasheem,
Jinjina kai Dr Hasheem yayi sannan yace "eh tabbas ta buga kanta a ƙasan floor ne.."
Dr Mansur yace "saidai idan bugata akayi, saboda idan buguwa tayi ita kaɗai ƙwaƙwalwarta bazai juye har haka ba,
a baya mun yanke shawarar kaita asibitin mahaukata ne a ɗorata akan sakatiri amma yanzu na canza shawarata baza'a kaita ba saboda tana buƙatar nutsuwa a yayin da take cikin kaɗaici wanda babu hayaniya a gurin, ta hanyar nan zamu samu nasarar magance matsalar ta, idan kuka fuskanta bata buƙatar hayaniya da takuri..."
Junaid ne ya ari bakin Dr yace "idan kuwa aka kaita asibitin mahaukata zata rasa sukunin ta ne..." Dr Mansur yace "tabbas hakane.."
Dr Hasheem kai a sunkuye yace "yanzu to Dr meka tsara akan wannan al'amarin?..."
Dr Mansur yace "Ni a yanda na tsara Lailah zata cigaba da zama a wannan asibitin, insha Allahu zan bata duk wani kulawar da take buƙata, zan san yanda zanyi na magance matsalar ta Insha Allahu..."
Dr Hasheem murmusawa yayi yana zubda ƙwallah yace "Nagode sosai Dr.." hannu yakai yana goge hawayen fuskarsa yana shirin miƙewa tsaye,
Dr Mansur yace "amma Dr Hasheem yakamata kaima ka tsaya a duba lafiyar jikinka ko? naga kaji raunuka sosai a jikinka..." Dr Hasheem komowa yayi ya zauna yana faɗin "Ok thanks"
Miƙewa Junaid yayi yana cewa "toh Ni zan wuce.."
Dr Mansur ne shima ya miƙe tsaye yana bashi hannu sukayi sallama, Junaid hannu yasa cikin pocket ɗinsa ya zaro damin kuɗi dollars dollars sun kai guda ɗari biyar ya miƙawa Dr Hasheem yana faɗin "ga wannan zaiyi maka amfani waran jinyar ƙanwarka..."
Dr Hasheem juyar da kai yake tsabar takaici kamar zai haɗiyi ransa, ba mutumin da yafi tsana a yanzu kamar Junaid, hannu yasa yana goge hawayen da yake zubo masa cikin ɓacin rai ya miƙe tsaye yana fuskantar Junaid yace "a'ah ka riƙe kuɗin ka bana buƙatarsu domin nima inada fiye da waɗannan..." ya kuma haɗe hannayensa biyu tareda durƙusawa ƙasi yana roƙan Junaid yace "dan Allah! dan darajar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ka fita daga cikin rayuwar mu, bama buƙatarka a cikin rayuwar mu, ni na rantse da rabbani waran da kake ma bazan biyo hanyar ba balle mu haɗu, duk abunda ya shafeka kuma na barshi har abada, asibitin mahaifiyarka yanda iyayena suka bar duniya haka nima na daina aiki acikin asibitin na, dan Allah Junaid ko a hanya ka gan mu kada ka nuna ka san mu ma dan Allah 🙏🙏..."
Junaid kawar da kansa gefe yayi yana murmushi shi abun ma dariya yaso bashi, hannu yasa ya ɗago Dr Hasheem tsaye yana faɗin "okay don't worry dat is your concern, I'll do my own business..." yana buga kafaɗarsa a hankali ya kuma cewa "quick recovery..."
yana kaiwa nan ya juya yayi ficewarsa,
"kai ɗin Dr Hasheem meya haɗa ka da Junaid kuma, naga ku ɗin abokai ne kuma ma naji kana cewa kabar aiki a asibitin su shin kasan a yanda zaka samu aiki yanzu kuwa?...."
a cewar Dr Mansur wanda idonsa ke kan Dr Hasheem..
Ajiyar zuciya Dr Hasheem ya sake tareda faɗin "Allah ya wadaran irin wannan Abokantaka, abokin da bazai iya rufa maka asiri ba ai ba aboki bane, abokin da burinsa yaga ya ƙuntata maka ai ba aboki bane, abokin gaskiya bazai so a taɓa tsokar jikin ɗan uwansa ba da sunan duka amma yau gashi Junaid abunda yasa aka aikata mun, yanzu yabar aboki ya koma babban maƙiyi na..." ya ƙarasa maganar yana huci..
Dr Mansur girgiza kai kawai yayi yace "Allah dai ya sawwaƙe..." ya furta hakan tareda miƙa masa takardar maganunnuwan da zai siyo..
karɓa Dr Hasheem yayi tareda zabura da sauri ya miƙe yana tafiya daƙer yana jan ƙafa kamar wani gurgu da haka ya fice...
Dr Mansur kallonsa yake har ya fice kawar da kai yayi yana murmushi,
(kuna ji ana cewa Dr Mansur toh ba tsoho bane, haɗaɗɗen saurayi ne fari kyakkyawa mai yawan murmushi, wanda kuɗaɗe suka ratsa shi, mahaifinsa asalin maloniya ne ya sanu a ko ina, wannan asibitin kuma mallakin Dr Mansur ne wanda dawowarsa daga ƙasar Egypt ya kammala karatun master's ɗinsa a bangaren likitanci hakan yasa ya buɗe babban hospital ɗinsa wato *IHSANN GENERAL HOSPITAL ABACHA ROAD ABUJA*..)
*****
________ Bayan fitar Junaid daga hospital cikin gari ya nufa yana yawon nuna photon Ayush ko akwai wanda yasan a yanda take,
amma har yanzu shuru babu amon labarinta, miƙar hanyar express road yayi wanda yake tsakanin Abuja to Kaduna tafiya yake a hankali da motarsa yana kallace-kallace ko zaiga Ayush, har ya soma barin cikin garin, kana ganinsa kasan akwai damuwa ƙarara a saman fuskarsa yana tafe yana maganar zuci "Allah Ubangiji ka haɗani da wannan baiwar takan, aina zan ganki Yushert?..."
tafiya yayi mai nisan gaske har yabar cikin garin Abuja sosai, parker motarsa yayi a gefe guda sannan ya fito ya tsaya a jikin motarsa yana kallece-kallece, acikin daji yake tsugugu domin ba alamar motsin mutane, ba kuma gida ko ɗaya sai kukan tsuntsaye ga kuma wani irin zugugun sanyi da akeyi, lokaci guda Junaid ya ƙanƙame jikinsa da hannayensa tsabar sanyin da yake ratsa shi, ba shiri ya shiga cikin motarsa ya ɗauko rigar sanyi da face mark ya sanya su tareda ɗaukar torch light ya saka a aljihunsa sannan ya shiga cikin dajin, tafiya yake ba ƙaƙƙautawa har saida duhu ya soma shiga, ya haɗu da macizai sunfi a ƙirga amma saidai ya wuce su yana ƙwalla ƙiran sunan Yushert, tazararsa da bakin ƙwalta tafiya ne mai nisan gaske a yayin da duhu ya biyo baya, domin ko gabansa baya iya gani kunna hasken torchinsa yayi ya cigaba da tafiya yana haske-haske duk yabi ya gaji, jikinsa har ciwo yake, ganin bazai iya cigaba da tafiyar ba ya tsaya a guri ɗaya ya haɗe hannayensa biyu a saitin bakinsa ya soma ƙwallah ƙiran Ayush a cikin dajin nan,
"Yushertttt! Yushertttt!! Yushertttt!!!..."
yana cikin ihun ƙiranta ne yaji ta bayansa ance "Yaya Junaid..."
da sauri Junaid ya waiwaya da murmushi a fuskarsa yana haska wacce ta ƙira sunansa, ganin Ayush yayi a tsaye tana sanye da doguwar riga kayinta ba mayafi, itama tana tsaye sai faman murmushi take, da saurinsa ya nufi gurin da take yana faɗin "my Yushert Ina kika shiga ne inata nemanki, kin wahalar dani sosai..." yakai hannu zai rungumeta gani yayi ta ɓace ɓattttt!
a firgice yayi baya ya faɗi ƙasi a zaune sai faman zazzaro ido yake jikinsa na kakkarwa, a ruɗe yake lalumar yanda torchinsa yake a yashe, cikin sa'a ya sameta yana ƙoƙarin tashi tsaye saiji yayi dajin ya soma ɗaukar dirin dariya, dariya akeyi ta ko ina, cikin ƙatuwar murya da kuma siririyar murya nan take muryoyi da yawa aka fara ƙiran sunan "Yushertttt! Yushertttt!! Yushertttt!!! Yushertttt!!!!" ana kokkoyan sunan da Junaid yake ƙira!
Junaid gaba ɗaya ya ruɗe wani irin haɗiyar yawu yayi duk ya haɗa gumi still muryar mutane yake ji ta saman bishiyoyin jejin,
Miƙewa yayi a razane ya soma cin uban gudu ko waiwaye baya yi, gudu yake sosai har saida ya daina jin dariyar mutanen daiden lokacin yayi tuntuɓe ya faɗi ƙasi, ɗagowar da zaiyi ƙwatsam sai yaga wata mata sai birgima take a ƙasi tanata ihu da tsohon cikinta, haskata yayi a ruɗe yace "Yushert?..."
ita kuwa Ayush kuka take tana ƙiran sunan Junaid "dan Allah Yaya Junaid ka temake ni, wayyo cikina ciwo zan mutu wayyo Allah nahhhh..."
da rarrafe yazo ya ƙaraso gurinta yana faɗin "Yushert! Yushert ki ƙwantar da hankalinki gani nazo gareki kinji koh, ki daina kuka..."
Ita kuwa cewa take "wayyo Yaya Junaid haihuwa zanyi ka danna mun cikina, raɗaɗin nake ji haihuwa zanyi, bazan iya motsawa baaa..."
Junaid hannu ya ɗora akan cikinta yana matsawa a hankali ga torch kuma a gefe yanda ya ajiye shi, yana cewa "zaki haihu yanzu ki kwantar da hankalinki, da ɗan mu zamu koma gida cikin ƙwanciyar hankali..."
Ayush tana nishi a hankali tace "yauwa Yaya Junaid yaro na ɗaya ya fito, cigaba da matsa mun cikin wayyo yaro na biyu ya fito, ahhhh yaro na uku ya fito, i love You Yaya Junaid ashhh yaro na huɗu ya fito, yauwa! yauwa!! cigaba ahhh yaro na biyar ya fitoo..."
Junaid zaro ido yayi waje ganin jarirai har guda biyar yace "Yushert har yara nawa zaki haifo mana ne?..."
Ayush tana murmusawa a hankali tace "yara Ashirin ma sun isa..." a wahalce Junaid ya aɗiyi yawu yace "Yushert yara Ashirin sunyi yawa ai...." kafin ya ƙarasa maganar yaji tace "yauwaaa yara biyar sun fito a jere, mammatsa mun cikin sosai yauwa yara biyu sun fito suma a jere, ahhssh ahhhh wayyo sauran kaɗan sauran yara takwas su fito..."
Junaid gaba ɗaya baya cikin hayyacinsa kawai matsa mata ciki yake lokaci guda kuwa tayi wani irin yunƙuri saiga sauran jarirai takwas sun wantsilo, ajiyar zuciya tayi sannan tace yauwa Masha Allah sun gama fito wa, yanzu zamu iya tafiya gida ko?.."
Junaid a tsorace yake ja da baya ganin yanda jariran nan suke miƙewa tsaye ƴan ƙananu dasu sai manya-manyan kayuwa, kayin jariri ɗaya yayi biyar