Showing 129001 words to 132000 words out of 186041 words
burge shi,
Ogah Junaid tsayawa yayi tareda goya hannayensa ta ƙirjinsa idonsa akan Judan,
Hafzat cikin tsoro tace "ga nan Uncle.."
waiwayawa yayi suka yi ido huɗu Judan yace "your welcome Ogah.." ya ƙarasa maganar yana sosa ƙeyarsa tareda miƙewa tsaye daga zaman da yake a hannun kujerar da Hafzat take, ya koma cikin kujerar gefe da ita,
shima Junaid zuwa yayi ya zauna yana faɗin "sannunka Judan, wato kazo ka samu yarinya shine zaka shishshige mata koh?..."
Hafzat dasauri ta tashi tabar falon ta koma cikin ɗakinta wanda yake gefe dana Mommy....
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 66 to 70
Bayan isar su prison suka tarar da Doctor Hasheem acikin wani irin hali gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, duk ya rarrame yayi baƙi ƙirin, a zaune suka tarar dashi guri guda wajen da babu jama'a sai iya shi kaɗai, Allah ne kaɗai yasan abunda ke damunsa ya kifa kansa da gwiwa, ɗayane daga cikin security prisoner ya rakosu har waranda yake Mommy tana ganin yanda Hasheem ya koma da gudu ta ƙarasa wajensa tana ƙiransa
"Hasheem!!! Innalillahi wa inna ilaihi raju'un haka ka koma? dubeka kamar mahaukaci subhanallahi..."
Daƙer Hasheem ya ɗago yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya duk yunwa ya gama cinye shi domin baya samun damar cin abinci saboda tsananin damuwar da yake fama dashi,
Maimoon gaba ɗaya jikinta ne ya ɗau kakkarwa ganin halin da Hasheem yake ciki har hawaye sun soma zubo mata, tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasi sabida kar Daddy ya ganta ga jariri kuwa a hannunta...
cikin firgici da ruɗani Lailah tace "wannan ne Yayan nawan? ya naganshi kamar Almajiri marar gata anya kuwa shine Yayana? kaiii ina tantama nidai dan Allah a temaka a kaini gurin Yayanaaa..."
lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka, Ammy ce ta dafa kafaɗarta tana bubbuganta alamar rarrashin tace "Lailah kiyi haƙuri wannan shine Yayanki"
Lailah shuru tayi ta sake baki tana kallon Ammy cike da mamaki lips ɗinta har rawa yake kamar maijin sanyi tace "wai da gaske ne wannan shine Yayana?.."
Ɗaga mata kai Ammy tayi...
shi kuwa Daddy juyawa ya yi yayi tafiyarsa, zuwa yayi ya buɗe murfin motar ya zauna domin bazai juri ganin Hasheem a cikin wannan halin ba kuma bazai fitar dashi daga prison yanzu ba..
Lailah zuwa tayi gaban Hasheem jiki na ɓari gudun kar taje mahaukaci ne domin yanayinsa ba maraba da mahaukacin,
Ga ya tara wani mahaukacin suma akansa zuwa gemunsa ga yayi baƙi ƙirin ga kuma kayan jikinsa yayi duƙwi-duƙwi tsabar datti don ko wanka baya samun halin yi bare wanki,
durƙusawa tayi a gabansa tana sharar hawaye tace "Yaya..."
shima kallonta yake cikin tausayawa ya kamo hannunta duk biyun yana zubda ƙwallah yace "Ƙanwata Lailah naji daɗi ganinki, kin samu lafiya sosai Alhamdulillah.."
itama tana kuka tareda faɗin "Yaya haka ka koma? a photo kafi haka kyau sosai, meyasa aka kawo ka nan Yaya?..."
Girgiza kai Hasheem yayi sannan yace "kiyi haƙuri Auta zan cigaba da zama anan, kedai ki rinƙa mun Addu'a kinji ko?..."
kuka ne ya kuɓuto mata da gudu ta tashi tayi waje tana kuka..
shima sunkuyar da kansa yayi ƙasi yana kuka mai cin rai, mommy ce ta dafa shi tareda cewa "kayi haƙuri Hasheem komai yayi farko zaiyi ƙarshe, mahaƙurci mawadaci insha Allahu zaka fito daga cikin kurkukun nan, zamanka anan bai dace ba..."
Ɗagowa yayi yana kallon mommy da jajayen idanuwansa wanda yasha kuka yace "a'ah mommy ku barni kawai na ƙarasa rayuwata anan, nan shine daidai dani, na tafka babban kuskure arayuwata, abunda ban taɓa aikatawa ba yau gashi an wayi gari nayi abun kuma hakan yayi sanadiyar shugowata gidan Ajali nah, ina fatan daga nan sai ɗakina na gaskiya wato kabarina, nan shine daidai da rayuwata, idan na fita daga nan da wani ido zan dubi waɗanda suke ganina da mutunci? shin mezance musu? na rigada na zubar da kimata da kuma mutuncin ahalin mu, wallahi tallahi Ni ba mutumin banza bane, ƙaddara ce tasa na aikata hakan, kunya bazai barni na fita daga cikin prison ɗin nan ba, dan Allah ku barni na mutu a cikinsa....."
yana kaiwa nan ya sake fashewa da wani irin matsanancin kuka..
Itama mommy kukan take domin ba ƙaramin tausayi ya bata ba, girgiza kai Ammy tayi tace "Allah Sarki abun tausayi, wallahi ko kaɗan banso anzo wannan gacin ba, naso ace an warware matsalar nan a cikin gida ba tareda kowa ya sani ba, amma Alhaji ya kama ya shigar da ƙara, gashi nan ai yanzu magana ta bazu ko ina, yanzu Maimoon bata shiga cikin mutane itama ko gurin ƴan uwanta bata zuwa saboda ƙyararta da sukeyi wai tayi cikin shege abunnan yana damuna matuƙa wallahi...." itama Ammy fashewa tayi da kuka ta juya ta nufi hanyar fita tana kuka...
Mommy miƙewa tayi tsaye tareda riƙo hannunsa tace "tashi tsaye maza kayi haƙuri"
shima miƙewa yayi da temakon mommy domin a halin yanzu bashida wani sauran ƙarfi a jikinshi,
ta jawo shi sukazo har gaban Maimoon wacce take tsaye itama da yaronta sai faman kuka take kanta a gefe guda, Mommy ta karɓi Rapeekh a hannunta sannan ta miƙawa Hasheem tace "nasan tinda aka haifi yaron nan baka ganshi ba, toh yanzu ka karɓeshi ka sanya masa albarka tinda mahaifinsa yana raye, ga jininka kaima insha Allahu duniya bazatai muku dariya ba..."
Hasheem karɓan yaron yayi ya ƙura masa ido yana zubda hawaye daga baya kuma ya fara jero masa addu'o'i yana tottofa masa, daƙer ya buɗe bakinsa yace "meye sunansa?..." yayi maganar idonsa akan Maimoon wacce itama kallonsa take, a yayin da ita kuma Mommy tabar wajen ta basu guri,
kamar baza tayi magana ba a hankali tace "Rapeekh"
jinjina kai yayi sannan yace "shine asalin sunansa?..."
tace "sunan mahaifinka ya samu.."
a hankali Hasheem ya ambaci sunan yace "Abubakar..."
Idonsa akan yaron baisan lokacin daya sau murmushi ba lokaci guda yaron ya shiga zuciyarsa, ji yake kamar bazai bayar da yaron ba,
shima yaron dake akwai wayo sai kallon uban yake yana buɗe ƙaramin bakinsa alamar dariya,
Kallonta yayi yana murmushi yace "yayi wayo sosai yanzu watansa nawa?..."
tace "a ranar daka shugo prison a ranar aka haifeshi..." dasauri ya maida idonsa kan yaron yana mai tausaya masa yace "kenam yanzu watansa biyar?..."
ɗaga masa kai kawai tayi ba tareda tace masa komai ba,
doguwar ajiyar zuciya yaja ya juyo yana fuskantar Maimoon a hankali ya ambaci sunanta "Maimoon.."
ɗagowa tayi itama tana kallonsa saida suka ɗau tsawon minti guda suna kallon junansu cikin tausayawa juna daga bisani yace. "dan Allah na roƙe ki da sunayen Allah ki yafe mun abunda nayi miki, nasan banyi miki daidai ba kuma nasan kin tsane ni amma ki gafarce ni, ina tsammani mutuwa yau ko gobe banason na mutu da hakkinki akaina, yau idan kika ce kin yafe mun kin gama mun komai! daman kullum tunani shine aina zan ganki in nemi yafiyarki...."
kafin ya rufe baki ta katse shi da cewa
"Bani yarona..." buɗe baki yayi zai mata magana tayi saurin dakatar dashi ta hanyar tsawa tana faɗin "nace ka bani yarona ko kai ka haifa mun shi ne?..."
kamar zaiyi kuka yace "gashi nan toh amma kice kin yafe mun dan Allah ko zan ji daɗi a raina..."
hannu tasa ta karɓi yaron cikin fushi, a farko taji tausayinsa amma yanzu ya fama mata tabon dake cikin zuciyarta, idan ta tuno da abunda yayi mata ji take kamar ta fasa masa kai da bullet, ita murna ma taji da Babanta ya tura shi prisoner...
juyawa tayi zata tafi ba tareda tace masa komai ba yayi saurin riƙo hannunta yana faɗin "dan Allah Maimoon ki temaka mun, idan kika tafi bansan ranar dazan ƙara ganinki ba, kuma ina buƙatar yafiyarki domin inaji a jikina mutuwa zanyi..."
A fusace ta juyo tana faɗin "toh sai mai idan ka mutu? shin mutuwarka zai dameni ne? ko yaronka mutuwarka bazai dameshi ba balle Ni, ka sake mun hannu na nikam idan kuma kana son maimaita mun fyaɗen toh Bismillah..."
Jikinsa na kakkarwa yace "Mai Mai Maimoonnn..."
"Shurt up bana buƙatar jin komai daga gareka wallahi tallahi I hate you" a tsawace tayi masa maganar dan dai babu kowa a wajen da babu abunda zai hana mutane taruwa a gurin,
ta cigaba da cewa "ka lalata mun rayuwata, ka watsar mun da mutunci na, nasan babu sona a cikin zuciyarka hasali ma tsanar da kake mun ne yasa ka aikata mun fyaɗe, kuma yarinyar da kake so ina maka albishir da cewa itama ka rasata domin yanzu haka tana gidan mijinta wato Junaid da tsohon cikinta, kamar yanda ka rasata haka nima ka rasani har Abada Abadan Abaadann! kuma ka rasa yaronka ma daga yau ne bazaka ƙara ganinsa ba saboda gobe ma insha Allahu zan bar ƙasar nan, bazan dawo ba kuma, idan kaga dama ka mutu acikin prison bai dameni ba, Mtsswww...."
tana kaiwa nan a fusace juyawar da zatayi taga Lailah tana tsaye ta bayanta sai faman zubda hawaye take ta kuma goya hannayenta biyu ta gaban ƙirjinta,
Maimoon tsayawa tayi tana kallonta domin bata san tin yaushe take tsaye a wajen ba, ganin babu abunda zata ce mata ne yasa ta ratsa ta gefenta tayi tafiyarta,
Lailah tana kuka ta ƙaraso gaban Hasheem tace "Yaya fyaɗe kayi mata? hakan yasa aka kawo ka prison? kenam yaron hannunta kaine Babansa? innalillahi wa inna ilaihi raju'un..."
Doctor Hasheem shima kukan yake yace "Lailah na aikata kuskure, ina neman yafiyar Maimoon..."
tace "Yaya ba abunda zan iya a wannan al'amarin, bazan iya tuna komai ba Yaya, ban san mai zance ba, duk tattaunawar da kuka yi akai duk naji su, amma bayan yanzu dana saurara bansan komai akai ba na manta wallahi, kayi haƙuri Yaya...."
tana kaiwa nan itama ta juya da gudu ta tafi tana kuka,
Durƙusawa yayi da gwiwowinsa ya ɗora hannayensa biyu a kayi yana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihi, Subhanaka inni kuntu mina zalimin, Allahumma ajurni fii musibati wa akhlif li khairan Minha....."
daga nan numfashinsa ya ɗage cakk ya faɗi ƙasi sumamme, tsabar damuwa da ƙuncin da yake ciki....
Ita kuwa Mommy tin fitar ta na farko bata tsaya sauraron kowa ba haka ta shige motarta taja tayi tafiyarta,
Itama Lailah turota akayi akan tazo ta ƙira Maimoon su tafi tazo ta tarar dasu suna wannan maganar har taji, suma bayan fitarsu jan motar Daddy yayi da gudu yabar prison kai tsaye gida suka nufa,
kowa a cikinsu ba wanda ya kula kowa, ita Maimoon ta rufe fuskarta da mayafin jikinta in banda kuka ba abunda take yi,
itama Lailah kukan take ciki²,
Sai Ammy da Daddy dake gaban motar.......
Bayan tafiyarsu Maimoon Doctor Hasheem yana ƙwance a ƙasi yakai kusan awa guda ba motsi ba kuma wanda ya ɓullo ta waran balle ayi masa temakon gaggawa, saida wani daga cikin prisoner yazo duba shi yaganshi shame-shame a kwance da gudu ya tafi ƙiran masu kula da su...
★★★★★★
Ata ɓangaren su Junaid kuma yana zaune da baƙonsa wato Soja Judan,
An aiko shi ne domin ya kawo saƙo daga ƙasar california shima ba sojan Nigeria bane daga can yake bayan rasuwar Angel ne aka bashi miƙamin Angel wato Commander California Army,
kafin ya isar da saƙonsa saida ya tambayi Junaid cewa "Ogah wannan yarinyar anan gidan take?..."
Junaid kallonsa kawai yake cike da mamaki yana zancen zuci cewar "abun zai ban mamaki gaskiya, shin yaushe Judan ya fara son mata? ni a sanina dashi bai cika kula mata ba ko kallonsu bayayi toh ya akayi daga haɗuwa da Hafzat har ya fara zaucewa haka...."
yana cikin tunani Judan ya katse shi da cewa "Ogah yadai kodai ka shiga tunani ne daban, wallahi Oga this girl she is a beautiful I like her.."
zaro ido Junaid yayi yana kallonsa ko ƙibtawa bayayi sai yanzu yayi ƙarfin halin cewa "Judan yaushe ka fara soyayya?..."
Murmushi yayi sannan yace "akan wannan yarinya na fara jin shauƙin soyayya, ina ido huɗu da ita naji wani irin sauyin duniya..."
kawar da kai Junaid yayi yana ƙunsar dariya domin ba ƙaramin dariya Judan ya bashi ba, ya kuma cewa "but Oga ina zaku bani ita?..."