Showing 21001 words to 24000 words out of 186041 words
Munafurr ganin Narasimha yaƙi kwanciya haka ya ɗaga takobinsa mai farfatsin wuta ya fille kan Narasimha dashi, cikin ƙanƙanin lokaci saiga kayin Narasimha a ƙasi ya faɗo,
amma duk da hakan gangan jikin Narasimha yana a tsaye yaƙi faɗuwa,
macizai kuwa duk sun harhaɗe masa ƙafafuwa da ko ina na jikinsa...
wani irin dariya Munafurr yake yi ya koma kan kujerar mulkin ya zauna tareda jingina bayansa a jikin kujerar ya ɗaura sahu ɗaya akan ɗaya yanata tintsirewa da wani irin mahaukacin dariya,
jin kururuwar dariyar yasa Bara'at fitowa falon cikin gaga'ar bacci take faɗin "wai meke faruwa ne?..."
saida ta fito tsakiyar falon tukun taci arba da Narasimha tsaye tsangamgam ba kayi sai wuya,
murtsike idonta tayi tana son tabbatar wa ko mafarki take, ganin gangan jikinsa ne a tsaye babu kayinsa ga kuma yanda macizai suke zarya a jikinsa,
idonta ta kai saitin kayinsa dake wurge a gefe, ido ta zaro waje da sauri takai idonta kan Munafurr dake zaune akan kujerar sarauta,
baki ta buɗe zatayi ihu, ya hura mata wani hayaƙi daga cikin bakinsa lokaci guda kuwa bakinta ya rufu sannan idanuwanta suka daina gani sai duhu kawai, ga ido a buɗe amma bata iya ganin komai, muryar ta kuma ya shaƙe babu halin magana ta zama kurmiya...
Damusa kuwa tin zuwan Munafurr ya nemi wani ɗan lungu ya ɓoye a gurin ko motsinsa ba'a ji, Damusan yana da hankali domin yasan indai suka haɗa ido da Munafurr to bazai barshi ba, shi kuma Munafurr a tunaninsa Damusa ya daɗe da mutuwa tin lokacin da ya wurga masa maciji a jiki...
Sarki Ramoud kuma sauƙa yayi a ɗakin Junaid yana ɓuɓɓuya saboda kar ya haɗu da Junaid, gani yayi babu kowa a cikin bedroom ɗinsa, yayi tunanin ko yana cikin toilet haka yake sanɗa zai wuce cikin ɗakin sirrinsa, hannu yasa ya tura ɗan ƙofar da zai shige, cikin sa'a kuwa ƙofar ta buɗu,
cikin muryar tsawa Sarki Ramud yaji ance "waye ne awaran nan?..."
Junaid ne a cikin ɗakin yana ta faman daddanna computersa tin daga lokacin da yaji zasu fita yaƙar sarki Ramud daga lokacin yake ta faman neman mafitar yanda zasuyi su je farmakar sa, ba bacci kullum acikin abu ɗaya yake,
Junaid ne ya taso a fusace ya fito cikin bedroom ɗinsa ganin babu kowa yasa yayi tsuka tareda faɗin "sarki zalimu! sarki Raamud wannan karan ba kuliya zaka turo mun ba, ba aljanu zaka turo mun ba ko kai da kanka zaka zo mun awannan lokacin kwananka ya kusan ƙarewa, domin ina daf da kawo maka farmaki"....
yakai idonsa kan agogon bangon ɗakin yaga ƙarfe 2 nadare, kansa gaɗi ya nufi hanyar fita ya buɗe ɗakinsa ya fice,
shi kuwa Sarki Ramud daman ɓoyewa yayi ata gefen wardrobe yana jin duk abunda Junaid yake faɗi, girgiza kai kawai yayi ya shige cikin ɗakin nan,
zoben hannunsa ne yake nuna masa yanda takobin yake ta hanyar bada haske, har yazo zai wuce yaga photon masarautarsa a cikin computer Junaid, tsayawa yayi yana kallon girman fadarsa a cikin computer jin motsin mutum yana shirin shugowa, ƙirjinsa yayi wani irin bugawa ga hasken da zobensa yake badawa alamun suna daf da gurin takobin kenam...
Junaid ne ya shugo hannunsa riƙe da ruwan Faro,
shi kuwa sarki RAMUD har ya ɗauki takobin ya murza zoben ya yi ɓacewarsa,
saiga Sarki Ramud acikin babban falon masarauta, ganin a yanda Narasimha yake yasa ya rikice yana faɗin "Narasimhaaa! NArasimhaa!! Narasimhaaa!!! ya nufi gurin da yake da gudun gaske bai san lokacin da yayi wurgi da takobin hannunsa bama,
takobin tsalle yayi ya faɗa cikin wani lungu sai a gaban Damusan da yake ɓoye a gurin, ko shi Munafurr bai lura da yanda takobin ta faɗa ba..
Sarki Ramud yana shirin rungumar Narasimha kawai yaci karo da macizai suna ta zarya a gangan jikinsa, kafin kace mai macijen nan sun faɗar da gangan jikin Narasimha ƙasi ga yanda sukayi fata-fata da jikinsa duk sun fiffige gashin jikinsa,
zuciyar sarki Ramud ne ya hauro cikin ɓacin rai ya kurma ihu tareda nufan yanda Munafurr yake a zaune zai kai masa duka,
Munafur riƙo ƙafar sarki Ramud yayi ya ɗago shi sama da hannu ɗaya yasa hannu biyu ya ɓalla ƙafar sarki Ramoud gida biyu kamar wanda ya ɓalla ice ya wurgar dashi gefe guda gurin da Bara'at take a zaune ba gani ba ji ba magana haka take zaune bata san a wani hali ake ciki ba,
sarki Ramud ƙafarsa ya riƙe yana ta kururuwar ihu ga ƙafa yanata lanjal-lanjal kamar zai tsinke tsabar an raba ƙashin ƙafar gida biyu......
Munafurr tashi yayi ya d'auko wani qaton kwalba Mai marfi ya d'auki kan Narasimha ya Saka aciki sannan ya rufe kwalbar,
'kiran wata 'katotuwar mujiya yayi tazo ya d'aura mata gangan jikin Narasimha ya bata umarnin taje ta jefashi cikin kogin ruwan da ba'a ganin 'karshenta....
ya nemi guri ya cigaba da zamansa akan kujerar masarautar ya d'auki hular sarautar Sarki Raamud ya sanya a kansa...
*TAB AKWAI YAƘI FAH, DOMIN YAƘIN SOJOJIN NAN ZAI IYA KOMAWA KAN MUNAFURR...*
*AUNTY ADITI GWARA FA KIYI KUKAN DA GASKE DOMIN INA TUNANIN SOJOJIN NAN HMMMMM, KUDAI FARA KUKA TIN DAGA YANZU AHAMMMM NIDAI BAKINA DA GOROO..*
*TOH READERS SHIN WANNAN PAGE ƊIN NAKU NE KO NAWA?...*
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 13 ➡️ 14
Ɓangaren su Junaid...
washe garin ranar sunday da safe Ayush tana kwance asaman gadonta, sai faman juye-juye take kwata-kwata a daren jiya ko rintsawa batayi ba, tana ta tunanin yanda akayi ta kusanci wani ba tareda sanin ta ba, acikin ranta take faɗin "tayaya hakan zata faru? yaushe hakan ya faru dani? bazan taɓa yadda da wannan video cewa nine ba" tana cikin wannan tunanin taji ana knocking ƙofar ɗakinta, sai da ta ɗan juma kafin tazo zata buɗe domin kafin ta tashi ma aiki ne tsabar yanda jikinta ke mata ciwo ga wani irin zazzaɓin da take, kafin ta buɗe saida ta tambaya "waye ne?.." murya ciki-ciki domin daƙer yake fitowa...
"Angel ce ki buɗe.." daga waje ne aka bada amsa, Ayush buɗe mata ɗakin tayi sannan ta juya waran da gadonta yake ta zauna a bakin gadon, itama Angen shugowa tayi tareda rufe ɗakin tazo ta zauna kusa da Ayush tana kwallonta cikin tausayawa, gashi yanda goshinta ya fashe gurin yayi jawur, lips ɗinta ma ya ɗan kumbura kaɗan, idanuwanta duk sunyi jawur tsabar kukan da ta sha, ga ta kwana batayi bacci ba..
bayan Angel ta ƙareta da kallo ta sauƙe ajiyar zuciya tana faɗin "Ayush bai kamata kisa wani abu aranki ba, nasan kina cikin damuwa sosai amma ki rinƙa danne wa, zaman kaɗaicin nan da kikeyi a cikin ɗaki shi kaɗai ma zai jawo miki ciwo,
Hmmm! na fahimci har yanzu baki gama sanin ko waye Junaid ba, shi ba irin mazan nan da za'a rinƙa nuna musu damuwa bane domin shi bai damu da ganin mutum acikin damuwa ba, kina ganin mommy gata can a ɗaki tana fushi da shi amma tin jiya baije ya dubata ba, cizonsa da kikayi bayan ya gama mutsul-mutsul sa haka ya tashi ya shige room ɗinsa nin tin daga lokacin ban ƙara ganinsa ba, duk da nima fece wa nayi cikin ɗakina amma ina kallonsa ta window"
bayan ta kai ƙarshe shuru ta ɗanyi tana kallon gefe guda daga bisani ta ɗago tana kallon Ayush ta kuma cewa "Ayush amma taya aka samu video nan? shin da gaske ne ko kuma ƙage ne don a ɓata miki suna?..."
Ayush da sauri ta juyo tana kallon Angel har idonta ya cicciko tace "wallahi tallahi Aunty Angel bansan da wannan video ba, wallahi ni bansan mutumin bama.."
Angel tace "toh amma ai acikin room ɗinki aka aikata hakan.."
Ayush cikin yanayin kuka take magana "wallahi bansani ba, ni bana fita waje, kuma bani da waya a hannuna ban ma iya waya bama kwata-kwata balle na ƙira mutum cikin ɗaki na..."
Angel cike da mamaki tace "to amma taya hakan zai faru? bincike ya nuna alokacin da duk aka tafi asibiti ne hakan ya faru, amma kuma abun zai ban mamaki...."
Ayush kuka ne ya kuɓuce mata sosai take yin kukan,
Angel shuru tayi kamar mai tunanin wani abu a zabure tace "ina buƙatar ƙara ganin video nan domin tabbatar da wani abu, in har da gaske kece kika aikata hakan da saninki zan gani, in kuma duk shiri ne nan ma zan gani, bayan ni soja ce haka kuma ni ƴar C.I.D ce mai bincike nice mai warware ƙullin da aka daɗe da ƙullawa, ko a wajen aikin mu ne duk abunda ya gagara ni ake nema domin na warware komai saboda haka ki kwantar da hankalinki insha Allahu zan magance matsalar kinji ko.." ta ƙarasa maganar tareda bubbugar kafaɗar Ayush wacce taketa sheshsheƙar kuka,
Angel fice wa tayi daga ɗakin ta nufi ɗakin Junaid tsayawa tayi tana knocking a hankali, zuciyarta tana ɗarɗar gudun kar har yanzu bai saƙƙo ba, tana cikin wannan tunanin taji har an buɗe ƙofar,
Junaid ne ya tsaya yana kallonta fuskar nan a ɗaure ba annuri yace "ya akayi?.."
bin ta gefensa tayi ta shige ciki tana faɗin "toh ka shugo mana..."
ɗan tsuka yaja sannan ya rufe ɗakin shima ya shugo ya nemi guri ya zauna yana kallon gefe,
itama Angel ɗin zama tayi a gefensa tana faɗin "Ogah Junaid wai har yanzu baka huce bane?..." shuru yayi mata bai ce komai ba,
ta kuma cewa "nazo ne akan batun case na video nan da aka turo maka.."
tsuka yaja sannan ya juyo yana kallonta da lufu-lufun idanuwansa da suke buƙatar bacci yace "meyasa kike son shiga abunda bai shafeki ba ne, so what's your problem about this robish thing..."
jan dogon numfashi tayi sannan tace "i want to close the case..."
dogon tsuka yayi ya juyo yana kallonta yace "mind your own personal business please Angel, wannan case ɗin bai shafeki ba, meyasa kike son wahalar da kanki akan abunda gashi nan a aikace ya faru da gaske, toh ma mezaki bincika?...."
murmushi Angel tayi sannan tace "ina son ganin wayanka"
yace "me zakiyi da ita?.."
murmusawa tayi sannan tace "i want to show you something..."
"which something?.." in short answer ya bata yana kallonta,
tace "please Ogah Junaid i beg you.." ɗaukar wayan yayi ya miƙa mata, da sauri ta kai hannu ta karɓa, kai tsaye whatsApp ɗinsa ta hau ta shiga kan number da aka turo saƙon, ta ɗauki number a wayanta tayi dialing call ji tayi number a kashe...
murmushi Junaid yayi tareda kawar da kansa gefe yace "hauka suke zasu bar layinsu a on.."
itama Angel murmushi tayi sannan tace "abun na munafurci ne shiyasa an turo ne domin a warware soyayya..."
Junaid yace "an turo dai domin a temake ni kuma ko da ba'a turo bama na rigada na yanke hukuncin rabuwa da ita saboda babu macen da zata rinƙa juyani kamar ɗanta.."
Angel tace "bazaka gane bane Ogah Junaid, shin babu wanda kake zargi a wannan al'amarin?.."
"kinga Angel banida lokacin sauraron tambayoyinkin nan, kin saka ni agaba kamar wata ƴar jarida kina mun tambayoyi shin nufin ki na amsa miki ne? you are mad! stand and get out inside my room, i don't what this robish..."
ya miƙe tsaye ya kuma cewa "give my phone" yana kaiwa hannunsa zai karɓa,
Angel a zabure ta riƙe hannun Junaid tana faɗin "laaa ogah Junaid kalli wani abu acikin video nan.."
jawo hannunsa tayi ta zaunar dashi tana nuna masa video tareda faɗin "ka kalli video nan dakyau Ayush ba'a cikin hayyacinta take ba.."
yayi tsuka tareda kallon gefe yace "daman taya zata zauna cikin hayyacin ta bayan tana rungumai da gardi.."
tace "ba haka bane wanda yake musu video yana kusa dasu, kuma da duk kan alamun akwai munafurci aciki, Ayushart tana da matuƙar jin kunya, inda ace da sanin ta wallahi bazata bari a ɗauki video ba, amma zan cigaba da bincike na..."
suna cikin wannan halin sai suka jiyo bugun ƙofa,
Junaid