Showing 66001 words to 69000 words out of 186041 words
littafin, nasan baka san asalin mahaifinka ba to ka duba wannan littafin domin shine ɗan asalin mai asali, kakanka wanda ya haifi mahaifinka shine sarkin wannan masarautar shine wanda ya mulki mutanen wannan ƙasar, wancan mutumin wato sarki Raamud wanda kake ƙiyayya dashi shine ɗan uwan mahaifinka domin sun kasance ƴan biyun kakanka ne, yana da ƴa mace guda ɗaya wanda suka haifa shi da matarsa Sarauniya Bara'at wacce Allah ya karɓi rayuwarta a halin yanzu, Gimbiya Mayushaert wacce kake tareda ita a gida itace ɗiyarsu, wannan littafin ni na rubuta shi da hannuna daga farko har ƙarshen labarin zaka gani, da zarar ka kammala karanta tarihin labarin zan ɗauke littafi na domin ban gama rubutuna ba kuma bazan gama ba har ƙarshen rayuwarku, wannan littafin na biyu ne littafin na ɗaya yana gurinka cikin ɗakinka kaje ka duba zaka gani, ga kuma amanar Damusa ka riƙe shi a wajenka domin amanar kakanka ne, na Barka lafiya sarki na gobe...."
Narasimha yana kaiwa nan yayi ɓacewarsa ɓatt.
Har saida Junaid ya tsorita, gumi ne yake yanko masa zuciyarsa cike da tambayoyi da al'ajabi gaba ɗaya kansa ne ya kulle yana wani irin tunani tunani ya furta a hankali "kenam mahaifina ɗan masarautar wannan ƙasan ne? toh amma taya mutane zasu fahimci haka? kenam sarki Raamud ɗan uwan mahaifi nane shiyasa ya addabi rayuwata a baya kenam? to amma wacece ɗiyarsa Gimbiya Mayushart? shin aina take?...". zuciyarsa cike take da tambayoyi ga hannunsa riƙe da littafi, ɗago kansa yayi ya kalli damusar dake kallonsa shima sai kallon juna suke shi da damusa,.
Damusan ne ya tafo gaban Junaid ya tsaya shima Junaid sunkuyawa yayi ya ɗora hannunsa akan Damusan yana shafa shi, tsananin ƙaunar Damusan ne ya shiga zuciyar Junaid,
miƙewa Junaid yayi ya nufi cikin fadar masarautar, shi kuwa Damusan nufan gurin sarki Raamud yayi yaje ya kwanta a kusa dashi ya ɗora kansa akan ƙafarsa, duk abunda Narasimha ya sanarwa Junaid sarki Raamud yana ji saidai babu halin yin magana domin yana alhinin mutuwar sarauniyarsa...
Junaid yana shiga cikin fadar idonsa suka sauƙa akan babban photon dake manne a saman bango, zaro ido waje Junaid yayi da ƙarfi ya furta "Yushert..." yana girgiza kai yace "a'a ba ita bace amma kuma kamar dai ita ɗin ce, wallahi Yushert ce! itace wallahi Yushert ce!! daman tana da haɗi da masarautar nan? kenam itace Gimbiya Mayushart?...."
yana cikin wannan halin yaji ƙarar jirgaye, da gudu ya fice yayi waje yaga har sun buɗe get sun shugo, ganin sojojinsu ne suka zo yasa yayi ajiyar zuciya ya furta "Alhamdulillah"
Jirgaye ne sun kai ashirin suka zo kwasan matattun sojoji waɗanda aka rasa rayukansu, yana tsaye yana ganin an ɗauki Angel nan danan hawaye suka fara gangaro masa, haka yana kallon yanda aka ɗaga Bara'at yana tunanin "maiyasa ta zaɓi ta mutu akan ni na mutu? meyasa? Bayan nazo da niyar ɗaukan fansata akanta shine ita kuma ta bada rayuwarta akaina? kuma ga tsohon ciki a jikinta innalillahi wa inna ilaihi raju'un Allah ya gafarta miki na gode da sadaukarwarki agareni sarauniya..." Haka yake wannan maganar zuci har aka zo kan sarki Raamud yana ganin yanda aka ɗaɗɗaure shi da igiyar kaca saboda suna ganin shine mai laifin kuma shi aka kawowa farmaki, girgiza kai Junaid yayi yana kallonsa amma ya kasa ai watar da komai shidai acikin ransa yasan bazai taɓa bari a cutar dashi ba tinda yanzu ya shiryu kuma bayan haka mahaifi ne a waransa tinda ɗan uwan mahaifinsa ne,
Munafurr kuma a leda aka tuttusa ɗan banza suka yanke shawarin za'aje can bayan gari a ƙone shi..
Junaid yana tsaye yaji wani daga cikin sojojin yace "Captain Junaid sannu da ƙoƙari, naga kaji ciwo sosai muje cikin jirgi a duba maka raunin..."
Junaid ba tareda ya furta komai ba yayi gaba abunsa, yana dab da fita daga cikin masarautar yaji sojoji sun fitar da bindigunsu sun saita Damusa zasu harbeshi, a gigice Junaid ya ɗaga musu hannu yace "ku dakata Please...."
******
Ɓangaren su Ayushert
Ayush ce take ta zirga-zirga a cikin ɗakinta zuciyarta sai faman harbawa take ga hawaye shaɓe-shaɓe akan fuskarta,.
tana cikin wannan zirga-zirgar sai ga mommy ta turo ƙofar ɗakinta da sallama a bakinta tana sanye da hijab ganin Ayush a wannan halin yasa ta faɗin "lafiya kuwa Ayush meyasa kike ta faman zarya a ɗakin ko abincin rana baki ci ba gashi yanzu anata ƙiraye-ƙirayen sallar Isha'i,
Ayush tafo wa gurin mommy tayi tana kuka tace "mommy ki taɓa zuciyata kiji zata fashe, bugawa take da ƙarfi hankalina ya kasa kwanciya inaji a jikina wani ya mutu..."
Mommy tace "ki kwantar da hankalinki Ayush Insha Allahu babu wanda zai mutu duk zasu dawo lafiya ƙlau..."
Ayush tace "a'ah Mommy sanyi nake ji na rasa wani ɓangare na jikina, akwai abunda ya faru, ba haka kawai ba..."
Wayar Mommy ce ta fara ringing a hannunta, ɗaga ƙiran tayi gabanta na faman tsinkewa tana gudun abunda za'a sanar mata, "kar kuma a sanar mun mutuwar yaro nah.." hannunta na kakkarwa tayi picking call tareda karawa a kunne tace "hello officer Sadik..." sanar mata yayi akan taje ta kunna tv domin ganin labarai akan yaƙin da aka gudanar,
"Amma Sadik Junaid fah yana nan lafiya kuwa?..." ya bata amsar cewa yana nan cikin ƙoshin lafiya sai raunikan da baza'a rasa ba...
daga nan hankalin mommy ya kwanta ta katse ƙiran tareda jan hannun Ayush tace "zo muje muga labarai..."
Bayan sunje sun sauƙa falon zama sukayi mommy ta kunna tv abunda suka fara ganin ana magana akai shine akan sojojin da suka gudu za'a sallame su a aiki sai lokacin da aka nemesu, gasu yanda akaita nuno photunansu har da Adity.
Mommy dariya tayi tana faɗin "yanzu Adity duk faɗanki har ki gudo a gun yaƙi."
Ita kuwa Ayush ko motsawa batayi ba balle ta murmusa fuskar nan ba Annuri ita kaɗai tasan abunda take ji a zuciyarta,
A labarai aka nuno waɗanda suka mutu a cikin sojojin aka nuno photon Rumana wacce boom ya tashi da ita,
Mommy ta girgiza sosai dajin mutuwar Rumana har da hawayenta, daga baya aka nuno Angel har da photon gawarta,
Ba mommy ba hatta Ayush saida ta miƙe tsaye, mommy cikin firgici da tashi hankalinta a tashe tace "ehhhhh Angel ta mutu innalillahi wa inna ilaihi raju'un Angelll..."
Ayush kam fashewa tayi da kuka tana faɗin "Aunty Maryam innalillahi wa inna ilaihi raju'un Allah ya jiƙanki Aunty Maryam" cikin kuka Ayush take magana, can sukaji ance mutum ɗaya ne ya tsira a cikin sojojin!
Ƙirjin mommy ne ya buga da ƙarfin gaske domin tana tunanin Junaid ma ya mutu tinda ance mutum ɗaya ne ya tsira, itama Ayush dakatawa tayi da kukan tanason ganin wayene ya tsira kar taji cewa Junaid ɗinta shima ya mutu, gani sukayi an nuno photon Ogah Junaid, sannan anyi masa video gashi ga Damusa a gefensa,
Sunyi farin cikin ganin Junaid a raye, mommy tace "toh aina ya samu Damusa kuma?..."
Ayush gabanta ne yaketa faɗuwa kar ace an kashe mata iyayenta, amma ta gane Damusan mahaifinta,
Gani tayi an nuno videon mahaifinta an ɗaɗɗaureshi da kaca anata jansa, ana sanarwa cewa an kamo babban mai laifi wanda ya gagari mutane....
Ayush hawaye ne ya fara wanke mata fuska ganin mahaifinta a cikin wannan yanayin,
Mommy miƙewa tayi tsaye tana zaro ido waje gani tayi sarki Raamud kamarsu ɗaya da mijinta wato mahaifin Junaid, kamar wanda aka tsaga kara hatta tsayin sumar kayinsu, shima mahaifin Junaid lokacin da yazo Nigeria haka sumar gashinsa yake daga baya ya aske,
Mommy ƙafarta ne ya fara kakkarwa ga hajijiyan da yake shirin ɗaukarta a hankali ta zauna akan kujera tana dafe da goshinta, ga hawaye yanda yake ta gangaro mata....
Ayush gani tayi an nuna photon Umanta da tsohon ciki a jikinta wai an kasheta,
A zabure ta tashi tsaye tana zazzarowa ido ta furta da ƙarfi cewa "Umaaa, wayyo Allah nah Umaaa na ta mutu sun kasheta, Junaid ya cuceni ya kashe mun mamanaaa...."
Mommy ji tayi Ayush tana wasu maganganu marasa kan gado,
Lokaci guda kuwa Ayush tayi wani irin razanannen ƙara ta kama kayinta ta faɗi saman kujera sumammiya.....
*AMMM NACE BAA HOW MARKET👋👋👋👋👋👋👋*
*Toh nidai na feceee🏃🏻♀️🏃♀️🏃♀️🏃♀️🏃♀️🏃♀️🏃♀️*
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 35 ➡️ 36
Bayan kwana biyu da gama yaƙi Junaid yana zaune a bakin gadonsa na hotel ɗin sojoji dake ƙasar California, ga kuma Damusa a gefe guda yana kwance bayan ya kammala cinye kayan maƙulashe da aka kawo masa domin shi wannan Damusan baya cin ɗanyen nama,
Junaid yana riƙe da littafin da Narasimha ya bashi a halin yanzu bazai iya karantawa ba har saiya koma gida tukun, burinsa shine ya koma gida yaga Mommynsa...
Ga tunanin Ayush ya cike masa ƙwaƙwalwa gaba ɗaya ya kasa fahimtar ya lamarin yake, maganar zuci ya shiga yi yana faɗin "daman Yushert ɗiyar maƙiyina ne? daman mahaifinta ne ya turota akan tazo ta gane masa sirrikan mu? mahaifiyarta ta zauna damu ba da zuciya ɗaya ba sai don ta cutar damu gashi kuma tayi sanadiyar mutuwar mahaifina, sannan mahaifinta shine babban maƙiyi ne still aka sake turo Yushert domin ta kawo ƙarshen mu, good!..."
tunowa yayi lokacin da sarki Raamud ya turo kuliya ta kawo masa takarda a ƙarshen rubutun yace a kula masa da Ɓingel..
A hankali Junaid ya furta "Ɓingel" yana jinjina kai, tareda faɗin "Yushert akwai abunda kike ɓoye mana, kuma asirinki ya tonu tinda har na gane cewa ke wacece, tambayar dana daɗe ina miki kika kasa amsa mun saboda bakida gaskiya..."
ya ƙarasa maganar yana mai jin takaici a ransa, tunowa yayi da cewa su ɗin ƴan uwan juna ne, sannan ya tuno da mutuwar Uma Bara'at abun saiya ƙara ɗaure masa kai yace "what's going wrong, meyasa maƙiyiyata zata sadaukar da rayuwarta a kaina? shin meyasa maƙiyina zai tayani yin yaƙi? kenam maƙiyana sun koma masoyana?..."
ya ƙarasa maganar yana sharar hawayen da suka zubo masa, miƙewa yayi yaje ya lalumo wayarsa wanda tin zuwansu ya kashe wayar ya ajiye,
kunna wayar yayi ya duba cikin contact ɗinsa number mommy ya ƙira bugu ɗaya kuwa ta ɗauka a hanzarce dake lokacin tana kan sallaya ta idar da sallar lafula misalin ƙarfe 12 na dare tace "hello my son rabin raina ashe zamu sake ganawa da juna? nayi missed ɗinka my son yaushe zaka dawo?..."
ata ɓangaren Junaid kuma zama yayi a bakin gado yace "it's okay my mom insha Allahu a cikin satin nan zan dawo gida, domin sai an yanka mana Visa..."
Mommy tace "Allah ya dawo daku gida lafiya ashe Angel kam kwana ya ƙare ita da Rumana.."
Junaid yace "Please ki bari saina dawo saboda yanzu kaina ne yake ciwo, ina Yushert?..." ya tambaya murya à sanyaye...
Mommy tace "yanzu kam tana bacci a ɗakinta bata da lafiya, tinda muka kalli video waɗanda suka mutu aka nuno photon Bara'at daga nan aka nemi hankalinta aka rasa, bansani ba ko sun san juna ko kuma Bara'at ta cutar dasu bayan mu, kodai na kai mata wayar?..."
rufe idonsa yayi sosai tsabar baƙin ciki yace "ok ki barta tayi baccin ta idan na dawo zamu yi magana..."
Mommy ta amsa masa tana sharar hawaye da haka suka yanke wayar Junaid yayi wurgii da wayar yahau saman gado yana tunanin abubuwan da suke yawo masa a kayi...
Mommy itama tashi tayi daga kan sallaya ta rage kayan jikinta ta sanya marasa nauyi sannan ta hau saman gadonta tana mai jimamin rashin Angel, sannan Bara'at ta tsaya mata arai ganin tsohon ciki a jikinta amma da haka aka kasheta, tayi matuƙar tausaya mata, tana cikin wannan tunanin har bacci ɓarawo yayi awun gaba da ita...
ta ɓangaren Ayush itama a zaune take a tsakiyar gadonta ta naɗe sawayenta kamar mai cin tuwo, sai faman kuka take idon nan yayi jawur hatta fuskarta yayi jawur tsabar yawan kuka, Umanta ne take mata gizo! Babban tashin hankalin ma shine ganin Uma da tsohon ciki,
wani irin ƙololuwar baƙin ciki ne ya tsaya mata arai, wani irin haɗiyar yawu tayi tana kuka tareda faɗin "an cutar dani sosai, an rabani da farin ciki na, an rabani da rayuka biyu mafi soyuwa a gareni wato mahaifiyata da kuma abunda ke cikinta nasan babu mai wannan aikin sai Junaid, domin burinsa shine yaga bayan iyayena, sannan yana iƙirarin zai nemo ɗiyarsu itama yaga bayanta, nasan idan har yasan nice ɗiyarsu nima kasheni zaiyi domin bashida tausayi da imani ko kaɗan acikin zuciyarsa, zuciyarsa ta gama ƙaiƙàshewa babu sauran imani a tattare dashi tinda har zai rufe ido ya kashe mata da tsohon ciki innalillahi wa inna ilaihi raju'un Allah ya isa na tsakani na dakai Junaid, bazan taɓa yafe maka ba, na tsaneka wallahi, tinda har ya iya kashe mace da cikinta to nima kasheni ba wani abu mai wahala bane agurinsa, ga mahaifina wanda yanzu babu cutarwa a zuciyarshi shima nasan kashe shi za'ayi, tabbas idan Junaid baiga bayan mu ba toh mutuwa yayi don haka zamana a gidan nan ya ƙare, babu amfanin zama guri ɗaya da maƙiya, duk da shiɗin ɗan uwa nane kuma jinina toh amma a yanzu na haramta wa kaina yin tarayya dasu domin su ɗin cikakkun